← Book details Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 37

Sashe 20

Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sashen Hajiya Dadda ta wuce. Ta samu tsohuwar a falo tana karanta jarida. Sallamar Asiya yasa ta ɗan tura gilashinta sama sannan ta ɗago tana kallon ƙofa dan bata gane muryar ba.

"Lah lah. Amarya ce da kanta?. Marhaban Marhaban"

Asiya zata zauna Dadda ta ce ta matso ta raɓeta. Asiya ta ƙarisa ta rungumi tsohuwar.

"Kinsan mu da muke kan gangara muna son jin É—umin mutane kusa da mu" tayi maganar tana dariya tareda zare gilashin idonta ta maida shi gidansa.

"Haba dai. Hajiya ai har yanzu da sauran ƙarfin ki, ai sai kin cika ɗari har da ɗaya tukunna"

"Ko shekaru nawa kayi a doron ƙasa ƙarshe dai sai ka ɗanɗani mutuwa, ko yaushe dai ta taho muna addu'ar ta same mu masu imani, kar ta ɗaukemu muna cikin shashanci da gafala"
Dadda ta nisa tace "Ya aka ji da haƙuri kuma, kiyi haƙuri ciwon ƙafa bai barni na je muku gaisuwa ba?"

Jiki a sanyaye Asiya ta amsa da cewa "Alhamdulillah Hajiya. Allah ya ƙara lafiya"

"Allah ya gafarta mata Amin"

Asiya tace "Amin"

Shiru ne ya ɗan biyo bayan haka kafin Dadda tace " ya aka ji da hayaniyar Kamfen kuma. Ita 'yar uwarki kullum sai an nunota a tv ko jarida tana yawon kamfen, bana tunanin tana kula da lamarin Saifu ko 'ya'yanta. Aisha ta ce min tunda aka kai mai suna gidan 'yan ƙwaya, sau ɗaya mahaifiyarsu ta ziyarceta. Kar ki manta fa ita ce sanadin lalacewar 'yar, yo ina ta zauna da su ta fuskanci matsalarsu ma, yau tana wannan ƙasa gobe tana wancan gari. Haka take tun tana ƙarama ƙafarta baya zama waje ɗaya"

Asiya bata yi mamakin wannan zance da Dadda keta sakewa ba. Dama idan mutum ya tsufa ba abinda yake so irin a saurareshi.
Akwai lokacin da matan Ale suke zagin Tabawa wai tana haɗa guri. Dama tun kafin tsufan Tabawa akwaita da gutsiri tsome, to amma shekaru yasa abin ya ƙara yin gaba. Sai dai baka zauna da ita ba, amma haka zata kawo zancen wannan ta kawo na wancan. Idan wani ma ya sake zuwa haka zata kwashe naka ta gaya mishi.

Dadda ta cigaba " kwanaki ma haka suka yi faɗa da ƙannenta. Saudah a gaban Uban ta rantse babu ruwanta da Bilkisu har abada. Halima kam tun ranan da ta kira Bilkisu da Boka suka raba gari. Yo idan ba Bilkisu ba, Haliman nan fa abar tausayi ce, ta kusa shekara talatin da biyar amma babu mashinshini, wannan ai ya isa ya taɓa mata lafiyar ƙwaƙwalwa."

Asiya tace " Hajiya, Anty Halima ita ce autar Alhaji ko?, lokacin biki kaman ita da Hajiya Umma suke ta shige da fice"

" itace Auta. Daga Rufaida sai Bilkisu, sai Saudah, mai suna, sai kuma ita Halima"

Asiya ta dinga gyaɗa kai tana sauraron tarihin 'ya'ya da kuma jikokin Hajiya Dadda. Ba wannan ne ya kawota ba amma kuma wannan ɗinma ba a banza ya tafi ba dan ta ƙara tsintar wasu halayen Bilkisu Kachallah.

"Ai Bilkisu a rayuwarta ita kaɗai kawai ta sani. Har yau tana juya kaf yayye da ƙannenta. Na yi mamaki da bata tada fitina ba lokacin da Saifu yace zai aure ki"

A zuciyar Asiya tace "saboda ta san abinda ta shirya min idan na shigo ba"

Labarin Saifuddeen da Dadda ta fara yasa ta tuna da É—anta Sa'ad.

"Saifu kaf halin ubansa ya É—auko. Dai dai da magana da tafiya duk irin tasa ce. Harta murmushi idan yai sai naga kamar Sa'ad ne a gabana" sai kuma ta fara goge hawayen daya fara zubo mata. Mutuwa sama da shekaru arba'in amma har yanzu idan ta tuno sai ta ji É—aci aranta kamar yau aka yita.

"Hajiya Allah ya gafarta masa"

"Amin, Amin fa. Ai Sa'ad ya tafi a sa'a, gashi ya bar baya da kyau. Allah ya ƙarawa ɗansa lafiya da nisan kwana"

Asiya ta amsa da Amin. Chan cikin zuciyarta kuwa tana tunawa da sati É—aya zuwa biyu baya babu wanda ta tsana a duniya sama da Saifuddeen Kachallah har take ganin da zai mutu ma da zata fi kowa jin daÉ—i.

Dadda ta miƙe ta shiga ɗaki ta kawowa Asiya hotunan tarihi. A nan ta ga hotonan bikin Dr Sa'ad Habu Kachallah da Aicha Ali Jallow.
Ashe Saifuddeen gadon kyau yayi. Duk da hoton black and white ne hakan bai ɓoye kyawun iyayensa ba musamman mahaifiyarsa wacce daga wajenta ya ɗauki manyan idanu da kuma dimple sai dai bai ɗauko farinta ba sai ya ɗau baƙi da tsawon Uban shi.

Yana daga cikin dalilan da zata iya cewa sun haddasa mata ƙiyayyar Saifuddeen a baya, irin yadda mutane suke kururuta shi. Kyaunsa, iya wankansa, tafiyarsa dama maganarsa.
A baya ta tsani muryarsa saboda sanyin muryar yayi yawa kamar na mace. Amma yanzu koyaushe ta tuna maganarsa "ina son ki Asya" sai ta ji tsikar jikinta ya tashi.

Lokacin da Dadda ta faɗa mata Saifuddeen bai taɓa ganin iyayensa ba sai a hoto, wani tausayinsa ne ya ratsa ta. Ashe gara ita ta rayu da tata mahaifiyar har zuwa lokacin data mallaki hankalin kanta. Amma shi...

Sai yamma liƙis Mahirah ta dawo daga Islamiyya. Lokacin Asiya da Dadda sun wuni hira, a nan Asiya tayi sallar Azahar da La'asar kuma suka ci abinci tare. Ta taso da tsofi kusa da ita dan haka duk tsawon zaman da suka yi bata gaji da Hajiya Dadda ba, ta ƙaru sosai kuma ta sake samun darasin rayuwa.

Duk da ahalin Habu Kachallah suna cikin arziƙi amma suma suna fuskantar jarabawa iri-iri, daga kan 'ya'ya, jikoki da ma 'ya'yan jikoki. Dama haka rayuwar take babu wanda zai tsira daga jarrabawar Allah, sai dai na wani ya banbanta da na wani.

Bayan sun keɓe da Mahirah ne ta tambayeta ko tanada hoton Hansa'u a wayarta.

Mahirah tace baza a rasa ba cikin hotunan da ta É—auke su ita da Junior lokacin tana gidan. Ta jima tana duba wayarta kafin ta samo hoto É—aya da Junior ya musu selfie. Fiskar Hansa'u na karkace amma dai duk wanda ya santa zai iya ganeta. Asiya ta tura hoton a wayarta sannan ta musu sallama ta tafi. A cikin mota ta turawa Fou'ad hoton tana addu'ar Allah yasa ya binciko mata agent RBK da gaggawa.

Lokacin data isa gida É—akin Sumayya ta fara wucewa, ta samu Summayar ta dawo tana sallah. Ta wuce nata É—akin dan a gajiye take.

Bayan ta gama sallar Isha ta kwanta tana tunanin abinda ya dace ta yi a wannan lokaci. Idan ta yi gaggawan yanke hukunci akan Bilkisu zata iya rasa bakin zaren da take son warwarewa, dan haka dole tabi komai a nitse sannan tayi shiru da bakinta har zuwa lokacin da zata san duka gaskiyar.

***

Cikin kwana biyun da Asiya tayi kafin Gwamna ya dawo ta yi su ne cikin takatsantsan da kuma shirye-shiryen wani ƙudurinta da take son aiwatarwa idan Gwamna ya dawo. A rana ta uku da take tunanin dawowan Gwamna har dare shiru babu ɗuriyarsa. Tsoron zaƙewa take shiyasa ta kasa kira ko ta masa text ta ji ko lafiya bai dawo ba. Besides da yamma ta shiga kitchen ta ga ana ta kan shirye-shirye wai Bilkisu ce ta bada umurnin girkin da za ayi saboda Gwamna na hanya. Haushi ya sa ta koma ba tareda ta yi abinda tayi niyya ba. Kenan bai damu da ita ba, har zai sanar da Bilkisu dawowarsa amma bai tuntuɓeta ya gaya mata ba. Haushi ya cika mata ciki ta kasa cin abincin dare.

Tana kwance kan gado duk bata jin daɗin jikinta. Ga haushin Gwamna da take ji, ga kuma baƙon wata da ke yi mata sallama. Junior ya shigo ɗakin wai ta masa labari.
"Junior bana jin daÉ—i ka bari gobe zan maka"

"No, jiya ma baki min ba"

Ganin ba haƙura zai yi ba yasa ta miƙe tace su je ɗakinsa.

"Wani labari zan yi"

"CY and the monkey"

"Ikon Allah. Idan CY ya kamaka kana masa dariya zaka gayawa 'yan garinku"

Junior ya fara dariya tun ma bata faÉ—i labarin ba. Tun ranan da ta bashi labarin indai ya tuno sai yayi dariya, kuma kowanni lokaci zata bada labarin sai ya ji kaman yanzu ne farkon jin labarin a bakinta.

Da ke a gajiye take, a gurguje zata bashi labarin ta huta da rigimarsa.

"Akwai wani abokina ana ce masa CY amma asalin sunansa Clement Yohannah. Watarana ni da shi muka je gidan zoo ɗaukan rahoto saboda tsohon Zakin gidan zoo ɗin ya mutu. Da muka gama naɗan rahoto sai muka fara yawon buɗe ido a cikin zoo ɗin. Muka haɗu da wasu 'ya'yan birrai suna wasa. CY ya ɗau camera yaje wajensu ya fara ɗaukansu hoto. Da ya matsa kusa da su sai suka watse sai guda ɗaya. CY ya shiga ɗaukanta tana rawa, ƙarshe data gudu sai ya bita. Ina kiran CY akan ya haƙura da Birran nan ya zo mu tafi amma yai kunnen ƙashi. CY ya bi Birrai har wajen duwatsu. Yana saƙale da camera a wuyansa ya riƙeta yana shirin ɗaukan wani Biri sai wancan Biri mai rawan nan ta zo bayan CY ta zabga masa bulala a wuya. CY ya riƙe kunne ya juyo da sauri dan ya ga daga ina aka dake shi, bai gama juyawa ba aka sake zuba masa bulala a tsakiyar kai. CY ya saka ihu ya fara gudu yana kiran 'Jesus my head ooo. I don die ooo' ai kuwa Birrai kusan biyar suka biyo CY da gudu dukkansu da bulala a hannunsu. CY ya yar da camera, ya yar da takalmi ya cigaba da ihu yana kiran 'i don die oo'

Har muka koma gida CY bai san inda kansa yake ba, da an taɓa shi zai fara 'i don die oo' kafin a kai gida kan CY ya kumbura suntun"

Tun kafin ta kawo nan Junior ya ke dariya. Itama dariyan ta fara, saboda tunowa da tayi wannan ne silar shaƙuwarsu da CY dan lokacin bata jima da fara bautar ƙasa a tashar Hill TV ba.

Gwamna da ke tsaye bakin ƙofa ya tako har bakin gadon. Ƙanshin turarensa da Asiya ta ji yasa ta tsaida dariyan, bugun zuciyarta ya ƙaru.

"Daddy" Junior ya faÉ—a yai tsalle ya faÉ—a jikin Gwamna.
Chapter 20 · 0% Book details