← Book details Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 73

Sashe 43

Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kambu...What did she just said?! Ni É—inne take wa kallon mahaifin ta?" Ya faÉ—a cikin zuciyar shi yana taraddadin dalilin da ya saka ta faÉ—a hakan,
Duk wannan soyayya da kulawa da yake nuna mata a fakaice har yanzu ƙwaƙwalwarta bata ganar da ita sonta yake ba shine tsaban wulaƙanci ta rasa matsayin da zata bashi sai na mahaifin ta? Ko yayi kama da wanda ya isa ya aifi sa'ar ta ne? Dududu shekaru 4 kacal ya bawa zayd  "am i that old?" Ya sake tambayar kanshi, ganin bayi da amsa sai kawai ya ci gaba da sauraron su,

"...mai É—aukar É—awainiyata ta yaya za'ayi na iya fuskantar sa a matsayin girlfriend É—inka ina jin kunyar sa gaskiya"

"Finally!!" Zayyad ya faÉ—a yana dariya "las_las kinyi admitting ke girlfriend dina ne and I'm happy to hear that, yanzu yaushe kike son ki fara kiran kanki matata?"

Ganin yana niman canza wa hirar akala yasa na katse shi ta hanyar jefo mishi tambaya,

"Kama tunamin....mai kacewa baby Hanan jiya banji ba?"

"Ehh!!! Miss jealous ba mun ƙarƙare maganar nan jiya ba, Please ki daina damun kanki a irin wannan dukda kuwa na san ni ɗin mai tsada ne amman naki ne ke kaɗai sai yanda kika so kiyi dani,
And it's not fair da kika saka ma ƙawanki such a lovely name amman ni kika barni da hamma, gaskiya ki sauya zani ban yarda ba"

"Hamma zayd Hajiya tana kira na ina zuwa"
Na faÉ—a tare da katse wayan jin motsin mutum kada wani ya fito ya tarar dani a haka,

Fa'iza ne ta fito cikin riga da wandon jeans tasha hula irin wanda akewa laƙani da baby cakwai hannun ta riƙe da plate wanda aka gama cin abinci a ciki daga gani kitchen zata maida shi,

Mikewa nayi na kira sunan ta da "aunty Fa'iza" kaman yanda na saba fuska na É—auke da murmushi don dukda tana da wuyan sha'ani wurin aibanta mutane da rashin kunya amman tana da kirki dai'dai gwargwado,

"Aarrrhhh international babe, our makauniya yaushe a gari? Oyoyo" ta faÉ—a tare da ware hannunta ta rungume ni ba tare da ta ajiye plate din ba,

Ta É—an rusuna tana cakalar kumatun Jannat tana mata wasa, itama murmushi ta maida mata ta gaishe ta don sun saba sannan ta mana jagora cikin bedroom É—in hajiya daga nan tayi wucewarta kitchen É—in,

  *******
"Hhh Saudatu kenan iyayen kunya, yaya kaga taƙi yarda ku haɗun gaka sirikin ta"

Tsananin takaici ya hana sulaiman magana yana jin zuciyar shi kaman zata yi aman wuta yayi saurin juyawa ya bar wurin, yama kasa fasalta abinda yake faruwa, a wani babi zai ɗauke ta? Anya kuwa Saudat ba twins bane? Anya ba hussainan Saudat bane take tare da zayyad suke son gwada shi? Anya babu wani ƊAURIN ƁOYE cikin wannan lamarin, ko fansa zayyad yake nima na ƙuntata rayuwar shi da yayi yasa ya fara soyayya da abun ƙaunar shi, dukda bai gaya ma kowa ba amman yayi tunanin kowa ya fahimci tuntuni yana son ta, yana tsananin sonta yana ƙaunar ta yayi tattalin ta ba zai bari ta suɓuce mishi lokaci ɗaya ba,

Daidai an buɗe mishi back seat na motar shi zai shiga zayyad ya cim mishi tare da janyo kafaɗar shi ya dawo baya yana ƙare ma fuskar sa kallo ganin yanda idanuwan sa suka rikiɗe sukayi jaa lokaci ɗaya,
"Lafiya kuwa babban yaya?"

Haɗiye wani abu mai ɗaci yayi da ƙyar ya iya buɗe baki yace "indai da gaske kake yi ba gurguwar fahimta nayi wa abun ba to KACI AMANATA zayyad"

"Cin amana kuma? What are you talking about....ban fahimci komai ba"

Da kaman ba zai sake tanka shi ba sai kuma yaga idan yayi hakan zai cutu ya tura ƙofar motar ta baya da ƙafan shi ya rufu kada driver ya saurari maganar da zasu yin ganin haka yasa wanda ya buɗe mishi mota ma yayi gaba sannan ya fuskanto shi,

"Tell me zayyad...wani mummunan abu nayi maka wanda ban sanda shi ba har ka zaɓi ɗaukar fansa ta wannan hanyar? Dame na cutar da kai a rayuwa da har ka dage wajen ganin maƙurar ɓacin raina"

Shiru yayi yana nazartan kalaman shi har yanzu ya kasa ɗago haske, ya kasa fahimtar saƙon da ɗan uwan nashi yake isar masa cikin ƙunar rai wanda a zahiri ya nuna,

"Kayi amfani da damar da na samar wa kaina ka sace zuciyar ta, kayi amfani da wasu siddabaru naka ka saka ta saki jiki da kai tana maka hira mai daɗi tana maka laƙani da nata tana lanƙaya sunan ka da rayuwar ta don kawai ka cutar dani??

Ba uwa ɗaya ce ta aife mu ba amman ban taɓa la'akari da hakan ba na ɗauke ka matsayin tsoka da jini ɗaya ke gudana a jikin mu domin na ɗauki mahaifiyan ka matsayin nawa kaman yanda naga ka ɗauki tawa a matsayin naka, tun kana ƙarami nake ƙoƙarin inganta rayuwar ka dukda nima ina halin ƙuruciya amman na san abinda kai baka sani ba yasa nayi fafutukar ɓoye aibin ka wajen ganin na sama maka gata kaman yanda ni da Nafi'u muke dashi, ka mallaki abinda zaka riƙe kanka harda da ƴan uwan ka idan mahaifin mu ya kasa amman a maimakon haka irin sakayyar da zaka min kenan?

Saida ka san cewa nayi nisa a ƙaunar Saudat zaka shiga tsakani na da ita zayd? A wani dalili?"

Daram..daram...dum...dum!! haka ƙirjin Zayyad ya fara lugude jin kalaman sulaiman na ƙarshe don sai yanzu ya fuskanci inda ya dosa, murya na rawa yace

"B..b..yaya k..kana son... Saudat fa kace?"

"Don't pretend please zayd, na sanka tun kana yarinta you are very cunning sometimes, amman ban taɓa tunanin you can stoop so low don kaga ka kaini ƙasa ba dan Allah me nayi maka" ya ƙarasa maganar a tsawace,

Ƙarasawa kusa dashi yayi zai taɓa shi yayi saurin ja da baya "bansan menene manufar ka ba, bansan shirin ka na gaba a kaina ba, daga ƙwace saudat bansan gaba mai zaka sake ƙwacewa ba amman dan Allah ko dan darajar iyalina da mahaifiyata da ya rataya a wuya na kada ka raba ni da rayuwata"

Zayyad baisan lokacin da hawaye mai tsananin zafi ya zuba daga idon sa É—aya bisa kuncin sa ba É—ayan kuma a bushe, irin kukan nan ne da akeyi na takaici yayi sakare yana kallon babban yaya, fuskarsa kaÉ—ai ya isa ya nuna kalaman sa daga zuciya yake fitowa,

Ko me Zaid ɗin yayi mishi kallon hawayen shi abu ne mai matuƙar wuya wanda yake saurin tsinka mishi zuciya, juyawa yayi saidai ko taku ɗaya baiyi ba ya jiyo muryan zayd yana faɗin,

"Bansan kana sonta ba yaya, da na san da haka ko kallo na biyu na shauƙi ba zan sake mata ba ballantana har na bar zuciya ta tayi zurfi a sonta"

"Ƙarya kake yi zayd, daga kai har saudat har kowama ya san da cewa ina ƙaunar ta, tayi lacking ilimi na sama mata shi, tayi lacking wayewa na sama mata shi, ina ƙoƙarin tankwasa zuciyar ta don ta furta min kalman so koma ta nuna hakan ba tare da faɗa ba amman ta fahimta kuma taƙi, shekaru 3 na ɓata ina jiran tsammani amma....."

"Wallahi ko kusa bamu da masaniya a kan soyayyar da kake mata, baka taɓa furtawa ba yaya kum...."

"Kuma ko ban furta ba amman ai na gwada, bayan matata ka taɓa ganin na kashe lokaci na a kan wata ƴa mace ne bayan Saudat??"

"Wannan mun É—auke shi a matsayin taimako ne, irin wanda ka saba yiwa mutane saboda Allah"

"Taimako? Da lokacin nawa ne zanyi taimako? There is nothing left to say you BETRAYED me kuma ba zan yafe muku a kan hakan ba, idan Saudat ce kuma gata nan na bar maka ita ina fatan hakan zai sanya ka farin ciki"

Ya juya kaman da gaske ya haƙuran ne saida ya shiga mota har sun fara ƙoƙarin fita daga gidan saboda jaraba ya buɗe ƙofar motar ya fito har lokacin zayyad na tsaye ƙeƙam a yanda ya barshi,

"Ban ɗauki soyayyar saudat don na sauƙe ba, don haka ni da kai mu zuba mu gani wanda zaiyi nasara...........🤦🏻‍♀️

_Amman seriously baku ga kaman Sulaiman yafi dacewa da saudat ba saboda hidimar da ya faɗa yana mata😜😝😅

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

🤍💚🤍
    *ƘARAMAR BAZAWARA*
           💚🤍💚

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

         *BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
  And *AISHA ALTO*

🌹🌹🌹FEEENERH MATAR SOJA 🌹🌹🌹

💃ina masoyan feenah matar soja  marubuciyar ✍️✍️✍️✍️

HARAMTACCIYAR SOYAYYA

AURAN SOJA

YAYAN GATA

KUSKURENA

BARIKI AURAN SOJA

WANAKE AURE

😍wannan karonma ta dawo muku  da sabon littafinta  mai suna 👉 ZANYI BIYAYYA😌  ina masoya hausa novels toga dama ta samu littafin ZANYI BIYAYYA  😌  yaxo muke da solo 💃💃 daban daban
domin san ku fadakantu ,waaxantu dakuma nishadi ku biyota awannan shahararran littafinta ZANYI BIYYAYYA😌  masu iya magana nacewa anayi dakai  yafi ba,ayi dakai karku bari abaku labari koda kudinka akace sai da rabanka🤸‍♀️🤸‍♀️🤸‍♀️🤸‍♀️🤸‍♀️

gamasu bukatar biya ku hanxarta  karku bari abaku labari kubiya ku karanta cikin Aminci, katin Airtel 200 zaku turo normal VIP   500  kuturo katinku ta wannan number  09011251444  ko ta Asusun banki na  7304736012 NAFISA SANI   fcmb yan niger🇳🇪 masu bukatar biya kunemi wannan number +225 48 15 39 03

36🧝🏻‍♀️
Na gaji da sadaukar maka da abubuwa masu daraja don na lura kai ɗin BUTULU ne mai saurin manta alkhairi, ga fili ga mai doki idan ka isa kada ka fasa karawa dani a yaƙin niman soyayyar saudat, ni kuma zan manta duk wata alaƙar dake tsakanin mu na gwada maka isa ta...ba don wai muhimmancin ta ya kai hakan ba A'a sai dan na ɗanɗana maka zafin yaudara ta da kuka yi,
Chapter 43 · 0% Book details