← Book details Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 73

Sashe 12

Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A'a ina gida, me ya same ki ne aunty muna naji muryan ki wani iri"

"Ba dole ba, wannan mutumin duk ya wargaza min lissafi, me yasa ze kaiku wani wuri ba tare dani bane bayan yasan duk tare muke a makarantar?"

"Aunty Muna na faÉ—a miki horo fa ze kaimu wurin nan laifi mukayi masa" Sulthana ta faÉ—a cikin kasashshiyar murya,

"Wani laifi ne wannan dan Allah nima nayi ya haÉ—a dani ya tura wurin nan ba zan yarda ku tafi ku barni ni É—aya ba wallahi, ki faÉ—a min wani laifi ne wannan kafin gobe zan aikata shi na ranste"

"Gaskiya ba zan iya ba aunty maimoona, ina tsoron wannan sirrin kaman yanda nake tsoron mutuwa ta, babban yaya zai iya katse min duk wani jin daÉ—in rayuwata saboda wannan sirrin dan Allah kada ki saka ni cikin matsala" ta faÉ—a kaman zata fasa ihu,

Shiru Muna tayi na Æ´an seconds sannan tace "wani sirri kenan? A ina yake wannan sirrin naje na bankaÉ—o shi don nima ayi min abinda nake so? Ki faÉ—a min yanda wannan sirrin yake yanzu yanzun nan inje na bankaÉ—o shi kowa yaji"

Kuka Sulthana ta saka tace "A'a wallahi kada ki jawo ma kanki Muna zqki shiga matsalar da fita daga cikin shi sai wani ikon Allah nidai ba zaki taɓa samun wani bayani daga gareni a kan wannan sirrin ba" kitt ta katse wayan bata bata daman sake mata wani tambayar ba,

Shiru Muna tayi tana tunani tare da jinjina girman wannan sirrin da har ƴar uwarta na jini bata so ta sani, dole ne kafin lokaci ya ƙure mata ta san koma menene, dan haka tayi saurin miƙewa ta shirya da nufin zuwa gidan su Sulaiman ta zauna a can dan tana da tabbacin a can wannan sirrin yake kuma ta ɗau aniyar nimo shi duk inda ya shiga ta fito dashi indai shine abinda zai saka itama a tura ta karatu ibadan,

**********
Zaune nake na saka hannaye na biyu na tallafo fuska na baki buɗe kaman yawu zai ɗiga na saka zango da ali nuhu a gaba ina ƙare musu kallo a TV kaman ba ni bace na gama kukan faɗuwar jarabawa ɗazu ina faɗin IS ME NO TV ba!

Awa na biyu curr ina zaune ina kallon film ko abinci na kasa tashi naje naci, sallan magriba ma a daddafe nayi don tun bayan da muka gama girka dinner aka kawo wutan nepa,

Aunty Yusrah tayi kiran duniyar nan nazo muyi karatu kaman yanda tace amman kaman wanda na na zauna a kan kunne na banma ji lokacin da ta kira nin ba, har ta gaji da zaman jira ta tashi ta ci gaba da sabgogin ta don bata son takura ni, gashi yau tunda rana ta kusan faÉ—uwa take jin ciwon jiki musamman bayanta,

Ban tashi daga gaban tv ba har saida Khamis ya shigo gidan gudun kar a sake min zancen komawa gidan su yarima,

1:30am
Naƙuda ya tashi ma aunty Yusrah.......🤦🏻‍♀️

_ban tsara littafi na a matsayin na kudi ba kuma bani da niyyar maida shi na kuÉ—i amman Idan har ban samu comments da suka kai 150 a duk groups É—in da nake Sharing ba in Allah ya yarda daga yanzu na daina turowa a WhatsApp mai son karantawa saidai yaje wattpad_

#vote
#share
#comment.

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

🤍💚🤍
    *ƘARAMAR BAZAWARA*
           💚🤍💚

    _(Cigaban matar kulle)_

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

         BY UMMU NAJMA

DEDICATED TO, MAI DAMBU
  And AISHA ALTO

_Addu'an neman tsari daga maƙiya_
اللَّهُمَّ مُنْزِلَ الْكِتَابِ، سَرِيعَ الْحِسَابِ، اهْزِمِ الأَحْزَابَ، اللَّهُمَّ اهْزِ مْهُمْ وَزَلْزِلْهُمْ
(Allaahumma munzilal-kitaabi, saree'al-hisaabi, ihzimil-'ahzaaba, Allaahumma ihzimhum wa zalzilhum.)
Allah, Revealer of the Book, Swift to account, defeat the groupsO Allah, defeat them and shake them.

09🧝🏻‍♀️
Sosai hankalin mu ya tashi ganin yanda take murƙusuwa tana faman yarfa hannuwa cikin azaba, wani lokaci tayi kuka idan ya ɗan sake ta kuma ta kama salati tana tallafe bayan ta, amman abu kaman ƙarawa ake yi duk bayan minti biyu sai ta daɗa shiga wani hali,

Kasancewar bata tare da Khamis lokacin aihuwar ta na farko yasa sai abun yazo masa a sabo duk ya rikirkice ya rasa wani abu ɗaya da zaiyi mata ma yana zaune riƙe da ita sai sannu yake yake faman jero mata yana mata fifita a maimakon ya sunkume ta mu tafi asibiti,

Nice ma mai azancin haɗa kayan da zamu tafi dashi wanda mama tamin bayanin za'a buƙace su don haka da an tashi tafiya da ita asibiti na tattara mu tafi dashi, na zuba kayan a ƴar ƙaramar jaka bayan ta gama galabaita Khamis ya riƙo ta ya saka ta a mota nima na shiga muka wuce asibiti,

Wuraren ƙarfe 4 ta haihu, muna zaune jingum_jingum muna jiran sakamako don ta ɗan dauki lokaci tana naƙudan hankalin mu gaba ɗaya ya tafi jikin ɗakin aihuwan muna jiran muji da wani labari za'a iske mu, doctor na fitowa ya Usman da Khamis suka ƙarasa wurin shi suna tambayar yanda aunty Yusrah ta samu kanta, da murmushi a fuskar shi ya miƙa ma Khamis hannu suka gaisa sannan ya sanar dasu ta sauƙa lafiya ta aifi ɗa namiji yanzu an tura ta ɗakin aihuwa,

(Nace ko Khamis bai lura likita namiji bane ya karɓi aihuwan?) A maimakon yayi rikici ko wani tashin hankali sai niman wuri yayi ya zauna yana hamdala ma ubangiji farin cikin dake shimfiɗe a saman fuskar shi ya gaza ɓoyuwa,

Tashi yayi a nutse ya buɗe ƙofar ɗakin ya shiga tare da rufowa hakan na nuna mana bayi son kowa yabi bayan shi kenan shiyasa muma muka yi zaman mu a waje amman a ƙage nake su gama abinda zasuyi na shiga na gano baby ko shima ya fito irin 'kuut' (cute) ɗinnan da ake faɗa,

Dago lumsassun idanun ta tayi wanda suke cike da gajiya ta zuba mishi da ƙaramin murmushi a saman lips ɗin ta, ga babyn da aka shirya aka kwantar mata dashi a saman ƙirjin ta yana jin ɗumin jikin ta,

Daidai saman goshin ta yaje ya sake mata peck tare da lumshe idanuwan sa yana jin wani sanyi da daɗi yana ziyartan zuciyar sa, dariyan Yusrah ne ya sanya shi ɗago kanshi ya zuba mata ido cike da so da ƙauna, he wonders what makes her so happy a cikin yanayin da take,

Cikin kasashshiyar murya tace "abinda naso kenan tun farko, amman Allah bai kaÉ—É—ara da rabo na bane a wancan lokacin, lallai shi mumini kada ya cire tsammani da rahaman ubangiji don bai san a lokacin da zai zo mishi ba, na kusan cire rai da ganin irin wannan ranar Khamis,

Na cire rai da farin ciki da jin daɗin rayuwar duniya lokacin da na rasa ka, amman ganin Jannat a gaba na da kuma amincewa da ƙaddara ta a yanda tazo min na yarda cewa Allah yana da ikon canza min ita a lokacin da yaso gashi abubuwa sun zamo kaman ba'ayi ba"

Baice komai ba don baiga alaman ta gama fitar da kalaman bakin ta ba, ya zura yatsun hannun shi a tsakanin nata sannan ya jawo su daidai bakin sa ya sumbata,

Hawaye ne zurr suka fara sauƙa daga idanun ta daga yanda take kwance amman wa'innan hawayen tana zubar dasu ne saboda farin ciki, ji take yi kaman babu wanda ya kaita Sa'a a yanzu because her family is complete kuma tana cikin farin ciki,

Saida ta sauƙe numfashi sannan ta jawo hannun shi dake riƙe cikin nata hakan yasa dole ya ranƙwafo ya daura haɓar shi saman kanta tana jin bugun zuciyar shi, sake sauƙe numfashi tayi a karo na biyo sannan cikin wani irin murya mai ciwo tace

"Banga wannan farin cikin ba lokacin da na aifi Jannat, all i see is tears, kuka suke min suna ambata min kalmar tausayi tare da ƴata, raina ya ɓaci sosai nayi kuka don sun maida min ƴa kamar shegiya, kowa kallon takaici yake mata a matsayin ƴar mutum mara hankali wamda bai iya kula da kanshi ba ballantana ya kula da wasu, saidai tun daga lokacin na saka wa raina wata rana zasu maye gurbin kallon tausayi da ƙasƙancin da suka min da kallon farin ciki suna min murnan kasancewa cikin masu nasara a rayuwa, ba zan iya rayuwa babu kai ba Abban Jannat"

Yatsun ta dake cikin nashi ya fara murzawa a hankali cikin sigar lallashi yana shafa bayan babyn dake kwance a ƙirjin ta, a nutse ya leƙa fuskar shi sannan ya ɗago idanun shi ya zuba mata duk tayi sukuku ga hamwayen da har yanzu basu bar sintiri a fuskar ta ba,

"Allah yayi miki albarka, Allah ya sanya ki cikin aljannah, ke alkhairi ce cikin rayuwata Yusrah, bansan ta yaya zanyi miki bayani ba amman ban taɓa jin abinda nake ji a yanzu ba a tsawon rayuwata, ba don keba maybe ba zan taɓa samun farin ciki ba har abada, ina yi miki so mai zafi ina tsoron wata rana kada ya illata ni"

"Ba zan taɓa bari wani abu ya cutar da kai ba, koda kuwa soyayya ta ce, zan zama jaruman da zata yaƙi duk wani cutarwa da zai sami familyn ta, i will love and protect you with my life"

"uhm_uhm, not with yours but with mine tunda nine shugaba ni aka sani da sadaukarwa ba masoya na va, i love You so much"

Murmushi kawai tayi tana binsu da kallon sha'awa lokacin da ya dauki babyn yana mishi addu'a, kusan bayan 15 minutes kafin ya buɗe ƙofar muka shigo lokacin an fara kiran assalatu na farko,
Chapter 12 · 0% Book details