← Book details Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 37

Sashe 17

Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai yamma kafin suka tafi, lokacin da aka dawo da Junior yayi futu-futu da shi wai ball ya buga. Da ke yaron kullum a takure yake, yanzu da ya zaga anguwa yai wasa da sa'anninsa da kuma wanda suka girmeshi sai ya langwaɓe jikin Ali yace ba zai tafi ba. Da ƙyar Asiya ta lallashe shi akan za a kawo shi gobe.

Bayan tafiyar su Mahira, Asiya ta shiga tattauna maganar da Mahira ta mata, da ma maganar Abba daya tsaya mata a rai tun jiya.

Ta kasa yarda cewa Gwamna ba shi da hannu a saceta da aka yi saboda alamu sun nuna shi munafukine. Amma yanzu kuma maganar Mahirah ya sa ta fara tantama da abinda ta sawa ranta.
A wani gefe kuma kalaman Gwamna na ranan suna kashe mata jiki, suna tunkuÉ—e duk wani haushinsa da take ji.

'Ina son ki Asya' duk lokacin da ta tuno waɗannan kalamomi sai ta dinga ji tsikar jikinta na tashi. Sannan ƙwaƙwalwarta na ƙoƙarin gano mata a wani siga za ta fayyace kalaman. Shin Gwamna yana sonta a matsayin matarsa ne, ko kuma a matsayin wacce ya kamu da soyayyarta?...

Kwananta biyar a gida ta warware kamar ba ita ba. Ranan ne kuma aka raba musu gadon Umma wanda Abba ko tsinke bai É—auka ba, dan cewa yai ya yafe nashi kason.

Washegari Abba yace ta tattara ta koma gidanta. Tun maganar da Abba ya mata take shakkarsa dan haka da yai maganar ko musu ba ta yi ba ta kira Yaya Bello tace ya zo ya É—aukesu bayan sallar magariba.

Abin mamaki gidan Gwamna ta É—auka za su wuce sai ta ga yayi hanyar gidan Gwamnati.
"Yaya Bello ka kaini gidansa bana son hayaniyar wanchan gidan"

"Mai girma ne yace nan gidan za a kawoki"

Tayi shiru ba dan ranta ya so ba, sai dan tana ƙoƙarin bin nasihar Abba. Shine da ikon sakata a duk inda ya ga dama, tunda sunan matarsa take amsawa.

"Mommy where is Hancha'u?" Junior yayi wa Bilkisu tambayar nan yafi a irga. Yanzun ma Safiyya ce ke zuba masa abinci shiyasa ya tambaya saboda tunowa da yai da ita.

"Na gayama kar ka sake tambayar Hansa'u a gidan nan. She's gone"

"Mommy why?"

"Ni kam ko yarinyar nan mayya ce, kullum minti É—aya biyu sai ka tambayi Hansa'u. Eat your food ko kuma na hanaka zuwa Kachallah house gobe"

"gidansu Ali zan je gobe"

"Waye kuma Ali?"

"Alin gidansu Asiya. Oops Anty Asiya"

Dai dai lokacin Asiya ta shigo dinning room É—in da sallama.

"Speaking of the devil" Bilkisu ta faÉ—a a ranta.

ÆŠakin da Asiya ta zauna kwanan baya an rufe shi. Ta tambayi wata mai aiki tace Bilkisu ce ta rufe.

"Ina buƙatar key ɗin ɗakina"

"Wani É—aki fa?"

Asiya ta haÉ—e gira tace "É—akin da ya dace da matar Gwamna"

Bilkisu Kachallah ta saka dariya, dariya sosai har da buga table. Asiya da Junior suka zuba mata ido...

11

Gwamna yana zaune a falo yana karanta jarida lokaci zuwa lokaci yana ɗan kurɓan tea. Safiyar Lahdi ne kuma ya yi niyyar babu inda zai je da safe sai yamma idan ya fita duba 'yarsa Nana. She's improving sosai, ba kamar farkon kaita ba, dan har kaman zarewa ta yi saboda ƙwayar data dena sha.

Kwanan Asiya É—aya kenan da dawowa gidan kuma tun dawowanta bata haÉ—u da Gwamna ba, sai yanzu da ta zo falonsa.

"Barka da safiya"

Tun da ta buɗe ƙofa yake binta da wutsiyar ido amma ba zaka gane hakan ba saboda gilashin da ke idonsa akwai ɗan duhu. Idanunsa da kullum suke a kumbure saboda rashin isashshen barci da hutu ya saka shi sanya gilashi a koda yaushe.

"An tashi lafiya?"

"Lafiya"

Shiru ne ya biyo bayan hakan na wasu mintina da za su iya haura biyu.

"Ranan a Asibiti..." sai tayi shiru saboda nauyin maganan. Har yanzu ta kasa yarda da maganar Sumayya amma kuma hoton data gani yana yawan yi mata shawagi a idanunta musamman idan ta rufe ido. Wani lokaci tana duba hoton a wayarta saboda ta ƙara fassara hoton da Sumayya ta ɗauka. Ta saka Sumayya goge hoton a wayarta, amma kafin nan sai da ta tura hoton zuwa nata wayar ba tareda sanin Sumayya ba.

"Ina jin ki?"

"Ina so ka manta da abinda na faÉ—a cikin bacci, saboda shirmen bacci ne"

Gwamna ya ajiye jarida akan cinyarsa ya kalleta yace "ni kuma sai nake ganin kamar kin faÉ—i abinda ke ranki ne, dan abinda ka kwanta da shi da shi kake tashi"

"A'uzubillahi. Ni wallahi ba abinda zai sa na yi irin wannan tunanin. Balle na furta munanan kalmomi haka" ta rage muryarta ƙasa ƙasa tace "sai kace wata karuwa"

Gwamna bai gane inda ta dosa ba amma yace "shikenan in kince a rufe maganar za a rufeta. Amma..."

"Allah shirmen bacci ne ba komai ba. Ka manta da duk abinda na faÉ—a" ta faÉ—a da sauri

Sai daya kalleta kamar mai nazari sai yace "shikenan zan manta da komai"

"Ina so na je garinmu. Mama bata da lafiya"

"Ki yi haƙuri zuwa wani lokaci sai kije amma ba yanzu ba"

Har ga Allah bata ji daɗi ba, sai dai kuma yanzu ta yi alƙawarin yi masa biyayya gwargwadon iyawarta tun lokacin da Abba ya mata faɗa...

***

Sati ɗaya Asiya ta lura Hansa'u bata gidan. Da ta tambayi masu aiki sai aka ce mata tunda ta tafi ƙauye bata dawo ba. Ta ja bakinta tayi shiru, dama saboda ta saba da ita a gidan ne yasa ta tambaya da bata ganta ba.

Asiya bata taɓa ganin Alhaji Abdullahi ba sai a lokacin bikinsu da Gwamna. Kafin nan kam tana jin sunansa amma ba za ta iya tuna takamaimai kamanninsa ba. Sai ga hotonsa a wayar Sumayya daga shi sai towel daya ɗaura a ƙugu. Ga tunbinsa ya fito kaman mai cikin wata takwas. Abin haushi harda riƙe ƙugu kamar wata mace.

Kanta ya É—au zafi saboda hoton da kuma inda ta samu hoton yana nuni da cewa shi ya turo hoton ta whatsapp.
A ina Sumayya ta san Alhaji Abdullahi?

Garin sauri saboda makara yasa Sumayya ta manta wayarta a gida. Asiya hotunanta na biki da akayi a gidansu take son turawa taci karo da wannan hoton.
Ta san password É—in Sumayya dan haka kai tsaye ta buÉ—e whatsapp É—inta ta fara neman tushen wannan hoto.
Sunan da aka yi saving da My Abdul ta shiga, kuma a nan ta tarar da hoton da aka tura, a ƙasan an rubuta "yanzu na fito daga wanka"
Ɗan saman chat ɗin kaɗan ta ga hoton da Sumayya ta tura masa wanda yake dishi-dishi saboda an riga an goge hoton akan wayar. Hoton ƙirjinta ne zuwa cikinta wanda babu riga babu komai.
Hannu na rawa ta fara bibiyar chats É—in wanda ya tsaya kusan sati biyu baya. Da alama an goge sauran ne saboda daga inda maganar ta fara ya nuna anyi wani a baya gogewa akayi.

Idan bata manta ba Alhaji Abdullahi cousin É—in Gwamna ne kuma abokinsa. Ba ta da masaniya akan iyalinsa amma ta san yanada mata da 'ya'ya. Nawa Sumayya take? Ko shatakwas idan ta cika to kwanan nan ne.
Ta ina ma suka haÉ—u? Ta sake tambayar kanta.

Haka ta riƙe wayar tana sintiri a ɗaki, zuciyarta na ayyano mata abubuwa dayawa. Kafin ta taho ranan kaman ta ji warin sigari tattare da Habibu amma bata sa hankali ba saboda ba a nitse take ba. Wace irin 'yaruwa ce ita da tayi watsi da lamarin ƙannenta haka? Kullum tana cikin jin haushin Gwamna ta ina zata lura da abubuwan da suke wakana a kusa da ita.

Lokacin da Sumayya ta dawo, É—akin Asiya ta fara shiga saboda ta gaisheta kamar yadda ta saba.

Asiya na zaune akan sallaya lokacin da ta shigo, da alama ta idar da sallah kenan.

"Wash! Anty Shahidah yau na zaunu, lectures tun safe har ƙarfe huɗu ko sallah ba a bari mun fita ba" Sumayya ta faɗa tana zama kan gado.

Asiya ta juyo ta kalleta da rinannun idanunta tace " Sumayya waye My Abdul?"

Sumayya ta shiga wuri-wuri da ido.

"Ba ki da bakine?"

"Wani É—an makarantanmu ne, na manta ban gaya miki bane"

"Yaushe Alhaji Abdullahi ya zama É—an makarantanku?"

Sumayya tayi shiru.

Asiya ta jawo wayar Sumayya a ƙasan sallaya ta buɗe ta nuna mata hoton tsoho mai tumbi. "Ki faɗa min gaskiya ko na ci uban ki a gidan nan"

"Cewa yai..cewa yai yana sona"

"A ina kika san shi" Asiya ta daka mata tsawa.

"Tun muna wancan gidan ne, ranan ya zo neman Gwamna shine ya sameni a falo muka gaisa"

"Sai kika bashi numbarki kina tura masa hoton nonuwanki ko?"

Cikin Sumayya ya juya saboda bata yi tsammanin Asiya ta ga komai ba. Ta É—auka hoton data nuna mata ne kawai.

"Cewa yai zai aureni"

"Zai aureki a whatsapp? Yaushe wuyanki yai ƙwari Sumayya. Har kin iya soyayya da babban mutum"

"Kema ai babban mutum É—in kika aura"

Asiya ta buÉ—e baki ta kulle, ta kasa magana saboda tsananin mamaki.

Duk da ƙirjin Sumayya na lugude saboda abinda ta faɗa hakan bai hanata jin haushin Asiya ba. Taya zata cewa My Abdul ɗinta babban mutum.

"Gaskiya ne Sumayya, na auri babban mutum kam. Sai dai ni ba a titi ya sameni ba, iyayena ne suka damƙa mishi ni" ta faɗa lokacin da ta iya danne zuciyarta daga abinda take shirin aikatawa na rufe Sumayyan da duka.

"Ba za ki zo ki fantsare a gidana ba, idan aure kike so zan kira Ale na faÉ—a mishi, dama shi ba son karatun yake ba. Daga yanzu na siezing wayarki"

Sumayya ta miƙe fuuu tayi hanyar ƙofa tana faɗin " sai ki faɗawa Ale ɗin ai, ki faɗa masa. Idan an tashi ki rinƙa nuna kin fi kowa a hakan ba abinda kike tarawa kanki sai zunubi, mijinki bashida daraja a gunki"

Asiya ta zauna daɓas a ƙasa lokacin da taji ƙarshen maganar Sumayya.

Salati ta fara tana tantamar lafiyar Sumayya ko kuma dai Aljanu gareta?.

Har dare bata sake jin ɗuriyar Sumayya ba. Tunaninta Sumayya zata gane nauyin furucinta ta dawo ta bata haƙuri amma hakan bai faru ba.
Chapter 17 · 0% Book details