← Book details Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 73

Sashe 6

Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Fans comment ɗinku na jiya ya sanya ni jimami😅 da masu cewa har yanzu Yusrah bata sayi mota ba, da masu tambayar dalilin da yasa Khamis ya barta take shiga napep bayi kaita duk inda zata je a motar shi, as you know ciwon haukan ya warke yanzu 😂 kuma shi arziƙi ba mafarki bane ballantana duk wanda ya kwanta yayi😆, I REST MY CASE* 🧘🏻‍♀️

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

🤍💚🤍
    *ƘARAMAR BAZAWARA*
           💚🤍💚

    _(Cigaban matar kulle)_

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *BY*
        *UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
  And *AISHA ALTO*

*kada kana yanke hukunci a kan mutanen da baka da masaniya a kan manufar su, hakan zai sanya ka maida masoyin ka maƙiyin ka, life is too short ka zauna da kowa da kyakkyawar zuciya*

04🧝🏻‍♀️
A wannan tafiyar ni ba Yusrah bace

Sunana Saudat Habib wanda akewa laƙani da boɗɗi, ƴar asalin jihar Adamawa muna rayuwa a ƙauyen wuroɓokki nida iyaye na, a halin Yanzu shekaru na 15,

Anyi mun aure tun ina da shekaru 11 da rabi da Yarima babban É—an mai gari wanda yake da shekaru 20, a wancan lokacin na kasance yarinya mai gata gaba da baya kasancewa ta mace mai cikakken asali an sanmu tun kakani kuma mahaifina ya kasance Malami kuma mai baÉ—a magani, bangaren kyawu da tsari saidai nace alhamdulillah domin dukda a lokacin ban cika mace ba amman Allah yayi min kyawun fuska shiyasa ma ake kira na boÉ—É—i wato kyakkyawa,

Wannan kyawun shi yayi destroying rayuwata, wannan kyawun shi ya zamo silar lalacewar farin ciki na da na iyaye na, saboda shi ya jawo ra'ayin Yarima gare ni ya sanar ma iyayen shi na yake so, as you know no body can say no to a prince,

A ƙauyen mu inada ƙawaye da yawa wa'inda muke fita siyar da nono wasu ƙauyukan dake maƙwaftar mu da kuma kasuwannin dake hanyar birni amman tun da nake ban taɓa shiga garin yola ba, babban ƙawata kuma itace furera, muna amintaka sosai don har talle tare muke fita da an ganni to anga furere shiyasa har sirrikan juna mun sani, na riga na san furere tana bala'in son yarima, kai ba ita kaɗai ba ma duk wasu ƴammatan ƙauyen masu ji da kyau da yarinta sun gama haukacewa a kanshi burin su bai wuce su zamo matar magajin mai gari ba, well nima harda ni a ciki inada wannan mafarkin, ai babu wanda yaƙi daɗi ko?

Wannan haukan da mata keyi a kanshi yana Yarima ya zamo mai tsananin girman kai ga tinƙaho, bayi da abokai saidai masu take masa baya harta tafiya a ɓokare yake yi ya wani turo ƙirji gaba yana fankama wai gashi wanda zai zama mai gari nan gaba, duk da mai gari ba adalin shugaba bane amman iskancin yarima da zalunci duk ya take nashi kuma ko sau ɗaya bai taɓa kwaban shi ba,

Idan yarima yazo wucewa a hanya ba ga yara ba, ba ga tsofaffi ba haka zaka ga kowa yana zubewa yana kwasan gaisuwa idan bakayi ba yayi maka mummunan hukunci kuma yasha bulus, amman duk da haka bai hana kwaɗayayyun ƴammata kai mishi buƙatun su da ya aure su ba dukda kowa yayi ma matan fulani shaidan kunya, amman da yawan su indirectly suke zuwa mishi,

Lokacin da Mai gari yace ma Yarima ya fitar da matar aure, yace duk duniya babu wanda yake so sai ni, a ranar daɗi naji kaman ya kashe ni, daga anyi maganar aure ma yarinya zata fara jin kunya amman murnan zan auri Yarima ya kasa ɓoyuwa dukda naga kaman iyaye na basu so ba amman babu yanda suka iya ya zamo musu dole su amince su bada ni,

Tun daga ranar mukayi hannun riga da Furera tun daga lokacin ƙiyayya mai tsanani ta shiga tsakanin mu amman ni ko a jiki na, indai zan auri Yarima komai ma ya faru, idan naje dandali kuwa kada kuga yanda ake koɗa ni ana wasa ni, tun kafin na auri yariman ma sun saka na fara jin kaina a sama nima yanzu na zamo wata, kuma da ikon Allah nida abin ƙaunata Yarima zamu mulki wuroɓokki bayan mahaifin shi ya sauƙa, bayan wata guda akayi mana baiko,

GA YANDA AKE WALIMAR BAIKO
Dafari de dangin baki daya zasu taru za'a yanka sa guda bayan an gama yankawa sai a kuma yanka su amma manya manya se a naman a qwarya already dama an hada wuta an É—aura babban tukunya sai a sa naman nan a tukunya yayi ta dahuwa bayan an kammala dahuwar wannan naman dama already an tatso nono kuma an dafa tsakii to wannan tsakin za'a zuba a cikin nonon se a zubama kowa naman da wannan hadin na nonon se Ana ci Ana rawa da waqa wasu sukan bari se angama sannan suyi rawan,

To ana cikin wannan rawan ne Yarima ya turo yaro ya kira ni a sirrince, a irin wannan lokacin bai dace naje ba amman ido na ya rufe haka na saɓi mayafina na faki idon mutane na fita,

can jikin wata babbar bishiyar kuka na hango shi a jingine, yana gani na yayi gaba ba tare da yace komai ba yana tafiya yana layi kaman zai faɗi, ganin hakan yasa bani da wani zaɓin da ya wuce na bashi, mukayi ta tafiya ba tare da ya tsaya ba kuma ba tare da ya bar layin ba har saida muka fita bayan gari yanda ba mutane da yawa sai gonaki,

Banyi aune ba naji yarima ya riƙo ni yana shinshine jiki na kaman mage, ga warin wiwi mai ɗaga hankali dake fitowa daga bakin sa dukda gaba ɗaya jikinsa ya amsa amman na wurin yafi ƙarfi, tsoro ya kama ni sosai na shiga firgice banda ɓari babu abinda nake yi, saida naji Yarima yana shirin sanya hannun shi cikin riga na kafin na saka wani ƙarfi da bansan daga ina yazo min ba na angije shi, sannan na matsa can nesa dashi ina kallon yanda idanuwan sa suka rine cikin maye ina kuka mai sauti,

Kafin nayi wani yunƙuri ya sake cafko ni yana faɗa min idan na gudu zai fasa aure na, kawai abinda yake gani a waya yake son gwadawa ai suma ance ba masu aure bane
WA'IYAZUBILLAH

Ni bansan me yake faɗa ba, banma gane mai yake nufi ba, abinda na sani kawai shine bani son riƙe ni da yake yi saboda baba ya sha faɗamin duk macen da ta yarda namiji yana taba jikin ta zata ganta da ciki, kuma ance matan aure ne kawai suke ciki ni kuma har yanzu ba matar aure bace,

Ban daddara ba duk da yanda yake tsorata ni da kalaman sa, na sake angije shi da gudu na koma gida, dukda kuwa na san zai iya sakawa a fasan domin sau biyu ana kai mata za'a aura ma Yarima sai magana ya fara ƙargo yace shi bayi so kuma dole a fasa,

A hankali na lallaɓa na shiga gida ba tare da kowa ya lura ba na wuce ɗakin Inna nayi kwanciya ta naci gaba da kuka har yanzu a tsorace nake,

Aikuwa washe garin baikon mu Yarima ya samu mahaifin shi da zancen ya fasa aure na, a nufin shi tunda na wulaƙanta shi zai saka a bar maganar auren sannan daga baya yabi ya lalata ni kaman yanda yake wa sauran yara kuma babu wanda ya isa yace shi yayi, amman mai gari ya katse mishi hanzari, tunda an riga anyi baiko babu maganar fashi dukda mutuncin iyaye na ne zai faɗi ƙasa warwas amman suma nasu mutuncin zai taɓu,

Tun daga son da yarima yake min ya ragu sosai dukda ba wani gwadawa yake yi yana so na ba ji da kai da fankaman shi kaɗai yake zubawa, amman yanzu wulaƙanci ya shigo ciki kuma mun iso gaɓar da ba gudu ba ja da baya,

Bikin mu sauran sati biyu aka fara hidima, mai gari da mutanen shi sunyi ɓarin kuɗi haka nawa iyayen, an zubar da Naira an zubar da jinin dabbobi anyi shagali wanda ba'a taɓa irin shi ba a wuroɓokki amman fa tsakanin amarya da ango har yanzu akwai giɓi,

Lalli duk abinda yayi farko zaiyi ƙarshe, an gama hidiman bikin mu da Yarima yanzu ya riga ya samu abinda yake so daga gare ni saura kuma zaman gaskiya da gaskiya,

Ban wani samu matsala a gidan su ba daga farko, dake nima bani da son jiki na shiga cikin su ana ta hidindimun gida saidai kuma mulkin ogan daga kaina ya fara, yarima jinshi yake kaman sarkin wani babban gari idan yana tare dani ko kallon cikin idon shi ban isa nayi ba, ɗan waya sha biyun da akayi min ma ban isa kwanciya a kanshi ba saidai nayi shimfiɗi a ƙasa na kwanta, kuma na tabbatar da safe kafin ya tashi na riga shi tashi na tattara kayan shimfiɗi na saboda ya samu daman wucewa ba tare da wani tsaiko ba idan ba haka ba jiki na ya gaya min,

Babban matsala, kuma matsala ta biyu da muka samu, bayan auren mu da kusan wata huÉ—u tsautsayi ya afka a kan babban yayan mu Aminu,

Wurin ƙarfe 8 na dare yana dawowa daga kasuwa bayan yaje saida Sa guda ɓiyu da za'ayi hidimar bikin auren shi nan da sati biyu, har ya wuce jikin wani kango ya dawo ya leƙa ciki saboda kukan mace da yaji yana tasowa daga wurin, leƙawa yayi tare da haska wurin ya hango yarinya wanda bata wuce sa'an boɗɗi ba kwance cikin jini, bai tsaya ɓata lokaci ba ya ciccibeta da nufin kaita gidan su ya ceto rayuwar ta ganin numfashin ta ya fara ɗaukewa

Haka ya dinga gudu da ita har ya shiga cikin ƙauyen su lokacin har 9 ta wuce, daidai ya karyo kwanan da zai sada shi da gidan su yaci karo da dandazon mutane an fito za'a je niman ta shi baima san a ƙauyen take ba dan baima tsaya yaga fuskarta ba,
Chapter 6 · 0% Book details