Sashe 12
Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tayi duk abinda za tayi cikin ya zube amma bai zube ba. Ƙarshe ta haƙura zuwa lokacin da za a haifeshi ta kashe jinjirin tace bai zo da rai ba.
Ta hana Badawiyya fita, ta dinga gana mata azaba, huron yunwa, aiki kamar jaka da tsoratarwa. Kafin ranan haihuwan gaba ɗaya Badawiyya ta fice daga kamanninta, in fact, ƙwaƙwalwarta ya taɓu.
Madam Bintu ce da wata tsohuwar ma'aikaciyarta mai suna Gamboji a cikin gidan, sai kuma maigadi da Dreba. Ranan da Badawiyya ta fara naƙuda Gamboji ce ta kira Madam Bintu akan ko za a kai Badawiyya Asibiti amma Madam Bintu tace fir haihuwan gida zata yi.
Gamboji tana tunanin ita zata karɓi haihuwan tunda ba laifi ta manyanta kuma ta taɓa karɓan haihuwan shekarun baya a ƙauyensu amma sai Madam Bintu tace ita zata karɓi haihuwan wai Gamboji ta je Dreba ya kaita kasuwa ta siyo kayan jarirai saboda ba abinda aka tanada.
Gamboji ta fita zuciyarta na wasu-wasi.
Badawiyya na cikin ƙunci amma Madam Bintu ko kaɗan bata tausaya mata ba, lokacin da kan yaron ya fara fitowa haka ta dinga turashi ciki da ƙarfi dan kar ya fito, so take ya mutu a ciki kar ma ya fito duniya. Badawiyya tun tana kuka har wahala yasa tayi dogon suma.
Ganin kan yaron ya koma ta ƙarfi sai ta fara duba alamun numfashi a tattare da Badawiyya amma bata gani ba.
"Sa'a biyu kenan, shegiyar itama ta koma"
Madam Bintu ta yarfe gumi ta fice daga É—akin tana jiran dawowar Gamboji.
Da Gamboji ta dawo kuwa samun Madam Bintu tayi a falo tana kuka.
"Madam miya faru?"
"Badawiyya ta mutu Gamboji"
Gamboji ta wuce É—akin da gudu tana salati.
"Madam ya aka yi? Lafiya na tafi na barta fa"
Ba ta iya yin musu ba lokacin da Madam Bintu ta ce tayiwa Badawiyya wanka ta mata sutura kafin ta dawo, idan ta dawo zata kira mutane ta faɗa musu cewa Badawiyya ta rasu wajen haihuwa, sannan babu mahalukin da zai san ita ce ta karɓi haihuwan Badawiyya.
Tana da 'ya'ya biyu a ƙauye, kowacce da iyalinta. Madam Bintu tayi alƙawarin kashe mata 'ya'ya da jikoki idan ta buɗe bakinta ta faɗi abinda ya faru.
Fitar Madam Bintu daga gidan, Gamboji ta kasa zaune ta kasa tsaye, jikinta sai ƙyarma yake. Ba wai bata taɓa yiwa gawa wanka bane amma wannan gawar daban ce. Ta sani Madam Bintu ce ta kashe Badawiyya.
Sanda ta fara yiwa Badawiyya wanka ne kuma baiwar Allah ta farfaÉ—o, da ke Allah yayi da sauran numfashinta a duniya.
Gamboji ta tsorata ta fice daga gidan da gudu tana ihu. Maigadi ne ya kamota ya fara tambayar lafiya. Da ƙyar Gamboji ta iya yi masa bayanin komai. Maigadi ya shawo kanta da ƙyar suka koma cikin gidan. Sai da Maigadi ya shiga ya tabbatar Badawiyya da ranta kafin ya fito ya sanar da Gamboji da ke zaune a falo tana rawan jiki.
Bayan ta shiga ta tabbatar Badawiyya ba mutuwa tayi ba sannan suka shiga shawaran ya za ayi, idan suka bari Madam Bintu ta dawo to ba makawa sun kaÉ—e sannan Badawiyyar ba zata tsira ba tunda sun ga manufar Madam Bintu akanta.
Ƙarshe Maigadi ya kawo wata shawara. Dake maiɗakinsa itama a gidan take sai kawai suka nemo taxi suka saka Badawiyya a ciki Kande matar Maigadi ta wuce da ita Asibitin Dr Mustafah wanda ya kasance likitan Alhaji Rufa'i kuma aboki gareshi.
Da Madam Bintu ta dawo Gamboji ta faɗa mata cewa 'yanuwan Badawiyya ne suka zo suka ɗauketa wai zasu binneta a chan ƙauyensu.
Tunda Malaminta ya faÉ—a mata babu mai sake É—ago maganar gado ta sawa kanta salama ko ma ya akayi da gawar Badawiyya bai dameta ba.
Ba dan an kaita wajen Dr Mustafah da wuri ba da mutuwa za ta yi na gaskiya saboda jini da taketa zubarwa.
Hansa'u ta shafa cikinta. Shekaru sun ja amma ba zata manta cewa akwai ɗan daya taɓa zama a ciki ba, ba zata manta cewa saboda Madam Bintu Likitoci sun tabbatar mata ba zata sake haihuwa ba.
Bilkisu Kachallah ɗaya take da Madam Bintu, shiyasa zata iya sawa a sace matar mijinta har ma tayi iƙirarin bata damu da lafiyarta ba.
Koma minene ta kusa ƙarisa aikinta tunda taga inda Bilkisu Kachallah take ajiye mahimman takardunta. Da zaran ta samu Engineer ɗinsu ya gano mata yadda ake buɗe akwatin shikenan komai ya ƙare. Game over. Ita kuma Madam Bintu Chadi sai ta karɓi komai da ta tara da gumin Alhaji Rufa'i ta kuma turata kurkuku..
Sai da Rabi'atul Badawiyya Kabir ta sarawa Oganta kafin ta zauna tana murmushi lokacin da ya ce Barka da zuwa Hansa'u.
Sai da ya sa aka kawo mata coffee kafin ya fara bayani.
"Badawiyya na san yadda wannan aiki yake da mahimmanci a gareki. Kin sadaukar da komai naki akan wannan case ɗin but unfortunately ƙasarmu bata buƙatar masu jajircewa irinki. Bilkisu Kachallah tanada protection daga sama"
"Ban gane ba"
Ya ja dogon numfashi yace "an rufe case ɗin, in fact yanzu ba a zargin Bilkisu Kachallah da Bintu Chadi da safarar miyagun ƙwayoyi"
"Impossible Sir, akwai audio proof na hirarsu, written document kawai nake jira kuma shima na kusa samu. Sir Bilkisu Kachallah da Madam Bintu suna shigo da ƙwaya ƙasar nan"
" na yadda Badawiyya, sai dai abinda zaki fahimta shine ba su kaÉ—ai bane masu wannan harka kuma an gano cewa ana bincike akansu shiyasa aka ce a rufe file É—in case É—in"
"Sir tayaya za a rufe? This people import things that kill our youths. Matasanmu sun lalace da shaye-shaye alot of criminal activities yana faruwa ne saboda shaye-shaye"
"I know. Amma daga sama ne Rabi'ah. Sunce a terminating assignment É—inki dan haka dole ki bar wannan case É—in ki dawo office"
"Ba zan iya ba Sir, i need this case, ka san case É—in nan is personal to me"
"I'm sorry, amma dole ki haƙura da aikin"
Badawiyya ta rintse ido tana jin wani ƙunci a ranta. Tayi tunanin zata samu abinda take so shiyasa ta jona aikin force tun lokacin data dawo ƙasar.
Case ɗin Bintu take nema aka bata harda na Bilkisu, ba zata iya zama wajen Bintu ba saboda zata iya kasheta abinda therapist ɗinta ya faɗa kenan shiyasa ta zaɓi zama gidan Bilkisu Kachallah dan tayi bincike.
"Ki yi haƙuri Badawiyya" Oganta ya sake maimaitawa.
"Ka bani lokaci dan Allah na ƙarisa aikin nan, just small time, dana samu papers ɗin ba zan turawa kowa ba sai DEA na America, they will intervane"
"Badawiyya it's risky"
"Sati biyu Dan Allah"
Oga yai shiru yana nazari sannan yace "sati biyu Badawiyya, idan ya wuce haka i can't cover for you, kuma zaki sa kanki cikin hatsari ne"
"Nagode Sir"
***
Wanda suka sace ɗalibai sun fito sun bayyana cewa suna buƙatar miliyan ɗari kafin su sake ɗaliban, amma basu yi maganar Asiya Kachallah ba.
A ɓangaren Gwamna Saifuddeen Kachallah kuwa ikon Allah ne yasa bai haukace ba, abubuwa sun masa yawa, ga yaran da ake nema ga kuma Asiya da kullum yake kwana da ita ya tashi da ita. Ina take? Tana lafiya? Wani hali take ciki? Rashin samun amsoshin nan ya birkita masa tunani.
A wani gefen kuma ga ayyukan Jaha sannan kamfen da ya zame masa dole.
Umaru Kwom ma yana taka tsantsan da wannan sabon yanayi. Maganar sace Asiya Kachallah ya ɓata masa shiri domin yanzu tausayin Gwamna ake maimakon zaginsa da ake a da saboda gazawarsa. Ba abinda ya ƙara ɗaga masa hankali sai da ya ga Bilkisu Kachallah ta zargi 'yan adawa akan cewa sune da hannu a wannan sace-sacen da ake kuma da sannu komai zai warware. Daga wannan maganar rating ɗinsa ya fara sauka yayinda na Gwamna S S Kachallah ya ke ɗaguwa.
Yayinda ake wasa da rayukan yara ƙanana saboda siyasa, su iyayen yara suna cikin tashin hankali marar misaltuwa. Akwai wata uwa wacce aka sacewa ɗa ɗaya da Allah ya bata sai da shock ya sata faɗuwa ɓarin jikinta ya shanye.
Su ma iyayen Asiya da basu san a wani hali 'yarsu take ba suna cikin jimami da addu'ar Allah ya bayyanata.
A inda aka ɓoye Asiya kuwa ta ƙi cin komai sai kuka, kullum saƙa yadda zata ɗau fansar duk wanda ya mata wannan abu take. Har lokacin ta ƙi cin abinci, ruwa kawai ta ke ɗan sha a famfo idan za ta yi alwala a banɗaki.
A kwana na huɗu da ɓatan Asiya aka sake sace wasu 'yan Islamiyya yara ƙanana irin 'yan rabin ajin nan su guda bakwai.
A ɓangaren Umaru Kwom ya ɗaura aniyar har a zo zaɓe ba zai bari Jahar Congo ta samu lafiya ba. Idan an ɓoye Asiya Kachallah ne saboda a ɓata masa shiri to zai ga yadda za su yi idan aka cigaba da sace ɗaliban makaranta, lokacin babu wanda zai tuna da wata Asiya Kachallah da aka sace.
A ranan da aka sace 'yan Islamiyya Gwamna ya sauke wasu Kwamishinoni da wasu special advisers guda biyar daga kan muƙamansu, ya naɗa wasu tareda faɗin suma zasu tafi idan ba a samo ɗaliban da aka sace da matarsa ba.
Asiya bata ga wannan news É—in ba. Lokacin data kunna TV tun bayan ganin rahoton mutuwar mahaifiyarta da tayi, taron addu'a da first lady Bilkisu Kachallah ta haÉ—a ake nunawa.
Taron mata ne kowa a wajen ya sha anko, wasu sun saka farin leshi da head gear orange, wasu kuma sun saka atampa blue.
Bilkisu Kachallah ta hau podium ta fara bayani kan yadda 'yan adawa suke ɓatawa Gwamnatin Saifuddeen Kachallah suna. Ta buge da karanta suratul Quraishi, ta karantata gayau babu tajweed ba komai, cike da kura-kurai. Ta haɗa da addu'ar Allah ya bayyana yaran da aka sace da kuma ƙanwarta Asiya. Daga ƙarshe ta buge da kuka.
Aka kira wata Malama tayi karatun ƙur'ani kafin aka bawa wata Evangelist dama ta zo tayi addu'a.
Wasu Mata Yarabawa suka fito suna addu'a da waƙa suna rawa, da suka gama aka kira wasu mata da suka yi shigar fararen kaya, basu sa takalmi ba, sannan ba ɗankunne a kunnensu. Suka dinga tsalle suna sumbatu duk dai da sunar addu'a.