← Book details Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 37

Sashe 5

Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gwamna yana duba wasu takardu COS ya shigo ya sanar da shi zaman da aka yi bai yi wani tasiri a case ɗin da aka yi ba kuma House gobe za su kada ƙuri'a ko a fara trial ko kar a fara .
Gwamna yai kaman bai ji shi ba ta hanyar sako zancen wani project da yake so ya fara.

A chan gidan Mr Silas ana jimamin rashin ganinsa sa da ba ayi ba tun daren jiya.
A ɓangaren mutanen Umaru Kwom ma sun shiga ruɗu saboda suna tunanin za su sameshi daren jiya akan za a kira shi shaida a kotu sai suka tarar baya nan, kuma ba a san inda ya shiga ba. An riga an biya shi Miliyan biyu saboda aikin da zai yi. Sai gashi kuma ya saɓa alƙawari.

Gwamna daga office Rehab center ya wuce inda aka kai Nana. Ita Zunnairah ƙasar waje mahaifiyarta ta kaita.
Sai yanzu da Nana ta shiga withdrawal stage ya ganta cikin yanayi na hauka ya ji hankalinsa ya tashi fiye da ma lokacin da ya gano tana shaye-shaye.
Zuciyarsa a cunkushe ya dawo gida bayan ya mata addu'ar samun lafiya.
Yana shiga falonsa ya tarar da Asiya tana zaman jiransa.

"Mi kike nema?"

"Ina so Dan Allah ka bani dama naje Lagos"

"Kin saba yin abinda kike so"

"Ka yi haƙuri" ta faɗa tana kallon ƙasa saboda ba za ta iya dubansa ba, tana buƙatar zuwa Lagos ko akwai abinda za ta iya samowa akan Lami Ninja.

"Akwai abinci a dining ko na kawo nan?" Ta faÉ—a lokacin da take shirin shigewa. Bai amsa ba ya wuce ya barta tsaye.
Bisa mamakinta tana cin abinci da junior ya zo ya zauna ta serving nashi. Har suka gama ci Bilkisu bata ɓullo ba, kamar ma bata gidan.

Lokacin da ta shiga É—aki ta fara haÉ—a kayanta Sumayya ta tambayeta ina kuma za ta je, tace mata Lagos.

"Anty Asiya kinada gajen haƙuri Allah. Yanzu ana cikin matsala za kiyi tafiya, idan wani abu ya sameki fa"

"Ba ruwanki da ni, ba zan iya zama komai ya lalace ba"

*"Kinada taurin kai Asiya, Ba kya jin shawara a rayuwarki, babban matsalarki kenan"* ta tuno kalaman Ubayd.

Ta zauna bakin gado riƙe da gyale a hannunta. Sumayya tayi gaskiya, Fou'ad yace zai nemeta idan ya samu evidence, C Y yace mata ta kwantar da hankalinta akwai abinda ya samu amma sai ya tabbatar da komai zai gaya mata. Miyasa ba za ta iya jira ba?

4

Wani ƙyamusasshen mutum ne zaune a kan Buzu yana muimui da baki alamar yana magana da Ruhanai ko Aljanu.
Ya kai kusan minti biyar yana buga ƙasa, yai rubutu akan ƙasar da ke kan wani faifai ya share, ya sake wani rubutun nan ma ya share.

Bayan ya gama bincikensa sai ya ɗago ya kalli mutumin dake gabansa yace "Akwai wata mace a jikinsa, tana da ƙarfi sosai, tauraronta yana da haske. Matuƙar tana tare da shi sai dai bai nemi abu ba amma yana nema, ya samu. Ita ɗin irin matan nan ne da aka haliccesu da baiwa, duk wanda suka raɓa sai rayuwarsa ta chanja, irinsu da za su auri faƙiri da bashi da anini, to da sannu sai ya samu wadata"

"Malam wace macece kenan? Matarsa ce ko 'yarsa, ko kuma wa? Sannan kana nufin Umaru Kwom ba zai samu nasara ba?"

Mutumin ya ƙyalƙyale da wata irin dariya marar daɗin ji, idan ka saurari dariyar da kyau ka ɗauka tsuntsuwa ce ke kuka.
Bayan ya gama dariyar sai kuma ya haɗe rai kamar bai taɓa dariya ba.

"Kai! Ubangiji kaɗai ke da sanin Gaibu. Wacece ita? kamanninta, ina take? Banida amsar su. Abunda aka faɗa mini shine, ita ɗin kariya ce a gareshi kuma zai ɗaukaka fiye da tsammani matuƙar tana tare da shi. Kabar batun tsige shi, an hasko mini shi akan kujerar mulki"

Mutumin da aka faÉ—awa maganar ya shiga ruÉ—u yana neman agaji ko akwai abinda za a iya yi. Malam Nawaso ya fatattake shi daga wajen, yana faÉ—in shi aikinsa yana da iyaka, kuma ya riga ya faÉ—a masa abinda ya zo tambaya.

Tunda ya bar wajen Malam Nawaso, ya shiga jujjuya maganar a ransa, yana neman ta yadda zai faɗi maganar ba tareda ya ɓatawa Umaru Kwom rai ba.
Lokacin da ya isa gidan Umaru Kwom, kasancewar akwai kusanci tsakaninsu bai tsaya wata-wata ba aka masa iso a falon Alhaji Umaru Kwom.

A ƙasan carpet ya zauna yana jiran fitowar Maigidansa. Minti bakwai sai ga Alhaji Umaru Kwom ya fito sanye da farar riga 'yar shara da wando. Tun kafin ya zauna mutumin ya shiga yi masa kirari yana faɗin sai ka yi Gwamnan Jahar Congo.
Umaru Kwom ya zauna akan kujera ya ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya yace "Bature kai ne da dare haka. Fatan ka taho min da labari mai daɗi"

Bature ya haɗiyi yawu maƙwot sannan ya fara washe baki yana zuba bayanin da ya tsara kafin tahowarsa.

"Ai Excellency, Malam Nawaso ya kai inda mutane suke maganarsa. Yace akwai nasara a tafiyarka, sai dai kuma..."

"Ka faÉ—i koma minene, ba yau muka fara jin labarai marasa daÉ—i ba "

Bature ya kaɗa baki ya cigaba da bayani " ya faɗamin cewa ɗaya daga cikin matansa tana da asiri mai ƙarfi a tattare da ita, ba zata taɓa bari Saifuddeen Kachallah ya faɗi a zaɓe ba. Yace ba za a tsige Saifuddeen Kachallah ba, sannan idan lokacin zaɓe ya zo za ta yi komai wajen ganin mijinta ya ƙara hawa kujera"

Jiki na rawa Umaru Kwom yace " akwai mafita? wani mafita ya bayar? sannan waccece a cikin matan nasa?"

Bature ya gyara zamansa, ganin haƙarsa ta soma cimma ruwa.
"Ai wato Malam Nawaso bai bayyana wacece a cikin matan ba, amma inaga ba zai wuce Bilkisu Kachallah ba dan matar nan da ka ganta ka ga hatsabibiya"

Ya karya murya ya cigaba " Malam ya buƙaci wasu abubuwa da za ayi amfani da su wajen yaƙar wannan Asirin. Yace akwai sadakar da zai sa ayiwa Aljanu kaman miliyan goma, saboda su dinga yi maka addu'a har ranan zaɓe"

"Nawa yake buƙata?"

"Ranka shi daɗe ya buƙaci kuɗi dayawa fa" Bature yai maganar yana sosa kai.

"Na ce nawa ne?"

"Miliyan goma cash"

"Shine kuÉ—i dayawa. Zan sa a haÉ—a maka shi gobe da safe sai ka kai masa. Ka tabbatar yayi duk abinda ya dace"

Bayan tafiyar Bature. Umaru Kwom ya zauna yana nazarin waccece a cikin matan Saifuddeen. Wani zuciyar na riya masa cewa Bilkisu Kachallah ce, amma kuma Asiya ma akwai alamar tambaya akanta. Yana da labarin ita ɗin jikar wani babban malami ne maiƙusumbi. Malaman zaure kuma akwai su da sirrika, ƙila kafin Kakanta ya rasu ya bata wasu laƙanin ƙarfi. Bai manta yadda take masa magana babu tsoro bare wani ɗar ba jiya data kira shi. Koma minene dai wannan zaɓen sai ya lashe, ko ta yanene...

***

"Baba, mi kake yi akan wannan zancen?. Monday fa House za su voting, kuma kasan saboda wannan abun waÉ—ansu sun fara maganar kar a bari Saifuddeen ya tsaya takara. Primary election is this Saturday amma saboda wannan abin an sake kaishi wata sati. I can't stand this"

Bilkisu ta faÉ—a cike da damuwa a ranta, abu É—aya da zata iya yi ta warware wannan maganar kuma zai iya jawo a bankaÉ—o nata sirrukan, shima kuma scandal ne da zai kawo wa Saifuddeen matsala a kujerarsa.

"Kin san dai ba zan zuba ido a tsige Saifu ba ko, dan haka ki kwantar da hankalinki"

"Baba there's no time"

" na yi waya da shugaban ƙasa, sannan mun zauna da party chairman na ƙasa, sun tabbatar mini House zata dismissing trial ɗin. Matsalar da zamu fiskanta shine, dole kotu ta wanke Saifu kafin zaɓe idan ba hakaba, zamu bar giɓi mai faɗi da Umaru Kwom zai yi amfani da shi wajen Kamfen"

"Indai aka warware maganar impeachment shikenan, sauran mai sauƙi ne"

Da haka ta ɗau kofin shayi ta kai bakinta ta kurɓi kaɗan, zafin daya ratsa harshenta ko kaɗan bai kai zafin da take ji a zuciyarta ba, saboda fargabar barin kujerar first lady of the state.

Zumar da ke ƙunshe cikin kujerar Mulki tanada wuyar sha'ani, saboda zaƙi da daɗinta. Da ka ɗanɗana, ko da ɗan kaɗan ne, to sai kayi da gaske kafin ka iya rabuwa da shi.
Alhaji Sani da 'yarsa dukkansu sun ɗanɗani zumar Mulki kuma sun san zaƙinta, ba abinda suka rasa na kuɗi da dukiya amma Mulki...suna son wannan Mulki ya kasance na su, har zuwa lokacin da aka ɗiba.

Yayinda ake cikin wannan kuma, an sako Mr Silas ya dawo gida.
Mr Silas ya sha bugu a hannun Yaya Bello kafin ya faÉ—i gaskiyar lamarin abinda ya faru shekaru shabiyar da suka wuce.
Lami Ninja ce ta biyashi kuɗi akan ya bar mata ƙofar ofishin Prof Kachallah a buɗe. Sannan shine ya tsaya stand by akan idan Saifuddeen ya fito ya saka masa ihu, ya tara masa mutane. Domin idan ya amince da buƙatarta ita zata fara fitowa daga office ɗin ba shi ba.

A ranan da Lami ta far wa Saifuddeen, da ƙyar ya samu ya turata gefe ya buɗe ƙofa ya fita, yana fitowa Mr Silas ya tareshi a bakin ƙofa yana faɗin wai ya ji ihun mace a cikin office ɗinsa. Lami na jin Mr Silas ya iso ta saka ihu tana kuka tana kururuwa, hakan ya sa Mr Silas ya riƙe Saifuddeen yana yekuwa har mutane suka taru. Da ke Saifuddeen bai iya magana cikin hayaniya ba haka aka fara maida zancen ƙarya, ya kasa kare kansa. Lokacin da aka yi case ɗin ya ƙaryata abinda ya faru amma duk da haka an rufe case ɗin ne ba tareda an yi dogon bincike ba saboda akwai masu yiwa Saifuddeen hassada cikin Malaman faculty ɗinsu...

Mr Silas na dawowa kuwa wasu mutane suka zo suka tafi da shi gaban Umaru Kwom.

Ya sha bugu kam dan ƙafafuwansa da ƙyar yake taka su. Ga bayansa da yake ji kamar an fafe ne aka bar masa ƙashin bayan kawai a waje.

"Mi suke buƙata a wajenka?" Ko bai tambaya ba ya san cewa Bilkisu Kachallah ce da wannan aikin.
Chapter 5 · 0% Book details