Sashe 14
Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Asiya ta zauna a ƙofar ɗakin Umma tana jiran dawowar Abba. Ita dai ƙarya Inna Yaha ta mata da ta ce Umma ta rasu. Sharrin Inna Yaha ne kawai zata ce Umma ta rasu. Umma na nan.
Gajiya, Yunwa, ciwon jiki duk ba sune damuwar Asiya ba. Ita dai tana so ace mata Ummanta na nan da ranta, abinda ta gani a TV ba gaskiya bane film ne.
Inna Yaha tace Musa ya je ya kirawo Abba a masallaci. A hanya suka haÉ—u dan ko minti biyu bai cika da fitansa ba ya shigo biye da Abba.
"Asiya, Asiya kina lafiya? Kema 'yan sanda ne suka kuɓutar da ke?" Abba ya tambaya yana riƙe hannun Asiya.
Tun da la'asar da suka ji labarin an samu É—aliban nan suke sa ran su ji an samu Asiya amma shiru. Ya kira Gwamna dan ya tambayi labarin Asiya amma Gwamna bai É—auka ba.
Bayan sun ɗan nitsu Abba ya fara yiwa Asiya nasiha akan mutuwa daga ƙarshe ya sanar da ita rasuwan Ummanta.
Mutumin da take tunanin zai ƙaryata labarin da ta ji sai gashi ya sake tabbatar mata da mugun labari.
"Abba da gaske sun kashe min Umma?"
"Kul Asiya. Kul kika sake magana irin wannan, sai kace jahila"
"Abba..."
"Addu'a zaki mata ba ƙorafi ba Asiya. Addu'arki take buƙata yanzu".
Asiya ta sunkuyar da kai sai hawaye.
" na kai miki ruwan wanka Asiya. Kije kiyi wanka, sai ki zo ki ci abinci" Inna Yaha ta faÉ—a lokacin data shigo falon.
Ba Asiya ba, shi kansa Abba ya yi mamakin kalaman Inna Yaha...
Gwamna na hanyar zuwa gidan Yallaɓai bayan ya bar Asibiti Abba ya kira shi.
"Da kanta ta dawo? Ba abinda ya sameta ko?" Gwamna ya faÉ—a cike da farin ciki yama manta da sirikinsa yake magana.
Yana gama wayar yasa aka juya da shi. Da farko gidan zai wuce direct sai ya ga idan yaje haka zai ja hankalin jama'a shiyasa ya fara zuwa chan tsohon gidansa. Ya ce Dreban Gwamnati da excort su wuce chan Government house yayinda shi kuma ya shige motarsa drebansa ya fice da shi.
Asiya ta jima a banɗaki tana kuka kafin tayi wanka ta fito. Lokacin da ta fito an buɗe ɗakin Umma, ta tsaya bakin ƙofa tana jiran ta ga ko za ta hango Umma kwance akan sallaya ko akan gado, amma bata gani ba. Gwani da Habibu ne a ɗakin suna magana.
Gwani yace "Anty, Yaya Ubaydu yace a gaisheki"
Ba ta yi magana ba sai ta gyaÉ—a masa kai...
Abba da Ubayd suna falo lokacin da Abba yai waya da Gwamna, jin cewa Gwamna yana hanya Ubayd ya miƙe yai wa Abba sallama. Dama yana jira Asiya ta fito su gaisa ne, amma tunda mai guri ya zo sai mai tabarma ya naɗe.
9
"Ina Sumayya?" Asiya ta tambayi Ali daya shigo gaisheta.
"Yau ta koma hostel"
"Har yanzu kana yawon dare ko?"
"A'a na dena... yeeh Gwamna yazo" ya miƙe ya fice da gudu jin ƙaran tsayuwar mota a gidansu.
Lallai yaro yaro ne. Ko sati bai cika ba da rasuwar Mahaifiyarsa, amma damuwarsa Gwamna ya zo gidansu.
Asiya ta sauke ajiyar zuciya ta zubawa abincin da aka kawo mata ido. Tuwon masara ne da miyar kuka, da alama cikin wanda aka rage na ɗumamen gobe aka ɗebo mata dan babu nama a ciki sai ƙullin balangu a leda da ke gefe. Sai kuma lipton da madara guda biyu na leda da aka ajiye a gefe.
Ta ɗeba sugar ta saka a lipton ɗin ta raugaya ta fara kurɓa kaɗan kaɗan. Duk da yunwar dake cinta hakan bai hanata jin haushin Gwamna ba. Da zata ga fiskarsa ruwan shayin nan zata watsa masa saboda yadda ta tsani fiskarsa...
Abba yai ta zarewa su Habibu ido amma yaran suka dake suka ƙi tashi daga falon, suka maƙalewa Gwamna suna cewa sai yayi hoto da su.
Gwani ne mai hankalin cikinsu dan haka Abba yace "Lukman ka je ka kira min yayarka"
"Abba abinci take ci" Ali yai saurin faɗa saboda matuƙar Gwani ya tashi suma ɗin aikansu za ayi.
Abba ya haÉ—e rai yace " Aliyu kayi tilawar yau ne?"
Ali yai saurin miƙewa dan yanzu idan yai ƙarya Abba zai sa shi karatun dole.
Ganin Ali da Gwani sun fita Abba ya kalli Habibu yace " kaje ka duba min lafiyar mashin"
Habibu ya miƙe yana ƙunƙuni.
Bayan yaran sun watse Abba da Gwamna suka sake gaisawa sannan suka yiwa juna jajen abinda ya faru.
Gwamna ya nisa yace " Sumayya bata nan ne? "
"Yau ta wuce hostel"
Ganin shirun yayi yawa Asiya bata shigo ba Abba ya miƙe yace yana zuwa.
Asiya ta ƙarisa shan shayi amma bata taɓa tuwon ba, bata da appetite na cin komai.
Abba yai sallama ya shigo É—akin.
"Ki je ku gaisa, idan kika dawo sai ki faɗi abinda zaki ci" babu wasa a yanayinsa hakan yasa Asiya ta miƙe ta shiga neman hijabi. Lokacin data fito daga wanka jallabiya sabuwa Inna Yaha ta kawo mata, tana tunanin ma ba zai wuce cikin kayan Faty bane data bar wa Hindatu.
Bata san miyasa aka tattara kayan Umma ba, bata san miyasa aka ma rufe wardrobe dake É—akin ba. Sai kuma ta tuna cewa yanzu fa kayan Umma sun zama na gado.
"Asiya ba zaki wuce bane"
"Abba hijab nake nema"
"Ke da mijinki sai kin wani tsaya neman hijabi"
Da cikin nitsuwa take, cewa za tai "Lah! Abba da kanka" sannan tayi dariya.
Yanzu kam babu abinda ta iya cewa, sai ta É—au gyalen kayan wanda har lokacin yana cikin ledar jallabiyar, ta yafa akanta ta fita.
Lokacin data shigo waya yake yi.
"Eh nina ce su wuce gida, ina tareda Asya, an sakota...Amin"
Ya ajiye wayar gefe ya kalli Asiya da ke tsaye ta riƙe ƙugu.
Abinka da farar mace har wahala tasa ta fara dishewa. Duk da haka tayi masa kyau, baƙar jallabiya mai duwatsu blue ya amshi jikinta duk da ramar da ta yi.
"Asya" ya furta cike da shauƙi.
"Ka zo ka gani ko sun karya min ƙafa ne? Ko kuma sun datse harshena?"
"Ki zauna mu yi magana Dan Allah"
hajijiya ta fara ji hakan yasa ta bi umurninsa ta zauna suna fuskantar juna.
"Ina miki ta'azziyar rasuwar Umma, Allah ya gafarta mata"
"Kanada bakin ta'aziyya dama. Ai na É—auka abinda kake so kenan"
Gwamna ya É—an zaro ido cikin rashin fahimta
"Asya bana so ki ɓoye min komai. Ki faɗamin yadda komai ya faru, ina suka kaiki? Mi suka ce miki?. Ina ganin kamar..."
"Kamar me? Har kana da bakin magana. You are a fraud Gwamna Saifuddeen, kai munafukine kuma Azzalumi. Har na fara tunanin tayaka Kamfen ashe kai ka riga ka shirya naka Kamfen É—in. You said it yourself ni hajar Kamfen ce, i mean nothing to you. Taya zaka sa a sace ni a ranan da mahaifiyata take kwance a gadon Asibiti. Taya zaka sa a hanani yiwa mahaifiyata addu'a?"
Gwamna ya miƙe tsaye ya tako zuwa gabanta hakan yasa ta yi shiru sai nishi da take sama sama. Ya sa hannu biyu ya miƙar da ita tsaye. Sai da idonsu ya haɗu kafin tayi saurin sunkuyar da kanta ƙasa.
"Asya kina tunanin zan sa a sace ki saboda Kamfen? Abinda suka faÉ—a miki kenan?"
Tayi shiru ta kasa magana saboda kusancinsu da yai yawa, turarensa da take shaƙa ma kaman jawota jikinsa yake.
"Wani irin ƙiyayya kike min Asya?, miyasa akoda yaushe ba kya min zaton alkhairi sai na sharri?. Aurenmu zai iya kasancewa ƙaddara amma ko a hakan, matar mutum matar mutum ce, no matter what. Idan zaki min adalci Asya, a iya zaman da muka yi ya kamata ki gane cewa bana wasa da iyalina, and you are my family"
"Kai kace su ɗauko ni. Kai ka tura min text kace na bisu. Akwai wanda ke da numba irin naka ne?. Ni ba yarinya bace, Excellency na san yadda 'yan siyasa suke zama a lokacin yaƙin neman zaɓe. Ka yi amfani da ni ne saboda ka samu mutane"
Ya san tana cikin raɗaɗin rashin uwa, ya san abinda ya faru dole ne ya taɓa tunaninta, amma idan da zata iya duban ƙwayan idanunsa da zata ga tsananin so a cikinsu.
Da ta san abinda yai saboda ita, da bazata ƙara tunanin zai iya cutar da ita ba.
"Ina son ki Asya" Asiya-Shahidah ta yi saurin ɗago idanu ta kalleshi. Shima ita yake kallo hakan ya bashi daman ƙarisa maganar "Ba zan taɓa cutar da ke ba, ba zan taɓa amfani da ke wajen neman duniya ba. Ina fatan watarana za ki fahimci hakan"
Bai jira mi zata ce ba, bai yi ƙoƙarin goge hawayen da ya gangaro mata ba. Bai yi ƙoƙarin ƙara wasu kalaman ba saboda babu amfanin yin hakan.
Har Gwamna ya fice daga falon Asiya tana tsaye tana rawar jiki yayinda hawaye ya cigaba da zubo mata. Ƙarshe tsayuwar ya gagareta, ta tsugunna a ƙasa jikinta ya cigaba da rawa. Kalaman Gwamna sun ratsa kowanni lungu da saƙo na jikinta.
*"ina son ki Asya"* ya fara maimaituwa a kunnenta, hakan yasa ta toshe kunnen da hannu biyu jikinta ya cigaba da rawa...
***
Lokacin da Gwamna ya isa gida kai tsaye ɗakinsa ya wuce ya zauna yana tunanin kalaman Asiya. Wani irin tsana ta masa ne? A iya saninsa da ita, shi bai taɓa yi mata komai ba.
Daya fito daga banÉ—aki ya ga Bilkisu zaune a bakin gado tana jiransa.
"Na É—auka gida zaka kawota ai?"
"Tana buƙatar kasancewa da 'yanuwanta"
"Hakane, fatan tana lafiya?"
"Ba kya ganin Baba ne ya sa aka É—auke Asiya?"
"Baba kuma!" Bilkisu ta faÉ—a tana kama baki.
"Anya Baba zai iya haka?, ni gaskiya ban yarda ba" ta faÉ—a ganin Gwamna bai yi magana ba.
"Junior yayi bacci ne?" Ya kauda maganar...
***
Lokacin da Asiya ta farka a gadon Asibiti ta ganta, kusa da ita Sumayya ce da kuma Bilkisu Kachallah.
Jiya da dare da Abba ya shiga falo ya sameta bata cikin hayyacinta. Har aka kawota Asibiti bata san inda kanta yake ba.
Da sassafe Gwamna ya zo ya dubata lokacin tana bacci.
"Anty Asiya ya jikin?" Sumayya ta tambaya murya ƙasa-ƙasa saboda tsoron Bilkisu Kachallah da take.