Sashe 29
Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Walima ce aka shirya a Kachallah House saboda taya Saifuddeen murnan cin zaɓe. Ƙarfe huɗu na yamma za ayi walimar iya matan family.
Dake maganar walimar cikin kwana biyu aka tsarata shiyasa ba a gaya mata ba sai yau É—in.
Asiya ta amsa da zata je, ba dan tana son zuwan ba sai dan kawai bata son musawa Hajiya Umma dan tana ganin girmanta.
Ta fi minti goma tana kallon numbar Gwamna ta kasa kira. Yadda suka rabu jiya ke dawo mata, miye matsalarsa da zamanta a gidan Gwamnati, minene dalilinsa na fitar da ita a gidan cikin dare? Ganin Shaiɗan ya fara tunzura mata zuciya sai kawai ta dinga Istigafari a zuciyarta, ƙarshe ta tura masa text akan zata je Kachallah House. Bata samu reply ɗinsa ba sai kusan ƙarfe biyu na rana, har ta fitar da rai ma akan zai reply sai kuma ta ga sunansa lokacin da text ya shigo wayarta tana biga game.
*ban amince ba*
Ga saƙon gajeriya amma abinda ta haifar a zuciyar Asiya yayi girma matuƙa.
Saƙonsa ya ƙara tabbatar mata akwai wani abu a ƙasa. Ko lokacin da suke zaman shiru ma bai taɓa hanata fita ba balle yanzu kuma da ya kasance akwai fahimta mai ƙarfi tsakaninsu.
Duk yadda ta yi ƙoƙarin hana kanta shiga damuwa saboda saƙonsa sai da hakan ta faru. Ta kasa zaune ta kasa tsaye. Mi yake faruwa? shine abinda take tambayar kanta. Rashin samun amsar yasa tayi ƙarfin gwiwa ta danna masa kira.
Kira har sau biyu amma bai ɗauka ba. Ta riƙe wayar a hannu kamar abin sadaka, ta tisawa fiskar wayar ido. Tun tana jiran ganin haske har ta karaya da shigowar kiransa.
Ganin ƙarfe huɗu saura sai ta kira Hajiya Umma tace mata ba zata samu zuwa ba ƙaninta ba lafiya ta je gidansu.
Har dare bata sake jin É—uriyar Gwamna ba. She was totally confused. Kwana biyu suna tare lafiya-lafiya amma cikin yini É—aya komai ya chanja mata. Bata gane wannan chanji ba, bata kuma san mi ya kawo wannan chanjin ba.
Ta gama tunanin duniyan nan amma duk abinda ta kamo sai ta ga bai kai dalilin da zai sa Gwamna ya mata haka ba...
***
19
Asiya tana kishingiɗe akan kujera hannunta riƙe da littafin Jojo Moyes mai suna Me Before You, a zahiri karatu take amma ranta baya ga labarin, kewar mutumin da yanzu ganinsa a TV yafi ganinsa a zahiri take. Ba za ta iya tantance irin damuwa da take ciki akan shi ba. Yana cin abinci? Yana bacci? sau nawa yake murmushi a rana, har yanzu yana tusa da Asuba? Mi yake a kwanakin da ba na uwargidansa ba.
"Ranki shi daÉ—e, Ranki shi daÉ—e" Asiya tayi firgigit ta kalli Uwani da ke risine a gabanta.
"Uwani lafiya?" Asiya ta faɗa tana saukar da ƙafafuwanta ƙasa.
"Yanzu aka kira daga gate wai wata yarinya tana iƙirarin ita ƙanwarki ce"
"Ƙanwata?. Yaya Bello baya nan ne?"
"Ina ga, dan Badamasi yace yarinyar duk tsoratar da ita da akayi taƙi tafiya sai rantse rantse take wai ƙanwar Sumayya ce"
"Mi tace sunanta?"
"Jummala Ale FaruÆ™"
Asiya ta yi shiru tana tuno waye cikin ƙannenta ake kira da Jummala. Babu wacce ta faɗo mata a rai amma sai ta cewa Uwani a shigo da yarinyar.
Da Sumayya na nan ma da ita zata tura ta dubo waye tunda babu wacce bata sani ba cikin 'ya'yan Ale, to bata nan ta tafi makaranta.
Asiya ta jingine kai tana ƙoƙarin saita tunaninta wanda har yanzu tafiya yake ga mutumin da ƙarfi da yaji ya mata kane-kane a cikin zuciya.
Yarinyar da Uwani ta shigo da ita falon Asiya tun daga babban falo taketa ihu da shirirtar ƙauyenci irin ta 'yan ƙauye.
Tana sanye da riga da zani na Atampa da suka yanƙwane saboda rashin guga da kuma zaman cikin babban mota. Hijabinta yellow shar dashi har wani wawal wawal yake a ido. Ta rungume jan jakar Ghana-must-go wadda tsabar tsofewa ya fara zare zare, ba wasu kayan azo a gani bane hakan yasa ta cukwuikwuye jakar a ƙirjinta kaman za a ƙwace mata.
"Adda Shahidah" hakan data faɗa ya bayyana haƙwaranta da suka dafe da datti har da wani green green ta saman haƙoran wanda yai kama da daɗaɗɗen kuka ne daya samu gindin zama a wajen.
"Adda Shahidah Jummala ce, aaf! Jummai, Jumman Delu"
Kafin ta gama lissafinta Asiya ta riga taga kamannin 'yan gidansu a jikin yarinyar, datti ne ya maida ta haka amma idan ta sha wanka zata iya fin Asiya ma farar fata.
Akwai wata Delu mai Daddawa da Ale ya aura kusan shekaru shabiyar da suka wuce alokacin Asiya ba zata wuce shekara tara zuwa goma ba amma akwai abinda zata iya tunawa game da Delu. Ƙazantar matar ya kai na misƙala zarratin, ga sana'ar Daddawa da take babu tsafta. Sai ya zamana koyaushe gidan yana nan gum, idan baka ɗauke kai bama ba zaka iya cikakken minti shabiyar a gidan ba koda kuwa kana sashen Ale ne wanda yake ɗan nesa da nasu ɓangaren.
Kwashe kwashen Ale ba irin macen da ba su gani ba a gidan. Delu ga ƙazanta ga kuma masifa. Sau uku tana aure tana fitowa kuma dukkansu babu rabo ciki, sai dai shigarta gidan Ale da watanni uku rabo ya ratsa tsakaninsu. Ta zauna ta haifi Aisha wacce suke kira Jummai saboda sunan mahaifiyar Delu ce. Jummai na da watanni biyar auren Delu ya mutu, sai data tafi ne ma suka san cewa saki na uku kenan aka yi dan haka babu kome. Jummai bata tashi a gidan Ale ba amma takan zo lokaci zuwa lokaci musamman a lokutan Sallah ko kuma idan tayi faɗa da Delu.
Abinda Asiya zata iya tunawa akan Jummai shine kusan shekaru uku da suka wuce taje hutu gida ta samu yarinyar ta zo gida. Fulani na mata magana tana mata tsiwa hakan yasa Asiya ta zo ta ɗauketa da mari. Yarinya sai ta kwanta ƙasa tana shure shure wai Aljanunta sun tashi. Asiya ta sa aka ɗauko mata bulala ta shiga zane Jummai ta ko ina, da ta ji wuya ta miƙe garau wai sun tafi.
"Waya kawo ki?" Asiya ta faɗa bayan ta ƙarewa Jummai kallo.
"motar Ubale na biyo"
"Mi kika zo yi? Waya nuna miki nan? An san da zuwanki a gida?"
"Kwarankwatsi ko kin koreni ba zan tafi ba. Nima ina son zama 'yar birni irin Sumayye. Ha'an ai ba Sumayye bace kawai ƙanwar matar Gamna"
"Bakin ki ne Gamna ai. Ba zaki jawo min masifar Delu ba, gobe zaki koma gidanku"
"Delu ta rasu, a gidan Ale nake yanzu"
Jikin Asiya sai yai sanyi. Ba zata iya tuna yaushe rabon da ta saka Delu a idonta ba tun bayan barinta gidansu. Ance ta sake aure a wani ƙauye bayan ta rabu da Ale iyaka abinda Asiya ta sani kenan.
"Yaushe Delu ta rasu?"
"Cikin Azumin bara"
Asiya tayi mata ta'aziyya sannan tace Uwani ta kai Jummai É—akin Sumayya tayi wanka ta chanja kaya.
Bayan tafiyarsu Asiya ta kira Ale dan ta tambayeshi ko yasan da zuwan Jummai.
Dama ta addabi 'yan gidan da fitina shiyasa babu wanda ma ya lura ta gudu daga gida idan ba yanzu da Asiyar ke magana ba.
Ale dai ya nuna Asiya ta bar Jummai a wajenta tayi kwana biyu ko zata nitsu.
"Baba idan na karɓi Jummai gaba sauran 'yan uwanta ma zasu iya cewa zasu bar gida"
"Kiyi haƙuri ta zauna a wajenki kafin na sama mata miji"
Bata da ƙarfin yin ƙorafi dan haka ta ce masa zata faɗawa Gwamna, idan ya amince shikenan.
Bayan wayarta da Ale sai ta gwada kiran numbar Gwamna ko wannan karan zai ɗauka, amma kamar koyaushe har wayar ta gama ringing ba a ɗauka ba. Bata tsaya ɓatawa kanta lokaci ba sai kawai ta tura masa text akan ƙanwarta Jummai ta zo zata zauna da su. Ba a jima ba kuwa ya mata reply da cewa babu matsala.
Lokacin da Sumayya ta dawo ta ga Jummai a ɗakinta ihu ne kawai bata kurma ba musamman data ga kayanta ajikin Jumman sannan ga yagaggiyar Ghana-must-go akan gadonta. Jummai ta sake tunzurata da cewa "nima na zo cin arziƙi, ai dukkanmu ƙannen matar Gamna ne"
Asiya na kitchen tana haÉ—a abincin dare Sumayya ta shigo fiskarta a haÉ—e kamar zata yi kuka.
"Anty Asiya, wai Jummai ta zo zama damu kenan?"
Ko kallon inda ta tsaya Asiya bata yi ba tace "kema ba kina zama dani ba"
"Anty, Jummai fa na da Aljanu, Wallahi zuwan da nayi hutu kusan kullum sai ta tada iskoki"
"Idan sun tashi akwai ayoyin ruqya zan karanta mata su"
Sumayya ta ƙara taƙune fiskarta tana hura hanci.
"Ki duba cikin kayan da ta zo da shi idan babu na arziƙi ki bawa Uwani taje ta ƙona su. Ki bata kaya guda biyu, zuwa gobe ko jibi zan mata siyayya. Kin san daga inda ta fito dan haka ki koya mata brush da duk abinda ya dace"
"Ni kam..."
"Zaki wuce ki bani waje ko sai na make ki a wajen"
Sumayya ta fice tana ƙunƙuni.
Asiya ta yi tsaki. Halayen da Sumayya ta tsiro da su yana bata mamaki, tamkar shigarta Jami'a ya chanja mata tarbiyya.
Da yamma lis Queen Bee ta kawo wa Asiya ziyara. Kallo ɗaya ta mata ta shiga ƙorafin ko lafiya?. Asiya ta kauda tambayar da cewa yanayin sanyin garin ne ya sa mata zazzaɓi.
Bayan sun gama lissafin kuɗi da kuma wasu chanje-chanje da suke son yiwa shagon Queen Bee ta kawo shawaran chanja sunan shagon daga Halaal salon zuwa sunan Asiya Kachallah. Asiya ta ɓata rai tace " sunana Asiya Faruƙ ki daina jingina min Kachallah domin bada shi za a tasheni ba ranan gobe. I'll always be Asiya Faruƙ Baba, aurena bai chanja komai ba"
"Na sani Bestie, wai kinga dai tunda kika samu wannan matsayi shagonmu ya ƙara samun ɗaukaka. Kuma a matsayinmu na 'yan boko dan kin amsa sunan Kachallah ai ba komai bane"