Sashe 39
Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murguɗa mishi baki nayi na kawar da kaina gefe saboda yasan dariyan da ya min ɗazu ya ɓata min rai, ya dafe ƙahon zuciyan shi tare da yin fuskan tausayi kafin cikin salon ɗazu ya sake furta 'I'm sorry babes'
"Zayd mu tafi ko?"
"Oh..ok..muje" ya shiga motar sulaiman ya tayar, har suka bar layin Rumaisa tana É—aga min hannu nima haka, shima yayi amfani da wannan damar a fakaice yake waving É—ina,
he wished akwai ranar da zai zo da zamu zamo masoyan sunna bisa inuwan aure mu buÉ—e soyayyar mu ma duniya kowa ya sani, a wannan lokacin ba zaiyi waving É—ina kaman matsoraci ba, he will shower me with lot of kisses yanda har ya dawo tunanin shi ba zai bar zuciyata ba ko na second É—aya,
 *****
A daren ranar aka ga wata ya kama gobe ne sallah, daman mai lallen mu tana ready tazo aka shera mana ja da ɓaƙi, duka lallen ya karɓe ni abunka da farin fata, ya fito darr yayi kyau, haka kawai naji inaso na nuna ma zayyad don sau da dama yana faɗa min yana son yaga hannun mace da lalle yana mishi kyau sosai amman ba zanyi gigin zuwa wurin da yake a halin yanzu ba saboda irin rabuwan da mukayi babban yaya ko yawon sallah ba zanje musu ba kada su sake riƙe ni,
Nayi ƙoƙarin kwanciya da wuri don nasan gobe ba hutu,
1/shawwal/1442
Tunda aka wayi gari muke ta kai komo ana ta hidiman gyara gida da shirya abincin sallah, ƙarfe 6 gari bai gama haske ba na ɗauki jannat muka fita kai markaɗen kayan miya,
Ina zaune ina jiran layi yazo kaina message ya shigo waya na nayi saurin ɗagawa na duba don nasan idan ba wai network bane to saƙon shi ne,
'''good morning babes.....kin kyauta da kika nesanta kanki dani gashi yanzu na kasa barci saboda tsoron wani abu zai iya faruwa dani kuma baki kusa balle ki kare mun, i miss you die'''
Murmushi nayi inajin raina fari tass, na ƙara janyo jannat jiki na matse ta a ƙirji na har saida ta saki ƙaramin ƙara, ta kai min duka da tsintsiyan hannun ta
"Aaauch aunty saudat kyaki kayya ni" ta ƙarasa haɗe da turo baki tana kallo na,
Ban kula ta ba na mayar mishi da saƙo kamar haka,
'''barka da safiya hamma zayd, kada ka damu kanka Allah ne yake bada lafiya kuma shi yake karewa insha Allah babu abinda zai same ka'''
Saida na duba spelling na tabbatar banyi kuskure ba gudun ajina ya zube sannan nayi sending na juyo wurin jannat dake faman jero ƙananun tsaki nace,
"Sauƙa min a kan cinya baƙa mara kunya"
"O'o naƙin ummi tace in makale miki ko kuma ki bayi a sace ni, tace wai baki da wayo"
"Lallai to shikkenan kuwa zan gwada muku rashin wayo na, zanga dawa zaki je masallaci amman idan dani ne saina ɓatar dake da shegen surutu kaman aku"
"Ni abbana zanbi ba zan tafi dake ba"
Ko 2 mins ba'ayi ba ya sake turo wani saƙon, hakan yasa na fita sha'anin ta na ɗaga wayan ina dubawa
'''maganar ki haka yake saudaty amman kuma É—an adam shi ya kamata ya fara kiyayewa, sannan Allah ya riga ya bani maganin matsalar da nake tsoro saidai kaiwa gare shi ne yayi min wuya, shiyasa nake tsoron kamuwa da ciwon zuciyan masoya'''
Murmushi kawai nayi dan na gano kan zancen nashi na share zancen ganin har an gama min markaÉ—en gashi jannat ta ishe ni da surutu na biya su kuÉ—in muka nufi gida ba tare da nayi masa reply ba shima bai sake turo komai ba,
Muna komawa na ɗaura shi a kan wuta sannan na shiga da jannat nayi mata wanka na shiryata sosai na cancaɗa mata kwalliya don babu laifi yanzu na fara ƙwarewa na feshe ta da turarukan uwanta da na ubanta sannan na koma ɗaki nima na faɗa wanka,
Wani daÉ—i nake ji na musamman ina fito da sabon É—inki na da jewelries harta undies sabo ne, lallai adon sallah daban yake ga wani nishaÉ—i da mutum yake ji babu gaira babu dalili, azumi ya saka jiki yayi lafiya sai kaji ka sakayau babu sauran damuwa a tare da kai,
Shiryawa nayi tsaff amman banyi kwalliya ba na tanada sai idan na dawo ban kuma saka turare ba sanin haramcin shi sabida zan iya cuɗanya da maza a hanyar tafiya don a ƙafa zamu,
8:30 na safiya yadiko ta gama shiri taje ta sauƙe miyan tuwon ta aunty yusrah ta ɗaura na shinkafa don ta matsa sai anyi abinci kala biyu, tare da khamis muka wuce masallaci,
10:17 muka shigo gida a gajiye na zuba a kujera don munci tafiya saboda tsakanin gidan da masallaci akwai ɗan tazara, ga gaishe_gaishe da aka tsaya yi da mutane ana ma juna barka da sallah kuna hanyar da muka je ba shi muka bi muka dawo ba kaman yanda yazo annabi (s.a.w) yakan saɓa hanya yayin zuwa masallacin eidi da komowa (amma mustahabbi ne saidai akwai falala a cikin sa)
Haka yadiko tazo kaina ta gama surutun ta ina jinta don bani jin zan iya taɓuka wani abu a yanzu amman duk lokacin da nayi niyyan yima mutanen nan tamɓele na tuna irin halarcin su gareni sai na fasa, a haka na ƙarasa kitchen na sha ruwan sanyi naci gaba da aiki,
 *****
dawowar su daga masallaci kenan suka yaɗa zango a parlor, sulaiman ko damar shigowa ciki bai yau yana jinshi wani iri babu walwala shi ba mai saka wa ranshi damuwa bane shiyasa bai iya shiga damuwa ba,
A yanayin yanda ya karanci saudat gaba ɗaya bata son kusancin shi a tare da ita, tana sakewa da kowa amman idan yana wuri sai ta koma kaman baƙuwa, ba wai raini irin wada take masu zayyad da nafiu bane yake son ya shiga tsakanin su ba Aa, amman yana son tana ɗan sakewa dashi tana faɗa mishi damuwowinta ba tare da ya tambaya ba, ko na kuɗi, ko na shawari ko wani abu da take son a shige mata gaba tana samun shi ba zayyad da yake marili ba,
Ko sonshi ne bata yi? Mata da yawa suna falling mishi saboda wani dalili nasu, wasu kuma saboda arziƙin shi amman me yasa ita ta zamo na daban dukda ya bata ƙofa ta soshi zai amince da ita amman ta kasa ganewa, abin yayi tsanani yanzu har gudun shi take yi, me yasa ta kasa son shi? Maybe yarinta ke hana ta gane soyayya amman yasan definitely nan gaba zata fahimci tana ƙaunar shi, for now zai bata space ne yaga gudun ruwan ta,
Fitowan hajiya yasa suka sarara da É—auke_É—auken hotunan da suke yi suna binta da kallo fara'a bayyane a fuskokin su kowa yaci ado cikin shiga ta burgewa haka itama hajiyan,
Zaytoon ne ta fara ƙarasawa gareta ta rungumeta ta gefe kaɗan
"Barka da sallah mama"
ÆŠan buga bayanta tayi a hankali sannan tace "barka da sallah zaytoonah fatan anyi sallah lafiya"
"Lafiya ƙlau"
"To Allah ya maimata mana"
Da "ameen" ta amsa ta gaisa da sauran yaran parlorn suna ma juna barka da sallah ana cikin haka aunty amarya ta shigo aka ci gaba da gaishe_gaishe saida duk cikin rundunan nan babu babban yaya,
"To mu fita ta waje ko photographern namu ya iso ta can kaman zaifi kyau"
Yuuu aka sake zuga aka bi bayan ya nafi'u daga can suka ɗaura daga inda suka tsaya sun saka iyayen su a tsakiya ana ta ɗauka, shi kuwa yana tsaye yana kallon su he wonders me yasa ake son kowa amman shi kaman ba'a son shi, he is not his parents favorite a wurin hajiya zatoon ne a wurin dady kuma zayd a wurin matar shi kuma kuɗi sai wani lokaci ƴaƴan ta, har yarinyar da ya bata zuciyan shi ma ya kasa gane alƙiblan ta wataƙil shima ba shine na ɗaya a zuciyan ta ba,
Hannunta ta É—aura a saman nashi tana mamakin yanda akayi har ta iso gaban shi bai ankara ba,
"Dan Allah sulaiman, na yau kawai ka saki ranka ka shigo cikin Æ´an uwanka kada zuciyoyin su ya sosu"
Hannun shi na hagu ya saka ya sosa ƙeyan shi idanun shi kan hannun ta dake riƙe da ɗayan nashi, he is strong he can fight all his problems alone ba zai bar kowa ya san matsalar shi ba don shi ba rago bane,
"Sule" ta sake kiran shi cikin nutsuwa, a firgice ya ɗgo yana kallon ta bayi son sunan ya tsani a ɓata mishi suna,
"Hajiyaa menene kuma wani sule, Please kada ma kiyi suji I don't like it"
Murmushi tayi irin nasu na manya, tace "nayi hakan nen don na samu attention ɗinka don na lura wani abu ya tafi min da nutsuwar ka" duk yanda sulaiman ya kai da girma amman har yanzu kallon yaro ƙanƙani take mishi, ita ta raine shi tayi mishi tarbiyya rabin halayen shi training ɗin ta ne don haka it's impossible ya ɓoye wani abu ta kasa ganewa.
"Yanzu damuwa ba abun damuwa bane Hajiya mun riga mun saba dashi kullum mu fita cikin wannan mu faÉ—a wancan kawai kuci mana da addu'a da albarkan ku muke ganin nasara a ko yaushe"
"To shikkenan Allah ya shige mana gaba, amman kaje ka sallami yaran nan dan babu wanda ka bada goron sallah a cikin su"
Ɗan Sakewa yayi kaman ba komai ya shiga cikin wasu pics ɗin aka ɗauka yayi ma ƙannen shi rabon kuɗaɗe iya yanda zai ishe su kafin ya koma ciki yayi zaman shi,
****
Zuba yayi a kan kujerar yana kiran sunan Allah ya kalli sulaiman da already shi yake kallo da ƙawataccen murmushi saman fuskarshi dimples ɗinshi suna masa sallama,
"Yaya ina so zamuyi magana if ur free saboda abu ne mai muhimmanci kuma ina so kayi mun kyakkyawar fahimta"
Yana fatan idan wannan ƙudurin shin ya cika zai bawa saudat goron sallan da babu wanda ya taɓa mata irinshi, zai mata albishir da zata zamo nashi, zai mallaka mata kanshi da zuciyan shi a yau idan babban yaya bai kawo masa cikas ba,
"Umm..hmm.. ina sauraron ka"