Sashe 8
Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da Asuba da ta tashi wayarta ta fara dubawa, babu missed call sai text message guda ɗaya wanda aka tura ƙarfe shaɗaya da rabi na daren jiya.
*Bello zai zo ya ɗauke ki ƙarfe goma na safe*
"Shikenan kawai" ta furta ranta a ɓace.
Da safe ta shiga banÉ—aki tana wanka ta jiyo ihun Ali da Gwani. Da sauri ta watsa ruwa ta sanya hijabi a saman zanin wanka ta fito.
"Mi ya sameta?, mi kuka mata?" Asiya ta daka musu tsawa.
"Ta fito daga kitchen ne zata shiga É—aki kawai muka ga ta faÉ—i" Ali ya faÉ—a kaman zai yi kuka.
Abba ne ya nemo mai mota aka saka Umma suka wuce da ita Asibiti. Saura kaÉ—an Asiya ta fita da zanin wanka Abba ya ce ta koma ta shirya, kafin ta fito sun riga sun wuce dan haka ita da Sumayya suka tsaida Keke suka bi bayansu.
Sai da aka basu damar ganin Umma data shiga ɗaki sannan ta cire niƙab da ya zama mata dole yanzu, indai bata son idon mutane akanta.
Sai yanzu ta lura da wata rama da Umman tayi. A tunaninta laulayin cikin ne ya figar da ita haka.
Bayan Umma ta farfaÉ—o Asiya take tambayarta miyake damunta?. Umma ta kauda kai gefe.
"Dama kin daɗe ba lafiya Umma, amma shine kike ta ɓoyewa. Ranan da kika koma Asibiti mi Likita yace?"
"Asiya ki barta ta huta" Asiya ta kalli Abba sannan ta kalli Umma dake kwance. Maganarsa yai mata kamar akwai abinda suke ɓoyewa, da alama wannan jinyar ba baƙonsu bane.
"Abba mi yake damunta?"
"Zamuyi magana idan mun koma gida"...
Ƙarfe goma da 'yan mintuna Yaya Bello ya iso ɗakin da suke, yaje chan gida ance suna Asibiti. Ya gaida Umma sannan yacewa Asiya Gwamna ne ya turoshi ya zo ya ɗauketa.
"Yaya Bello ina zan je kana ganin Umma a kwance"
Umma dake kwance ta yafito ta tace ta tashi ta tafi tunda Sumayya na wajen.
"Sumayya zata tafi makaranta"
Ta É—au wayarta ta danna numbar Gwamna wanda ta rasa dalili amma da *His Excellency* ta saving numbarsa.
Bayan ta amsa sallamarsa tace "Umma tana Asibiti, kayi haƙuri ba zan iya zuwa ba"
"Allah ya bata lafiya, a isar min da gaisuwa"
Ganin idon kowa akanta yake yasa tace "za ta ji, mungode"
Zuwa dare aka sallamesu saboda Umma ta takura akan zata tafi wai ta samu lafiya.
Lokacin da suka koma gida Abba ya samu daman yiwa Asiya bayanin ciwon Umma. Haka Asiya ta tsaya galala tana kallon Abba cikin rashin fahimta.
Umma na da ovarian cancer sai kace shirin film. Tukunna ma yaushe suka sani amma suka sakata a duhu babu wanda ya gaya mata?.
Kusan watanni biyar kenan da suka san da zaman ciwon a jikinta, tana shan magani amma yanzu cikin daya shiga jikinta bazata shi yake galabaitar da ita.
Asiya haushin kanta ta fara ji sannan ta maida haushin kan ciwon Umma, kan Abba da Ubayd da suka ɓoye mata ciwon, kan jaririn da bai tashi zuwa ba sai yanzu, bayan kusan shekaru goma da suka wuce tana cikin ƙoshin lafiya.
Abba yace "Tana zuwa check-up amma yanzu suna maganar kaman ya shiga stage IV, amma basu tabbatar ba sai sun sake yi mata wasu gwaje gwaje"
Asiya ba ta ce masa komai ba ta miƙe ta wuce ɗaki, gefen Umma ta kwanta ta ƙanƙameta ta fashe da kuka...
Sai da Asiya ta ƙara kwana uku kafin ta koma gida, chan asalin gidan Gwamna. Bata so tafiya ba, Umman ce ta tursasata akan matuƙar bata tafi ba sai ta saɓa mata, akwai aure akanta ba zata zo ta tare mata a gida ba. Ganin ta samu ƙwarin jiki Asiya ta tafi da niyyar kullum za ta zo ta dubata kafin su sake komawa Asibiti.
Ranan data koma gidanta Gwamna bai leƙota ba, bata damuba saboda yanzu lafiyar Umma ne a gabanta.
Wasu mata da suka zo dubata ma ƙin fita tayi. An fara Kamfen suna neman matsuguni a jikinta, bata da ƙarfin yin hayaniya yanzu. Ta godewa Allah data samu ta yanke alaƙa da Umaru Kwom sannan aka wanke sunan Gwamna. Ita yanzu koda zai saketa bata da matsala saboda burinta yanzu shine ta kasance kusa da Umma.
Washegari Gwamna ya shigo da safe misalin ƙarfe takwas saura kwata. Asiya na ɗaki Sumayya ta shigo tace mata Gwamna ya zo yana jiranta a sama.
Rigar bacci ne a jikinta dan haka ta É—aura hijab ta fita.
Lokacin data gaisheshi, fiskarta da ke kumbure ya fara lura da shi, sannan idanunta da suka ƙanƙance.
"Ya jikin Umma?"
"Alhamdulillah" ta amsa tana jujjuya wayar hannunta.
"Ina so a fita da ita waje, akwai wanda zai zo gobe saboda passport É—inki ke da ita da kuma mutum biyu maza da za su iya binku"
Da ba Umma bace ƙila zaginsa za ta yi akan yadda suka maida fita Asibitin ƙasar waje kamar tafiya anguwa, ƙila tace masa bata son sadaka da kuɗin talakawa, ƙila kuma tace masa bata son burga da nuna isa. Amma lafiyar Ummanta ake magana ba za tayi wasa da wannan dama ba.
Asiya ta É—aga ido ta kalleshi, shima ita É—in yake kallo, ta rasa dalilin dayasa kaifin idanunsa ke tsoratar da ita, take kasa jure kallon cikin fararen idanunsa. Ta maida dubanta ga wayanta tace
"mun gode, Allah ya saka da alkhairi"
Shiru ne ya biyo bayan haka kusan minti uku kafin tace " ina so naje na shirya ƙarfe tara zamuje ganin Likita"
"Bismillah" ya faÉ—a yana mata nuni da hannu alamar zata iya tafiya.
Akwai maganar da ya ke so suyi, akwai tambayoyi daya ke son yi mata amma a yanayinta baya tunanin zata fahimci koma minene yake son faÉ—a dan haka zai bari zuwa lokacin da take cikin kwanciyar hankali.
A ranan da Gwamna yazo gidan Asiya, a ranan aka sace wasu ɗalibai 'yan Sakandare su goma shaɗaya daga wata makarantar gwamnati dake cikin jahar Congo. Irin haka ya faru farkon hawan marigayi Gwamna Saminu Bacchi inda aka sace wasu ɗalibai huɗu a hanyarsu ta zuwa Makaranta, an samu an karɓo yaran kuma daga nan ba a sake sace ɗalibai ba.
Maganar satan ɗalibai ya karaɗe jaha ya karaɗe ƙasa baki ɗaya. Ko'ina sai maganar satan ake. Kwana ɗaya kwana biyu shiru babu labarin za a sako ɗaliban sannan kidnappers ɗin basu fito sun bayyana mi suke buƙata ba.
***
Bilkisu Kachallah ta dawo daga taron mata da aka yi ta tsaya a tsakiyar falonta tana kallon TV saboda kanun labaran da ta ji ya ja hankalinta.
Umaru Kwom ne a wajen Kamfen ya jefi Gwamna da rashin bawa rayukan al'umma mahimmanci, taya za ayi a sace raya ƙanana 'yan ƙasa da shekaru shabiyar kusan kwana biyar amma babu abinda Gwamna ya iya yi akai?. Ba a ji daga jami'an tsaro ba balle 'Yan kidnappers da suka sace yaran, mi hakan ke nufi?
"He's behind this. Shine da wannan aikin, Umaru Kwom yanzu kuma dirty tricks ka fara? Mu zuba mu gani" ta snapping hannunta, daga haka ta É—au gyelenta ta wuce É—aki.
A ɓangaren Gwamna kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye saboda wannan lamari. Ya dakatar da fita Kamfen saboda ya bada hankalinsa ga case ɗin sace yaran nan. Daga wajen Alhaji Sani ya fara fuskantar matsin lamba saboda ajiye fita kamfen da yai a gefe, yayinda Umaru Kwom na chan yana fita Kamfen yana kururuta maganar satan ɗaliban da aka yi.
Ya yi meeting da Commisioner of police ya fi sau ba adadi amma duka shiru ne domin kwana bakwai kenan babu labarin yaran da aka sace.
***
A kwana na goma shaɗaya da ɓatan ɗalibai jikin Umma ya tashi, cikin dare aka wuce da ita Asibiti. Ba a sanar da Asiya bama sai washegari...
"Umma ya jikin?. Umma an kusa gama haÉ—a takardun, naki ne ma ya bada matsala, Insha Allah da zaran an gama harhaÉ—a takardunki zamu fita"
Tana yiwa Umma bayani ne da hannu, Umma da ke rigingine a kan gado ta kalli Asiya ta mata murmushi. Duk da bata da ƙarfin jiki haka ta fara mata bayani da yaren Kurame.
"Ki kwantar da hankalinki Asiya, sauƙi na Allah ne. Idan da yiwuwar na samu waraka to ko a nan ɗinma zan samu, dan haka babu inda zan je, idan Allah zai ɗau raina ina son kasancewa kusa da iyalina"
"Babu abinda zai sameki Umma, ba abinda zai sameki, zaki warke, cancer ba mutuwa ba ce, ki dena faÉ—in haka"
"Allah ya miki albarka Asiya. Ina alfahari da ke, ko ba na nan na san za ki zama uwa ta gari ga ƙannenki."
"Umma ya isa haka, dan Allah ya isa"
Asiya ta faÉ—a tana goge hawaye.
"Ki bari na yi magana Asiya Shahidan Gwani. Kinada kyakykyawan zuciya amma kina da taurin kai, kinada riƙo. Ki yi ƙoƙari ki yaƙi Shaiɗan akan wannan" ta ja dogon numfashi sannan tace " Na yiwa Ubaydullah mata"
Asiya ta zaro ido waje, baki na rawa tace "Um...ma"
"Ki haƙura da mijin da Allah ya baki, ki masa biyayya, ki riƙe aurenki da kyau. Nan da wata ɗaya Ubaydullah zai auri 'yaruwarsa Salma"
Ta san Salma. 'Yar Umma Hussaina ce matar da ta raini Ubayd, matar da saboda shaƙuwa bai taɓa kukan rashin uwa ba, saboda ita ne ko da yai wayo bai dawo wajen Abba da zama ba, sai dai ya dinga zuwa yana komawa.
Ba za ta manta Salma ba, ita ce ta rubuto mata wasiƙa kusan shekaru biyar da suka wuce take roƙonta wai Dan Allah ta bar mata Ya Ubayd. Ita ce lokacin da aka saka aurensu ta shiga damuwa tayi ta rashin lafiya kamar ba zata tashi ba.
"Ummaaa" ta kira da ƙarfi duk da ta san mahaifiyartan ba ji za tayi ba.