Sashe 36
Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Daddyn Alinah ka sake duba batun nan dan Allah. I want to help..."
"Adaeze ki haƙura da wannan case ɗin Dan Allah, for my sake. Ki duba condition ɗinki, this is not an ordinary case da zaki je sau ɗaya sau biyu, this can take a long while"
"Zunnoon, please!" Ta faɗa tana marairaice murya tareda riƙo hannunsa ɗaya
Justice ya sauke ajiyar zuciya yace "Adaeze da condition É—in ki zaki dinga jeka ka dawo tsakanin Congo da Abuja? Idan baki damu da lafiyarki ba think about our baby"
"We'll be fine my love" ta ƙarisa maganar tana kwantar da kanta a ƙirjinsa.
Jin bai sake cewa komai ba Zaytoonah ta sani yanzu kam ya haƙura.
***
"Hajiya Bilkisu Kachallah ta gyara zamanta da kyau sannan ta dubi Madam Bintu ta ce "kina tunanin zan bari a bata special treatment ne? No no no, you know me ai"
"Shegiya Bilkisu kenan yadda kowa yake rayuwa a kurkuku haka zata yi?"
"Of course, ita wacece da za a ɗagawa ƙafa"
Madam Bintu da gatse tace "Matar Gwamna ce"
Bilkisu Kachallah ta fashe da dariya har da tafa hannu.
"Idan akwai Gwamna a cikin prison to Asiya zata amsa sunan matarsa, otherwise, ni kaÉ—ai zan amsa sunan har ya gama tenure É—insa biyu"
Madam Bintu ta saka ihu "ina yinki tawan"
Suna cikin ƙyaƙyatawa da dariya wata mai aiki ta shigo ta rusuna gabansu tareda faɗawa first lady cewa Uwani staff ɗinta na chan gidan Gwamna tana son ganinta.
"Uwani?" Bilkisu ta maimaita da mamaki.
"Ok ki shigo da ita"
"Lafiya dai ko?" Madam Bintu ta tambaya tana kurɓan juice
"Bari ta zo mu ji"
Minti biyu sai ga Uwani ta shigo jiki a sanyaye.
Bayan ta gaishe da matan biyu sannan ta duƙar da kai ƙasa tana tunanin ta ina zata fara bayani musamman gashi ba Bilkisu kaɗai bace a falon.
"Miya kawo ki?"
"Dama dama..." Uwani ta fara inda-inda
"Banida lokacin wasa, ki faÉ—i abinda ya kawoki ko kuma ki bamu waje"
Uwani ta sauke ajiyar zuciya sannan tace "ina son komawa garinmu"
"A wani dalili?" Bilkisu ta tambaya fiskarta É—aure.
"Hankalina zai fi kwanciya idan nayi nisa da nan garin"
"Babu inda zakije. Ke Uwani!"
Uwani sai da ta ji hanjin cikinta sun kaɗa dan ba ƙaramin firgita tayi da tsawar da Bilkisu ta mata ba.
"Babu inda zaki je"...
Har Uwani ta koma chan gidan Gwamna bata daina rawar jiki ba. Babu yadda za ayi ta kuɓuta daga hannun Bilkisu. Lokacin da Bilkisu ta tunkareta da maganar saka ƙwayoyi cikin akwatunan Asiya ba ta bata damar cewa e ko a'a ba. Umurni ta bata kuma ta san rashin bin umurnin akwai matsalar da zai jawo tunda babu abinda Bilkisun bata sani ba gameda ita.
Tun da aka kama Asiya ta kasa yin bacci, duk da umurnin Bilkisu ta bi, randa gaskiya ta bayyana itama za a iya turata kurkuku. Wani mafita gareta daya wuce ta yi shiru da bakinta ta zubawa sarautar Allah ido.
*Congo state Prison*
Ko a mafarki Asiya bata taɓa tunanin zaman kurkuku ba, kafin a kawota nan ta taɓa zuwa gidan kurkuku na Congo lokacin tana Jami'a ta zo ɗaukan rahoto na wani assignment da aka basu. A rahoton data kawo tayi nuni da yadda gidan kurkukun ke cikin yanayi na neman agaji: ƙazanta, rashin ruwa mai kyau da kuma abinci wadatacce, ga kuma uwa uba cikowa da wajen yai. Sai gashi wai an wayi gari ita Asiya Shahida Faruƙ Baba ta fara irga kwanaki a gidan yari, yau kwana na shida kenan. Kwana shida tana kulle kamar wacce tayi kisan kai, kwana shida babu wani daya zo dubata koda kuwa lawya ne, kwana shida bata san miyake faruwa a wajen dogon katangar daya zagaye kurkukun ba. Hakanan kwana shida na wani sabon babi a cikin rubutacciyar ƙaddara wacce tun kafin zuwanta duniya an riga an rubuta.
Kwanaki biyun farko, É—akinta ita kaÉ—ai ne kuma abinci mai kyau ake kawo mata duk dama ba wai ci take ba dan azumin dole ta É—aurawa kanta. Sai kuma a kwana na ukun aka zo aka chanja mata É—aki, a hasashenta É—akin da aka ajiyeta shine mafi muni a cikin kurkukun.
Tana cikin ɗaki wata warden ta zo ta buɗe ƙofa tace " Hajiya Asiya akwai wata lawya dake son ganinki" warden ɗin mai suna Bisola ita kaɗaice ke yi mata magana cikin girmamawa da kuma tausasa harshe, amma sauran kaman wanda aka musu karatun rashin mutunci musamman kwanaki ukun nan.
Lokacin da aka fito da Asiya tana cikin tafiya ita da warden Bisola ta ji an kira sunanta.
"Asiya Kachallah"
Kaman ta wayi mai muryan hakan yasa ta juya, ai kuwa sai idonta ya gane mata Hansa'u cikin kayan firsina riƙe da fartanya a hannu.
"Hansa'u" Asiya ta faɗa da ɗan ƙarfi.
"Anty Bisola barin yi magana da waccar dan Allah"
"Hajiya Asiya da ƙyar aka bawa Lawyar data zo wajenki minti goma, kuma ya fara reading tun lokacin da aka ce na kawoki"
Asiya ta yi murmushin takaici tace "muje"
Ta É—agawa Hansa'u hannu sannan suka tafi...
24
Asiya ta kalli Lawyar da aka ce ta zo ganinta da kyau tana mamakin a ina ta santa. Matar wacce ta kira kanta da suna Barrister Zaytoonah ba zata wuce shekaru ashirin da tara zuwa talatin ba, sannan ga mamakinta ciki ne gareta da zai iya kaiwa wata bakwai zuwa takwas, dake tanada ƙiba ba zaka iya fidda ainihin adadin watannin ba musamman ga wanda bai da masaniya sosai akan ɗaukan ciki da kuma girmansa.
"Na san kin yi mamakin ganina. Mun haÉ—u sau É—aya a wajen dinner É—inku da Gwamna amma bana tunanin zaki iya tunawa. Mijina abokin Gwamna ne sosai"
Barrister Zaytoonah ta yi shiru tana nazarin Asiya sannan ta cigaba "ina so ki faɗamin duk abinda kika sani musamman gameda ƙwayoyin da aka samu a cikin ɗakin ki"
"Ban san komai akan ƙwayoyin ba, ban san ya akayi aka samesu a cikin akwatunan kayana ba"
Barrister Zaytoonah ta fito da tab ɗinta daga jaka ta kunna wani video ta miƙawa Asiya wayar tace kin taɓa kallon wannan video?
Asiya ta gyaÉ—a kai tace " inaga bai fi kwana biyu ko uku dana gani ba wannan abin ya faru"
"Lokacin da kika gani kuma kika ji da kanki an ambaci sunan matar Gwamnar Congo a matsayin uwarɗakinsu, miyasa baki fito kin ƙaryata ba? ko kuma ki nemi a ƙara bincike a tabbatar da ƙaryar abinda mutumin ya faɗa?"
Asiya ta haɗe rai ta ƙi magana domin gani take tambayar rainin hankali Barr. Zaytoonah ke yi mata.
"Asiya ina jin ki"
"Asiya?"
"Times up Barrister" wata warden ta faɗa da ƙarfi.
"Zan tafi Asiya amma zan dawo gobe" Barr Zaytoonah ta faɗa. Har zata fita sai ta juyo ta faɗi wani magana da ya ƙara tunzura Asiya...
Duk yadda Asiya ta so a kaita wajen Hansa'u babu wanda ya saurareta. Warden Bisola ce ta fito ta gaya mata gaskiya cewa umurni ne daga sama akan kada a bari Hansa'u wacce suke kira da Badawiyya tayi mu'amala da kowa. Lokacin da aka kawota kurkukun sai da aka yi kusan wata uku ba a barinta ta fita yin aiki ko wani abu, daga É—aki sai É—aki. Ta haÉ—a da cewa da alama wani yaga lokacin da Badawiyya ta kira sunan Asiya dan ko aikin da take ba a bari ta gama ba aka maidata É—aki aka kulle.
Asiya ta girgiza kai cikin takaici. Hansa'u itace fitilar da zata haska mata sirrin Bilkisu Kachallah. Duk abinda ya faru idan ta fito sai ta ga bayan matar nan.
Wani abu daya tsayawa Asiya a rai shine bayanin da Barr. Zaytoonah ta mata cewa Gwamna ya fito duniya yace ya cire hannunsa a case ɗinta, dan haka kada ta yi tunanin zata samu alfarma a kotu, gaskiyarta da kuma addu'a ne zasu kuɓutar da ita.
Washegari da Barr. Zaytoonah ta zo Asiya ta bata haÉ—in kai wajen amsa tambayoyinta koda tambayar da ta sani na rainin hankali ne.
Ranan Monday kuwa aka gurfanar da Asiya a gaban kotu.
Abu na farko da Barr Zaytoonah tayi ta fafutuka akai shine akan a bada bail ɗin Asiya. Idan ya so a cigaba da bincike tana gida. Sai dai faufau Alkali ya ƙi bada haɗin kai, kotu ta tashi ba tareda an cimma wani abin kirki ba, aka ɗaga sauraron ƙara zuwa sati biyu masu zuwa, zuwa lokacin ana sa ran hukumar NDLEA zata gama binciken data fara.
A ɓangaren CY kuwa, yana nan lokacin da aka yi zaman kotu, haka ya zubawa Asiya ido kamar mai kallon TV. Mahaifiyarsa Mrs Kimberly ta faɗa masa cewa ita da mijinta za su yi iya ƙoƙarinsu akan case ɗin Asiya amma gani yake kaman ba abinda suka yi tunda gashi anƙi ma a bada bail ɗinta.
He wished he could protect her lokacin da aka fito da ita daga kotu 'yan jarida suka mata chaa, duk da kuwa akwai securities masu hana su amma kowa ya san 'yan jarida da naci.
Haka ya bi bayanta da kallo har aka sakata cikin mota suka bar haraban kotun.
Dole ne ya binciko gaskiya cikin sati biyun nan kafin zaman kotu na gaba.
***
Rikici ne ya ɓarke tsakanin dattawan Congo tun lokacin da Mr Lamara Damana ya sanar da wasiyyar Yallaɓai ta ƙarshe kafin 'ya'yansa su tafi da shi ƙasar waje. Kowa yana ganin rashin dacewar chanja tsari da aka yi. Taya Yallaɓai zai naɗa wani shugaban daban ba ɗaya daga ciki manya uku da suke da damar maye gurbin muƙaminsa ba, abin takaicinma wai, wanda aka naɗa baya cikin ƙungiyarsu ta dattawa. Anya ma ba ƙarya Mr Lamara ya sharara ba, duk da ma dai sun gani a rubuce kuma da saka hannun Yallaɓai cewa Boss Lady ce zata maye gurbinsa.
Wasu kuma kalmar Boss Lady na nufin mace ce zata shugabance su, MACE fah!wannan abin ya fi tsaya musu a rai fiye da ma chanja tsari da aka yi. Koma wacece Boss Lady ba za su mara mata baya ba. Duk cikinsu babu mai shekara ƙasa da hamsin amma ace sai wata ƙaramar alhaki mace ta zo ta jagorance su sai kace wasan yara. Dan me ake kiransu Dattawa?.