← Book details Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 37

Sashe 22

Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai kuwa yana É—aurawa ko minti biyar bai kai ba Asiya ta gani, dama ta jona wifi na gidan tana aiki da wayarta dan haka tana ganin notification daga www.kasasapoems.com ta yi saurin buÉ—ewa.
Sai da ta karanta waƙar sau uku tana nazarin ma'anar waƙar wanda yai kama da yanayin da ta shiga lokacin da Gwamna ya kissing ɗinta.
"Allah kaɗai ya san wacece KaSaSan nan. She's a good poet amma ko mi yasa take ɓoye kanta oho" Asiya ta furta a fili.

Gaba ɗaya ranan wasan ɓuya Asiya ta yi da Gwamna dan bata bari sun haɗu ba kwata-kwata, ɗakinta ma kullewa tayi saboda kar ya mata shigowar bazata irin wadda yai da safe.

Washegari Sunday bata san da yaushe ya fita ba, hakanan kamar tare suka fita da Bilkisu.
Sai da ta karya, kusan ƙarfe shabiyu na rana ya turo mata saƙo.
"Na fita bamu gaisa ba, mijin Rufaidah ne Allah ya masa rasuwa yau da Asuba. Ba zan dawo ba sai dare"

Rufaidah dai yayar Bilkisu Kachallah ce, idan haka ne ai dole ta je musu ta'aziyya, sai dai bata san ina ne gidan ta ba.

Tura masa saƙo tayi masa ta'aziyya tareda tambayarsa tana son zuwa gaisuwa.

Ya mata reply da cewa zai turawa Bello address ɗin sai ya kaita gidan da yamma dan a gidan iyayensa ake karɓar gaisuwa.

Ƙarfe biyar Asiya ta shirya ta kira Sumayya da ke ƙunshe a ɗaki tun safe, tace ta zo ta rakata gidan rasuwa.

Lokacin da suka je gidan ta ci sa'a ta ƙofar baya mata ke shiga dan maza sun cika gaban gidan. Niƙab ta sauke ta fito daga mota suka shige gidan.

An cika gidan maƙil saboda mamacin shima wani ƙusan Jaha ne, ɗan babban gida ne kuma ta wajen Uwa yanada haɗi da familyn Kachallah.
Asiya ta isar da ta'aziyyarta ga iyalen mamaci, ta ɗan zauna kaman na minti goma shabiyar sannan ta tafi. Ta haɗu da yayye da ƙannen Bilkisu a wajen amma bata ga Bilkisun ba...

***

*"mace bata juya mace. Musamman wanda taurarinsu ke da ƙarfi. Dan haka dole maza uku kawai za ki iya juyawa. Idan mace ta taɓa zoben gaba ɗaya aikin zai warware"*

Matar da aka yiwa kashedin nan ta tuno da kashedin da aka mata lokacin da aka bata zoben nan. Gashi mutum biyu da take son juyawa sun taɓa zoben amma zuwanta gidan rasuwa ya sa aikin da aka mata a zoben ya warware.
Da ta sani da bata je gidan rasuwan nan ba sai data cika dukka sharuɗɗan Shri Hari Bansari. Kafin zoben nan ya isota daga ƙasar India kusan sati shida kenan.

Ta kira wanda ya haÉ—ata da Shri amma yace ana cikin ranaku masu mahimmanci a lissafin taurari dan haka Shri baya magana da kowa yanzu har sai kwanakin nan sun wuce tukunna.

Tanada tabbacin zata samu cikar burinta da zaran ta iya juya waÉ—annan mutane uku.

Ta furzar da iska mai zafi tana tunanin sai yaushe ne zata samu cikar burinta?...

***

Da dare Asiya ta jira isowar Gwamna amma shiru har shaÉ—aya hakan ya sa ta kwanta duk da kuwa akwai maganar da take so suyi koda kuwa tana kunyar haÉ—uwar ta su.

Washegari da sassafe ta shiga sashen Gwamna ta wuce ɗakinsa saboda ta ji fitarsa sallar Asuba. Gyara masa ɗakinsa ta yi sannan ta fito, ganin Safiyya ta fara gyara falon na shi sai ta haƙura ta sauka ƙasa dan ta je ta haɗa masa abin karyawa. Cook ɗin gidan ta lura kaman ma kishi yake da ita, dan duk lokacin da tace za ta yiwa Gwamna girki sai ta ga yana tsumewa.
Lokacin da ta gama komai Safiyya ta tayata É—aukowa, suka shirya komai a dining É—in falonsa.

Daga inda take shirya plate ta jiyo muryan Bilkisu tana magana sama-sama.

"Ban gane daga yanzu kwana bibbiyu zaka dinga yiwa kowa ba. Don't tell me ka fara kwana da ita. Magana nake maka Saifuddeen, did you sleep with her?"

Bata jin maganar Saifuddeen saboda a hankali yake tasa maganar.

"You told me you married her for political reason. Kace da zaran komai ya lafa zaka rabu da ita. Miya kawo maganar haƙƙi kuma yanzu?, answer me... answer me"

Kaman zata bar wajen jin an buɗe ƙofa sai kuma ta tsaya dan dole ne ayita da wajewa. Kalaman Bilkisu sun kaɗata amma yanzu ba da bane, dole ne ta ji daga bakin shi kansa Saifuddeen ɗin kafin ta zartar da hukunci.

"Asya" Ya kira da sigar mamaki dan bai tsammanci ganinta a wajen ba.

"Saifud..." Bilkisu ta yi shiru ganin Asiya a wajen.

Wani abu ne ya ɗarsu mata a zuciya lokacin da suka haɗa ido da Asiya. Kamar yadda Tsu Zhang ya faɗa, Shri Hari Bansari ma ya sake jaddada mata cewa matuƙar Asiya ta rabu da Saifuddeen to ba zai ci zaɓe ba, sannan ba zai sake yin kowanni irin mulki ba. Dan wannan ne kaɗai ta ke daurewa da kasancewar Asiya a matsayin Matar Saifuddeen, koma minene yarinyar ke da shi ba zata taɓa bari yai tasiri a jikin Saifuddeen ba, saboda kar a samu matsala idan ya shimfiɗa sabon Gwamnatinsa.

Ganin irin kallon da Bilkisu ke mata yasa Asiya ta matsa gefen Gwamna ta sa hannunta cikin nashi tace "Maman Nana an tashi lafiya?"

"Maman Nana?. How dare you insult me"

"Insult you? How? baki da 'ya mai suna Nana ne?"

A wajen Dadda ta ji gulman wai Bilkisu bata so a kirata da Maman wane ko Maman wace saboda hakan na nuna tsufan mutum.

Bilkisu ta kalli Asiya sannan ta maida dubanta ga Gwamna tace " ina nan ina jiranka"

Bayan fitar Bilkisu Asiya tayi ƙoƙarin cire hannunta cikin na Gwamna amma sai ya riƙe gamgam yana faɗin " not so fast"

Ta sunkuyar da kai tana jin kunyar abinda ta aikata. Bai sake hannunta ba har sai da ya zauna a kan kujera yace "na makara, amma zan ci koda kaÉ—an ne"

A gurguje ta zuba masa farar shinkafa da kuma farfesun kaza ta haÉ—a masa da fresh apple and pineapple juice data haÉ—a.

Yana cikin ci ya riƙo hannunta yace "naga saƙon ki jiya, kiyi haƙuri meeting ne ya riƙe ni shiyasa ban dawo da wuri ba. Mi kike buƙata?"

"Kana sauri ai, zamu yi maganar idan ka dawo?"

Ya ajiye sokali yace "ba abinda ya fi sauraron buƙatar ki mahimmanci yanzu, anything else can wait"

Wani murmushin jin daɗi ne ya kuɓuce mata. Saboda bata tsammanci zai saurareta ba.

Da ƙyar ta iya haɗa kalmomin bakinta saboda har lokacin hannunta ɗaya na cikin nashi. Sannan bata san mi zai ce ba idan ya ji buƙatar tata.

"Minene?"

Asiya ta ja dogon numfashi sannan tace " ina so na maka kamfen"

Cike da mamaki yace "miyasa?, besides saura sati huÉ—u a rufe Kamfen ma"

"Idan Bilkisu zata maka kamfen miyasa ni ba zan maka ba? Ko dai maganarta gaskiya ne, you married me ONLY for political reason?" Ta ƙarfafa kalmar only ɗin saboda da gaske tana son sanin ko shi kaɗai ne dalilin.

Maimakon ya bata amsa sai yace "zan yi magana da Bello, za a haÉ—aki da securities naki sannan Dan Allah ki kula da kanki"
Miƙewa yai zai tafi tace "Dan Allah ka ƙarasa abincin"

Juice ɗin kawai ya kurɓa ya wuce ya barta a wajen...

15

Ƙarfe biyu na rana Queen Bee ta shigo wajen Asiya.

"Kai! ƙawalli irin wannan tsaro. Kin san sai dana nuna musu hoton da muka ɗauka dake ranan dinner. God! Mulki akwai daɗi, yanzu ni da bestie ɗina sai an yi bincike kafin a barni na shigo na ganki"

"Yi haƙuri, ban san zaki zo ba dana sa an musu magana" Asiya ta faɗa tana miƙa saboda bacci take aka kirata wai tayi baƙuwa.

Queen Bee ta tsaya kallonta har da taɓe baki.

"What!" Asiya ta faɗa tana riƙe ƙugu.

"Shahidah tell me the truth ciki gareki ko?"

"Ungo naki Bahijjah, ke kika min cikin ai"

"Seriously bestie kin yi ƙiba. Yaushe ne na ganki a Asibiti kaman skeleton amma gashi yanzu kin cicciko ta ko'ina. Kin ga wuyar ki kuwa?"

Asiya ta sa hannu ta fara shafa wuya tana faɗin Allah bata yi ƙiba ba.

Bayan sun nitsu, aka kawowa Queen Bee abin taɓawa ta buɗe ciki ta fara cin pepper chicken da aka kawo mata da kuma cupcake sai Berryblast 5alive.

"Zan shirya kamfen wannan saturday, ina buƙatar taimakon ki"

Queen Bee ta fara gyaran murya tana tarin shaƙiyanci.

"Bana son iyashege. FaÉ—i son ranki bana son kame kame"

"Allah! Allah!. Bari dai nayi shiru. Kai wannan abu da mamaki yake. From --- ni ban san mi kuka gani ajikin wannan tsohon ba. Allah ya sawwaƙa na crushing ɗinsa. Uban wa ya isa ya haɗa shi da My Ubayd..."

Asiya ta wurga mata filo tana faÉ—in "Bahijja kinci gidanku"

Queen Bee ta fara dariya tana faÉ—in "ina son irin wannan soyayya"

Sai da ta ga Asiya ta ɓata rai kafin ta dena tsokalarta.

Suna zaune Sumayya ta zo ta wuce su bayan ta gaishe da Queen Bee a tsaitsaye.

"Yaushe Sumayya ta dawo haka?"

"Mi kika gani?"

"Mi na gani? Da haka take yi idan ta shigo? Tukunna ma shiga jami'ar ne ya sata chanja shiga, baki ganin a kafaɗa ta lanƙaya gyalenta ne?"

"Hmmm. Kin san dai ko kai ka haifi ɗa sai dai ka tsawatar masa sannan ka masa addu'a ko?. To ni dai yanzu sai addu'a dan idan nace zan yi magana raina ne kawai zai ɓaci"

A hankali ta warware mata yadda komai ya faro da kuma matsayin da suke yanzu.
Queen Bee ta taɓe baki tana jimamin wannan batu, daga ƙarshe itama ta bata labarin wata 'yar yayarta da ta falle kwanan baya, ƙarshe ma taje haɗuwa da wani saurayinta ne babban yayansu ya hangota ta shige gidan ya bi bayanta, ya mata shegen duka ya tiso ta gida.

"Ban faɗawa Yaya Bello ba saboda na san dukan kawo wuƙa zai mata. Kuma Excellency yace na bita a hankali"

"Ehm ehm, Excellency manya"

Asiya ta watsa mata harara...
Chapter 22 · 0% Book details