Sashe 27
Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tafi hour 1 tana tufka da warwara ta rasa wani hukunci ne É—aya ya dace da abinda ya faÉ—a tunda a kaikaice yayi mata maganar ko dai ya faÉ—a ne don ya kawar da maganar da take mishi da kuma wanda take son isar mishi cikin hikima wato neman wasu kuÉ—aÉ—e daga gareshi a lokacin? Idan kuma da gaske yake fa yake?
Ganin ba zata samu amsan hakan ta hanyar tambayar kanta ba yasa ta ɗauki wayarta tana jin yanda ƴarta take zunduma ihu amma a yanzu bata da nutsuwan kulata, ƙarshe kiran nanny ɗinta tayi tazo ta ɗauke ta ita kuma taci gaba da trying numbern Sulaiman,
 ********
I was Shocked!! For a moment zuciyata ta kasa gaskata abinda idanuwa na suke gani har saida naga Zayyad yana buga jikin shi a jikin ƙafar Centre table wanda ko shi ba ƙaramin girgiza yake yi ba, jikin shi ya ƙame kaman mai farfaɗiya sai ihu yake yi abun gwanin tausayi,
Babban mutum magidanci, that kind and sweet Zayyad, my heart desire wanda a ko yaushe nake mafarkin kasancewa tare dashi shine a cikin wannan yanayin da ko ƙaramin yaro ba za'a so mishi ita ba?
"Rumaisa ina containern maganin shi da yake wurin ki? Ban samu nawa ba!" Shine maganar da ya fargar dani amman na kasa ayyana komai jiki na ya mutu ina tsaye a wurin Ruma ta koma ɗakin ta da gudu da nufin ɗaukowa Sulaiman kuma yana ƙoƙarin riƙe shi da duk wani ƙarfin shi amman ya kasa sai ji ma kanshi rauni yake yi a garin haka shima yaji masa ciwo a ƙafa, da kuma guiwan hannun shi,
Amman haka ya riƙe ɗan uwanshi ba tare da ya damu da halin da yake ciki na cutarwa ba dan basu iya controlling ɗinshi idan ba su uku shi da dady da Nafi'u ba, a hakan ma da ƙyar,
Fitowa riƙe da wannan dai farin ƙaramin containern Ruma tayi ta miƙa wa Aunty Amarya ita kuma ta buɗe ta mika ma sulaiman da nufin ya shafa mishi amman abin yayi mishi yawa ba zai iya ba, yana karba Zayyad yayi ball dashi wanda su kansu basu san ina ya shiga ba,
Zan iya taimakon shi, ina da sani a kan hakan amman ta yaya? Ta wani hanya zan taimake shi ba tare da mun aikata zunubi ba? Iyakacin ruƙiyya da na taɓa yi a rayuwata ma mata ne zallah, ta yaya zan iya haɗa jiki na da namiji da sunan nema mishi sauƙi daga wurin Allah?
Amman ganin idan na bar Zayyad a haka ba tare da nayi wani abu ba zai cutu yasa nayi shahadar ƙarasawa kusa dashi dukda tsoron shi ya kama ni amman a hakan na durƙusa na fara rero ƙira'a, saidai fa matsatstsakun kan bawan allan nan sai toshe kunne naga yana yi yana ƙoƙarin kawo min gwabza,
A taƙaice dai ruƙiyyan nan bai kammalu a haka ba saida babban Yaya ya riƙe min shi, na manna baki na a saitin kunnen shi ina karatu ina kuka irin wanda mahaifiyar shi take yi tana mishi addu'a,
Munji jiki kam babu ƙarya dan kunsan hidima da namiji kuma majiyin ƙarfi ga ƙarin wani ƙarfin na mutanen ɓoye dake jikin sa,
Allah ya yafe min ko dan tsarkakuwan niyya ta amman lokacin da yayi wani yunƙuri ya birkito ni ina jin yanda ƙirjin shi yake gogan nawa wasu sakwanni na tsohuwar ƴar hannu yana isa cikin jikina dukda shi baima san yayi hakan ba taimakon da Allah yayi min ɗaya bani azumi a ranar da shima ya kama hanyar garin su,
Bai É—auki lokaci sosai ba abun ya lafa a wurin su saboda yakan fi hour 1 da rabi wani lokaci ana abu É—aya shiyasa idan ya tashi yake jinya na tsamin jiki da raunukan da suke jawo masa, amman a wuri na ya daÉ—e sosai tunda har ya jigata haka,
Ruwa na buƙaci su bani a kofi suka kawo min na zam_zam wanda basu rabuwa dashi saboda Zayyad, na karɓa nayi addu'a a ciki sannan na miƙa ma sulaiman ya bashi aka shafa mishi sauran a fuska, ya kira mutumin dake bashi rahoto kullum saboda shine amintaccen sa a gidan suka tattare shi zuwa bedroom ɗinshi,
Na bisu da kallo ina taraddadin tsawon lokacin da Zayyad ya É—auka yana fama da wannan laluran, tun a yarinta suka shige shi ko da girman sa? Koma gadan shi yayi? Allah masani,
Saida suka kwantar dashi yanda zai samu hutu sannan suka fito daga ɗakin tare da rufo ƙofar har lokacin muna tsaye a parlorn Aunty Amarya sai zuba min godiya takeyi tana saka min albarka kaman bakinta zai tsinke abun tausayi yanda matar nan take kuka,
Zaunar da ita mukayi muna lallashin ta ni da Ruma tare da faɗa mata kalamai masu sanyi duk da bani da tabbaci amman ina da yaƙinin Zayyad zai iya warkewa na dinga nusar da ita tana haƙuri kuma tana yawan godiya ma Allah don wannan jarabawar da Allah ya ɗaura musu zai iya datar dasu a lahira,
Yana zaune a kujerar dake kallon namu ya ƙura mana idanu ga aunty Amarya ta kwantar da kanta saman kafaɗa na ta lafe kaman wata ƙaramar yarinya, tunda wannan matsalar yake tashi bayan a wurin dady babu a inda take samun comfort idan bayi nan sai yau a wurin ƴaƴan ta,
"Daƙiƙiya! Daƙiya!! Daƙiƙiya!!! Lallai jiya ya faɗi kalmar da ta zamo mishi guba a yau, ya jife baiwar Allah mai ɗumbin ilimi mai amfani da sunan da ake kiran ƙasƙantacce dashi, gashi wanda yake kira da daƙiƙiya tayi abinda shi ya gagara yi tsawon shekara da shekaru,
Lallai kada ka wulaƙanta ɗan adam a duk halin da ka ganshi don baka san wani irin baiwa Allah yayi mishi ba,
 ******
5:40pm
Sake duba agogon hannun shi yayi kusan 30 minutes kenan yana zaman jiran dawowar su boɗɗi amman shiru, gashi an kira Ruma yafi sau a ƙirga bata yi picking ba daga ƙarshe ne aka kira Aunty Sadiya ta shaida musu mun daɗe da dawowa tun kafin ayi sallan la'asar muka bar gidan, sai aka tura junior yaje part ɗin su Zayyad ya duba ko sun dawo,
Yana zaune suna taɓa hira da Hajiya sulaiman ya shigo part ɗin cika da girmamawa Khamis ya miƙe ya miƙa mishi hannu tare da ɗan durƙusawa suka gaisa sannan ya koma ya zauna yana binshi da kallon tambaya,
Bakin shi bai furta komai ba amman kallon da hajiya taga yana miƙa ma Khamis yasa ta gane yana niman ƙarin bayani tace
"Ya zo ɗaukan ƙanwar shi ce Saudat yanzu aka je kira mana ita"
HaÉ—e fuska yayi gaban shi na faÉ—uwa, ya gama sakankancewa zaman Saudat zai É—aure a tare dasu shi da har ya saka ta a makaranta ya shigar da ita cikin tsarin rayuwan gidan da mutanen cikin ta sai kawai azo a tafi da ita?!
Noo! Ba zai bar hakan ta faru ba, ya gama shiri ya tsara duk yanda yake so abubuwa su kasance, sannan the worst part shine yanzu Saudat ta san sirrin da suke ɓoyewa shekara da shekaru idan ya barta ta tafi wani wuri kaman ya buɗe surrin ne ma kowa ya gani, ba zai bari wani daga sama ya wargaza mishi plan ba dole kawai yayi wani abu a kai,
 ******
"Dan Allah ki bar kukan nan haka boɗɗi, tun ɗazu bakiyi kuka bq sai yanzu da hankalin mu ya kwanta?" Ruma ta faɗa itama tana shirin zubar da hawaye "ɗazu fa ke da bakin ki kike faɗa ma aunty Amarya wannan lalura ƙaddara ce amman kema gashi kina yi kaman baki aminta da ƙaddarar ba na yau da kika gani kawai?"
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, Rumaisa ina jin kaman zuciyata zata tarwatse na kasa sabanta mata da jarumta a kan abinda ya shafi Hamma Zayyad,
duk lokacin da wani abu ya same ni shi nake fara samu na faÉ—a mishi don ina da tabbacin zai kore min shi, amman yanzu na farko ma na gagara mishi wani babban taimako nayi sake na fita daga cikin hayyaci na har na barshi yaji rauni"
"A'a kinyi bakin ƙoƙarin ki wallahi Allah ya saka miki da alkhairi mun gode sosai boɗɗi"
"Muje mu sake duba shi kafin a sha ruwa dan Allah"
Fita mukayi a bakin ƙofa muka ci karo da junior dake bai san abinda ya faru ba yasa da fara'ar shi yazo gaba na yana fankama shi a dole wai saurayi na yace "Girlfriend"
"Na'am boisfirens (boyfriend) É—ina yaya akayi?"
"Hmm ashe baki sona?"
Saida dariya ya suɓuce ma Ruma ganin yanda ya haɗe rai yana cin magani kaman wani babba,
"Haba my junior, ina sonka mana sosai ma me ya faru?"
"To gashi nan wannan yayan kin yazo ɗaukan ki zaku tafi gida ki barni, kuma yanzu aunty Ruma ta ɗauke hankalin ki ko hira ma baki zuwa wuri na, idan kika tafi kika yaudare ni a wani wurin na barki da Allah daman na san ba wani sona da yawa kike yi ba" ya ƙarasa maganar yana tafiya muka bishi da kallon mamaki yanda yaron nan yake zubar zance,
Sam banso haka ba, banji daɗin zuwa Khamis a wannan lokacin ba musamman yanzu da nake son kulawa da Zayyad da kuma lafiyar shi amman har duniya ta naɗe khamis yana ɗaya daga cikin mutanen da ba zan taɓa iya musu muusuu ba duk abinda suka sani saidai idan ya kauce ma Shari'a,
Naji daɗin ganin aunty amarya da Sulaiman sun bar parlor hakan ya bamu daman wucewa cikin ɗakin Zayyad cikin sauƙi, yana barci amman ƙaran buɗe ƙofar mu ya tashe shi,
Kallo ɗaya nayi masa na sake fashewa da kuka tare da toshe hannu na da tafin hannu na ina ganin yanda ya kwaile jikin ƙafan shi wurin yayi fari sol dan ba'a saka mishi magani ba tukunna bisa umarnin sulaiman ne kada a bari wani ya raɓe shi har sai ya dawo cikin hayyacin shi koda kuwa doctor ne,
Daddafawa yayi ya miƙe ya zauna tare da jinginar da bayan shi jikin pillow yana kallo na, yayi ta kallo na ba tare da ya san abinda zai faɗa ba,