Sashe 23
Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da dare Asiya ta shiga ɗakin Gwamna ta tabbatar komai tsaf-tsaf kafin ta fito ta zauna a falonsa tana jiran dawowar sa. Ƙarshe da ya zo ma falon baƙi ya wuce bai ƙaraso personal sitting room nashi ba saboda yana tare da wasu manyan mutane da zasu yi meeting na gaggawa.
Lokacin da ya gama da su ƙarfe ɗayan dare har ta gota. Ransa ya matuƙar ɓaci saboda duk zaman da suka yi jayyaya ne kan wasu 'yan China dake son buɗe kamfanin ƙere-ƙere a jahar.
Tun yana mataimakin Gwamna ya kawo shawaran kada a bari baƙi daga wata ƙasa su sake buɗe babban kamfani a jahar. Yana so ya haɗa hannu da wasu manya su buɗe kamfanin ƙere-ƙere saboda mutanen jahar Congo zasu fi amfanuwa da shi. Kamfanin da ke titi ya kamata ya zamo mallakin jahar Congo ba na wasu bare ba.
Yayi mamaki da ya ga Asiya kwance kan gadonsa tana barci. Like, bai tsammanci hakan ba. Ganinta da yai sai ya sassauta masa zuciya. Ya cire kayansa ya shiga banɗaki yai wanka tareda alwala ya fito ya shirya cikin kayan bacci sannan ya kwanta ɗaya gefen. Chan kuma ya kasa haƙuri ya gangaro inda take kwance ya rungumota jikinsa tareda kissing kanta da kuma wuyanta. Yai addu'a ya kwanta.
Asiya ce ta fara tashi saboda alarm ɗinta na ƙarfe huɗu da rabi da yai ƙara. hannunsa ɗaya yana ƙirjinta, ɗayan kuma yana kanta.
Anya shawaran da ta É—aukawa kanta shi zai fishsheta kuwa?
Ta fara ƙoƙarin cire hannunsa a ƙirjinta dan ta samu ta bar gadon amma sai ta ji ya sake mannata jikinsa yana faɗin "sleep"
Ta yi shiru tana ƙyafƙyafta ido a cikin duhu, ƙirjinta yana bugawa da ƙarfi ƙarfi.
Kusan minti biyar ta sake yunƙurin barin gadon, nan ma aka sake jawota baya.
"Sal... Sallah zan yi" ta faÉ—a da dasashshiyar muryar bacci.
"Please stay a few minutes"
Ta yi shiru tana sauraron bugun zuciyoyinsu da kusan a tare yake bugawa.
Kusan minti uku suna haka sai ta ji yace "kada ki tursasawa kanki abinda ba kya so. Kada kiyi abinda zai jawo miki baƙin jini a gurin jama'a. Bilkisu a gidan da ake siyasa ta taso, she has it in her. Duk abinda take yi tana yi ne saboda tana son yi, she's inlove with politics tun kafin muyi aure. Background ɗin ki aikin jarida ne, kada ki sa kanki cikin abinda baki da masaniya akai"
Asiya tayi shiru tana nazarin kalamansa.
"Asya siyasa akwai ruÉ—u acikinta"
"Ba ka so na shiga harkar siyasa saboda inada ƙayyadadden lokaci a wajenka ko?"
"I want to protect you"
Asiya ta ce "Allah protects me. Duk abinda zai same ni yana cikin ƙaddarata ne"
"Akwai abubuwa dayawa da baki sani ba Asya. Zai fi kuma idan baki san su ba"
Ta jaa dogon numfashi saboda abinda take son faÉ—a yana da nauyi.
"Kafin Umma ta rasu tace bata yafe ba idan na kashe aure na"
Ta yi shiru tana tunanin yadda zata faÉ—i sauran maganar ba tareda ya mata wani fahimta ba.
"Zaki zauna dani ne saboda Ummanki?"
Ya katse shirun na su.
Ƙila da suna fuskantar juna da bazata iya faɗin abinda tayi niyya ba, amma akwai duhu, sannan ta bashi baya ne.
"I want to help my husband... zan zauna da kai saboda na samu albarkar aure"
Ya gane sarai mi take nufi amma sai yace "albarkar aure fa haihuwa kenan"
Da sauri ta tureshi ta bar gadon saboda ya sassauta riƙon da ya mata.
Kunna wutan ɗakin yai, hakan ya sa ta gane hanyar banɗaki tayi ba ƙofar fita ba.
"A banÉ—aki za a fara neman albarkar ne?"
Ta sa hannu biyu ta toshe kunnenta sannan ta fice daga É—akin da sauri.
Gwamna Saifuddeen yai murmushi mai sauti.
Soyayya takan iya shiga mutum sannu a hankali, kamar soyayyar sa da Misturah. Akwai kuma soyayyar da take iya shigar mutum farat É—aya, sannan ta dabaibaye zuciyar mutum ta hana shi sakat.
Soyayyar Asiya ta masa shigar kwab É—aya ne. Kamar da wasa ya dinga tunaninta a lokutan da bai shirya ba.
Kafin wannan rana da murmushinsa ya zamo silar buɗewar wani babi daya jima da rufewa a zuciyarsa. Ya san 'yar jarida Asiya Shahidah Faruƙ Baba saboda muryarta da ya zamo shaidarta a duk lokacin da take bada rahoto. Bai taɓa ƙare mata kallo ba, sai wannan rana mai tarihi.
A wani É—akin taro yake zaune shi É—aya yana huci saboda shirmen da aka gabatar masa ya sa shi koran duk wanda yake zaune a É—akin taron.
Tunanin mi ya kai shi harkan siyasa yake bayan mutanen da suke zagaye da shi kusan kaf É—insu Aljihunsu suka sani ba wai yadda za a inganta rayuwar talakawa ba balle har a kawo cigaba mai amfani a Jahar ta su.
Gilashin daya zagaye É—akin taron mai duhu ne, na ciki zai iya kallon na waje amma kuma na waje ba zai iya kallon na ciki ba.
Tafiya take ita da wani saurayi wanda yanzu ne ya fahimci saurayin lokacin CY ne.
*"Yanzu sai ace dan ganin Gwamna na yi kwalliya. Mi ma ya kaini saka jambaki... mtsww"*
Ta ciro hankerchief a jakarta ta shiga goge bakinta, sai data gama gogewa ta shiga tura baki, ta turoshi gaba, ta baje shi, ta ƙumbushe shi, duk dan ta saita bakin nata.
Ganinta a wajen ya sashi yin murmushi, ƙila da ta san ana kallonta da baza ta yi wannan shirmen ba.
*"Aseey lets go now"*
CY ya faɗa da ɗan ƙarfi.
Ranan suka fara zuwa neman izinin interview da Gwamna.
Wannan murmushi shine mafarin komai. A rannan haka ya wuni da nishaÉ—i, duk lokacin daya tuno da 'yar jarida Asiya sai ya É—an murmusa.
***
Kwanaki biyun Asiya tayi su ne cikin sassauta zuciyarta ga mijinta. Ba za ta ce tana son shi ba, amma tunda ta shirya gyara aurenta dole ta yi duk abinda ya dace dan ganin bata yi wasa da damar ta ba. A rana ta biyu da ta saka filo a tsakiyar gadonsu Gwamna ya faɗa mata maganar da ya sata kunya sannan ya sata tunanin anya bata ƙwaran wannan bawan Allah.
"Ki kwantar da hankalinki, ba gangan jikin nake so ba. Duk lokacin da zuciyar ki ta buga saboda Saifuddeen ke da kanki zaki cire waɗannan" ya ƙarisa maganar yana nuna pillow data jera...
Duk shirye-shiryen da ake Bilkisu Kachallah bata san Asiya zata yi Kamfen ba. In fact ranan Asabat da sassafe ta fita saboda akwai wani sabon kayansu da aka shigo da shi saboda zaɓe.
Ƙarfe takwas Asiya da tawagarta suka fita zuwa wajen taron da suka shirya. Queen Bee, Halima Kachallah, Mahirah SSK, Sa'ad SSK, Nawwarah Isa Kachallah sune suka takawa Asiya baya. Yayinda Yaya Bello ya zamo Chief security na Asiya, sai CY ya zamo Campaign Director.
Taro ne na manyan mata, matan talakawa har ma da nakasassu.
***
"Wannan da kike gani, idan mutum ya sha ɗayan sa zata kai shi awa ashirin da huɗu bai nemi komai ba. Wannan na wanda zasu kasa su tsare akwatunan zaɓe kenan"
"Ya za ayi a raba musu ba tareda sun san cewa da wannan manufar za a basu ba?"
"Inaga a fara sayar da shi a farashi mai rahusa. Idan lokacin ya zo sai a basu shi kyauta, bayan zaɓe komai ya lafa sai a siyar da shi a farashi mai tsada saboda lokacin jininsu ya saba da shi, idan ba su samu ba ba za su taɓa jin daɗi ba"
"Ka tabbata kuÉ—inmu zai fito?"
"Sosai ma Excellency"
"Shikenan"
Wayar Bilkisu yai ƙara. Ganin Madam Bintu ya sa ta sallami manager ɗinta.
"Hello"
"Bilkisu kina ina, Asiya ta fara kamfen?"
"Kamfen kuma?"
"Ki kunna TV ki ganta da idon ki"
Bilkisu hannu na rawa ta chanja tashar tv dake ofishinta zuwa tashar Congo News.
Asiya na tsaye jikin podium ta yafa gyalen tutar jam'iyya, tana sanye da dogon riga shadda da ya sha aikin hannu kalalolin tutar jam'iyya. Babu kwalliya na azo a gani a fiskarta amma tayi kyau na É—aukan hankali.
"Ba za mu yi alkawarin kawo chanji ba, saboda ba abinda zamu iya chanjawa a wannan jaha. Ni da ku da ma waɗanda suke gida mun san mi ya kamata mu yi jahar Congo ta samu cigaba, ta samu haɓakar arziƙi. Dan haka muna muku alƙawarin Insha Allahu Gwamnatin Saifuddeen Kachallah zata haɗa hannu da ku saboda mu taru mu gyara jahar mu mai albarka..."
Idon Bilkisu ya hango Junior da ke tsaye gefen Asiya yana wasa da bindigan roba. Kamar haɗin baki kuma sai aka hasko matan dake zaune gaba-gaba inda ta ga ƙanwarta da kuma 'yarta Mahirah.
Ta taɓa zuwa Kamfen da Mahirah amma Halima Kachallah cin amanar da zata mata kenan?.
Ganin an hasko mutane suna ihu suna kiran sunan Asiya ya sa Bilkisu Kachallah ta buga teburin gabanta da ƙarfi tana faɗin "ba zan taɓa bari ta fini haske ba"
A ɓangaren Yallaɓai da Alhaji Sani Kachallah duk sun saurari speech ɗin Asiya.
"She's a very good political orator" Yallaɓai ya faɗa yana shafa gemu.
"She's eloquent" Alhaji Sani ya faÉ—a bayan ya gama ganin speech É—in.
A ɓangaren Umaru Kwom ma ya ga speech ɗin hakan kuma ya sanyaya masa jiki, musamman daya tuno kalaman Asiya a waya.
Ubayd da ke zaune a office kuwa ajiyar zuciya ya sauke yana faɗin gaskiya ne da aka ce tsakanin miji da mata sai Allah. Kwanan baya a wannan office ɗin ta ke iƙirarin zata tarwatsa shi, yanzu kuma gata tana faɗin tana tareda mijinta ɗari bisa ɗari. It hurts, amma ya zai yi tunda Allah ya riga ya rubuta Asiya ta Saifuddeen Kachallah ce...
16
Gwamna na office ɗinsa yana kallon talabijin wayarsa ta hau ƙara. Ya ɗau wayar.
Daga ɓangaren Yallaɓai yace "da tun farko ita ka bari ta jagoranci tafiyarka. Ina maka albishir, mun samu ƙarin sponsors biyu dalilinta"
"Don't bring her into this" Gwamna ya daka masa tsawa.
"Don't underestimate her. Ka bata dama, zaka sha mamaki"
"Kar ka..."
Yallaɓai ya kashe waya ya bar Gwamna da baki buɗe.