← Book details Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 73

Sashe 38

Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jan hanci nayi na É—ago tare dayin fuskar tausayi "hajiya ai babban yaya ne ya hana ni tafiya, tun shekaran jiya na faÉ—a mishi rashin lafiyan abulkhairin amman yace ba zanje ba"

"Maganar banza ma kenan, tashi kije ki shirye naga wanda ya isa ya hana ki tafiya idan shi yake da iko dani ba ni nake da iko dashi ba"

Yess!! Na miƙe ina ji kaman na taka rawa a wurin, idan sulaiman yayi sake na tafi yau wallahi ba zan dawo ba, sake gani na ma sai yayi da gaske dashi da lesson teachern sai naga ta iyawan su,

Cikin nishaɗi nake zuba kaya na a cikin akwati ina yi ina rera waƙa Ruma ta shigo,
"To wai kije inji shi tunda kinje kin haÉ—a mishi wuri"

"Inji shi, shi wa?"

"Babban yaya mana, ba kinje kin haÉ—a mishi bomb wurin hajiya ba, Kika faÉ—i abinda bai faru ba?"

ÆŠaga kafaÉ—a nayi cikin halin ko in kula nace "to ina ruwa na? Ai komai ya faru shi ya jawo tunda shi ya fara min dole, mai tsoron ta kife shine gawan fari"

"Haka ne kam zancen ki gaskiya shiyasa ma da nagan shi yazo da bulala ban wani damu ba saboda nasan keɗin jaruma ce, kawai kije ya shargwaɗa miki su a gadon baya ki tashi ki kaɗe mishi a wurin" ta ƙarashe tana dariyan mugunta,

Har na kai ƙofa da gudu na dawo wurinta, cike da tsoro jiki na har mazari yake yi nace "dan Allah da gaske kike Rumaisa? Duka na zaiyi?"

Bata bar dariyan ba ta gyaÉ—a min kai " eh mana ba kince mai tsoron ta kife shine gawan fari ba? Bismillah jaki ki gamu dashi"

"Ke baki san wasa bane? Wasa fa na miki, dan Allah duka na zaiyi? Muje ki bashi haƙuri a madadi na dan Allah nasan ke zai saurare ki" kafin na kai ƙarshen magana na har idona ya fara tara ruwa,

"Hhhh matsoraciya kawai, wasa nake miki da'allah, muje na raka ki kinsan yayan namu bayi son jira ba kaman masoyin ki yaa Zayd bane"

"Wassh har kin ƙara min bugun zuciya da kika ambaci sunan shi" na faɗa hannu na a kan ƙirji na ina faman lumshe ido,

Duka ta kai min a kafaɗa sannan ta ja hannu na da ƙarfi muka fita daga ɗakin tana faɗin "lallai yarinyar nan idon ki ya buɗe tun kafin ki tafasa kina niman ƙonewa"

  *****
Murmushin fuska na ne ya canza zuwa fuskar tausayi yayin da naci karo da babban yaya zaune a ƙaramin parlorn aunty amarya ya wani hakince a kan kujera ƙafar shi ɗaya kan ɗaya kaman wani gidan shi,

Gaban shi na ƙarasa na tsuguna kaina a ƙasa nace "gani babban yaya"

"Na ganki ai ban makance ba" ya faÉ—a ba tare da ya kalli wurin da nake ba ballantana na saka ma raina zai bani izinin zama

Saka wa baki na sakata nayi naci gaba da kneeling a wurin kaman wanda aka sakani Ruma na can gefe a tsaye har sanda yayi niyyan magana,

"Uhm kince yaron auntyn ki babu lafiya a wani asibiti ne aka kwantar dashi?............amsa nake nima ba cewa nayi ki zuba min idanuwan kin nan ba"

"D..d..dama..umm...aa..nan...."

"Wait! Manta sunan asibitin kika yi ko da suka kira kin basu faÉ—a miki bane?"

"Eh! Na manta ban tambaye su ba"

"To ki kira ki tambaye sun, idan sun faɗa miki sai kizo ki same ni a mota muje a duba shi, kema ki shirya Rumaisa sai mu tafi tare" ya miƙe tare da maida hulan shi ya saka wayan shi a aljihu sannan ya kama hanyan fita,

"Aa anfa sallame su, yanzu suna gida ne"

Juyowa yayi yana min wani irin kallo sannan yace "to shikkenan sai muje gidan a duba su"

"Nima zan tafi tare daku yaya"

Juyawa mukayi duka muna kallon shi, zayyad ba dai fara'a ba kullum fuskar shi a sake yana zuba murmushi ga tukuicin dimples dake ƙawata shi,

Ƙarasawa wurin shi sulaiman yayi yana jan hannun rigan shi ya duba lafiyar shi saboda ɗazu ya shiga duba shi ya samu yana barci
"Haba bro don't embarrass me in front of these kids mana"

"Ya zayd mu É—in ne kids É—in? Harda ehem.. É—inka ita ma kid ce?"

"Just shut up Rumaisa!" Ya faÉ—a yana dariya "nayi dana sanin barin ki kisan sirrika na you are nothing more than a blaster"

"Wasu sirrikan ne naka da Ruma ta sani ni ban san dashi ba? Yana da dangantaka da saudat ne? Cos i can clearly understand that she is referring to her"

"Of course not bro! It's nothing serious kada ka É—aga hankalin ka mu tafi ko?"

   ***
Ko da muka shiga mota a baya na zauna tare da Ruma sulaiman da kanshi yake driving Zayyad na zaune a passenger seat, dukda ina matuƙar jin daɗin sautin ƙira'ar sheikh sudais da yake bi kuma karatun na sanya ni nutsuwa,  amman hankali na a tashe yake saboda ina ta kiran aunty yusrah bata ɗauka ba, da alama text ɗin da na tura mata ma bata gani ba don na tabbata zatayi replying idan ta buɗe,

Tsayawa mukayi a hanya muka sayi fruits masu tarin yawa sannan muka ci gaba da tafiya,

"Sai ki mana jagora mu shiga ko?"

Yaya akayi sulaiman yasan gidan khamis? Ko da yake ba abun mamaki bane tunda ma'aikacin shi ne, yasan gidan mama ma ballantana nan? a hankali na buɗe kofar na fita sannan suka biyo ni a baya zayyad na janye da akwati na, ina ta salati a zuciyana kada a gano ƙaryar da na shirya,

A watan Ramadana ma ba'a bar gulma ba, idanun ƴan unguwan mu kaman zai faɗi ƙasa an ganni da manyan samaruka masu hannu da maiƙo sai binmu ake da kallo har abun ya damu zayyad tunda shi bai saba shiga cikin mutane ba,

Saida nida Ruma muka fara shiga muka nima musu izini kafin suka shigo muka yaÉ—a zango a parlor sannan aka shiga gaisawa, yadiko sai kaffa_kaffa take dasu,

"Yaya mai jikin dai?" Sulaiman ya tambaya yana kallon abulkhairi dake kwance a hannun Ruma yana barci,

"Mara lafiya kuma?" Yadiko ta tambaya?

Nan da nan aunty yusrah ta harbo jirgin, ta san bai wuce ƙarya na sharara musu dan na samu dawowa ba,

Janyo hannun jannant tayi ta tura mishi ita "gata nan jikin da sauƙi"

yarinya sai ƙifi_ƙifi take da ido taga ana turata wurin baƙon da bata taɓa ganin shi ba, ta canza hanya da gudu tazo jiki na ta ɓuya tana leƙa shi,

"Amman kaman namiji ne aka ce bayi da lafiyan ko?"

"B..ba.ba namiji bane ita ce mantawa nayi"

"Oh itace abulkhairin kenan!!"

Dariya zayyad ya saka Ruma da aunty yusrah suna taya shi, tsaban mugunta harda sunkuyawa yana ƙyalƙyalawa, sai ya ɗago ya kalle ni ya sake kwashewa da dariya,

"Ke dai saudat Allah ya shirye ki yasa ki daina munanan daɓi'u" cewar yadiko,

Caraf ruma ta amshe da "Haba yadikon mu, har wasu munanan É—abi'un take dashi bayan wannan"

"To wannan ɗin ance miki karamin abu ne? Ko ƙarya ɗabi'a ce mai kyau?" Ta maida duban ta wurin babban yaya da ya haɗe gabas da yamma duk dariyar nan da ake ko murmusawa baiyi ba shi abun ma haushi ya bashi don yana da tabbacin nayi ƙaryar ne don na guje mishi,

"Yaya sunan ka ma baba na?"

"Sulaiman"

"Yauwa sulaiman to saudat ƙarya tayi muku daga Jannat har abulkhairi babu mara lafiya, bansan wani dalilin bane yasa take mana wannan mummunan fatan ba..............🤦🏻‍♀️

#vote
#share
#comment

*Ummu Najma ce😘*

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

🤍💚🤍
    *ƘARAMAR BAZAWARA*
           💚🤍💚

    _(Cigaban matar kulle)_

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

         *BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
  And *AISHA ALTO*

32🧝🏻‍♀️
Horn ɗin motar khamis ya kuɓutar dani daga faɗan yadiko, hamdala nayi caraf na miƙe na fita buɗe mishi gate sannan ya shigo da motar shi ciki,

Tattaran laidodin kayan da yazo dashi a mota nayi dukda ya hana ni ina binshi ina ɓuya a bayan shi har muka shiga parlorn shima da mamaki yake kallon mutanen dake zaune a ciki,

Bai taɓa tsammanin akwai ranar da Allah zai kawo sulaiman boss cikin gidan shi ba shiyasa da ya ganshi harda ƙaramin oga zayyad hankalin shi ya tashi sosai don a tunanin shi wani abun naje na ɓaro mishi dukda kuwa ya san ni ɗin ba fitinanniya bace,

Gaishe su yayi ya zauna a parlorn ni kuma na ɗauki hanyar kitchen da kayan hannu na tunda na shiga naƙi fitowa inajin yadiko tana mayar ma khamis abinda ya faru, faɗan da bata yi min da ba sai yanzu take juye mishi, yayi shiru yana jinta idan ta kai comma ya bata haƙuri kafin taci gaba, Saida su zayyad suka saka baki kafin ta haƙura tayi shiru,

Ban fito ba har saida naji sun tashi tafiya a hanyar fita daga kitchen É—in naci karo da khamis, har nayi shirin amsan nashi faÉ—an amman baice min komai ba bayan
"Kinyi dai_dai, gidan ku da dangin ki sune mutuncin ki ba bare ba"

Wannan kalaman nashi saida ya sosa min tsohon tabon dake zuciyata, ina kewan gida sosai ina kewan iyaye na da dangi na, ya Allah ka gwada min ranan da zan koma wuroɓokki in gano halin da iyaye na suke ciki,

  ****
Duk sun fita waje amman shi sai baya_baya yake yana son yaga fitowa na don ba zai iya tafiya ba idan bamuyi sallaman ƙarshe ba, yasan zaisha kewa na amman bayi da yanda zaiyi dole ya dinga haƙuri a halin da ake ciki,

Har jikin motar su mukayi musu rakiya abun mamaki sulaiman bai min zancen ranar komawa na gidan ba ya sa kai cikin mota ya make,

Saida ya faki idon kowa kafin ya buÉ—e baki ba tare da ya fitar da sauti ko kaÉ—an ba ya furta I LOVE YOU ta yanda wanda ya kalli bakin sa ne kawai zai iya fayyace abinda ya faÉ—a,
Chapter 38 · 0% Book details