Sashe 2
Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Basu ƙara sama da 1 hour ba yace su tashi su tafi, saida suka isa parking space sannan yace ma Zayyad ya saka drivern shi ya tafi da motar shi gida sai su tafi tare a nashi,
Sosa ƙeyan shi ya fara yi yana kallon shi ta ƙasan ido yace
"Daman..um ni na tuƙo motar ban ɗauko driver ba"
Saida Sulaiman ya duba hagu da dama yaga babu wanda yake kusa dasu tukunna ya matso daff da Zayyad, murya can ƙasa amman a cikin fada yace
"Are You crazy?? Cikin yanayin ka kana É—auke da matsalar nan kake driving, ban haramta maka driving gaba É—aya ba? Yanzu idan wani abu ya same ka fa?"
"Kayi haƙuri yaya hankali na yana tashe ne kuma ba zan iya jiran driver na ya dawo ba ya fita aika ma Aunty amarya, drivern Hajiya kuma yaje ɗauko Batool daga school anyi musu hutu"
Baice masa komai ba ya juya Zayyad ɗin ya bishi a baya suka ƙarasa jikin wata blue Porsche Panamera aka bude mishi back seat saida ya saka Zayyad ya shiga kafin shima ya shiga aka rufe musu ƙofar suka kama hanya,
 ******
*MAFIAS QUATERS*
Daidai jikin wani tamfatsetsen gate Black mai design na golden color naga sun tsaya aka wangale musu gate din suka shiga ciki, gida ne wargajejen gaske amman hawa É—aya ne gare shi kuma an kasa shi gida biyu saidai ginin da fentin da girman su duka É—aya,
A maimakon su shige ciki sai suka tsaya gaba da gate din kadan Sulaiman ya zuge glass ɗin side ɗinshi yayin da ɗaya daga cikin masu gadin wanda ya ɗan manyanta ya ƙaraso ya rusuna tare da dunƙule hannun shi yana masa jinjina da kirari "Allah yaja kwanan ranka shi daɗe, Allah ya baka yawan rai" fuskar shi kadai zai nuna maka bayi jin daɗin kirarin da mai gadi yake masa, Zayyad da yasan ba gamawan yanzu ba ya lumshe idanun sa sannan ya kwantar da kanshi a jikin seat dan yasan yanzu Sulaiman zai fara tambayoyin shi masu wuyan ƙarewa,
"Malam lado su waye suka shigo gidan nan bayan fita na?"
Saida ya sake jinjina masa kafin yace "Allah ya baka yawan rai babu wani baƙo wanda ya shigo gidan nan bayan fitan ka, saidai hajiya Nana da hajiya Sulthana sun fita tare da oga Zayyad awa 2 da suka wuce kuma sun dawo awa 1 da ya wuce amman ba tare dashi ba suka dawo"
"Ba zallan baƙi ba a yaran gida babu wanda ya shigo da safe?"
Yayi wannan tambayar ne don yasan yanzu sun ɗauki ƙannen matar shi kaman ƴan gida ne kuma yana so yasan yaushe Sulthana tazo har taje ta tunkari Zayyad da wannan maganar,
"Allah ya baka yawan rai direban Hajiya ya É—auko Hajiya fatima daga makaranta bayan ita babu wanda ya shigo da safe saidai su da suka fita suka dawo amman jiya bayan ka tafi Hajiya Sulthana ta shigo kuma inajin a nan ta kwana"
"Very good, bayan haka kuma sai me ya faru?"
"Ranka shi daÉ—e Naga Hajiya Rumaisa da oga sadiq tare da junior sun fito daga sashen aunty amarya sun shiga sashen Hajiya amman tafiyar su da tata ba É—aya ba bata ma daÉ—e da komawa ba"
"Bayan su akwai wanda ka lura da alamar tambaya a kanshi a cikin ma'aikata ko masu wucewa ta waje?"
Girgiza kai yayi yace "babu Allah ya baka yawan rai, kowa yana aikin shi yanda ya kamata"
"Toh Masha Allah" ya zaro 3k a cikin aljihun wandon Zayyad ya miƙa mishi, yaji lokacin da ya ciri kuɗin a aljihun shi amman ko gizau baiyi ba ballantana yayi magana "aikin ka yana kyau malam lado, kaci gaba da saka min ido a cikin gidan nan kada ka yarda ayi baka gani ba,
"Insha Allah ranka shi daɗe" sauƙe ajiyan zuciya Zayyad yayi jin yau information ɗin nasu ba mai yawa bane, wato tunda Baba ya hana shi installing CCTV cameras a cikin gidan shine ya baza spies suna ɗauko masa komai da komai, ya zamo kaman shine shugaba a gidan gaba ɗaya kowa umarnin shi yake bi, dake baba ba mai yawan faɗa bane shiyasa suka fi tsoron Sulaiman a kanshi,
*****
"Gashi nan ya dawo wallahi" fa'iza ta faɗa ma Sulthana dake ta kai kawo a wurin zuciyar ta cike da fargaban gamuwan su da sulaiman, ko minti ɗaya bata ƙara ba ta shiga part ɗin da ke gaban ta a guje,
Batool dake amsa waya tana ta faman kashe murya ta É—ago tana kallon Fa'iza da alaman tambaya tace "waye ne ya dawo Fa'ee?"
"Oh tambaya ma kike yi? To yaya Sulaiman ne"
"Mtsww to sai mene dan ya dawo zaku fara gudu sai kace wanda kuka ga aljani? Ni bansan dalilin da yasa kuka ɗauki tsoron shi kuka saka ma ranku ba, mutum ba duka yake yi ba, ba zagi ba, bayi shiga harƙan kowa amman duk kunbi kun damu kanku a kanshi"
"To wallahi a halin yanzu da kiyi karo da Babban yaya gwanda kinyi karo da ƙaton aljani me kai 10 domin da safen nan Nana da Sulthana sun taɓo shi a kan matsalar ya Zayyad"
Sauƙe wayar kunnen ta tayi, ba shiri tayi disconnecting kiran a razane ta zaro ido tare da dafa ƙirji tace "dan girman Allah??"
Fa'iza bata tsaya ta ƙarasa sauraron ta ba ta arci na kare ta shige part ɗin da ɗazu Sulthana ta shiga shine na Hajiya mahaifiyar su saboda ta hango shi yana tunkaro su gadan_gadan, Batool ko tsayawa saka takalminta bata yi ba da socks ɗin ƙafanta light green haka ta taka da ɗan iskan gudu ta rufa ma fa'iza baya suna zuwa dukkan su suka ɗuru daki ɗaya suka rufe da key,
Kowa ta ƙame a angle guda zuciyar su yana bugun tara_tara da kalolin salati ɗauke a bakunan su, Nana da tayi mai gaba ɗaya harda hawaye suke gangaro mata saman fuska tasan yau idan ba wani ikon Allah ba sai tayi nadaman zuwan wannan rana,
Yana shigowa yaga babu kowa a main parlo sai Junior dake zaune yana playing video game yana ganin shi ya bari ya ƙaraso wurin sa,
"Kaje ka kira mun duka ƴammatan dake cikin gidan nan" ya bashi umarni a taƙaice,
Ɗakin da suka shiga ya fara zuwa Yana knocking tare da kiran sunan su ɗaya bayan ɗaya yana isar da saƙo, saida yaji sun amsa shi kafin ya fita daga part ɗin ya nufi ɗayan ba'a daɗe ba ya dawo lokacin su Nana suna fitowa daga ɗakin da suka buya, har zasu samu wurin zama yayi saurin gwada musu ƙasa da yatsun shi "on your kneels"
Kaman zasu fasa ihu suka zuba kan guiwowin su, kallon junior yayi tare da tambayar shi "ina Ruma?"
"Tana wanka ne babban yaya amman ta kusa fitowa"
Tsaki yaja ya kama hanya ya fita fuuu bai tsaya ko ina ba sai part ɗin dake gefen wanda ya fito yana shiga ya samu babu kowa a parlo sai masu aiki dake dusting ya wuce ya shiga daki na uku dake ta hannun hagu, yana shiga ya ƙarasa bakin ƙofar bathroom yayi masa wani bugu ɗaya da ƙarfi kaman zai ballashi cikin kururuwa yace "Rumaaaaaa"
Ba don ta rufe da key ta ciki ba babu abinda zai hana ƙofar buɗuwa, Ruma kuwa ta gama saka sabulu a jikin ta harda fuskar ta taji wannan kiran da ya saka ta kunna shower ta sake ma kanta ruwa harda gashin kanta saida ya jiƙe shaƙaf dukda ba wani tsayi sosai yake dashi ba amman saida ya sauƙo ya rufe mata idanu da kunne saboda yana da cika,
Ruwan bai gama ɗauraye ta ba ya sake yi ma ƙofar wani duka a ruɗe ta laluɓa ta jawo towel a jikin hanger ta maida gashin da ya rufe mata ido ta baya ta buɗe ƙofar ta fito, gefen wuyan ta da jikin ƙafanta duk kunfa haka ko hijab bai barta ta saka ba yaja hannun ta suka fita amman wannan karon ta ƙofar kitchen suka fita don shine yake ta baya babu wanda zai ganta, a haka suka shiga part ɗin hajiya tana rungume da towel a hannu,
Har zatayi kneeling yanda taga ƴan uwanta sunyi ya hana ta yace ta zauna a kujera kaɗa garin haka towel ɗin ya buɗe, Ruma baƙaramin basu dariya tayi ba don ta fito sakk mahaukaciya amman duk cikin su babu wanda ya isa ya dara a gaban shi babu ma mai kwanciyar hankalin yin dariya suka baza kunne suna sauraron shi,
"Wato kun zama Æ´an iska ko kun kaida mu abun wasan ku??"
Shiru sukayi suna ƙifi_kifi da ido ya sake maimaita tambayar shi a tsawace
"Nace kun zama Æ´an iska ko?"
Girgiza kai suka fara yi hawayen da Sulthana take maƙalewa suka fara zubowa da Ruma da bata san mai ya faru ba itama ta saka kuka don duk cikin su itace ƙarama bata da taurin rai irin nasu,
"A'a babban yaya kayi haƙuri dan Allah"
"Duk shegiyan da ta sake buÉ—e baki ta bani amsa sai naci mata mutunci shashashu wawaye,
kwanaki na tara ku irin haka na muku warning lokacin da mene ya faru?"
Shiru sukayi suna binshi da ido yace "ba zaku bani amsa bane Æ´an iskan yara"
Murya na rawa suka haÉ—a baki wurin faÉ—an "lokacin da Ruma ta faÉ—a ma Batool da Fa'iza matsalar Ya Zayyad"
"Wani hukunci nayi mata?"
"Ka maida ita makaranta a Lagos"
"To billahi zan ci muku mutunci ƙananun ƴan iska tunda ku na farko bai zamo muku ishara ba nasan maganin ku ƙauye zan kaiku nayi muku aure a can wallahi idan wani yaji wannan maganar kunji na rantse"
Ai nan parlo ya karaɗe da kuka ko wannen su saida ta zubar da hawaye harda wanda ba dasu aka ce za'ayi ma aure a ƙauyen ba don shi da Nana da Sulthana yake yi, yasan su Batool da suna da niyar faɗa ma wani da sun daɗe da faɗa,
"Kayi haƙuri babban yaya wallahi ba zamu sake ba"