Sashe 34
Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Asiya bata ma yi yunƙurin zuwa wajen inauguration ɗin ba tunda taga duk abinda ake uban gayyar bai sakota ciki ba. Ranan da ta kira dan ta masa godiyar biyawa Ale da Abba kujerar hajji da yai ƙin ɗaukar wayarta yai. Ta yi kwanaki tana nemansa ya ƙi ɗaga wayarta, ko ta'aziyyar Dadda sai text ta masa. She yearns for him, she longs for him, she misses him. Daga ƙarshe zuciyarta, gangan jikinta da ruhinta duka sun zama mallakinsa. Yanzu kam babu tantama ta san wannan shine gaskiyarta.
Ta dage da addu'a sosai musamman da zuciyarta ya fara bata cewa ƙila da gaske ne akwai hannun Bilkisu Kachallah a chanjawar Gwamna Saifuddeen. Sai dai kuma Allah yana amsa addu'ar bayinsa a duk lokacin da suka roƙe shi, zai iya yiwuwa a jinkirta amsar saboda wani dalili mai girma da kai baka sani ba, Allah shine masanin gaibu. Shi ya halicceka shine kuma ya tsara rayuwarka ya kuma san mi ya dace da kai yaushe kuma ya dace ka samu.
Asiya ta banzatar da shawaran Jummai na yin sadaka. Mafarkin da ta gaya mata, ba yarda dashi tayi ba balle kuma har abin ya dameta...
A falo Asiya, Jummai da kuma Sumayya suka zauna suna kallon rantsarwar da ake yiwa Gwamna Saifuddeen Sa'ad Kachallah.
Duk wani motsawar laɓɓansa lokacin da yake rantsuwar yana kan idon Asiya ko ƙyaftawa na dole take saboda tana son ganin duk wani motsinsa.
Bayan an gama rantsuwar suka wuce wajen da za ayi inauguration party É—in wanda tun da sassafe ake ta nuna highlight na yadda aka shirya wajen.
Asiya miƙewa ta yi da sauri saboda ganin Bilkisu Kachallah ta riƙe hannun Gwamna tana dariya, shima yana ɗan murmusawa.
Kusan ƙarfe goma shabiyu na rana Queen Bee ta kira wayar Asiya.
"Bestie ashe Gwamna shine KaSaSa" ta faÉ—a da muryan da yafi kama da ihu.
"Ban gane ba?"
"Ba kya kallon TV ne, yanzu Bilkisu Kachallah tace Gwamna ɗan baiwa ne cikin baiwar da Allah ya bashi akwai rubutun waƙa, wai yafi shekara ishirin yana rubutu... yawwa ki kalli tv Dan Allah ya fito zai karanta ɗaya daga cikin waƙoƙinsa"
Kafin Queen Bee ta gama maganar ma Asiya ta riga ta isa gaban TV da ke falonta inda dama a nan tayi kallo da safe lokacin da ake rantsar da shi.
*"Attaruhu"* Gwamna ya faɗi sunan waƙan da zai gabatar, hakan yasa mutane dayawa darawa, wanda basa jin Hausa kuwa suka shiga tambayar ma'anar abinda ya faɗa. Sau biyu ya taɓa performing poem a gaban mutane lokacin da yake degree ɗinsa na farko a ƙasar waje.
Ɗimbin jama'ar da ke wajen suka zuba masa ido suna sauraron waƙar da zai yi amma sai da yai tsayuwar kusan minti ɗaya bayan ya ce Attaruhu kafin ya fara karanta waƙar.
Zuciyar Bilkisu Kachallah ya kai ƙololowar baƙin ciki saboda ba abinda ta shirya ba kenan. Ta bayyana cewa shine KaSaSa saboda abu ɗaya ne kawai, wato ya mata waƙa ya yabeta a idon mutane amma sai ya karanto waƙar da ta sani dan Asiya Shahidah yayi ta. Ta sani harta nambarta a wayarsa ya saving ne da Attaruhu. A da bata ɗauka komai ba amma yanzu kam ko sunan sai ta saka ya chanza a wayarsa. Da ta san waƙar da zai yi kenan da bata bayyana baiwarsa ta rubuta waƙa ba.
Gwamna sai da ya ƙara stanza biyu akan asalin waƙar da ya taɓa rubutawa watannin baya, a ƙarshe ya bayyana zuciyarsa tana dokawa ne ga Attaruhu. Yana gamawa aka masa standing ovation aka rinƙa tafi raf raf raf saboda ya burge kowa a wajen, duk da ma mutanen wajen sun ɗauka waƙa ce kawai yai cikin waƙoƙin daya taɓa rubutawa, amma shi da yai waƙar, Bilkisu Kachallah da kuma Asiya Kachallah sun san wacece ATTARUHU.
Hawaye fal a idon Asiya har bata ganin TVn sosai ta sa bayan hannunta ta shiga gogewa, amma tana gogewa wani na sake gangarowa.
Ta wuce É—akinta da gudu, tana faÉ—awa kan gado ta furta kalmomi ma su tsada gareta wanda ko Yaya Ubayd zata iya tuna sau nawa ta furta masa su. *"I love you Excellency. I love you Saifuddeen Sa'ad Kachallah"*
Bayan tafiyar Asiya Jummai ta kalli Sumayya tace "ni kan Gamna rawa yai ne naga Adda Shahidah na kuka?"
"Ki ji min sharri, rawa kika ga yayi?"
"Yo naga sai jujjuya hannu yake yana ta girgiza kai, kuma sai naga Adda ta fara kuka"
"Allah ya yaye miki Jummai" Sumayya ta faÉ—a bayan ta ja tsaki.
***
Bikin inauguration ya zama abun faÉ—a a gari domin kuwa ko'ina ka shiga sai Allah wadarai ake da irin almabazzaranci da aka yi a wajen. Kwana biyu aka yi ana shagalin bikin, kuma duk ciki babu wanda ba ayi baÉ—ala a wajen ba.
Ga Asiya, wannan sabon yanayi ya sakata cikin nishaɗi, bata damu da yadda aka yi biki ko aka ƙare ba, all that matters shine Gwamna Saifuddeen shine KaSaSa sannan har yanzu yana sonta. Ta maimaita kallon wajen da yai waƙar Attaruhu ya fi sau ɗari cikin kwanaki biyun nan.
A kwana na uku ne kuma CY ya kira Asiya, ya mata wani zance mai tada hankali. BBC eye sun fitar da documentary na masu ciniki da kuma safaran miyagun ƙwayoyi, inda wani mutum da ba a bayyana asalin sunansa ba da kuma fiskarsa ya bayyana cewa yana yiwa matar Gwamnan jahar Congo aiki. Shine agent ɗinta mai shigo mata da miyagun ƙwayoyi ta ɓoyayyiyar hanya.
"I know it's not you Asiya, amma kina ganin Bilkisu Kachallah tana irin wannan harka? Could it be saboda Agent ɗin nan tana bincike akanta yasa aka ɓoyeta"
"Ban sani ba CY, ina ka samu bidiyon?"
"Sun riga sun cire shi a yanar gizo amma na riga na samu videon kafin a sauke shi daga net. I'm having a bad feeling about this, kina ga Gwamna ya sani?"
"Ban sani ba CY, amma zan tuntuɓe shi na ji".
Bayan Gwamna yaƙi ɗaga wayarta, office ɗinsa ta kira, Sakatarensa ya ce mata ai ɗazu Gwamna ya wuce Abuja.
Asiya ta shiga ruɗu tana tunanin wa kuma zata tuntuɓa da wannan zance. Ƙarshe ta ce bari dai ta bari Gwamna ya dawo. Ko bai zo inda take ba ita zata je inda ya ke.
***
"Ina son kujerar Yallaɓai"
Lamara Damana ya zaro ido waje da mamaki.
"I need it fast, saboda tsohon nan yana so ya bani ciwon kai"
"Boss, idan babu Yallaɓai mahaifinki shi zai gaji matsayinsa haka dokan gidan ya faɗa"
"Lamara babu ruwana da dokarsu, abinda na sani shine zan zama shugaban ƙingiyar dattawan Congo, akwai kaso mai tsoka Mr Damana. Mi zai faru idan ka amsa sunan Senator Lamara Damana, kafin nan ma idan na samu kujerar Yallaɓai zan sa shugaban ƙasa ya baka minister, shekaru huɗu masu zuwa ka amsa sunan Senator"
Lamara Damana ya motsa baki yai maganar da ta saka Bilkisu Kachallah kwashewa da wata shegiyar dariya.
***
Daga bakin gate aka fara hayaniya da jami'an NDLEA da kuma securities masu tsaron gidan Gwamna. Sun nuna za su yi bincike su kuma sun ce sai Gwamna ya bada izini, Gwamna kuma baya gari. Fitowar Jami'a Dahlia daga cikin motar ya kawo sulhu domin tana ɗaga badge ɗinta na DEA ta ƙasar America securities ɗin suka shiga rarraba idanu.
Asiya na É—aki Jummai da Sumayya suka shigo É—akinta da gudu dan sun tsorata da ganin jami'ai kusan takwas da ke bin urmurnin wata baturiya wacce suke tunanin ita ce Ogan su.
Asiya ta fito jiki a sanyaye dan yanzu ta gama waya da Fou'ad Salisu kuma duk akan labarin da CY ya gaya mata ne.
"DEA, Maryam Dahlia Aliyu" baturiyar ta faÉ—a tana yiwa Asiya kallon tsana.
Bayan Asiya ta nemi dalilin zuwansu sai jami'ar ta shiga yi mata bayani " mun samu labarin an kawo wasu miyagun ƙwayoyi gidan ki, munada search warrant dan haka ki bamu haɗin kai"
Ta sani babu komai a gidan amma kuma haka kawai sai jikinta ya ɗau rawa, musamman da ƙwaƙwalwarta ya fara hasaso mata possibilities na samun miyagun ƙwayoyi a gidan indai da gaske Bilkisu Kachallah tana safaransu. Dukkan jami'ai takwas suka saka hand gloves a hannunsu sannan suka bazama gidan neman muggan ƙwayoyi.
"Ina so ki sani cewa babu abunda zai hana zuwanki kurkuku matuƙar aka samu hujja akan ki. Ban damu da matsayinki ko ina kika fito ba"
Minti shabiyu sai ga wasu jami'ai biyu sun fito da sauri ɗaya daga cikinsu yana riƙe da farar leda ɗauke da farar hoda.
"We found something"
Da Asiya da Agent Dahlia suka shiga rige-rigen zuwa ɗakin Asiyar bayan jami'in ya ce a ɗakin ƙasa aka samu.
Cikin akwatunan kayanta guda uku aka dinga ciro wasu lejoji ɗauke da farin hoda da wasu abu ƙanana kamar duwatsu.
Kallo É—aya Agent Dahlia ta yi wa kayan tace "cocaine, meth, fentanyl" sai kuma ta É—ago ido tace " you are under arrest Asiya Kachallah"
"Ban san ya aka yi wannan ya shigo nan ba. Ban san wa ya saka a nan ba, ba ni Matar Gwamnar ake nufi ba Bilkisu Kachallah, Bilkisu..." ta haÉ—iye maganar ganin Agent Dahlia ta saka mata ankwa a hannu. Koma mi zata faÉ—a a nan kam bashi da amfani. Taya aka shigo da waÉ—annan kayan aka saka a É—akinta cikin akwatinta amma bata sani ba?
Jiya ta wuni a chan gidansu, saboda yau Abba za su wuce Saudiyya shiyasa ta je masa sallama, komai zai iya faruwa a tsawon awanni biyar zuwa shida da tayi bata gida.
Jami'an suka shiga É—aukan hotunan abinda aka gani da kuma yadda aka same su kafin daga nan suka shiga kwashe kayan suna sawa cikin akwati guda É—aya.
Lokacin da Agent Dahlia ta fito riƙe da Asiya. Sumayya da Jummai sai suka fashe da kuka musamman Jummai da take tunanin mafarkinta ya tabbata Adda Shahidarta zata yi zaman kurkuku.
Kafin kace me gaba É—aya gari ya É—auka.
Matar Gwamna Asiya Kachallah tana safaran miyagun ƙwayoyi. An kama Asiya Kachallah da buhuhunan kayan maye da miyagun ƙwayoyi irinsu cocaine, codein, har da masu cewa buhun marijuana sun fi hamsin aka gani a gidan...