← Book details Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 73

Sashe 66

Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Tunda na fara rubutun wannan book ɗin ban taɓa shiga farin ciki da jin daɗi irin na jiya ba💃💃😇🥳 lallai na yarda masoyi alkhairi ne a rayuwar mutum duk yanda yake🤩 saƙonni daga ko ina sai tuttuɗowa kawai suke😃 dukda dai wasu na rashin jin daɗin haɗin da akayi ne😩 har bacci ɓarawo ma da ƙyar ya samu ya ɗauke ni🥰 yanda kuka saka ni farinciki kuma Allah ya saka ku kwatankwacin shi😍😘*

50🧝🏻‍♀️
Inaso in hana shi, amman zuciyata tana ingiza ni, ina so na dakatar dashi na tuna masa irin wurin da muke amman shine mai controlling ɗina a yanzu, ya tafiyar da tunani na gaɓa ɗaya babu abinda nake gani a gaba na sai shi ina amsan saƙonnin da yake tura ma duka ilahirin jiki na.
Ban gane halin da muke ciki ba har saida Zayyad ya kusan kaiwa ƙasa ƙafafuwan shi sun kasa ɗaukan shi, jikin shi na son tuna mishi har yanzu shi mara lafiya ne bai gama warwarewa ba tukunna.

Saurin saka hannu nayi na riƙo shi ta taimakon ƙarfen jikin gadon da ya kama be kai ƙasa ba, na saka dukkan ƙarfi na don na taimaka mishi ya tashi dai_dai lokacin da aka fara knocking ƙofa.
A hakan dai na taimaka mishi ya koma gadon ya kwanta na gyara mishi kwanciya na rufe shi da duvet sannan maida ɗankwali da gyalena na ƙarasa jikin ƙofar na buɗe.

Fa'iza da Ruma ne rike da niƙi_niƙin basket na abinci sai Sulaiman biye dasu a baya. Hanya na basu suka shige ina musu sannu, alhajin na kwance kaman patient din tsakani da Allah ya saka fiskan tausayi kaman bashi bane ya gama murje ni yanzun nan ba.

Karɓan baskets ɗin nayi na ajiyesu a wurin da ya dace suka miƙo min ƴar ƙaramar jaka wanda kayan da zan sauya yake ciki.
Me suke nufi? Kwana suke so nayi a nan?.
Ban gwada reaction din komai a fuskana ba muka gaisa dasu saidai tun bayan kallo É—aya da nayi ma Sulaiman É—azu ban sake yarda mun haÉ—a ido dashi ba, bansan ma da wani ido zan kalle shi ba tsananin kunyar shi ya gama kama ni.
Kaina a ƙasa na tambayi Fa'iza "aunty Fa'iza ina aunty?"

Murmushi mai sauti tayi tace "ai yanzu na tashi daga kujeran aunty kin hau kin zauna, aunty kuma babban yaya ya tura ta gida sai gobe da safe zata dawo duba ku insha Allah, ina dai babu wani abinda kike buƙata?"

Girgiza kai nayi tare da faÉ—in "babu"
Idanun Sulaiman na kan Zayyad amman kunnuwan shi suna jiyo mishi sautin muryata sai ƙoƙarin yaƙi da zuciyar shi yake yi, 'yanzu ita matar ƙaninka ce, don't feel anything for her please' shine abinda yake faɗa ma kanshi.
"Inaso zamuyi magana dashi, give us privacy please" ya faÉ—a ba tare da ya juyo ya dube mu ba.

Hannu na su Ruma suka ja muka fita daga É—akin sai murna takeyi na yanzu burinta ya cika na dawo cikin su dindindin.
Muna fita Sulaiman ya juyo wurin Zayyad da lokaci ɗaya ƙwalla ya cika a idanunn shi ƙiris suke jira su zubo don har can ƙasan zuciyan shi yake jin guilt ɗin abinda ya faru, yasan yayi ma Sulaiman maƙura na rashin adalci da bai iya danne zuciyan shi ya haƙura ya barshi ya auri boɗɗi ba, ya kasa controlling zuciyan shi ne duk yanda yaso yayi ƙoƙarin cire ta farat ɗaya ya gagara a maimakon haka ma sai koma baya da ya samu saboda tursasawan da yake yi ma zuciyan shi.
Gashi babban yaya ba tare da wani tunani ba yayi mishi sadaukarwan da harga Allah idan da shine ba lallai ya iya mishi ba.

"I'm sorry ya Sulaiman! I'm very sorry" ya faÉ—a kaman zai fasa ihu idanun shi a cikin nashi,
Murmushi Sulaiman yayi ya ɗan buge shi a kafaɗa tare da faɗin "it's ok Zayd, nine ma wanda ya kamata ya baka haƙuri saboda na nuna son kaina sosai, ni mai baka abu ne matsayin ka na ƙaramin ƙani na ba mai kwacewa daga gareka ba, and that's what I finally got to do.
ni babba ne nafika sanin ya kamata, bai kamata ace na bari mace ta shiga tsakanin mu ba, macen ma wanda da babu ita a cikin rayuwar mu a da lokacin da muke gwagwarmaya, tun kafin abubuwa su lalace ya kamata na dakatar da komai but i failed to do so har na barka kaso cutar da kanka"

A É—an firgice yace "wallahi ba abinda kake tunani bane babban yaya, i did not poison myself ko su doctors É—in sunce an samu poison a cikin jini na ne? Nifa musulmi ne nasan hukuncin wanda ya kashe kansa da gangan why would I even do that?"

Lumshe idanunshi yayi bakin shi ɗauke da ɗan ƙaramin murmushi yanda Zayyad ya marairaice ya tuna mishi da lokacin da suke yarinta, idan akayi laifi tun kafin azo a bincika aga waye yayi zai tunkari Sulaiman ya fara rantse_rantse har sai yarda ba shi ɗin ne yayi ba kafin hankalin shi ya kwanta, don dukda yanda suke tare yafi tsoron Sulaiman sau ɗari a kan dadyn su dan shi mutum ne da Allah yayi shi bayi da tsanani.

"Koda sunce min sun gani ba zan yarda dasu ba Zayyad, nasan dukkan abinda zaka iya aikatawa da wanda ba zaka iya aikatawa ba.
And to be honest i love Saudat amman son da nake mata be kai wanda nake maka ba jini na, you are the brother that I love the most kuma har yanzu babu ya kai a wuri na, kaidai ka ci gaba da roƙon Allah ya tabbatar da zaman lafiya da ƙaunar juna a tsakanin mu, Happy married Life bro"

*******
"Ina ne nan?"
"Shima exit ne da zamu iya bi mu fita daga asibitin, yauwa aunty Saudat kinsan me?"
"Meye?" Na tambaya a little bit annoyed ganin yanda suke cikin wani jin daÉ—i da farin ciki kaman ba yayan su bane kwance a gadon asibiti ba lafiya gashi nima sun fito dani yawo, duk girman asibin nan gaba É—ayanta babu inda bamu zaga ba, su ko É—an damuwan rashin lafiyan shin basu ji ne?

"No! bake ba, na tuna yanzu ke baki isa kisa ƙafanki ki fita can..." ta faɗa tana nuna gate "ba tare da izinin yaya Zayd ba, don haka... Aunty Fa'iza kinsan me?"

Girgiza kai kawai tayi Ruma taci gaba da cewa "naga wani gift shop a ƙarshen titin nan, kinga kuma bamu haɗa ma wa'innan newly weds ɗin gift ba, so i think we should go and check it out kafin babban yaya ya fito"
"Ok, amman kuma dare yayi sosai fah Rumaisa, past 11 yanzun idan wani abu ya faru fah? kinsan halin babban yaya"

"Babu abinda zai faru sai alkhairi, da driver zamu je fah ni wallahi bani son tsoron kin nan wani lokaci kema kaman ba teruwa ba"

"Ohk to ki bari ya fito aje a kan idon shi mana sai muga ƙarshen teranci, ƴar rainin sense kawai"

Haba! Abin yaso ya bani mamaki ganin sun haɗu wuri ɗaya ba'a taɓa yar hali ba, ni banma san lokacin da suka fara shiri har haka ba, banyi aune ba sai jin muryar su nayi daga nesa suna faɗin.
"Aunty saudat ki koma ciki wurin angon ki, sai anjima"

Sanyi akeyi sosai shiyasa ban tsaya ɓata lokaci ba na koma ciki gashi ko sallan magriba banyi ba ballantana isha na tsaya ɓata lokaci a jikin Zayyad.
A hanya muka ci karo da babban yaya, har n buɗe baki zanyi mishi magana ya ɗaga kai kaman bai taɓa ganina ba ya wuce, abin ya ɗanyi min zafi kaɗan dan da ko sallama mayi kafin ya wuce.

Shigana ɗakin na samu Zayyad ya shiga toilet, zama nayi a bakin gadon na jira shi ya fito da towel ɗaure a ƙugun shi jikin shi na ɗigan ruwa alamun harda wanka yayi,
Oh gosh, why ne? Me yasa wannan mutumin zai fito gabana ba riga haka?
Yaso ya tsokane ni amman ganin Sallah ne a gaban mu yasa yace
"Babes shiga kema kiyi alwala ki fito muyi Sallah" ya faÉ—a tare da shimfida mana darduma,
Cire jewelries dina duka nayi na saka su a drawer sannan na ajie gyalena na shiga wurin da ya gwada min a matsayin toilet ɗin, tsayawa nayi ina kallon wurin shikkenan ni kuma abinda ƙaddarata tazo min dashi kenan a asibiti zanyi spending daren amarci na, taɓe baki nayi kada na ɓata mishi lokaci nayi alwalan ina fitowa na samu har ya gama shiryawa na same shi muka tada Sallah, mukayi magriba da isha sannan na zauna ina lazumi shi kuma yaci gaba da jero sauran sallolin dake kanshi,

Kafin ya idar na firfito da kayan abincin da aka kawo na ajiye komai ready, saida ya idar sannan nayi serving ɗinshi na tura mishi plate ɗin gaban shi yana dai kallo baice min komai ba, saida na jawo wani plate ɗin dan zuba nawa yayi caraf ya riƙe hannuna yana aika min da harara.
"A da kenan da nake cikin kaÉ—aici zan iya cin abinci ni kaÉ—ai amma yanzu ina dake i don't have a reason to be lonely anymore"

Ajiye plate ɗin nayi na ɗauki wani ƙarin spoon zan saka a cikin abincin shin da nufin muci tare kaman yanda yaso ya karɓa ya wurgar, bani son wani abinda zai saka mu faɗa kaman yanda mukeyi over a small issue a da, shiyasa bance komai ba na ɗauki cokalin da na saka mishi ɗin na fara ci,
"Babes horo da yunwa zaki mun ne? Won't you feed me?"

What? Ni ko cin abinci a kwano ɗaya ban taɓa ƴi da yarima ba but Zayyad wants me to feed him.
Kaina a ƙasa na saka spoon ɗin hannuna na dibi abincin na kai bakin shi still yaƙi karɓa ba.
To me yake so ne?
" Da yatsun hannun ki nake son kiyi feeding ɗina ba da ƙarfen nasara ba" ya bani amsa kaman ya karanta zuciyana.
Chapter 66 · 0% Book details