← Book details Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 37

Sashe 13

Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asiya na zaune tana kallo yayinda ƙwaƙwalwarta ke lissafin abinda yake faruwa.
Ita É—in hajar Kamfen ce, ita É—in decoy ce, ita É—in bata da matsayi a wajen Gwamna Kachallah sai dai yai amfani da ita ya yar.
Bata san ina ta samu ƙarfi ba, lokacin da aka nuno Gwamna Saifuddeen Kachallah yana magana table ɗin dake ɗakin ta ɗauka ta bugawa TVn tana faɗin *I hate you Saifuddeen Kachallah*

8

"Kana da ƙarfi a wannan jaha Yallaɓai. Taya za ka bari Umaru Kwom ya juya garin nan. Jahar nan gaba ɗayanta a ƙarƙashin ikonka take, ko dai tsufa ya sa ka yi sanyi?"

Yallaɓai ya fara murmushi yana shafa gemunsa. Ya kai minti ɗaya yana haka kafin yace "Zan kira Commisioner of police, za a nemo yaran cikin awa arba'in da takwas, amma ina da sharaɗi?"

"Ka san babu abinda zai gagareni"

"Saifuddeen zai sa hannu a takardar yarjejeniya"

"Idan wannan ne an gama"...

***

Gwamna Saifuddeen Kachallah bai bar Office ba sai ƙarfe shabiyu saura na dare. Yana isa gida ya tarar da Bilkisu ta kalmashe ƙafa akan kujera tana jiransa. Daga yanayin kayan jikinta ya san akwai abinda take buƙata.

"I'm tired Bilkisu"

"Na sani Baby na. Na san yadda abubuwan da suka faru suke damunka"

Ta riƙo hannunsa suka ƙarisa ɗakinsa. Suna shiga ta shiga taya shi cire kayan jikinsa.

"Akwai yadda za a yi a ƙwato yaran nan" Gwamna yai saurin ɗago ido ya kalli Bilkisu, tayi saurin kauda kai tareda jawo ƙaton towel ta fara ɗaura masa a ƙugu.

"Bilkisu talk to me" yai maganar kamar ya shiga zuciyar Bilkisu ya ga mi take shirin faÉ—a.
Sai da ta ƙarisa ɗaura towel ɗin ta kamo hannunsa suka fito daga banɗaki, ta zaunar da shi a bakin gado. Kamar wani ƙaramin yaro haka yai galala yana binta da ido.

"Ba yaran kaÉ—ai za a sako ba har da Asiya "

"Go straight to the point please"

Bilkisu ta ƙarisa wajen bedside drawer ta ɗauko wani file ta zo ta ajiye a kan cinyar Gwamna Saifuddeen.

"Darling sign the agreement"

Ba sai ya buÉ—e file É—in ba ya san wani agreement take magana akai domin kafin a fara wannan hatsaniyar Alhaji Sani ya kawo masa file É—in kuma ya rantse ba zai sa hannu ba.

"Bilkisu kin san mi aka rubuta a ciki kuwa? Baba ne yasa ki ko?"

"Darling this people are powerful, ba za su bari ka hau kujeran nan ba sai kayi abinda suke so, idan kuma har ka hau, to ba za su bari ka aiwatar da komai ba har sai kayi yadda suka ce"

"Two years na farkon tenure ba zan ɗau ma'aikata ba, babu ƙarin albashi, zan yanke wasu benefit da allowance na ƙananun ma'aikata, zan yi titi a iya wajen da aka shata min, 80% na cabinets nawa zaɓa min su za a yi... This is absurd Bilkisu, miye amfanin mulkin idan ba zan iya aiwatar da komai da kaina ba"

"Its just two years, daga nan sai ka yi duk yadda kake so"

"No Bilkisu, ki cewa Baba yai haƙuri but i still can't"

"Idan yaran nan suka mutu, ba lallai ka iya samun nasara a zaɓen nan ba. Idan Asiya ta mutu, bana tunanin zaka yafewa kanka Saifuddeen"

"Ba zan yi ba, idan na yi wannan zan siyawa kaina tsinuwa ne daga wajen mutanen da suka zaɓeni. Ba wannan bama. Allah zai tambayeni Bilkisu, Allah zai tambayeni"

Bilkisu ta kamo hannunsa da suke rawa ta riƙe gam cikin nata.

" a duniya babu wanda zai soka sama dani Saifuddeen. Ba wai ina so ka amince saboda kada ka yiwa talakawa aiki bane, ina so ka kuɓutar da yaran nan da ma matarka saboda rayuwarsu tana cikin haɗari. Umaru Kwom is a monster, ba damuwarsa bane idan Asiya ta mutu ko kuma duka ɗaliban nan suka mutu. Shi dai burinsa ya ɓata maka suna saboda ya ɗaukaka nasa sunan. Ka ga dai how desperate he was a kan case ɗin Lami Ninja. Kaine Gwamna amma sune da ƙarfin iko, idan ka amince da sharaɗinsu zasu sa a nemo yaran nan, because they know the right button to press"

"Miyasa ba za a nuna min right button É—in ba?, miyasa ba za a barni na danna button É—in ba"

"Come here Darling, idan baka so shikenan, we'll find another way" ta rungumeshi tana É—an shafa kansa fiskarta É—auke da murmushin mugunta.
Gwamna yai lamo jikin Bilkisu saboda ba abinda yake buƙata sai hakan.
A zuciyarsa addu'a kawai yake yi domin ita kaɗai ke kawowa zuciyarsa sanyi. Ashe lokacin da yake mataimakin Gwamna bai san komai ba gameda siyasar Jahar nan. Tun ranan farko da Alhaji Sani ya kaishi gaban Yallaɓai a matsayin Ubangidansa, mutumin kwata-kwata bai masa ba, yana da nuna gadara kaman yafi ƙarfin kowa.

***

"Ina zaku kai ni?, ina zaku kaini?" Asiya ta faɗa tana ƙoƙarin tirjewa. Daga bayanta aka kwaɗa mata bakin bindiga a ka, hakan ya sa ta faɗi ƙasa a sume...

Gwamna na zaune a office COS ya shigo.

"Ranka shi daɗe kana da saƙo"

Gwamna ya buɗe envelop ɗin da aka miƙa masa. Kafin ya fito da abinda ke ciki COS yace "Your Excellency demands na kidnappers ɗin kenan"

Hoton da Gwamna ya gani ya sa shi miƙewa tsaye ba shiri.
"Mi suke so? Mi suke buƙata?"
Babu komai a cikin envelope É—in sai hoton nan hakan ya sa ya juya bayan hoton inda aka rubuta MILIYAN ÆŠARI BIYAR NAN DA KWANA BIYU.

Ba shiri Gwamna ya zauna akan kujera. Ba wai kuÉ—in ne ya É—aga masa hankali ba. Kwana biyu da suka rubuta na nufin za su iya yiwa Asiya komai idan ba a kawo kuÉ—in ba nan da kwanaki biyun.

Ya rintse idonsa amma hoton Asiya yake gani zaune akan kujera an ɗaure mata hannu, ƙafa da baki. Yanayinta na nuni da tana cikin wahala.

"Mi za mu yi ranka shi daÉ—e?"

Gwamna bai yi magana ba sai kawai ya ɗaga masa hannu. Bayan COS ya fita. Gwamna Saifuddeen ya shiga tunani. Umaru Kwom, Yallaɓai, Alhaji Sani duk wasa suke da hankalinsa. Amma ba abinda zai iya a halin yanzu sai dai yai abinda zai ceci rayuwar ɗaliban da aka sace da kuma matarsa.
Asiya bata cancanci hakan ba. Bai sani ba ko tama san mahaifiyarta ta rasu. Ko ya zata ji idan ta dawo ta tarar da rasuwan?.

Yana fita daga office kai tsaye gida ya wuce. File É—in nan yana nan a saman drawer har yanzu. Ya É—auki file É—in ya fice daga É—akin cikin sauri...

"Your Excellency, kaine da kanka a gidana" Yallaɓai ya faɗa yana saukowa daga matattakala.

"Bismillah, ka zauna" ya nuna masa kujera yana murmushi.

Gwamna ya ajiye takarda akan center table yace " 50% na cabinets nawa ne, na yarda ba za a ɗau sabbin ma'aikata ba, amma ba za a rage albashin ƙananun ma'aikata ba"

Gwamna da Yallaɓai suka tsaya kallon kallo, kowa da abinda ke ransa. Gwamna ji yake kamar ya shaƙe tsohon nan kowa ya huta. Shi kuma Yallaɓai yana hasaso wani abu gameda Gwamna Saifuddeen ne.

"Shikenan, na yarda da gyaran da kayi"

"Idan wani abu ya samu matata ko kuma É—aliban da aka sace yarjejeniyarmu ta tashi"

"Ba abinda zai same su"

Gwamna ya duƙa ya saka hannu a takardar. Yana ɗagowa Yallaɓai yace "seal"
Gwamna bai yi magana ba, ya ciro seal ya manna akan takardar.

Lokacin da Gwamna ya tafi, Yallaɓai ya shafa gemunsa yace "Aff! tanada tasiri a rayuwarka"

***

A kwana na uku da Gwamna Saifuddeen Kachallah ya sanya hannu a yarjejeniyar Yallaɓai, 'yan Sanda suka gano maɓuyar kidnappers suka far musu. An kashe kidnappers biyu yayinda sauran suka tsere. An kuɓutar da ɗaliban nan duka, inda aka wuce da su Asibiti saboda a tabbatar da lafiyarsu.

Gwamna na samun wannan labari ya fara murmushi yana hamdala. Ya damu da ɗaliban kamar yadda ya damu da matarsa amma jin cewa ba a samu Asiya ba sai hankalinsa ya tashi. Ya dai yi ƙoƙarin danne zuciyarsa.

Sawa yai a shirya masa tafiya Asibitin da aka kai yaran, zai je ya dubasu...

A ɓangaren Umaru Kwom Kuma tamkar ya haɗiyi ransa saboda baƙin ciki. Bai san miyasa Commisioner of Police ya shammace shi ba, bayan irin maƙudan kuɗin daya bashi.

Lokacin daya kira shi ya tambayi bahasi cewa yai Yallaɓai ne ya basu umurnin su nemo yaran kota halin ƙaƙa.

"Yallaɓai" ya furta sunan da ƙarfi.

Tabbas Yallaɓai ya fi shi ƙarfi, ya yi zama ƙarƙashinsa kuma ya san tasirinsa a jahar da ma ƙasa baki ɗaya.

Ba a jimaba ya ɗau waya ya kira Yallaɓai. Ya jima da rabuwa daga jikin Yallaɓai, amma har yanzu akwai shakkarsa a ransa. Yana riƙe da wayar zuciyarsa na bugawa da ƙarfi ƙarfi.

"Umaru Inuwa Kwom"

"Yallaɓai" Umaru Kwom ya kira da tausasashshiyar murya kaman ba shi ke ta zagin Yallaɓai ɗazu ba.

"Yau ka tuna dani kenan"

"Yallaɓai ban san miyasa ka bawa Saifuddeen dama ba tun a wancan tafiyar. Saifuddeen ba zai taɓa baku abinda kuke so ba, he's incompetent. Ba shi da ƙarfin zuciyar yin siyasa"

"Kayi Kamfen É—inka ta hanyar da ta dace Umaru. Maganar sace yara ba inda zai kaika"

"Yallaɓai..."

Kafin yai wata maganar aka katse kiran.

Idan har wannan ba zai yiwuba. Zai yi amfani da kuɗi ya sayi ƙuri'u.

***

*"Idan kika buÉ—e baki kika faÉ—i abinda ya faru tamkar kin kashe Iyalen Malam Nuhu Principal ne..."*

Asiya ta buɗe ƙofar gidan su ta shiga, kashedin da aka mata na yawo a kanta.
Tunda akayi sadakan uku gida ya watse.
Musa ta gani yana cin abinci a ƙofar ɗakin Inna Yaha. Yana ganinta ya miƙe zumɓur yana kiran mahaifiyarsa.

"Inna ga Anty Asiya, Inna..."

Inna Yaha tana sallar magariba ta katse sallar ta fito da gudu. Tun rasuwan Umma jikinta yake a sanyaye.

Abinda bai taɓa faruwa ba sai ga Inna Yaha ta rungume Asiya.

"Inna Yaha ya naga É—akin Umma a rufe da kwaÉ—o?"

Maimakon Inna Yaha ta bata amsa sai kawai ta fashe da kuka.

"Ina Umma? Ta je anguwane?"

" Ummanki bata nan Asiya. Ki shigo ciki" ta kamo hannunta zata kaita É—aki. Asiya ta tirje tace "ki gayamin inda taje"...
Chapter 13 · 0% Book details