← Book details Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 73

Sashe 4

Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saidai fa kada kuyi tunanin Sulaiman yana da sauƙin hali ta wani wurin, yanda yake a turɓune haka yake ma kowa harda matan shi wanda yake kwana yake tashi da takaicin ba don Allah ta aure shi ba, Sulaiman bayi raga ma kowa bayi barin kota kwana, mutum ne mai tsatstsauran ra'ayi mai jin kai da isa mutum ne kaifi ɗaya amman kuma adali ne a tsakanin mutane sonkai shine abinda bai sani ba,

Harta wa'inda yake cewa yana missing ɗinsun idan suna tare dashi basu kwasan ta daɗi, wanda kawai suke ganin rahama da murumshi a fuskar shi sune  iyayen shi da aunty amarya kishiyar mahaifiyar shi kuma uwa a wurin Zayyad dasu Ruma sai kuma ɗaiɗaiku a cikin al'umma,

**********
11:02pm
Kwance nake a kan gadon ɗakin suka buɗe ƙofar amman basu shigo ba, kallon yanda na duƙunƙune cikin hijabi Yusrah tayi a tunanin su nayi barci ne ta juya wurin Khamis fuskar ta ɗauke da damuwa, murya can ƙasa tace

"Abban Jannat har yanzu fa babu wani canji daga wurin Saudat, shekaru 2 kenan harda rabi amman bata yi overcoming fear ɗinta ba, kwata_kwata taƙi sakewa a cikin mu wallahi bani jin ɗadin hakan bani son ganin boɗɗi cikin damuwa ko kaɗan"

Jan hannun ta yayi suka bar wurin tare da jawo min ƙofar ya rufe, saida suka shiga bedroom ɗinshi sannan ya zaunar da ita a kan gado ya riƙo kafarta da suka kumbura yana matsa mata su da ɗan ƙarfi don haka suke yi a kowani dare tunda ta kusan shiga watan aihuwan ta, idan ba haka ba bazata iya barci ba tayi ta mitan ciwon jiki kenan,

"Insha Allah wata rana zata saba, tunda tana zuwa makarantar boko da islamiyya tana hulÉ—a da mutane she will get use to staying with all of us, ai abun ba lokaci É—aya bane nima daga farkon zuwa na da ita nayi tunanin hakan amman daga baya sai na lura a hankali take sabawa da sabon environment É—inta"

"Ka gani fa tunda tazo gidan nan yau da yamma banda gaisuwa babu abinda ya shiga tsakani na da ita, ko magana nayi mata saidai tayi min murmushi kawai ga aiki ta hana ni ko É—aga tsinke"

"Ai hakan ne ya kamace ki baby, kina samun hutu zirga_zirgan ki yayi yawa zaki iya saka wa baby na rashin lafiya, amman kinga lokacin cikin baby Jannat hankali na kwance kina gado abinki kina hutawa"

Qyalqyalawa tayi da Dariya tace "that was the craziest moment"

Shima Khamis dariyan yayi yace "i agree saboda a lokacin ina tsakiyar craziness a lokacin ne nake tashe ina jin kaina wani daban nima za'a aifa min baby, kinsan ance feelings ɗin mai partial craziness is multiple times na mai cikakken lafiya, so abu na saurin faranta mana kuma abu na saurin ɓata mana and we are very sensitive, bansan yaya zanyi miki bayani ba amman komi namu over ne shiyasa na wahalar dake a wancan lokacin kusan watanni 6 zuwa 7 fa kikayi kina kwance a wuri ɗaya kina marisa ba tare da kin sani ba, I'm sorry once again baby"

Saurin saka tafin hannun ta tayi ta toshe bakin shi tana girgiza kai, "stop apologizing please ka bani haƙuri yafi sau a ƙirga, da ace ban haƙura ba da bazan dawo naci gaba da zama tare da kai ba"

Shiru Khamis yayi yana kallon cikin idanuwan ta kafin can ya kwashe da dariya harda tafa hannu, ya kwanta a gadon yana ci gaba da tiƙan dariya, kallon shi Yusrah ta tsaya yi ta rasa dariyan da yake faman yi na meye ɗaya, saida ya tsagaita sannan ya tashi ya zauna idanun shi duk sun tara hawaye yace
"Baby I'm really sorry, kinsan maganin da nake baki a ina nake samo su?"

Girgiza kai tayi alaman A'a

"A wurin masu kurbe_kurben nan, faɗamin sukayi maganin yana kwantar da hankali yana maganin gajiya kuma yana saka nutsuwa da ƙara lafiya shiyasa nayi ta ɗirka miki ashe normal ƙwaya ne na masu shaye_shaye.........🤦🏻‍♀️

Don't forget to follow
Vote
Share
And comment as you read 💖

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚

_(Cigaban matar kulle)_

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*BY*
*UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*

*Babban jin daɗin rayuwa shine ki kasance cikin rufin asiri a gidan iyayen ki ko gidan mijin ki, a duk yanayin da muke ciki na ƙasa damu zamu dinga dubawa ba na sama ba, Allah yayi mana babbar ni'ima mu gode masa*💡

03🧝🏻‍♀️
"Ƙwaya fa kace??"

Dariya Khamis yaci gaba dayi har hawaye suna sauƙa saman fuskar shi, yana gyada mata kai ko magana ya kasa,

"That means duk abinda nake ji kaman a saman ɗakin nake kwance ko inji na fita hayyaci na ko in dinga ganin abubuwan dake zagaye dani suna motsi da kuma abubuwa da yawa dake caza min ƙwaƙwalwa ko tashi na kasa yi ashe duk effect ɗin ƙwaya ne?"

"Over dose ma kuwa, biyu sukace ake sha ni kuma nake baki uku" ya faɗa tare da sake saka dariya yana riƙe cikin shi, Yusrah kuwa sake baki tayi shaaa kawai tana kallon ikon Allah gaba ɗaya Khamis ya gama goge mata hadda, ta rasa me zatayi masa ko kuma me zata ce masa ɗaya,

"Ashe ba laifin Jannat bane da take da gagara kaman rainon maza, ka gama mata training tun tana ciki" sai kuma tayi tagumi cikin jimami tace "oh Allah yayi yarinya ta tana da tsawon rai ne ba don anyi gaggawar bani agaji ba da na rasa ta, maybe nima da ka daɗe da rasa ni wallahi banyi tunanin zanyi rai ba lokacin da nake kwance a asibiti, ban taba shiga mawuyacin hali irin wannan ba" ta ƙarasa hawaye na zuba a idon ta ba tare da ta sani ba,

Barin dariyan Khamis yayi ganin sauƙar hawayen ta, ya cire hannun da tayi tagumi dashi sannan ya rungumeta suna a zaune yana shafa bayan ta a hankali,
"Shiyasa nake roƙon ki ki yafe min baby, nasan halin da na saka ki abu ne mai wuyar mantawa, it's ok ma idan baki son ki yafe min amman ki daina zubda hawayen ki don Allah, na faɗa miki ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba suna ƙona min zuciya sosai"

A maimakon tayi shirun saboda rarrashin ta da yake yi sai ƙara sautin kuka tayi tana yinshi mai gunji
"Wallahi na yafe maka Abban Jannat zuciyata ba zata taɓa iya zama da fushinka a cikin ta ba tana son ka da yawa, i just can't help it when I think of the past"

"Then it's better if you stop thinking about it, it might affect my baby ummm" ya fada yana share mata hawayen fuskar ta,

"kinga kin manta ma baki rama kiss dinki na dazu ba, idan ya kai gobe kuma ba zan yarda ki rama ba idan kin yafe kuma Shikkenan"

Jan hanci tayi ta juyo tana kallon shi da rinannun idanuwanta ta murguda mishi baki haÉ—e da faÉ—in "na yafe"

"Bazai yiwu ba, idan kin yafe ni ban yafe ba so silently come here ki rama abun ki"

**********
"Tsoro É—aya? Kinsan Allah yanda naji muryan shi kaman mayunwacin zaki yayi kururuwa wai Rumaaaaaa saida na saki fitsari a jiki na"

Dariya suka saka gaba ɗaya dakin banda Nana da Sulthana da suka haɗe fuska suna faman harare_harare, timm suka ji ƙaran faɗuwan Batool a ƙasa saboda tsananin dariya,

siririn tsaki Sulthana taja tayi kwanciyar ta a gadon dake gefen na Nana dake ɗakin gadajen kwanan mutum biyu ne sai tima timan wardrobes daga dungu zuwa dungu da kuma arm chairs guda biyu ta bakin ƙofa, a yanda suka tsara zaman ɗakunan idan zaytoon tana ƙasa lokacin hutun makaranta suna kwana tare da Batool a ɗaki ɗaya saboda sune manya sai Nana kuma sukan kwana tare da Sulthana wani lokaci,

Idan kuma ba lokacin hutu bane, Nana da Fa'iza suke kwana tunda Ruma ba a gari take karatu ba zaytoon da Batool ma haka kuma basu iya kwana mutum É—aya a É—aki,

cin fuskan da suke musu ya fara isanta sunfi one hour suna zaune sun kasa su a tray suna tsokanar su suna kwasan dariya, gwanda Nana idan aka faÉ—a mata wani abun takan mayar musu da martani amman ita bata isa ba tunda a alfarma take zaune cikin gidan,

Miƙewa Batool tayi ta koma seat ɗinta ta zauna still tana dariya tace "ai Rumaisa'u kinyi ƙoƙarin tunda fitsarin kaɗan kika sake bakiyi masa sauran a hanya ba, nifa lokacin da ya shigo dake har dan ɗiba da gudu nayi tunanin yayi gamo da aljana ce a hanya ashe kece kika fito kaman aljana baɗalu"

"Hmm Wai don ma bani nayi laifin ba kenan, kinsan lokacin da na takalo shi saida ya jimɗe ni? A sanadiyar haka har na gama zama na aka gargaɗa ni Lagos ko inuwar ya Zayyad na gani ya shigo wuri bani raɓan wurin"

Fa'iza ne ta amshe da " ai wallahi suma da ɗan iskan duka ya musu da bulalan timan doki ma da wannan hayaniyar da yazo yana mana bamu san hawa ba bamu san sauƙa ba, ita Nana hafsa saboda shegen iyayi da kaɗifiri kinga abinda bai kamata idanun ki su gani ba shine zaki je ki samu karere ki faɗa mata, gashi ai a sanadiyar haka zaki je ki haɗu da dangin su oduduwa"

Naushin Fa'iza a baya Nana tayi saboda ita ce take zaune a bakin gadon ta, rai a bace tace
"Dalla malama tashi ki fita min a É—aki tunda ba naki bane, kema ai wata kareren ne"

"Amman dai gidan ubana ne ko? Ba yawon gantali nazo ba?"

Tashi Sulthana tayi ta zauna tana nuna kanta tace "Fa'ee nice mai yawon gantalin?"

"To wa ya sani? Nidai kunji ban kira suna ba ko?"
Chapter 4 · 0% Book details