Sashe 10
Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gwamna ya fito da waya ya kira wata numba. Daga yadda yake faɗa ka san ransa ya ɓaci matuƙa.
Bayan tafiyar Yaya Bello, Gwamna ya kira Abba yai masa ta'aziyya tareda neman ƙarin bayani gameda waɗanda suka zo ɗaukan Asiya, tsabar ruɗewa ya ma manta cewa Gwani Mahaifiyarsa ya rasa amma haka aka bashi waya bisa umurnin Gwamna, Gwamna ya shiga jera masa tambayoyi kamar ɗan jarida.
"Ya abin ya faru? Wani irin kaya suka sa? Ya kamanninsu yake? Mi suka cewa Asiya da suka zo? Mi Asiya tace kafin ta tafi?"
Abu É—aya ne Gwani bai faÉ—a ba saboda lokacin hankalinsa baya wajen, wato batun text da Asiya ta gani daga numbar Gwamna.
"Darling calm down, kanata ihu tun É—azu, zaka sawa kanka ciwon kai fa"
"Someone kidnapped Asya kina cewa ina ihu, Bilkisu ina mulkin garin nan amma aka sace min mata, kin san mi za a faÉ—a gobe kuwa?"
"To naga dai Asiya ba ƙaramar yarinya bace. Besides, zai iya zama 'yan adawa ne..."
Wani irin kallo ya mata wanda yasa ta haÉ—iye sauran maganan da tayi niyya. Ta tsani irin wannan lokuta da kaifin idanun Saifuddeen ke tasiri akanta.
Ba abinda ta iya cewa har ya fice daga falon sai huci da take akai akai.
***
Asiya sai da tayi awa shida tana barci kafin ta farka. Lokacin data farka akan gado ta tsinci kanta, ta buÉ—e ido tana É—an daddanna goshinta saboda nauyi da takeji a kan. Kusan sakan goma kafin hankalinta ya dawo jikinta har ta hankalta da inda take da kuma abinda ya faru.
ÆŠakine madaidaici, yana da komai na amfani a ciki, akwai: TV, fridge, AC, fanka, da kujeru guda biyu, table da kuma gado.
Kai tsaye ƙofar ɗakin ta nufa ta shiga bugawa da ƙarfi, bayan ta murɗa hannun ƙofar ya ƙi buɗuwa. Ta dinga bugawa har sai da hannunta ya fara zafi. Ta je ta buɗe banɗakin dake cikin ɗakin amma shima babu hanyar fita aciki, dan ko window ɗin wajen ɗan ƙarami ne, kuma kaman ta baya aka kulle dan yaƙi buɗuwa ma.
Duk wani ƙoƙarinta na ganin ta fita daga ɗakin ya faskara. Ta tsugunna a tsakiyar ɗakin ta fashe da kuka tana kiran Umma Umma...
Tafi awa biyu tana kuka kafin ta ankara ko sallah bata yi ba. Ta duba agogon dake manne a bangon ɗakin, ƙarfe tara da rabi na dare. Ta shiga banɗaki ta ɗauro alwala abin mamaki data fito ne kuma ta lura da wata akwati da aka jingine a gefen gado. Tayi saurin buɗewa dan ganin mi ke ciki. Kaya ne a ciki duka jallabiya, hijabi guda biyu da kuma underwear na mata. Da alama wanda ya kawota ɗakin bai shirya saketa da wuri ba.
"Ya Allah albarkacin mahaifiyata ka fitar dani daga wannan wajen. Ya Allah mahaifiyata bata da lafiya tana buƙatata kusa da ita Ya Allah ka fitar dani daga wajen nan. Ya Allah na roƙe ka da girman zatinka da girman ƙudirarka, na roƙeƙa da ƙuwwa da ke jikin kalmar La'ilaha Illallah, na roƙeƙa da ƙarfin ayatul Kursiyyu, na roƙeƙa da girman Al'arshinka, Ya Allah na roƙeƙa da jinƙai da kake yiwa dukkan bayinka, ya Allah ka kuɓutar dani daga hannun koma wanene ya ke son cutar dani, Ya Allah Ya Hayyu Ya Ƙayyum ka kaini wajen mahaifiyata a daren nan, Ya Allah kai kaɗai kake baka da abokin tarayya. Mala'iku, Manzanni, Annabawa, Aljanu da sauran Mutane dukkanmu muna ƙarƙashin rahamarka ne Ya Allah, sai abinda ka ce Rabbul Izza, kaine Kun Fa Ya Kun Ya Allah. Kai ne Ar-Rahman, kaine Jalla Jalal. Ya Allah kowanne ganye yana faɗuwa ne da saninka, Ya Allah kowanni numfashi na halittun dake duniyar nan yana fita ne da iliminka, Ya Allah ka fitar dani daga wajen nan naje na ga Umma ta"
Addu'o'in da Asiya ta dinga yi kenan bayan tayi sallah har baccin da ba ta shiryawa ba ya É—auketa.
*"Asiya-Shahidah"* wata murya mai sanyi ya tashi Asiya daga baccin da take yi mai daÉ—i. Umma ta gani a gefenta tana mata murmushi.
Ta tashi zaune da sauri tana faÉ—in "Umma ke kika kira sunana? Kin fara magana ne?"
*"Asiya-Shahidah"* Umma ta sake faÉ—a da murya mai sanyi fiskarta É—auke da murmushi.
Asiya ta rungume Umma tana hamdala, tana faɗin ta ƙara kiran sunanta. For the first time a rayuwarta ta ji maganan mahaifiyarta.
"Kiyi ta kiran sunana kawai Umma, ba zan gaji da ji ba"
*"Allah ya miki albarka Asiya-Shahidah"*
Farkawa da tayi daga mafarkin da ta ke yi, yai dai dai lokacin da aka buÉ—e kofan É—akin.
Ta miƙe da sauri tana faɗin "mi kuke so a wajena? Wa ya sa ku kawo ni nan?"
Bindigar dake hannun mutane biyu da suka shigo ya hanata yunƙurin ficewa daga ɗakin da ta yi.
"Umurni aka bamu akan mu kawoki nan har zuwa lokacin da za a sakeki"
"Wa?, Gwamna?, Umaru Kwom?"
"Ba mu da ikon bayyana miki komai, amma an bamu saƙo ɗaya mu gaya miki"
"Kun san ko ni wacece kuwa? Kun san matsayina a jahar nan kuwa?"
Wata mata sanye da uniform ta shigo É—auke da tray É—in abinci, ta ajiye akan table sannan ta fita.
"Ance mu faɗa miki cewa ki kunna TV da ƙarfe tara na safiyar yau saboda za a nuna jana'izar mahaifiyarki live"
"Jana'iza?, Mahaifiyata?, mi ya sameta?, me kuka mata?"
"Ance mu faÉ—a miki cewa idan kika zauna babu taurin kai har zuwa lokacin da za a sakeki, babu abinda zai samu 'yan uwanki"
Bata ma gama jin mi mutanen ke faɗa ba ta zauna daɓas a ƙasa hawaye na zubo mata. Har suka fita ba tayi ƙwaƙwƙwaran motsi ba. Kasa yarda tayi da abinda suka faɗa.
"Umma is fine, ba abinda ya samu Umma, Umma tana Asibiti tana bacci, ba abinda ya sameta, babu abinda ya samu Ummata" ta dinga maimaitawa kamar mai taɓin hankali.
***
7
Misalin ƙarfe bakwai na safe Alhaji Umaru Kwom yana karyawa aka kira shi aka sanar da shi rasuwan sirikar Gwamna, da farko ma mahaifiyar Bilkisu Kachallah ya ɗauka sai da wanda ya kira ɗin ya jaddada masa cewa matar Malam Nuhu Principal ce.
Bayan ya ajiye wayar yai murmushi. Matarsa da ke gefe tace "Alhaji lafiya naga kana murmushi, ba maganar rasuwa aka maka ba?"
"Rasuwa ce da ta buÉ—e min wata dama"
"Wa ya rasu?"
"Mahaifiyar Asiya Kachallah" ya amsa mata har lokacin bai bar murmushi ba.
Hajiya Mariya ta yiwa Umma addu'ar samun rahama yayinda mijinta ya cigaba da cin abinci ba tareda ya amsa addu'ar da Amin ba.
***
Jiya yadda Gwamna ya ga rana haka yaga dare, bai rintsa ba ko kaÉ—an.
Lokacin daya je Kachallah House tambayar Alhaji Sani yai ko yana da hannu wajen sace Asiya amma yace masa bai da masaniya akan haka.
"Baba dan Allah kayi haƙuri idan ma ..."
"Saifu baka yarda dani bane? Kana ga zan maka ƙarya ne?"
"Ka yi haƙuri, ba haka nake nufi ba"
"Ba zan yi wasa da rayuwar iyalinka ba Saifu. Ina zargin Umaru Kwom da hannu akan wannan, amma zan sa a bincika mani komai"
To mi Umaru Kwom yake nufi da sace Asiya? Da wannan tambayar ya raya darensa, yayinda wani ɓangare na zuciyarsa ya ke zargin kansa da sakaci da yai da rayuwar Asiya. Idan da ya haɗata da masu tsaro ƙila haka ba zai faru ba.
Ahalin gidan Malam Nuhu GidaÉ—o Principal kuwa sun kwana sun tashi ne da juyayin mutuwar Umma da kuma rashin sanin inda Asiya take.
Tun dare aka yiwa Umma sutura ana jiran gari ya waye a kaita makwancinta.
Washegari da safe gidan ya cika sosai, 'yanuwa da abokan arziƙi da ke kusa duk sun zo.
Tun safe aka fitar da labari cewa Allah ya yiwa mahaifiyar Matar Gwamna rasuwa.
Abin mamaki tawagar Alhaji Umaru Kwom ce ta fara isowa kafin ta Gwamna ta iso, minti shaɗaya tsakani. Gwamna rufe idonsa yai da baƙin gilashi saboda kar a ga kumburarrun idanuwansa. Gwamna yana isowa ƙarfe tara da minti biyar aka yiwa Umma Sallah sannan aka wuce da ita maƙabarta. Gwamna Saifuddeen bai yi niyyar wucewa maƙabarta ba amma yana shiga mota Alhaji Sani ya kirashi yace ya wuce maƙabarta saboda Alhaji Umaru Kwom nan zai je.
Innalillahi akan aikin ladan ma sai an saka siyasa a ciki. Haka dai aka wuce da Gwamna maƙabarta.
Asiya bata kunna TV ba. Tsoro take ji, gani take idan ta kunna ne abinda aka faɗa zai tabbata, amma idan bata kunna ba Ummanta za ta kasance kwance a Asibiti ba abunda ya sameta. Sai kusan ƙarfe goma da rabi saura ta samu ƙarfin gwiwar kunna TV ɗin.
Kamar yarinya haka ta zauna a gaban TV ta naɗe kafafuwanta ta riƙe fiskanta da hannayenta biyu.
Hill TV ta kunna, ta san suna ƙoƙarin fitar da labarun gaskiya ba kamar Congo News ba.
Ƙarfe goma da rabi suka sako maimaicin labaren safe. Labarin farko a kanun labaren shine rasuwan mahaifiyar matar Gwamna wato Asiya Kachallah.
Haka Asiya ta baza ido tana kallon labaran. Aka nuna wajen da Alhaji Umaru Kwom yazo yana gaisawa da su Abba, aka nuna wajen da Gwamna shima ya iso, sannan aka ɗan nuna wajen da ake yiwa gawar Umma sallah, aka nuno wajen da ake saka gawar Umma a cikin ƙabari.
Daga ƙarshe aka nuna Gwamna yana yiwa iyalen Malam Nuhu Gidaɗo ta'aziyya sannan aka nuna Alhaji Umaru Kwom shima yana yiwa Gwamna da iyalinsa ta'aziyya.
Da gangan ɗan jarida ya tambayeshi ko miye dalilin daya sa ya halarci sallan sirikar Gwamna sannan har ya zo maƙabarta akayi biso da shi.
Umaru Kwom ya karkata kai yace *"watoo, ita siyasa ba gaba bace"* kafin ka ce me a duniyar yanar gizo mutane sun É—auki kalmomin Umaru Kwom suna masa kamfen da shi *#Siyasa ba gaba bace*
Ta ko'ina a faɗin jihar sai maganan ƙarfin hali, jajircewa da kuma imani irin na Umaru Kwom ake. Hatta wasu masu faɗa aji a ƙasar sai da suka yaba da Umaru Kwom.