← Book details Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 37

Sashe 19

Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gwamna ya sa hannu ya jawota jikinsa ya fara bubbuga bayanta a hankali. Kamar shiga jikinsa da tayi ya ƙara mata ƙwarin gwiwa ne na yin kuka, dan buɗe baki tayi da kyau ta fara kuka kamar ƙaramar yarinya. Bai hanata ba har sai da ta gaji da kanta tayi shiru tana ajiyar zuciya akai-akai.

Wannan ne karo na farko da suka kasance cikin irin wannan yanayi na kusanci. Da ta daina kukan sai ta maida hankalinta kan bugun ƙirjinsa da take ji. Ya kamata ta tashi daga jikinsa amma ta rasa taya zata fara, kunyarsa take ji da kuma kunyar yadda gangan jikinta ke jin daɗin kwanciyar da tayi a jikinsa.

A ɓangaren Gwamna shima wannan kusancin yayi tasiri a jikinsa. Ji yake kamar su dawwama a haka.
Babu wanda yayi yunkurin sake wani sai da wayar Gwamna tayi ƙara, hakan yasa Asiya tayi saurin barin jikinsa ta miƙe da sauri sai taji an riƙo hannunta.
"Ina zaki je?"

"Ban... banÉ—aki" ta faÉ—a ba tareda ta juyo ta kalleshi ba.

Ƙin fitowa tayi daga banɗakin har sai da ta ji alamar ya fita daga ɗakin sannan ta fito.

Ta tsaya gaban madubi tana kallon fiskarta da ke jiƙe saboda alwala da ta yo.

*"a duk lokacin da kike cikin tsananin fushi to ki yawaita yin Isti'aza. Idan kin samu dama ki yi alwala ki yi sallah raka'a biyu ki nemi tsari daga Shaiɗan, idan kina da lokaci ki buɗe Alƙur'ani ki karanta saboda samun nitsuwa"*

Nasihar Gwani kenan, wani lokaci da daɗewa da take gidan Ale, wata Amaryar Ale da suke kusan sa'anni ta cire mata kayanta daga igiyar shanya ta zubasu a ƙofar ɗakin Tabawa kan kashin Awaki. Da ta zo ta ga kayan aka ce mata Basira Amarya ce ta zuba su a wajen, sai kawai taje ta ɗau jarkan manja a ɗakin Fulani ta shiga ɗakin Basira ta buɗe akwatunanta guda uku kowanne ta zuzzuba manja a ciki, ta ɓata mata duka kayanta. Data gama ta wuce gidan Gwani.

Da Fulani ta dawo daga anguwa ta dinga bala'i a gidan wai sai an biyata kuɗin manjarta. Itama Basira data ga akwatunanta sai ta fara masifa, ƙarshe sai da Aljanunta suka tashi.
Ale ya dawo ya samu gidan a rikice, aka gaya mishi abinda Asiya ta aikata. Ala tilas ya biya Fulani kuÉ—in manja, ita kuma Basira dama da Aljanun suka lafa sai ta wuce gidansu.
Bayan Isha yaje ya samu Gwani ya faÉ—a masa abinda Asiya tayi. Gwani bai wa Asiya magana a ranan ba sai washegari data dawo daga makaranta ya kirata É—akinsa ya fara mata nasiha akan yawan fushi.

*"Ki daina saurin aikata duk abinda zuciyarki ya haska miki Asiya-Shahidah. Yin hakan zai saka miki rashin nitsuwa, zai sa ki cikin ƙunci"*

"Allah ya ƙara maka rahama Gwani"

Asiya ta furta a fili sannan ta wuce closet ta ɗauko hijabi ta tada sallah. Data gama tayi addu'ar Allah ya sanyaya mata zuciya ya kuma bata ikon kula da tarbiyyan 'yaruwarta dama sauran ƙannenta.
Shigowar Gwamna ɗakin ya sa ta fasa buɗe Ƙur'anin da ke gabanta.

"Asya a mana addu'a zan wuce Abuja"

"Yanzu?"

"Flight ɗin ƙarfe shaɗaya na dare ne"

"Allah ya kiyaye hanya" ta faɗa tana sunkuyar da kanta ƙasa saboda idanunta da suka faɗa nashi.
Murmushi yai ya ƙaraso wajen da take zaune. Ganin ya zo daf da ita sai ta fara ƙyafƙyafta ido tana tambayar kanta mi zai yi kuma?. Ba dai abinda ya faru ɗazu ya buɗe mishi wata dama bane.

Hannunta É—aya ya kamo yace " kwana biyu zan yi na dawo. Ina neman alfarma Dan Allah. Za ki min?"

Ba tareda ta É—ago ta kalleshi ba tace "minene?"

"Kada ki yiwa Sumayya faÉ—a. Na yiwa Abdullahi magana kuma zan tabbatar cewa ya rabu da ita completely. Andddd..."

"And?" Ta maimaita ganin bai ce komai ba.

"Ki rage zafi kin ji"

Za ta yi magana ya manna mata peck a goshi yace na tafi. Bai jira farfaɗowanta daga ɗaukewan numfashin hucin gadin da tayi ba, ya miƙe ya bar ɗakin.

Sai ya zama mentally gani take har lokacin yana ɗakin, har lokacin laɓɓansa na dai-dai tsakiyar goshinta, hakan ya sa ta kasa buɗe idanunta.
Ba zata iya fassara yadda hanjin cikinta ya taƙune ba. Ko butterflies ne, ko ma wani abun ne daban, ta dai ji wani abu ya fara mata yawo a ciki hakan ya sa ta sa hannu ta riƙe cikin nata.

"Anty Asiya" muryar Junior ya fargar da ita daga yanayin data shiga. Bata san iya tsawon lokacin data zauna a wajen ba bayan tafiyar Gwamna.

"Junior baka yi bacci ba?"

Ƙarfe tara ne dokar baccinsa ko yana so ko baya so. Ɗan kwanakin nan data dawo ta ke ɗan kula da yaron yasa ta san kusan komai nasa.

Yana sanye da Pyjamas kalar sky blue ganin fiskarsa sai ta hango fiskar Gwamna Saifuddeen.

"Tell me a story" ya faÉ—a yana zama gefenta.

Tunda ta bashi labarin CY da Biri kullum sai yace ta sake bashi labarin baya gajiya da jin shi.

"Wani labari?"

"CY and the Monkey"

"Ka ga dare yayi, idan Mommy ta san baka yi bacci ba zata yi faÉ—a"

"Mommy bata nan"

Ta jawo shi jikinta sosai tace "barin koya maka addu'ar bacci, gobe sai ayi labarin"...

A ɓangaren Gwamna Saifuddeen kuwa, yana fita daga gida ya dinga murmushi. A cikin mota kafin su kai airport kasa haƙuri yai ya fito da wayarsa ya fara duba hotunan Asiya ciki harda wanda ba zata taɓa tunanin yana da su ba.
A zuciyarsa yana fata wannan chanjin ya zamo mai É—aurewa.

Bayan Asiya ta kai Junior ɗakinsa sai ta dawo ta naɗe sallaya ta kwanta. Maimakon bacci ya zo sai bacci ya ƙaurace mata, ta dinga juyi akan gado tana ƙoƙarin hana ƙwaƙwalwarta tunanin mutumin da a da ko sunansa bata son ji. Sai chan tsakar dare bacci ya saceta.

***

Washegari da Asiya ta idar da sallar Asuba ta yi Azkar, sai ta fara tilawa.
Wanda zata yiwa karambanin haɗa masa breakfast baya nan, dan haka ba zata wahalar da kanta ba. Bata ma jin ƙarfin fita waje.
Kamar jiya haka yau ma Sumayya ta fice daga gidan ko leƙa Asiya ba ta yi ba.

Asiya tana cikin karatu ta lura da wata takarda acikin Ƙur'anin. Da chan tana da yawan ajiye kuɗi acikin ƙur'ani, amma rabonta da yin hakan har ta manta. Ta jawo takardar tana son ganin ko na minene, ƙila ma irin ayoyin addu'a da take rubutawa Umma ne.

*Dear Asiya...*

*zan so ki yarda da mijinki, ki taimaka masa saboda shi ba maƙiyin ki bane. Ki yi hankali da Bilkisu Kachallah, ita ta sa aka sace ki, kuma zata iya yin fiye da haka. Shawarata gareki shine "don't act stupid, act smart"*

*Agent R.B.K (Hansa'u)*

"Hansa'u?" Asiya ta furta cikin kaÉ—uwa.

***

13

Tabbas Biri yai kama da Mutum. Abinda Asiya ta faÉ—a kenan a ranta.
"What should i do?.
Idan na tunkari Bilkisu Kachallah haka, zata iya ƙaryata komai. Tukunna ma ina Hansa'u ta shiga?".
Tun kafin wannan rana bata taɓa ganin Bilkisu Kachallah a matsayin matar da za ta sota har ta karɓeta hannu bibbiyu ba. Yanzu kuma ta sake fahimtar manufar wannan mata akanta.

"Think Asiya, Think Shahidah"
Asiya ta faÉ—a tana bubbuga kanta da yatsun hannunta biyu.

Ta jima tana saƙa da warwara, kafin ta tsaida mafita ɗaya. Dole ta nemo Agent RBK ɗin nan, a wajenta ne zata samu amsoshin tambayoyinta.

"Excellency yace na dinga amfani da ƙwaƙwalwata. Letting my emotions get over me shiyasa na haɗa hannu da Umaru Kwom kwanan baya"

Ta saka kanta a tsakiyar cinyoyinta tana huci.
"Rashin tunani yasa nake zargin Gwamna da sawa a sace ni while he's innocent. He's always innocent, ni ce na tsane shi"

Ta É—ago kanta tana faÉ—in "miyasa ma na tsane shi?"
Ta gama tunanin duniyan nan bata gano ƙwaƙwƙwaran dalilin da yasa ta tsani Saifuddeen Sa'ad Kachallah ba, domin tun kafin ta aure shi ta tsane shi balle tace aurenta da yai shine dalilin.

Ƙarshe wani tunani ne ya zo mata hakan yasa tayi saurin janyeshi daga ranta dan ba tunani ne mai kyau ba.
Ta É—au wayarta ta kira numbar Fou'ad Salisu amma bai É—auka ba dan haka ta tura masa text.

***

Asiya ta sauko ƙasa kenan suka yi kichiɓis da mai girma Bilkisu Kachallah da ke shirin haurowa. Kallon-kallo suka fara yi dan kuwa babu wanda yake da niyyar matsawa ɗan uwansa.

Bilkisu daga wajen rabon kayan Kamfen take. Ba ita tayi rabon ba amma jimawa da ta yi a tsaye tana karɓan gaisuwa da jinjina daga waɗanda suka karɓi kayan da aka basu ya gajiyar da ita.

An raba kwalin sabulai, kwalin spaghetti mudun sugar da shinkafa sai kuma turmin zani mai hoton Bilkisu da Saifuddeen.
Kanta kamar zai tsage saboda hayaniya da kuma ihu da ta dinga yi a mic lokacin da take ihun 'Jama'a, Congo sai waaa?'
Matan talakawa da miskinai suka dinga wage baki suma suna ihun 'Congo sai Saifuddeen Kachallah' ko kuma suce 'Congo sai SSK'

A zuciyar Asiya ji take kamar taje ta shaƙe wuyar wannan munafukar mata amma ta dinga bawa zuciyarta haƙuri da cewa ba yanzu ba, akwai lokaci.

A ɓangaren Bilkisu kuma tunanin yadda za ayi ta fitar da Asiya daga gidan Gwamnati take. Indai aka ci zaɓe to dole ne ta koma chan gidan, saboda ba za ayi Matan Gwamna biyu a gidan Gwamnati ba. A nan gidan there will be only one Governor's wife, Bilkisu Kachallah.

Ganin Asiya bata da niyyar matsawa yasa Bilkisu ta ƙariso ta bangajeta ta wuce. Asiya tayi saurin riƙe kafaɗanta saboda ba ƙaramin bugu Bilkisun ta mata ba. Magana take so ta faɗa amma sai ta lura da Safiyya dake wajen riƙe da jakar Bilkisu Kachallah tana wiki-wiki da ido.
Ba ta son ma'aikatan gidan su fara gulman matan Gwamna suna faɗa, shi yasa ta kauda kai ta sauko. Safiyya ta ɗan duƙar da kai tana faɗin "ranki shi daɗe" Asiya ta haɗe rai ta wuce ta.

Tana fita daga gidan Motarta ta shiga Yaya Bello ya wuce da ita Kachallah house. Rabonta da gidan tun ranan da za a kawota gidan miji.
Chapter 19 · 0% Book details