Sashe 30
Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar dama jira take tayi wannan magana Asiya ta fusata "zai iya saki na any moment from now, idan hakan ta faru zaku maida sunan shagon Asiya Faruƙ ne? Bamu buɗe shagon saboda zan zama matar Gwamna ba. Da matsayina ko babu our business is doing fine, kuma da yardar Allah zamu cigaba da samun alkhairi a cikin sana'ar mu. Bama buƙatar chanja sunan shago, bama buƙatar sunan Kachallah kafin mu samu ɗaukaka. Allah ke ɗaukaka mutum ba..."
"Shahidah?" Queen Bee ta kira a ɗan tsorace saboda tsananin ɓacin ran data gani a tattare da Asiya ga kuma kukan da ya ci ƙarfinta har ta kasa ƙarisa kalamanta.
"Mi yake faruwa? Kina da matsala da Gwamna ne?" Tayi tambayar tana rungumo Asiya jikinta.
"Ya dena kula ni Bahijjah, ya dena shiga harkata, tunda yace na dawo wannan gidan sau É—aya na saka shi a ido, bai iya min magana sai dai yai text. Ban san matsayina a gidan nan ba, ban san mi yake nufi dani ba"
Queen Bee ta shiga bata haƙuri har ta samu ta nitsu ta dena kuka. Tana shirin bata shawara. Jummai ta fito da gudu tana ihu.
"Lafiya?" Asiya ta daka mata tsawa.
Jummai ta miƙa mata hannunta na hagu tana faɗin "Sumayya ta ƙona min hannu"
Asiya da Queen Bee suka zaro ido cike da mamaki dan ba ƙaramin ƙonewa yatsunta huɗu suka yi ba.
"Mi ta saka miki a hannu?"
"Wani abu ne kamar almakashi tace min wai yana miƙar da yatsun mutum shine tace na gwada na gani"
"Shahidah ina jin flat iron ne" Queen Bee ta faɗa tana ƙara duba hannun Jummai.
"Idan ban sa Yaya Bello ya min maganin Sumayya a gidan nan ba zata sa min hawan jini"
Queen Bee ne ta shiga ƙwalawa Sumayya kira yayinda Asiya ta wuce da Jummala ɗaki dan ta mata first aid.
A tsorace Sumayya ta fito dan bata É—auka wautan Jummai ya kai harta manna flat iron a hannunta ba bayan taga irin tiririn da yake fitarwa.
Lokacin da Sumayyar ke straightening gashinta da flat iron ɗinne Jummai ta shiga yi mata tambayar ƙauyenci, ƙarshe sai tace mata yana miƙar da hannu ma, wai ta gwada ta gani.
Kamar da wasa da Sumayyan ta ajiye flat iron tana amsa waya Jummai ta ɗauki flat iron ɗin ta sa yatsunta ciki ta matse kamar yadda taga Sumayya na yiwa gashinta, sai kuma zafin ƙuna yasa ta yarda abin tana ihun zafi. Duk da an cire flat iron ɗin a wuta amma dake be huce ba shiyasa ya ƙonata sosai.
Queen Bee ta shiga yiwa Sumayya faÉ—a kamar zata cinyeta duk dama bata san matsayin Jummai a wajen Asiya ba amma ta ga kammannin jini a tsakaninsu.
Lokacin da Asiya ta fito da Jummai Sumayya ta tsugunna ta bawa Asiya haƙuri bisa umurnin Queen Bee sannan ta cewa Jummai tayi haƙuri.
"Idan kin yi na gari dan kanki Sumayya. Ke da Jummai matsayi É—aya kuke a wajena, kuma yadda kike zaune dani babu takuri ba zan yarda ki takura mata ba. Ku wuce ku bani waje"
Bayan tafiyarsu Asiya ta riƙe kai tana faɗin wannan kaɗai ya isa ramar dani ba sai matsalar Excellency ba"
"Jummai ma 'yar Ale ce?"
"Ya zamu yi da Uban da Allah ya haɗamu da shi. Ba dan ta zo gidan bama na manta da ina da ƙanwa Jummai"
"DaÉ—in abin ma dai dukkanku kyaunsa kuke É—aukowa"
"Ni dai Umma na É—auko"
"Wallahi ana ganinki an ga Ale, ke da kin É—auko gaba É—aya kyaunsa ma da baturiya zaki zama sak"
Asiya tayi shiru saboda Ummanta data tuno. Rashin Uwa babu daÉ—i. Da Umma na nan da ko zuwa gida tayi ta kalleta za ta samu sassauci cikin lamurranta.
Maganar Gwamna da Queen Bee ta sako ne ya kauda hankalin Asiya daga tunanin Umma...
***
Mutane da dama su kan ɗauka cewa ƙarfin iko ko mulki kaman kuɗi yake. Idan kana da shi ƙaruwa zai yi ta yi domin kuwa zuciyarka ba zata taɓa nitsuwa da kaɗan ba kullum cikin nema zaka kasanca.
Bilkisu Kachallah ta fara ganin tasirin zobenta sai dai juya mutum uku kacal bai isheta ba, chan cikin zuciyarta tana neman iko akan duk wanda ta ga dama. Hakan ne ya sa ta matsawa Malamanta na ƙasar India dana ƙasar China akan a ƙara mata ƙarfin mulki, tana so duk wanda zai yi jayyaya da ita daya tunkareta to tsoro da firgici ya hana shi magana.
Shirye-shiryen bikin naɗin Gwamna Bilkisu ta saka gaba, bata da lokacin 'ya'yanta kona mijinta, so take ta haɗa inauguration party da babu wanda ya taɓa yi a ƙasar. Ba tada matsalar kuɗi dan haka komai da take shirin yi sai ya fito da sunanta a tarihin jahar dama ƙasar gaba ɗaya.
Abun daya sake ɗauke mata hankali shine batun wani kasuwanci da take son farawa. Dake yanzu babu wani sirri na Yallaɓai da bata sani ba shiyasa data fahimci yana cinikin makamai ana kaiwa ƙasashen maƙota da suke fama da yaƙe-yaƙe hakan yasa itama tayi shawaran zuba jari a ciki. Babu tunanin illar hakan a ranta sai dai kawai miliyoyin daloli da ta ke hangowa idan komai ya tafi dai dai.
Sannu a hankali wanda suke kusa da Gwamna suka fara fahimtar akwai lauje cikin naÉ—i domin, mafiya lokuta yana sako zancen zai yi shawara da mai É—akinsa wanda kuma sun fahimci Bilkisu Kachallah yake nufi.
20
Yau safiyar Litinin an tashi da ruwa tun Asuba, hakan yasa garin ya É—au sanyi. A irin wannan lokuta mutum kan so ya kasance cikin bargo dan yaji É—umi yai barci mai daÉ—i.
A ɓangaren Gwamna Saifuddeen Kachallah yana tsaye a bakin window na ɗakinsa, ta jikin gilashin windon yake ganin yadda ruwan sama ke cigaba da tsalawa kaman da bakin ƙwarya. Tun Asuba ake ruwan kuma har yanzu babu alamar zai tsaya nan kusa. Tsawa da walƙiya aka tsala wanda ya dawo da hankalin Gwamna daga nisan kiwo da yai. Zuciyarsa ta tafi ne ga kyakykyawar surar daya gani a jikin gilashin tana masa murmushi, cikin kwanakin nan yana kewarta irin kewa na fitar hankali amma ya rasa dalilin da yasa zuciyarsa ta kasa yunƙurin zuwa gareta. a ranakun da ya je chan gidansa baya nemanta, sau ɗaya da ta je gareshi kuma bai bata fiska ba, bai saurareta ba ƙarshe ma sai ya sakata hawaye domin tsawa ya daka mata akan ta fita daga ɗakinsa.
Taya mutum zai yi kewar abar sonsa sannan ya kasa isa gareta. Taya zuciya da gangan jiki zasu so kasancewa da masoyiya amma idan hakan ta faru sai zuciya ta shiga ƙunci?
Ya furzar da iska yana mai sake kallon gilashin dake gabanshi, sai dai wannan karan saukan ruwan sama yake gani ba wai fiskar Asiya ba.
Yau Asiya ta tashi ne da matsananciyar zazzaɓi. Tun ranan da Gwamna Saifuddeen ya daka mata tsawa ya koreta a ɗakinsa ta kamu da wannan zazzaɓi, maimakon yadda kwanaki suke tafiya jikinta yai sauƙi sai ma komai ya sake lalacewa, ga kuma matsalar Sumayya da Jummai kullum cikin faɗa suke, tayi alƙawarin ba zata raba musu ɗaki ba, idan ma zasu ci kansu ne to sai dai su ci.
Tunda tayi sallar Asuba ta duƙunƙunu cikin bargo tana rawan ɗari.
Kusan ƙarfe goma na safe Jummai ta shigo ɗakinta. Bata ji shigowarta ba har sai da ta hawo gadon ta fara taɓata.
"Adda Shahidah Gamna ya zo, Gamna ya zo"
"Miye haka zaki cika min kunne da ihu"
"Wallahi na ganshi, dogo ne kaman Dogo mai nama na ƙasan layinmu. Ya min wani turanci ban gane ba nace masa Yas Yas Jummala Ale Faruƙ"
"Bakinki ne Jummalan ai. Matsa ki bani waje"
Miƙewa tayi ta wuce banɗaki. Shawaran Queen Bee take son gwadawa.
Duk abinda yake faruwa harda laifinta a ciki. Data bashi haƙƙinsa ƙila wannan ba zai faru ba.
Wanke fiskarta tayi ta fito saboda ta san bai daÉ—ewa a gidan, kar ta tsaya wanka ya tafi.
Hangame baki tayi ganinsa tsaye a É—akinta. Shi É—in ne dai da take mararin gani iya tsawon lokacin nan.
Shima ƙura mata ido yai yana bin ilahirin jikinta da kallo. Rigar barcinta mai laushi ne daya tsaya mata dai dai gwiwa, rigar kalar ƙwai da aka kaɗa wannan yasa ya dace da fatar jikinta.
"Ex Excellency"
"Dadda bata da lafiya, kije ki gaisheta"
Ya faÉ—a a hankali.
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta matso inda yake ta kamo hannunsa tace " tana Asibiti ne?"
Haɗuwar hannunsu ya motsar da zukatansu duka. Bai iya taɓuka komai ba har ta saita fiskarsu sannan ta fara kissing ɗinsa a hankali, a nashi ɓangaren wani kewarta ne ya ziyarce shi hakan yasa ya jawota jikinsa sosai ya shiga shafa ko'ina na jikinta.
Bata san ya aka yi suka kai gadonta ba har ma ya shiga ƙoƙarin rabata da rigan jikinta sai kuma komai ya tsaya chak. Kaman wanda aka tsikara ya tashi a kanta ya fice daga ɗakin, tsabar sauri har sai daya buge kansa da gini dan ƙofar ɗakinma bibbiyu yake gani.
"Ya Salam! Minene a jikina ne?" Asiya ta faÉ—a tana shinshina jikinta.
Ƙarfe biyar na yamma ta kira Halima Kachallah ta tambayeta wani Asibiti aka kai Hajiya Dadda.
Zuwa ƙarfe shida ta isa ɗakin da aka kwantar da tsohuwar. Dake ɗakin a cike yake da 'yan dubiya bata wani jima ba ta tafi.
Washegari da safe sai ga kiran Abba wai ta yiwa Gwamna godiya ya biya masa Hajji na wannan shekaran. Kaman haÉ—in baki ko awa É—aya ba ayi ba Ale ya kirata wai yana hanya zai zo godiya Gwamna ya biya masa kujerar Makkah.
Da Ale kaɗai ya biyawa sai ta yi tunanin ko roƙonsa yai amma kuma wannan ya nuna ra'ayin kansa ne ya biya musu.
Abin ya ɗaure mata kai dan bata san ma'anar hakan ba. Yana gudunta amma kuma yana ƙoƙarin yiwa iyayenta irin wannan Alkhairi.
"Anty Asiya ki yiwa Jummai magana, sau biyu ina saka sabon MaClean a banÉ—aki tana shanyewa"
Asiya ta ce "To ki gaya mata abin wanke baki ne ba na sha ba"
Sumayya ta amsa "Wallahi na gaya mata amma ta ƙi denawa"
"Kira min ita"