← Book details Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 73

Sashe 58

Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"She is!!!
Sannan wannan karon ba zan bari kayi nasara a kaina ba saƙon da ka bayar a faɗamin ya riske ni na cewa nima namiji ne na gwada mazantaka na sannan idan inaso zan iya shiga takaran niman auren saudat aga ni da kai waye zaiyi nasara,
To ba takara ni zanyi da kai ba, ƙwaceta zanyi daga wurin ka saboda ita tawa ce, she belongs to mee!!"

Da faɗan haka ya sake juyawa yana fitar da huci kaman wanda zai cike da hayaƙi, zai shige ciki ya tsinkayo muryar Sulaiman na faɗin
"A duk lokacin da kazo da wani matsala naka nakan yi ƙoƙarin maida shi first priority na, ba zan huta ba har sai naga nayi maka maganin shi to yanzu lokaci ne da zaka biya ni wa'innan alkhairan da nayi maka, ka haƙura da boɗɗi ka fita daga rayuwar ta gaba ɗaya dan Allah Zayyad"

Juyowa ya sake yi a karo na biyu ya kalle shi a kaikaice sannan yace
"You know what? Na gaji da gorin da kake min Sulaiman, gaba ɗaya ka saka na kasa sakewa da rayuwata kana saka ni naji kaman kaine ka busa min numfashi ko kuma bani bashin rayuwata kayi da yanzu kake buƙatan na biyaka,
If that's the case ka faɗi ko meye kake so zan baka, harta abinda ka taimaka min na mallaka ma idan kana so zan iya haƙura na bar maka shi amman banda Saudat!
Bazan bar maka ita ba....bata cikin abinda zaka iya samu daga wuri na saboda ita É—in mutum ce ba wani haja da kowa zai iya mallaka ba and i respect her alot" da faÉ—an haka yayi tafiyar shi ya bar Sulaiman tsaye da sakakken baki al'ajabi ya mugun kamashi dan ko a mafarki bai taba tunanin Zayyad zai iya tsayayya dashi haka ba.

*******
Ruma ya tarar a parlour ta baje takardu a gabanta tana karantawa dan sun fara text É—in first semester sai anty dake zaune tana kallon Africa tv 3, Fa'iza kam daman wurin zamanta part É—in hajiya ne, su junior da Farooq kuma suna makaranta.

Sallama yayi musu suka amsa bai sake ce musu komai ba ya nufi hanyar bedroom É—inshi, har yayi rabin hanya ya canja ra'ayi ya juya ya nufi hanyar bedroom É—in dady dake part É—in.
Shigar shi yayi daidai da fitowar dady daga toilet, gaida shi Zayyad yayi kafin ya nima ma kanshi wurin zama.

"Yaya dai Zayyad wani abu ya faru ne?" Dady ya tambaya yana karantar yanayin fuskar shi.

Sai kuma yaji nauyin buƙatar da yazo dashi yasan zaiyi ma mahaifin nashi banbaraƙwai kuma ba lallai bane ya fahimce shi, amman wannan ne kawai hanya ɗaya da zai iya defeating Sulaiman.
A É—arare ya fara kwaro mishi bayanai kan cewa yana son Saudat kuma yana so a shiga mishi gaba wurin niman aurenta.

Shiru dady yayi yana nazari kafin yace "wannan wani irin shirme ne Zayyad, yarinyar da kake faÉ—a ba ita bace É—n uwanka ya tura mu wurin mahaifinta? Ko baka sani bane?"

"Ban sani ba dady, sai yanzu amman shi babban yaya yasan tunda ita nake so na aura"

Tsaki dady yaja yace "tashi kaje ka kira min Sulaiman É—in yanzu kuzo tare, wannan ai shashanci ne"

Lokacin da ya fita ya samu har Sulaiman ya tafi, a take dady yasa aka kira shi suka dawo sannan aka zauna zaman Shari'a kusan irin wanda akayi musu kwanaki lokacin da suka ɗau gaba da juna, don kowanne a cikin su fitar da abinda ke cikinsa kawai yake yi, ƙarshe abin da yafi ƙarfin dady saida ya kira wa'inda ya tafi dasu tambaya wa Sulaiman izini suma suka shiga cikin maganar.

Mutum ɗaya cikin su dagewa yayi a kan saidai Zayyad ya haƙura ya nemi wata dan ba zasu koma a kan wannan maganar ba mutuncin su ya zube, dady ma yaso yarda da maganar shi amman Zayyad ya kafe har da musu kuka shi bazai haƙura ba saidai Sulaiman ya haƙura.

Duk abinda akeyin nan su Hajiya basu sani ba har aaka ci aka cinye don yasan halin mata kowacce cikin su bayan ɗanta zata bi daga ƙarshe kawai sallaman su yayi yace suje zasu ƙarasa tattaunawa a tsakaninsu manya duk hukuncin da suka yanke zasu sanar musu.

****
Tun wannan lokacin da akayi magana har yanzu shiru kusan wata guda kenan dady baice ma Sulaiman ko Zayyad komai ba, gashi har su Saudat sunyi jamb sun fara shirin zana exams.
Aikin office ya taru yayi ma Zayyad yawa tunda suka samu matsala da Sulaiman yake masa mugunta saboda shine a saman shi yana sashi over working, shi kuwa Zayyad haka yake jurewa don kawai yasan idan ya gwada abin bai dame shi ba Sulaiman zaifi jin haushi.

Ganin shirun yayi yawa gashi Saudat ta kusa dawowa ayita ta ƙare yasa ya sake tunkarar Dady da maganar, da yaga da gasken gaske yake yi shine yace masa yaje zasu yi shawara da Khamis tunda shine kaman wakilinta a yanzu kafin ya musu hanya su ƙarasa wurin mahaifinta.

Washegari da yamma dady ya tura aka kira khamis, irin tarban da suke mishi a kowani lokaci wanda yake ƙara mutuncinsu a idon shi, shi sukayi masa kafin nan ya shiga ganawa da dady ya shaida masa abinda ke faruwa.
Ran khamis idan yayi dubu ya ɓaci har ya gagara ɓoyewa dady kuma ya fahimci hakan, amman haka yayi ta lallaɓa shi har ya yarda zai shige musu gaba su sake komawa wurin baba ba don ranshi ya so ba,
Yana tunanin irin kallon da dattijon mutumin nan zaiyi mishi da kuma tunanin wani kalan riƙo yayi ma Saudat wanda take matsayin amana a gare shi, gaskiya shi basuyi mishi adalci ba kaman ba manyan mutane masu nazari da tunani ba,
Ko dayake it's obvious, daman hankalin wasu iyayen yakan gushe a kan buƙatun ƴaƴansu.

*****
Yana fitowa ya hango Sulaiman zaune a balcony yana ƴan danne_danne a waya gaban shi da kayan motsa baki amman shi bai lura da Khamis da ya ƙura mishi idanu cike da tsana da jin haushi ba,
Cikin ranshi yana ayyana irin rashin aiki da hankali da mutanen gidan gabaki É—aya sukeyi musamman shi Sulaiman dake amfani da kuÉ—i yana shiga jikin kowa da kowa, daman ya riga da yasan double promotion da akayi mishi a wurin aiki kwanaki ba don Allah bane kuma ya shirya rabuwa da komai indai a kan Saudat ne.

Bai gama tunani ba sai ganin Sulaiman ɗin yayi a gaban shi har ya ƙaraso bai sani ba.
"Assalamu alaikum" ya faɗa tare da miƙa mishi hannu sukayi musabaha,

"Uhmm.. khamis kayi haƙuri da abinda yake faruwa nasan an ɗaga maka hankali, kasan sha'ani na rayuwa ya gaji haka dukda har ga Allah banso ayi dragging ɗinka cikin rikicin nan ba, Zayyad har yanzu tasowa yakeyi nutsuwa bai gama zama mishi ba shiyasa ya aikata haka dan Allah ka manta da abinda aka faɗa maka kada ka sa shi a ranka kuma ba sai an kaiga iyayen Saudat ba, ni zan zame mata irin mijin da take so insha Allah"

Sai yanzu ya daɗa tabbatarwa Sulaiman na da ƙarancin tunani don tabbas hannunka mai sanda yayi masa, baisan me yasa suke tunanin saudat abin wasa ne a wurin shi ba, ko dan ya sake musu sun ɗauki ragamar kulawa da rayuwarta shine suke so su gwada mishi bayi da iko da ita?

"Bani da ikon haɗa abinda Allah ya raba, kawai ku bari mu gani meye zai zaɓa mana domin nashi zaɓin shine daidai" shine kawai abinda khamis ya faɗa yayi mishi sallama kana ya tafi ya barshi tsaye a wurin.

*****
"Damn it... Damn all of them!" khamis ya faɗa a tsawace tare da buga cup ɗin hannun shi a jikin garu, da taimakon Allah ba glass bane da tuni ya tarwatse, Yusrah dai tana zaune tana kallon ikon Allah dan tunda ya dawo daga gidan Hajiya ya juye ya dawo kaman wani taɓaɓɓe.

"Abinda fa yasa na kasa faɗa maka komai tun da farko kenan saboda ina tsoron reaction ɗinka, Zayyad soyayya sukeyi da Saudat don itama ina da tabbacin tana sonshi sai kuma daga baya Sulaiman ya fito kan cewa shima yana sonta har ya samu ya shiga tsakanin su ba tare da sanin Saudat ɗin ba, yarinyar nan tayi kuka sau ba adadi, da ƙarancin shekarunta sun taru su biyu sun saka mata damuwan da babba ma ba zai iya ɗauka ba.
She is really suffering abban Jannat, Saudat is the real victim in all this mess...."

"Amman dan girman Allah me yasa kika ha'ince ni Yusrah? Har irin wannan abin zai faru a gidana a kan amanar da na ɗauƙo amman baki faɗa min ba? Why??"

"Saboda tsoron irin wannan yanayin, kayi haƙuri nayi tunanin matsalar ba zata ƙara girma bane sh....."

"Amman gashi kin lalata komai ai" ya katseta a tsawace.
"Kada ki sake min irin haka wallahi idan bakiso ranki ya ɓaci, su kuma bazanje na same su na faɗa musu dukkan su babu ma wanda zan bawa ita wallahi" fuuu yayi hanyar ƙofa da sauri Yusrah ta miƙe ta riƙo hannun shi.

"Haba abban Jannat, ka tsaya muyi magana mana don Allah baka ji ƙarshen bayani ba kawai ka ɗau zafi?

"Babu abinda zanji YUSRAH ai wannan ma maganar banza ce in dauko yarinya amana a maida ita kaman zanin sayarwa a kasuwa saboda rashin mutunci? Dan K.....🙊 Ubansu daga Sulaiman boss ɗin har Zayyad ɗin babu mai auren ta a cikin su idan sunga dama sai su kore ni a aiki mutanen banza kawai,
Wallahi ni zanje in samu baba na sanar dashi su wasu irin mutane ne ya hana su duka sai inga mai zasu iya, jahilai masu ƙaramin tunani.............🧚🏼‍♀️

#vote
#share
#comment

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

WATTPAD: Polohttps://my.w.tt/4ZfEeBpVecbp
OR
@ayeeshatmuhd

*BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
Chapter 58 · 0% Book details