← Book details Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 73

Sashe 47

Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amman ya sota kuma har yanzu yana sonta, da ace ɗan adam ke ɗaura ma kanshi soyayya da Saudat bata shiga ko cikin jerin kaso na 10 cikin kalan matan da yake so ba, amma tun tana tatsitsiya yake sonta tun a lokacin yake mata kallon ƙwaila amman hakan bai saka shi ya janye ba, saidai yanzu dole ne ya janye ɗin dan ba zai taɓa auren ta a matsayin bazawara ba musamman ma a yanzu da baisan dalilin da ya fito da ita daga ɗakin mijin ta ba idan ta tabbata bazawaran ce da gaske kenan,

Da ƙyar ya iya jan jiki ya fitar da kanshi daga cikin motar cikin wani kasala da ya dirar masa saboda baƙin ciki ya shiga gida yana layi kaman wanda yayi maye,

a yanxu Sadiya ta fara saduda tayi sanyi kusan rabin makaman yaƙin ta tayi watsi dasu don faɗan yafi ƙarfin ta a yanzu gashi bata da mataimaki, saboda the more tana ƙoƙarin hana faruwan wannan al'amari tsakanin Saudat da sulaiman sai taga kaman daɗa angiza shi take yi tana ƙara ma wutan fetir,

Ta kaɗa ta rawa abu yaƙi ci don har sharri suka taɓa yi ma saudat a lokacin bikin Muna kan cewa ita ta sace gold ɗin sadiyan wanda yafi kowanne tsada bayan ita da hannunta ta ɗauka ta bata kan tasa, da taƙi daga farko sai sadiyan ta nuna fushinta sosai tana cewa ita bata ɗauke ta kaman dangi bane yasa take maida mata hannun kyauta baya, da ta matsa sai Saudat ɗin ta amince gudun ɓacin ran babban yaya da taga kaman ma ba sakawa zatayi ba sai ta saka mata shi a wuya kuma ta hana ta cirewa dashi dole taje dinner,

Ana tsaka da biki wuri yayi wuri taro na manyan mata da haɗaddun maza masu ji da isa da kuma dukiya a tsakiyar su Sulthana tazo ta fizge sarƙan har saida taji ma saudat ɗin ciwo a wuya, ƙarar da ta sake da tsawan da Sulthanan take mata ya sanya wurin yayi tsit hankalin kowa ya dawo kansu,

Har akayi komai aka gama Sadiya bata ce komai ba dukda rantse rantsen da Saudat ɗin take yi haka ma babban yaya yana zaune ƙeƙam kaman gunki ya zuba musu idanu ɓari ɗaya na zuciyar shi yana ayyana mishi da gaske sata tayi wani ɓari kuma yana tunatar dashi irin nagartan Saudat din,

Zayyad!! Mutum ɗaya wanda da ƙyar ya samu zuwa bikin saboda zaman wuri ɗaya ya ishe shi shine kaɗai mutumin da yazo gaban kowa da kowa ya take mata ya aybanta abinda Sulthanan tayi don itama da nata haushin ta ƙwace mata saurayi, ganin shirin su yana niman faɗuwa ƙasa warwas yasa ta yi maganar "dalilin da yasa Sadiya bata bawa saudat sarƙan haɗe da ɗan kunnen shi ba indai a gaske batan tayi"

Shima zayyad ya mayar musu da cewa "ai ita ba doluwa bane da idan ta sata zata saka kuma ta shigo cikin su dashi har ta bari su gani" wannan kalamin shi ya tabbatar ma sulaiman duk abinda ya faru shiri ne kawai don a sanin shi Saudat batayi wayon da zata saci abu mai tsada kaman wannan har ta siyar ba yana da tabbacin bata san darajar shi ba,

A sannan ne zayyad ya raba gari da Sulthana ita kuma uwar gayya consequences ɗin da hakan ya jawo mata yasa tayi danasanin fara shi a rayuwar ta don taga tashin hankalin da bata taɓa ganin irinshi ba a wurin mijin nata,

Kallon shi tayi cikin wannan yanayin amman tosashshen ƙwaƙwalwarta bata faɗa mata taje ta tare shi taji me ya same shi ba har ya wuce ciki, shi kuma a lokacin yana tsananin buƙatar mai kulawa ko mai sauraro daman saudat ɗince yakan kira wani lokaci koda tana makaranta ya saka a bata waya ya ɗan tambaye ta shawarin ta a kan wasu abubuwa wanda bata ɗauki hakan a matsayin wani abu ba amman yau Saudat ɗin ita taji masa ciwo.a zuciya,

Zayyad bai faɗa min komai da ya faru a ranan ba, bayan ya farfaɗo ma da aka kira sulaiman aka faɗa mishi ciwon shi ya tashi bai gwada wani matsanancin damuwa ba, bai yashi hankalin shi ya daburce kuma ya dawo a kan ƙafar shi kaman da ba, sai kawai yayi masa addu'a ya kashe wayar kan cewa za'a fara nima mishi magani kwanannan insha Allah,

Aunty ta jingina hakan ne da cikar buri da biyan buƙata da suka samu zayyad ya riga ya fara aiki shiyasa babu sauran damuwa,

Cikin sati biyu rikici sosai ya ɓarke a tsakanin su suka dawo basu yin ko ga maciji ina gefe bansan me yake faruwa ba saidai ya rage kirana a waya yanzu bamu yin dogon hira, kullum muryar shi cikin damuwa ina ji a jiki na akwai abinda yake ɓoye min amman idan na tambaye shi sai yace min babu komai,

A wannan yanayin da suke aka samu mai maganin da aka fara kai zayyad kuma alhamdulillah yanzu ana samun dama dama kaɗan tunda magani sai a hankali..........🤦🏻‍♀️

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

🤍💚🤍
    *ƘARAMAR BAZAWARA*
           💚🤍💚

    _(Cigaban matar kulle)_

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

         *BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*

39🧝🏻‍♀️
A kiÉ—ime na juyo ina kallon shi don ban gane abinda suke nufi ba dukkan su, a dalilin me zaisa zayyad hana ni bin babban yaya? Kuma a kan waye sulaiman yake magana?

Sassauta murya nayi yanda sulaiman dake tsaye a jikin motar dake gaba na ba zai jiyo mu ba nace
"Hamma zayd bamu kaÉ—ai zamu fita ba fah! Kuma baka san inane zamu je ba me yasa zaka ce kada na bishi?"

"Ok tun yanzu har zan fara jayayya dake?"

Irin tone É—in da yayi amfani dashi wurin magana yafi kama da na babban yaya ba na zayd da na sani mai magana ko yaushe cikin sanyi da lallami ba, shiru nayi inajin wani iri na kasa komai ga sulaiman da ya tsare ni da idanuwa khamis yana jifa na da mugun kallo, ina taku É—aya kaman a kunnen shi yace,

"Dan girman Allah boÉ—É—i kada ki bishi gani nan zuwa inda kuke, kada ki bari ya yaudare ki da kalaman shi ya sanya katanga a tsakan...."

"Mahaifiyarki zata gaji da jira Saudat, iyayen ki na tsumayen ganin ki kizo muje kiga halinda suke ciki"
Kalaman shi da naji dirin sauƙar su kenan cikin ƙwaƙwalwa da zuciyata,
A iya sanin da nayi wa babban yaya babu wasa ko ƙarya a tsakanin mu ko fuskar shi da mutanen da yake tare dasu kaɗai ya isa ya tabbatar min da gaskiyar zancen shi,

Wasu hawaye masu sanyi ne naji sun fara bin kunci na, ban gansu ba amman har naji sanyin ciwon dake cin zuciya ta tsawon shekaru sama da 5, disconnecting kiran nayi ba tare da na sani ba da gudu na nufi motar da naga aunty yusrah a ciki na shiga muka É—au hanya,

Fakan idon ya Nafi'u wanda Jannat ta saka a gaba da surutu tayi ta Mintsile ni a cinya tana harara na,
"Kina son ku saka ƙafar wando ɗaya da abban jannat ko? Ana miki magana kin tsaya kina shiririta ma mutane sanin kanki ne bayi son rawan kai tun kafin ya saɓa miki ki shiga hankalin ki"

Maganar ta ya shiga kunne na amman banji abinda ta faÉ—a ba, my mind was absent ganin abunda ke faruwa yau É—in nayi kaman a mafarki,
kwantar da kaina nayi a saman kafaɗar ta da hannu na zagaye kunkumin ta na rungume ta sannan na saki kuka mai zafi koda zanji sauƙin abinda yake taso min,

Bubbuga baya na takeyi a hankali cikin sigar lallashi ya Nafi'u ya miƙo mata kwalin tissue ɗungurungum tana share hawayen fuska na dashi, ni kuwa ji nakeyi kaman na ƙwace tuƙin motan daga wurin shi don gudun da muke surfawa a titi bayi min sauri babban buri na a yanzu kawai na ganni a gaban Inna ta da baba na,

A maimakon mu ɗauki hanyar wuroɓokki sai naga munyi parking a ƙofar asibiti, rasss naji ƙirjina ya buga ganin suna fita daga cikin motar babban yaya har ya nufi cikin asibitin, hakan kenan na nufin babu lafiya, wani nawa yana cikin matsala,

Ganin bani da niyyan motsawa yasa yusrah taja hannu na muka fita, a hankali take tafiya ina biye da ita a baya zuciyana yana bugun uku_uku baki na ɗauke da kalolin salati har muka isa room 6 ya saka kai ya buɗe sannan ya tsaya a jikin ƙofar yana kallo na,

Zaune take a saman gadon anyi mata matashi da pillow ta jingina bayan ta da jikin gadon, inna ta ƙara tsufa sosai a cikin shekaru 5 kacal saboda wahala da damuwa da har wrinkles sun fara bayyana saman fatar ta, ji nayi zuciyata ta karye lokacin da na saka idanu na cikin nata, kallo ɗaya zakayi mata kasan har yanzu tana jinjiki amman hakan bai hana ta sakin murmushin da na ɗauki tsawon lokaci ban ganshi ba cikin sassarfa na ƙarasa wurinta sannan na zuba a kan guiwa na tare da kifa kaina a kan cinyar ta na shiga rero kuka mai tsuma zuciya,

Babu wanda yayi ƙoƙarin rarrashina don a yanzu kukan shine mafi a'ala domin zai rage min wani abu daga ƙuncin dake zuciyata, munfi 4 minutes a haka wurin ya ɗauki shiru sai sautin kuka na kawai dake tashi, da ƙyar inna ta iya ɗaga hannun ta saboda nauyin da zuciyarta tayi ta ɗaura shi a kaina,

"Tashi boɗɗi am, innar ka tana lafiya ka daina kuka babu abinda ya same mu" shine kalaman da ta dinga maimaitawa har na rarrashi kaina na ɗago ina sake ƙare ma fuskarta kallo, she is my first love, mutum na farko da ta yarda dani sama da kowa dukda a lokacin bata nuna ba,
Chapter 47 · 0% Book details