Sashe 1
Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*THE GOVERNOR'S WIFE*
......MATAR GWAMNA........
(Book Two)
HAKKIN MALLAKA
©Azizat Hamza
Wannan labari da duk abinda ya ƙunsa mallakar AZIZAT HAMZA ne. Banyarda wani ko wata su juya min ko da shafi ɗaya na labarin ba tareda izini na ba. Ban yarda a yaɗa min shi ta kafafen sada zumunta ba (ko karanta shi a youtube channel ko haɗa audio book ko document na shi) ba tareda izini na ba.
Littafin ba na kyauta ba ne. Za'a iya tuntuɓar numbana dan ƙarin bayani 08137311900 ko email ɗina azizathamza [email protected] ko wattpad account ɗina @ Azi_zat.
Bismillahir Rahmanir Rahim.
01
*Bama yi...Bama yi....Bama yi. A tsige Saifuddeen Kachallah, a tsige Gwamna Kachallah*
" 'Yan Daba kenan da suka wargaza taron buÉ—e Congo Stadium da aka yi a safiyar yau. Kamar yadda kuka gani jifa kawai suke ta ko'ina amma mun samu labarin cewa Gwamna ya samu ya bar wajen lafiya..."
Bilkisu Kachallah ta yi saurin kashe TV zuciyarta na tiriri. A karo na ba adadi ta sake kiran numbar wayar Gwamna amma taji ta a kashe.
Hawaye ne ya shiga sauko mata, bata cika yin kuka ba. Ba za ma ta iya tuna rabon da tayi kuka ba.
"Ba wanda ya isa ya tsige ka a kujerar nan, babu wanda ya isa ya tsigeka. Ƙarya su ke, ba macen da ka taɓa ciwa zarafi, i can bet my life for that. Saifuddeen ka buɗe wayarka please?"
Za ta yi faɗa da shi, ta yi fushi da shi, amma soyayya ɗaya ce kuma ta bawa Saifuddeen tun ba ta da wayo. Ba zata taɓa bari a ci zarafinsa ba matuƙar tana numfashi.
Goge hawayenta tayi ta kira wani number.
"A nemo min wacece Lami Ninja"
Tana faɗin haka ta miƙe ta shige ɗaki, Kachallah House za ta je ƙila chan zai wuce, hankalinta ba zai taɓa kwanciya ba sai ta gan shi...
Tun tuni take tsumayin kiran Gwamna, ya kamata ace ya ga saƙonta. So take ya kira ya mata faɗa, ya kirata munafuka, macuciya, azzaluma kamar yadda ta dinga kiransa a baya. Miyasa bai nemi kariya ba?, miyasa ya tsaya har suka zo?
Tana jin ringing wayarta ta É—auka ba tare ta ga sunan mai kiranba.
"Hello Excellency"
"Ina fata hankalinki ya kwanta da abinda kika sa aka masa. Ki ji tsoron Allah Asiya, ki ji tsoron Allah"
Kiit aka kashe wayar.
Ta cire wayar daga kunnenta a hankali ta ce
"Ya Ubayd kayi haƙuri, na yadda na tafka kuskure. Amma koda Gwamna zai sake ni ba zan tafi ba sai na wanke sunansa. I promise"
Tukunna wacece Lami Ninja?
Kiran numbar Fou'ad Salisu tayi bugu biyu kafin aka É—aga.
"Fou'ad wacece Lami Ninja?"
"Nima ɗazu da na ga labarin na fara bincike. So far dai abunda na gano shine, cikakken sunanta Lami Haladu. Ta yi Jami'ar Congo lokacin da Gwamna yake koyarwa a chan. Na sa a duba min ina take yanzu da kuma dalilin wannan ƙaran data shigar amma ban samu feedback ba. I'll keep you posted idan na samu labari"
"Nagode"
Lokacin da ta fito daga banÉ—aki Sumayya na zaune tana jiranta.
"Gwamna ya dawo?"
"A'a, yanzu first lady ta fita inaga wajensa za ta je"
"Ƙila Kachallah house zai je" Asiya ta furta tareda zama a bakin gado ta kifa fiskarta kan cinyoyinta.
"Anty ke kika sa aka jefi Gwamna ko?"
"Kar ki dameni Sumy, ki barni na ji da abinda ke raina"
Sumayya ta ja baya saboda yadda Asiyar ta hayayyaƙo kamar zata maketa.
***
Gwamna gidansa ya wuce bayan ya kashe duka wayoyinsa, ya kuma bada umurnin duk wanda ya zo kar a bashi damar ƙarisowa wajensa. Yana shiga ɗakinsa ya kwanta kan gado ko takalmi bai cire ba.
Bai taɓa tunanin tsanar da ta masa har ya kai haka ba. Ba damuwarsa tsige shi da za ayi ba, ko kuma jifansa da 'yan daba suka yi. Damuwarsa yadda ta saka 'yarsa cikin wannan lamari, she's willing to destroy his daughter's life saboda cimma burinta.
*Dan Allah ka yafemin, ka bar wajen taron nan yanzu please, akwai 'yan daba da za su jefeka idan aka tashi*
Yana karanta saƙon komai ya dawo masa. Ba yadda za ayi ta san za a jefe shi sai idan tanada hannu a ciki. Dan ya tabbatar da zarginsa sai ya ɗan rankwafar da kansa gefen COS ya raɗa masa magana a kunne
"Asya ce 'yar jaridar da ke wa Climax rubutu ko?"
"Excellencyyy" COS ya faÉ—a a hankali, hakan ya tabbatar da zarginsa.
Abinda ya ɗaure masa kai shine yadda tayi rubutu tana kiransa *Rapist* idan shi ɗin mai fyaɗe ne zai ƙyaleta wata biyu da kwanaki da suka yi tare bai nemeta ta ƙarfi ba.
Tunani ya shiga yi wacece ma Lami Ninja da ake faÉ—a.
Ya kai kusan minti biyar kafin ya iya tuno abinda ya faru shekaru shabiyar da suka wuce.
Lokacin da ya ke koyarwa a jami'ar Congo, 'yanmata da dama sun yi ta damunsa, wasu da maganar soyayya wasu kuma da tayin iskanci. Office ɗinsa kullum ba a rasa wasiƙar mace tana masa tayin soyayya. Saboda yadda mata ke masa idan sun zo office ɗinsa shiyasa ma ya hana mata zuwa office ɗinsa, duk wani abun da zai haɗashi da mace ɗaliba to a cikin aji ne ko a wajen aji amma banda office. Shi har staff mata bai tsira daga harinsu ba. Yana ɗaya daga cikin dalilin dayasa yake son Misturah saboda har ta gama ba ruwanta da shigewa Malamai, shima bata sake da shi sosai ba sai da ta gama makaranta.
Akwai wata ɗaliba a aji huɗu da take yawan masa kallon karuwai duk lokacin da ya ke koyarwa, da sun haɗa ido da shi sai ta fara cize leɓe tana kashe masa ido. Idan kuwa tambaya za ta yi a aji to sai dai ta tashi tsaye tana magana tana shafa ƙirjinta. Ta taɓa zuwa office ɗinsa ya koreta. Dake 'yar duniya ce ko ya akayi ta sa masu shara suka buɗe mata office ɗinsa oho. Ya dai shigo office watarana ya zauna kenan ta fito daga bayan labule tsirara. Da farko tsorata yai dan ya ɗauka Aljanace ko mahaukaciya.
"Ko sau ɗaya ne Dr Saifuddeen ka taɓani, kar kayi komai ma ni kawai ka sa hannunka ka shafa jikina zan haƙura da haka"
Banda matarsa Bilkisu a lokacin zai iya rantsewa bai taɓa ganin mace tsirara a gabansa ba sai ranan.
"Ki sa kayanki ki fita min daga office" ya daka mata tsawa idonsa a rufe.
"Ko kayi abinda nace ko na maka sharri. Ihu zan saka sai an shigo an same mu a haka kuma nace ta ƙarfi ka dannneni"
Ƙoƙarin fita daga office ɗin yai ta tareshi. Ya sha ji ana cewa akwai ƙaƙƙarfan mata, amma bai gamsu ba sai ranan. Kokawa suka fara da ita, shi yana son ya kai ƙofa ita kuma tana son danneshi ta ƙarfi...
***
"Baba mi yake faruwa? Ina Saifuddeen? Ya ban ganshi a nan ba" Bilkisu ta faɗa tana sheshsheƙar kuka.
"Kwantar da hankalinki, yana lafiya"
"Ina yake?"
"Zauna tukunna"
Bilkisu ta zauna gefen mahaifinta.
"Yana buƙatar hutu, ki bashi kamar awa biyu kafin ki je ki sameshi a chan gidansa"
"A'a Baba, ni yake buƙata. Kai baka San halinsa bane, ba zai taɓa magana ba, komai yake damunsa ba zai yi magana ba. Dole na je wajensa, ba zan iya rayuwa ba idan wani abu ya sameshi"
"Shi ya buƙaci hakan, ya yi min text akan yana buƙatar kaɗaici. Ki barshi ya huta"
Ta goge fiskarta tace "Baba wace karuwar ce Lami Ninja?"
"Lokacin da kika je haihuwa a America akwai wata É—aliba da ta yiwa Saifu sharri. Ta shiga office É—insa ta far masa, it was a scandal saboda yarinyar Karuwar Malamai ce, amma an rufe maganar tun lokacin"
"Miyasa ba a gayamin ba, Wallahi dana san da wannan da tuni na sa an ƙona shegiya. Waya gaya mata mijina yana shiga trash can"
"Ba wannan ne matsalarmu ba, Umaru Kwom yana so yai amfani da ita wajen ganin an tsige Saifu. Dole ne mu bi komai a hankali"
"Baba, Saifuddeen bai mata komai ba. Ƙarya take, i know my husband"
"Na sani, amma lokacin da abin ya faru an gansu tare a office É—insa. Its something..."
"Baba, ba abinda ya shiga tsakaninsu" Bilkisu tayi maganar da yarda na ban mamaki. Ko shi Alhaji Sani a da yana kokonto ko abin ya faru ko kuma bai faru ba, amma yadda 'yarsa tayi maganar da absolute certainty cewa babu abinda ya faru, sai ya ji ya gastata. Ita take zaune da Saifuddeen shekaru shabakwai, ita ta san mi zai iya yi, mi ba zai iya ba akan mace.
"Ita kuma karuwar bayan komai ya lafa sai na sa an ƙona mata fiska"
Alhaji Sani ya sake baki yana kallon 'yarsa, yadda Bilkisu ta yi maganar nan mai ƙwatan Lami Ninja a hannunta sai Allah.
***
Lami Ninja a gidan Umaru Kwom aka mata mafaka tun lokacin data shigo jahar.
Umaru Kwom tun kafin Fou'ad Salisu ya gano cewa account ɗin Sa'ad Kachallah na Alhaji Sani ne shi ya riga ya sani saboda shi ba yaro bane, mutane irin Saifuddeen Kachallah ba za su iya cin dukiyar talakawa ba. Tarihin Saifuddeen ya shiga dubawa tun sanda aka haifeshi har zuwa yanzu da yake kan kujerar Gwamna. Bai samu komai ba hakan yasa ya tafi jami'ar Congo neman ƙwaƙwaf. A nan ya samu wanda ya gaya mishi shekaru da daɗewa akwai wani abunda ya faru da wata ɗaliba, amma an rufe case ɗin an wanke sunan Saifuddeen saboda matsayin Alhaji Sani.
Yai bincike har ya gano inda Lami Ninja take, ta buɗe ƙaton club a Lagos tana kuma sana'ar fitar da 'yanmata waje karuwanci.
Tun kafin ta faɗa masa cewa ita ta nemi Saifuddeen ya riga ya sani amma yace ta fito tace Saifuddeen ya ci zarafinta, sannan saboda haka ne ma ya bata carryover a course ɗinsa. Ba dan kuɗin da yace zai bata ta amince da hakan ba sai dan yayi alƙawarin idan har bata yi yadda yace ba zai sa a ɗaureta, yanada shaidu akan mummunan harka da take yi.
"Mi zai faru idan aka gano cewa ƙarya nake?"
"Ke macece, babu wanda zai ƙaryata ki"