← Book details Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 37

Sashe 24

Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A dai dai lokacin kuma Bilkisu Kachallah ta shigo office ɗin kamar walƙiya. Kamfen ɗin Asiya ya girgizata matuƙa, sai da take tahowa ne a cikin mota sun zo dai dai wani round about ta lura da ƙaton bill board da ke ɗauke da hoton Asiya inda aka rubuta suna *first lady Asiya F B Kachallah*
Tun da aka fara Kamfen bata taɓa ganin an saka poster na Asiya ba. Duk wani souvenirs da aka raba tun daga riguna, zannuwa, littattafai, memos, key holders, calenders, jakukkuna da sauransu. Hoton Saifuddeen ne ko na Bilkisu ko kuma nasu su biyu.

Kafin a ƙaraso da ita sai da ta ga posters na Asiya guda shiga kuma kowanne an saka first lady kafin sunan.

"I am the first lady. The only first lady" ta furta a fili.

Irin kallon da Bilkisu take binsa da shi tun kafin ta ƙariso ya san ba lafiya ba. Miƙewa yai daga kan kujerarsa ya nufota.

"Don't touch me"

Tsabar sauri a office ɗinta ta bar gyalenta, ɗaurin ɗankwalin ma dai ya karkace kusan reto ma yake, ikon Allah ne yasa bai kai ƙasa ba har ta iso da shi a haka.

"Let's sit please" ya faɗa yana nuna mata kujerun da ya ke zama ya karɓi baƙi.

"Ban zo dan na zauna ba. Why did you allow her to campaign?. Miyasa baka gaya min ba?"

"Ki zauna tukunna" yai maganar yana kamo hannunta. Bilkisu ta wafce hannun tace "ka amsa min tambayata"

" Just like you, Asya is my wife. Ban ce ki min Campaign ba, kin yi ne a karan kan ki, itama kuma ban sata ba, ita da kanta ta zaɓi yi. Don't give me that face Bilkisu, kin sani sarai bana sa ido a harkan mutane"

"I accepted your marriage to her only...only" sai ta yi shiru tana huci. Dole ne ta ƙara haƙuri na ɗan lokaci kaɗan. Abinda ya ke mai mahimmanci shine
Saifuddeen ya ci zaɓe, it doesn't matter who campaigned.

Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta kalleshi ido cikin ido tace "idan ka ci amanata ba zan yafe ba"

Daga haka ta juya ta fice daga office É—in fuuu kamar yadda ta taho.

Gwamna Saifuddeen ya rakata da ido har sai da ta fice. Bai gane matsalar Bilkisu da Kamfen É—in Asiya ba. Sai kuma ya tuna da abinda ake kira kishi...

***

"Nagode Anty Halima. Allah ya saka da Alkhairi" Asiya ta faÉ—a tana murmushi.

"Amin ba komai, yiwa kai ne. Bari mu wuce"

Asiya har bakin mota ta raka Halima Kachallah kafin ta koma cikin gida.

Tana fitowa daga wanka aka gaya mata akwai wasu mata dake son ganinta. A gurguje ta shirya ta fita. Wasu matan manya ne guda uku wanda suka halarci Kamfen É—inta.
Biyu daga ciki a da suna tare da Bilkisu Kachallah ne amma sun raba gari tun kafin Saifuddeen ya hau kujerar Gwamna.

Yabo da jinjina ne ya kawosu tareda neman matsugunni a wajen Asiya.
Suna zaune da Asiya, Bilkisu Kachallah ta dawo. Sai da ta bi su da kallo É—aya bayan É—aya kafin ta bar wajen bayan ta ja dogon tsaki.

Washegari gidan talabijin na Hill TV suka nemi hira da Asiya. MD da kansa ya bugo yana neman wannan alfarma hakan yasa Asiya ta amsa gayyatarsu.
Da yamma ta je studio ɗinsu. Kowa jikinsa rawa yake ana ƙoƙarin burge matar Gwamna, musamman wanda a da basa shiri da Asiyar. Yadda sukeyi sai ya bawa Asiya dariya, watanni kaɗan baya ita ɗin ƙaramar ma'aikaciya ce a tashar amma auren Gwamna ya bata wani matsayi mai daraja cikin al'umma, Allah ya ɗaga ta, ta yiwa tsohin ma'aikatan fintinkau.

Daren ranan, interview É—in da aka yi da Asiya ya zamo abin kallo ga miliyoyin jama'a, a ciki da wajen jaha.
Yayinda hankalin mutane ya karkata ga yadda ta iya sarrafa harshe, ta iya haɗa kalmomi su bada ma'ana sannan ka ji maganar na taɓa maka zuciya. A wani ɓangare kuma wasu suna yabon kyaun surar ta ne da kuma iya wankanta.

Kan kace kwabo, posters na Asiya sun zagaye gari har ma yafi na Bilkisu Kachallah zagawa.
Cikin abinda bai fi sati ɗaya ba sunan Asiya ya koma *Hasken Talakawa* is like mutane na ƙara son SSK ne saboda Asiya Kachallah. Duk inda ta je tana nuna cewa Talaka yana da mahimmanci kuma sai ya bada haɗin kai za a samu cigaba mai amfani.
Yadda mutane ke ƙaunarta lokacin da take aikin jarida yanzu abin ya ninka haka. An manta da duk wani ƙarairayi da aka yi tayi a baya kafin aurenta da Gwamna. Abinda ake gani shine in har mace kamar Asiya na tareda Gwamna Saifuddeen to za a samu cigaba sosai a jahar.
Asiya tana bayyana matsalolin da ake fuskanta a jahar da kuma yadda Gwamnatin Saifuddeen ta shirya magancesu bisa tsari, hakan ya sawa talakawa hope.

Gwamna yayi mamakin yadda Asiya ta ke iya composing kanta ta bada speech mai ma'ana da kuma É—aukan hankali. Bai sani ba ko dan ya mata gorin cewa ba a haifeta a gidan da ake siyasa bane, amma cikin kwanakin nan ta nuna masa cewa ta fi ma wacce ta taso tsundum a gidan siyasa iya siyasar.

Ranan Kamfen ɗinta na ƙarshe a wata ƙaramar hukuma tayi. Mutane kaman ruwa haka aka cika stadium na wajen don ganin Asiya Kachallah, wannan ya ƙona ran Bilkisu Kachallah matuƙa saboda clearly mutane sun fara nuna musu banbanci, mutane sun fi ƙaunar Asiya a kanta.
Na lokaci kaÉ—an ne, sunan Asiya zai shafe a bakunan mutane, da sannu sunan Bilkisu Kachallah sai ya zamo national anthem na jahar.
Ranan da Bilkisu Kachallah ta rufe nata kamfen ɗin, kwana huɗu bayan na Asiya bata samu rabin mutanen da suka zo wajen na Asiya ba duk da kuwa ita ɗin tayi a cikin Congo ne yayinda Asiya tayi nata a ƙaramar hukuma.
Duk yadda taso ɓoye ɓacin ranta hakan ya faskara dan kuwa fiskarta babu walwala kwata kwata har aka gama taro. Ihu da ta dinga yi ma ba kamar na kullum ba domin gwiwarta ya sace babu ƙarfin gwiwar ɗaga murya.

Ta yi ƙoƙarin danne ɓacin ranta da tunanin zobenta zai isota nan bada jimawa ba. Shri Hari Bansari ya gama bautan ranaku masu alfarma a gareshi.
Idan zobe ya zo, ba Gwamna Saifuddeen ba, gaba ɗaya jahar za su dawo ƙarƙashin ikonta.

Sai da Umaru Kwom ya rufe kamfen ɗinsa kafin Gwamna Saifuddeen ya rufe nashi. A bayyane take mutane na tareda SSK sama da Umaru Kwom. Hatta waƙoƙin zaɓe na SSK yafi na Umaru Kwom daɗi musamman wanda wani haziƙin mawaƙi ya rera yana yabon Gwamna da amaryarsa Asiya Shahidah.

***

Asiya na zaune gefen Junior Gwamna ya shigo. Asthma É—insa ce ta tashi É—azu bayan ya gama tsalle-tsallensa a waje shi da wasu yaran ma'aikata na gidan., ba inhaler kusa da shi shine ya shiga mawuyacin hali kamar zai shiÉ—e yaran suka gudu, sai da wani security ya ganshi ya kawo shi cikin gida wurjanjan. Aka ci sa'a Gwamna na kusa ya fito da inhaler É—insa ya matsa masa a baki, still ya jima kafin yaron ya dawo dai dai

"Ya jikin na shi?"

Gwamna ya zauna gefen Asiya bayan ya kissing goshin Junior
"Da sauƙi"
Bata ankara ba taji ya kamo hannunta, yanzu kam har ta saba da irin haka dan indai suna tare baya rabo da riƙe hannunta ko kuma ya kissing goshinta ko kumatunta.

"Zan fita, zan je wajen Baba"

"Allah ya kiyaye hanya"

"Amin" ya kissing goshinta sannan ya miƙe ya fita.

Ta cigaba da kallon Junior tana tuno yadda kwanaki suka dinga tafiya da sauri har haka. Gobe Jummu'a za'a ɗaura auren Ubayd da Salma, jibi Asabat za a yi zaɓen shugaban ƙasa yayinda sati biyu na gaba kuma za ayi zaɓen Gwamnoni. Tunda ta gama kamfen ɗinta bata sake fita daga gidan ba. Duk wani shirye shiryen biki da ake yi ta ƙi zuwa gidan. Ta dai aikawa Inna Yaha kuɗi, sannan ta turawa Faty ma kuɗin gudummawa saboda hidimar bikin da za a yi. Ba zai kyautu ba idan bata halarci ko ɗaya daga cikin hidimar bikin ba, idan tayi haka zata zama butulu. Ko babu komai, Yaya Ubayd Yaya ne a gareta, sannan ko dan darajan Abba dole ta je.

Ba wai tana jin haushin auren bane amma ta rasa ya akayi zuciyarta ya rasa samun sukuni tunda satin bikin ya shigo.
Ta miƙe ta koma ɗakinta saboda ta fara shiryawa domin shaiɗan ke jefa mata wannan wasu-wasi. Matuƙar tana auren Saifuddeen, Ubayd ya haramta mata har abada. Soyayyarsa ta fara gushewa a zuciyarta sai dai abinda ba za a rasa ba daga shaiɗan wanda ke motso mata rayuwar soyayyarsu ta baya a wasu lokutan.

Ta kan tsinci kanta da damuwa idan Gwamna bai kirata ko ya mata text ba a kwanakin da ba nata ba. A ranakun da ya kasance nata, idan har tafiya ta kamashi ba zai kwana a gari ba gadonta na mata faɗi. Duk da idan yana nan ɗin, filo take jerawa tsakaninsu, kasancewar su kwance a gado ɗaya yana sa mata nitsuwa. Duk ranan da ba su kwanta tare ba, tana yin kewar numfashinsa, ƙanshinsa, tusarsa idan ya shiga banɗaki da Asuba zai yi fitsari, abin mamaki har ƙwaƙwalwarta ya haddace sautin tusar ta yadda a ko'ina ta ji zata ce tasa ce.
Ta kan yi kewar wata rana da take al'ada suna kwance tayi tusar gaba ba su jima da bacci ba dan haka sarai ta san ya ji tusar amma ta kafse ta rintse idonta tana Allah yasa kada yai magana. Ko sakan arba'in bai cika ba ta sake wata tusar mai ƙara, wannan karan ta fita ta baya ne dan haka bayan ƙaran da tayi har da wari. Asiya ta ji kaman ta nitse cikin gadon saboda kunya.

"Gaskiya za a ciki tara. Domin daga yanzu Gwamna ya saka dokar hana tu..." Asiya ta sa hannu ta toshe masa baki, tana ji a ranta kaman ta fasa ihu.
Ƙoƙarin cire hannun yai amma ta hana sai ma ƙara matsowa da tayi tana faɗin "ai kaima kullum kana yi idan ka shiga banɗaki, nima idan ka sake yi zan ci tarar ka ehe"
Chapter 24 · 0% Book details