← Book details Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 37

Sashe 28

Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idan da bai yi tunanin hakan ba to yanzu Bilkisu ta ankarar da shi. Mr Paul da ya ke son haɗa ma sa manaƙisa a wajen Yallaɓai dole ne ya nuna ma sa cewa kafin mutum ya ga biri to biri ya gan shi. To sai dai wani hanzari ba gudu ba, idan ba mutuwa ko kuma an tsige Saminu Bacchi ba, babu yadda za ayi Saifuddeen ya zama Gwamna.

"Ki je zan yi tunani akai"

Da wannan Bilkisu ta bar falon mahaifinta amma babu gamsuwa a tareda ita saboda bata ga alamar Baban nata is desperate kamar yadda take ciki ba.

A hanyar komawarta gida ne Chief of Staff Lamara Damana ya kirata.

Munafukai dama basa rasa gulma. Daga barinta gidan Gwamnati har an kai masa gulmar abinda Sha'awanatu Bacchi ta yi mata.

"Ina so mu haÉ—u mu tattauna wani batu, ni dake zamu benefitting da wannan shawara"

Lokacin da Bilkisu Kachallah ta haÉ—u da COS. Dama zani ne ta tadda muje, dan haka yana faÉ—a mata interest É—insa akan É—aura Saifuddeen kujerar Gwamna tace tana tareda shi É—ari bisa É—ari.

COS shi ya kawo mata Medical report ɗin Saminu Bacchi ita kuma tasa aka kawo mata wani ƙwaya mai ƙarfi. Mai hawan jini idan ya sha ƙwayar sama da 2gram a lokaci guda sai ta saka shi cikin temporary shock, idan ba ai taimakon gaggawa ba sai mutuwa saboda ƙwayar tana ƙara gudun bugawar zuciyar mutum ne.

COS ya san ciki da wajen gidan Gwamnati kuma ya san yadda Saminu Bacchi yai amanna da shan giya. Shi ya saka aka zuba masa ƙwayan a kwalbar giyansa saboda nan ne hanyar da Saminu Bacchi zai sha ƙwayar cikin sauri ba tareda kuma an zargi komai ba...

Saminu Bacchi ya mutu, Saifuddeen ya hau kujerar Gwamna, yanzu kuma zai fara sabon tenure na shi.

*"Baba zaka gani, Bilkisu Kachallah ce zata mulki jahar nan. Sai na nuna maka cewa muma mata munada damar yin duk abinda muka ga dama. All of you will answer to me, only me"*

Ta sake duban zoben dake yatsarta tayi murmushi.
Ba zata taɓa manta yadda Baba ya fifita Saifuddeen akansu ba, saboda kawai shi namiji ne su kuma mata. Lokacin da ta gayawa Alhaji Sani cewa political science zata karanta saboda tana son yin siyasa abinda yace bai bar ranta ba har yau *"ke macece Bilkisu, ki karanta economics ko wani course ɗin daban. Ko kin karanta political science ba za ki shiga siyasa ba, ki bar mu maza muyita fama da wannan. Ga yayanki Saifu, shi nake tunanin zai gaje ni. In fact sai ya zama Gwamnan jahar nan"*

"Ke macece" Bilkisu ta maimaita kalmomin data fi tsana a rayuwarta.

Daga yanzu sai da bazarta za su yi rawa.

"From now on, I make the rules"
Ta furta dai dai an buÉ—e musu gate É—in gidan Gwamnati...

18

"Excellency ina neman alfarma"

"Minene?"

"Ina so nayi amfani da email ɗinka wajen tura wani saƙo"

"Ok"

Gwamna ya miƙawa Asiya wayarsa yana faɗin "hope i'm safe dai ko?"

"Akwai abinda kake ɓoyewa ne?" Tayi maganar tana kama ƙugu

"Kin san 'yan jarida akwai su da juya magana"

Asiya ta haɗe rai ta tura baki tace " su kuma 'yan siyasan fa, Ka manta cewa duk bayan minti biyu suke juya tasu maganar" ta juya zata bar wajen, ya sa hannu a ƙugunta ya jawota jikinsa.

"Not so fast, ai bamu gama magana ba. Tawa 'yar jaridar ba irin sauran bane, gaskiya take nema ido rufe and sometimes she missed it"

"Eh É—in, ai idan idonka a buÉ—e yake tsole maka shi za ayi"

Yai dariya ya sake ƙanƙameta saboda ƙoƙarin ƙwace kanta da take.

"Ina tunanin maida CY É—aya daga cikin special adviser É—ina. Or what do you think?"

Juyowa tayi tana kallonsa, har lokacin hannunsa na ƙugunta.

"Kana ganin CY ya chanchanci matsayin?"

"Miyasa kika ce haka?"

"Bana so ka bawa wani matsayi saboda ni, that's very bad. Idan ka fara da haka ba inda zamu kai. Ko waye kake son bawa matsayi should earn it, ba wai dan yana haÉ—i da kai ko da matarka ba"

"Na ji Matata"

Yai maganar tareda tallafo fiskarta ya manna mata light kiss a baki. Asiya ta rufe ido tana jin kanta na yawo a iska.
Ganin ta rufe ido sai yai kissing saman idanunta, ya sake kissing hancinta wannan yasa Asiya ta shige jikinsa tana dariya dan ta san ina ne next bayan hanci.

Ya sa hannu ya rungumeta sosai yana faÉ—in " gashi har kin fassarani, ni dama daga nan zan tsaya"

Ta cigaba da dariya jikinsa tana jin daɗin yanayin da suke ciki. Yanzu ta dena tsoron taɓata da yake yi, in fact she longs for it, har idan bai taɓata ba ta kan ji haushi a ranta.

Bayan fitan Gwamna Asiya tayi amfani da wayarsa wajen tura wa KaSaSa saƙo ta email ɗinsa. Deep down tana fata mawaƙiyar ta amince da buƙatarta na rubutawa Gwamna Saifuddeen waƙa, tana son ta karanta waƙar ranan inauguration ɗin shi.
She loved poetry amma har yau bata iya rubutawa ba...

Da dare Gwamna ya duba wayarsa ya kalli saƙon da Asiya ta tura sai yai murmushi. Ta riga ta goge saƙon data tura da email ɗinsa dan haka a wayarsa da yake amfani da shi wajen hidimar rubutunsa ya ga saƙon da ta rubuta.

*Dear KaSaSa...Na jima ina bibiyar rubutunki bana gajiya da karanta waÆ™oÆ™inki. A matsayina na matar Gwamnar Jahar Congo ina neman alfarma, ki rubuta min waÆ™a na yabo da jinjina ga mijina Gwamna Saifuddeen. I want it to be a surprise, so ki tura min reply ta email É—ina mai suna [email protected]*

Ba kalmar data É—au hankalinsa sai kalmar MIJINA data rubuta. Kenan... sai kawai yai murmushi.

***

"Ina ga waÉ—annan su zasu kasance candidate namu. Ku duba ku gani"

Yallaɓai ya miƙawa Mr Paul wasu takardu. Mr Paul ya karɓa ya rarraba takardun dan kowa ya gani. Bayan sun gama gani suka yi na'am da list ɗin sai mutum biyu da Alhaji Sani Kachallah yai ƙorafi akansu amma ganin cewa shi kaɗai yai ƙorafin sai kawai aka buga stamp akan cewa list ɗin za a ba wa Gwamna Saifuddeen.

Da yammacin ranan kuwa Bilkisu ta samu Yallaɓai ta tambayeshi mutanen da aka saka a list. Yana miƙa mata list ɗin ta karɓa ta kekketa shi ko karantawa ba ta yi ba.

Yallaɓai ya zaro ido da mamaki amma ya kasa cewa komai.

"Zan duba mutanen da suka dace, ko suna cikin list ɗinku ko basa cikin su wanda na zaɓa za a saka"

Yallaɓai ya gyaɗa kai.

Tana isa gida ta samu Asiya na zanawa Nana lalle.

"Mommy ki ga hannuna yayi kyau"

"Wani irin ɓata guri ne wannan? Za a iya yin baƙi a kowanni lokaci amma kun zauna anan kuna ɓata waje"

Asiya ta kalli Bilkisu sai kuma ta sunkuyar da kanta ta cigaba da sakawa Nana lalle a ƙafa. Tun jiya da Nana ta ga lalle a hannunta ta dinga damunta akan tana so ta mata irinsa. Bata ga aibun zamansu a nan ba, ba falon da ake karɓan baƙi bane, zamansu a wajen ma saboda Queen Bee data zo ne Nana ta fito wai a mata lalle shine kawai suka fara a wajen.

Bilkisu ta tauna leɓenta na ƙasa tana ƙoƙarin shanye rashin mutuncin Asiya. The mighty Bilkisu Kachallah tana tsaye amma ta yi kaman bata ganta ba.
Wannan iyayi da Asiya ta ke ya isheta. Yau yau zata sa Saifuddeen ya mayar da ita gidansa, idan aka rantsar da shi kuma guguwar zaɓe ya lafa sai ta sa ayi waje da ita. Ta riga ta gama amfani, ba abinda zamanta zai ƙara musu yanzu.
Ta wuce fuuu ba tare da ta sake cewa komai ba.

Da dare da suka kwanta Bilkisu ta riƙo hannun Gwamna Saifuddeen, lokacin da hannunsu ya haɗu zoben hannunta yai wani ƙyalli na sakan da bai wuce ɗaya ba.

"Darling, ina so ka maida Asiya gidanka"

"Asiya?"

"Yes" ta faɗa tana shafa ƙirjinsa.

Yana son tambayar dalili amma kuma ya kasa.

Ganin yayi shiru sai ta cigaba

"Ina so ka hanata fita hidima kowanni iri. Kuma bana so ka bata haƙƙin matarka"

Ta yiwa Yallaɓai haka kuma ya ci shi, dan haka shirun Gwamna akan zancenta bai zo da mamaki ba. Dan ma ta ƙara tabbatarda ƙarfinta sai tace
"Ina so kace mata ta bar gidan nan a daren yau"

Gwamna Saifuddeen ya kalleta a firgice amma kuma hakan bai hanashi miƙewa ba, ko takalmi bai sa ba ya fice daga ɗakin ya nufi ɗakin Asiya.

"Excellency ka bari gobe sai na tattara na koma chan É—in tunda baka son zamana a nan" Asiya ta faÉ—a bayan Gwamna ya tasheta daga bacci ya mata maganar barin gida.

"Ba zaɓi nake baki ba, umurni ne"

"Allah ya baka haƙuri" Asiya ta faɗa a tunzure dan taga abin nasa ma rainin hankali ne. Taya zai zo ƙarfe goman dare yace ta tattara ta koma ɗaya gidan.

Babu wanda ta kira cikin masu aikin gidan, da kanta ta shiga haɗa kayanta. Tana yi zuciyarta na ƙuna, yadda take jefa kayan cikin akwati kaɗai zai tabbatar maka ɓacin ran da take ciki. A cikin zuciyarta tayi alƙawarin ba zata sake zama a wannan gidan ba, na ƙarshe kenan da zata zo, idan ya ga dama chan gidansa ma zai iya ɗauketa ya kaita duk inda ya ga dama.

Ƙarfe shabiyu da rabi saura na dare Asiya ta shiga ɓangarenta na gidan Saifuddeen. Wajen yayi shiru kuma da ɗan ƙura dan da alama an kwana biyu ba a gyara ba.
Haushi da ke cinta ya ɗauke duk wani bacci da take ji. Ta cire hijabi ta shiga gyara ɗakinta, data gama ta koma falo shima ta fara gyarawa. A ƙalla ta yi kusan awa uku kafin ta gama komai ta zo ta yi wanka sannan ta faɗa gado sai baccin gajiya. Bata tashi bama sai ƙarfe bakwai na safe. Ta miƙe da sauri tana hailala sannan ta shige banɗaki ta ɗauro Alwala, data idar da sallah sai ga kiran Hajiya Umma.
Chapter 28 · 0% Book details