← Book details Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 73

Sashe 52

Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Ita ɗin masoyiyar masu masoya ce🥰 ita ɗin ɗaya ce cikin zaɓaɓɓu😍 ita ɗin tana zama abin alfahari ne ga wa'inda suka santa da wa'inda ke tare da ita🤩 ita ɗin ZAINAB BAWA ce marubuciyar BIBIYATA AKEYI, AUREN FARI and more💓 wannan shafin sadaukarwa ce a gareki😊 ina miki son so fisabilillahi💝*

42🧝🏻‍♀️ 
Gyaɗa kai baba yayi bayan yaji bayanin Sulaiman wanda kallo ɗaya zakayi mishi ka fuskanci tsantsar damuwa da fargaba da yake ciki, daman yasan wannan ranan tana zuwa....ko ba daɗe ko ba jima yasan rana irin wannan zaizo da asirin da yayi ƙoƙarin birnewa tsawon shekaru masu tarin yawa dai buɗu a idon duniya, saidai alhamdulillah tunda ya riga da ya cika alƙawarin da ya ɗauka ma zayyad da familyn shi gaba ɗaya kuma martabar su ya riga da ya ɗagu zuwa matakin da har abada ba zai faɗo ba,

Numfashi ya furzar a hankali yace "toh shulaimanu shidai lafiya Allah ke badawa shaidai ɗan adam yayi nashi ƙoƙarin wajen shamo magani, yanda aljanu shuka rabu kala_kala cikin jinsuna kaman ƴan adam haka hanyoyin kamuwa dashu da kuma rabuwa dashu shuka rabu kashi_kashi, yanzu dai ba zan baka tabbaci akan Zaidu zai warke ba amman zamuyi iya ƙoƙarin mu da ikon Allah, shaidai zansho shai mun koma wuroɓokki don al'amarin babba ne"

Jimm sulaiman yayi yana tunani, indai hakan zata faru tofa lallai shi zai tsara komai yanda za'a bawa su malam ardo da zayyad kariya yanda mutanen garin ba zasu samu wani dama na cutar dasu ba sannan ya kasance tare dasu don ganin komai ya tafi dai_dai,
Shi da yaso fita harƙan shi gaba ɗaya ya watsar da sha'anin shi saboda yaudaran shi da yayi! Me yasa ƙaddara zatayi mishi haka? Har ƙoƙon ranshi yake ƙaunar Zayyad ba zai taɓa barinshi da ciwo ba bayan sun sami hanyar maganin shi,

_shikkenan zaiyi masa saboda Allah idan yaga dama yaci gaba da cutar dashi Allah zaiyi mishi maganin sa_

Numfasawa sulaiman yayi yace "shikkenan baba insha Allah za'ayi yanda kace, daga zaran inna ta samu lafiya zamu je ƙauyen dukda dai kaman yanda na faɗa daga farko banso komawan ku can ba naso a sama muku matsuguni a nan ku zauna cikin kwanciyar hankali saidai babu matsala a hakanma, insha Allah ni nayi muku alƙawarin babu wanda ya isa ya sake cutar daku zaku koma gida kuci gaba da rayuwan ku kaman kowa"

Cike da jin daÉ—i malam arÉ—o ya gyada kai yana murmushi tare da jinjina karamci da dattakon wannan yaro,
"Allah yasha ka gama da duniya lahiya shulaimanu, banshan dame jan biya ka ba, ka inganta rayuwar shaidatu ba tare da kuna da wata dangantaka ba gashi muma kana ta hidima damu, Allah ya shaka maka da alkhairi, Ubangiji Allah ya kareka daga dukkan sharri da mai sharri,

Da "ameen" ya amsa daÉ—in addu'an malam arÉ—o yana ratsa shi, zama yayi kaÉ—an suka tattauna akan yanda tafiyar zata kasance sannan suka koma É—akin da inna ke kwance yayi musu sallama kan zai wuce, yana jin kaman ya É—auki saudat ya tafi da ita amman ba zai iya ba saboda idanun iyayenta,

Shi karankanshi yasan yayi kewarta sosai gashi kwana biyu yana ganinta a cikin yanayin da yake so dukda a halin yanzu tana cikin tashin hankali amma burinshi bai wuce kullum yaga murmushi a saman fuskarta ba kuma zaifi so ace idan tana tare dashi take yi,

Kawar da tunanin yayi a ranshi ya tada motar ya tafi saida ya isa gida ya umarci drivern zayyad É—in yaje ya É—auko shi sannan ya wuce wurin dady ya faÉ—a masa abinda ya faru da safen ya kuma sanar dashi hukuncin da suka akan lafiyqr zayyad É—in,

Dady ya gamsu kuma yaji daɗin hakan baiyi wani ƙorafi akan zuwansu wuroɓokki ba sai fatan samun nasara, daga nan ko ciki bai shiga ba ya wuce gida don yasan da zaran aunty amarya taji wannan zancen toh babu abinda zai tafi dai_dai musamman idan tasan sulaiman gaban kanshi yayi ba tare da ya shawarce kowa ba, don maganin da sukeyi kwanaki ma ita take kawo musu cikas idan akace su koma rana kaza sai ta saka zayyad yaƙi zuwa ko kuma taƙi bashi maganin da aka kawo, a cewarta wahala kawai suke ƙara bashi da maganin,

Da yammacin ranan dady ya tattari kan iyalanshi gaba ɗaya suka tafi asibiti duba jikin inna harda wa'inda basu so zuwa ba because he consider me as part of his family, saida suka je ne yayi nadaman zuwa da Nana don Sulthana ta fita wayo ita ta kama kanta kaɗan, haka ta zauna ta dinga yaɓa ma iyayena magana a fakaice abin saida ya kusan zama faɗa tsakanin mu domin kalaman da take jifan su dashi yayi tsauri,

Dukda nasha rarrashi a wurin su aunty da su hajiya amman saida nayi kukan takaici bayan sun tafi, nidai Allah yamin katangar ƙarfe tsakanina da yarinyar nan banma san yaya zamu ƙare ba idan na shiga gidansu a matsayin matar Zayyad,

******
Ba zato ba tsammani ya jawota baya ya dungurata a tsakiyar ɗaki sannan ya rufe ƙofar ɗakin, yaushe ya shigo ciki bata sani ba? Tunaninta ne ya katse lokacin da sulaiman ya ɗaga bulala ya shargwaɗa mata a gadon baya ta wani boƙare tare da saka ihu, da gudu ta miƙe ta nufi ƙofa amman a rufe ya garƙame da key,

Ihu nana take kaman wanda ake zare ma rai tana buga ƙofar ɗakin wanda yasa mutane fitowa don ganin abinda ke faruwa, taku ɗaya sulaiman yayi ya sake jawota ya shauɗa mata wani a kan cinya,
bata san laifin me tayi mishi ba, ita dai tasan bayi duka amman bata san me ta masa yake son kasheta a halin yanzu ba,

Taƙarƙarewa yayi ya sake zuba mata wani a take numfashinta ya tsaya cakk sautin kukanta ya daina tashi sai gurnani,

Shi da yayi dukan ma sai haki yake yi ya gwada ta da bulalan hannun shi yana jifanta da mugun kallo yace,

"Na daɗe ina taraki Nana Hafsah yanzu kin fara ƙure ni, wallahi kinji na rantse miki indai ba zaki nutsu kiyi hankali ba zaki sha baƙar wahala a hannu na shashasha mai banzan ɗabi'a, ziciyar ki baƙiƙƙirin kamar fuskar ki shiyasa har yanzu kika rasa mashinshini baki nufin kowa da alkhairi, Allah idan baki gyara ba haɗuwar mu na gaba ba zata kai wannan kyau ba"

Ita dai ta saurare shi sama_sama amman bata iya fassara kalamansa ga numfashinta dake barazanar barin jikinta tana kuka mai haɗe da gurnani, sai yanzu ya kula buga ƙofar da hajiya takeyi tana kiran sunan sa, hankalin sa kwance ya ƙarasa ya buɗe ƙofar ya fita,

"Me yake damunka ne sulaiman wannan wani irin zalunci ne?"

Kallon yanda su Ruma sukayi kanta suna kuka yayi yaja tsaki saikace wanda ya kasheta, Junior kuwa abin yayi mishi sugar don a gaban idanunshi taci mutuncin iyayen girlfriend É—inshi,

"Hajiya she is just putting a drama ni babu abinda nayi mata bayan barazana, razana ta kaɗan kawai nayi" daga faɗan haka yayi gaba ya bar hajiya da baki sake cike da al'ajabi da kunnuwanta taji sauƙan bulalu amman yace mata wai _barazana_

Bayan ya koma gida bai samu nutsuwa ba saida ya kirani a waya ya ƙara bani hakuri gashi sadiya ta shiga partial yaji don ta zama kaman babu itane cikin gidan harta yaranta ta daina kula su ta daina musu komai wai tana so sulaiman ya gano amfaninta ne yasan tana da muhimmanci a rayuwan dukkan su shi kuma hakan dq takeyi yana kara saka mishi matsuwa na ganin ya auro Saudat tazo ta ɗauki ragamar gidan baki ɗaya sai yaga ta allon ta,

Munsha hira na kusan rabin hour dukda taɗinmun ya ta'allaƙa ne akan shirin tafiyan mu wuroɓokki amman hakan ya sama mishi nutsuwa sosai, while a nawa fannin i can tell that sulaiman is becoming soft...so tender indeed da har yasa tsoro da kuma fargaban shi da nakeji a raina ya ragu sosai,

8 days later

7:30am
Annashuwa, nutsuwa, farinciki, ga kuma iska mai daÉ—i dake kaÉ—awa a hankali cikin albakataccen daji mai kawace da bishiyoyi daban_daban da tsuntsaye masu shawagi suna daÉ—aÉ—a kunnuwan bil adama da sautin muryoyin su masu daÉ—i,

Zaune nake a passenger seat na rungume kanwata indo a ƙirjina idanu na a lumshe babban yaya zaune a gefe na hankalin shi a kan titi yana driving, mahaifiyata da mahaifina kuma suna back seat, ya aminu, jaɗe, khamis, da zayyad suna motar dake gabanmu da motar police suma guda daya a gaban su motar bayanmu kuma ya Nafi'u ne ke driving da matan jaɗe da na ya aminu sai kuma ƴaƴansu, suma da na police guda ɗaya a bayan su making 5 cars in total,

Na daɗe ina burin irin wannan dawowar, na daɗe ina mafarkin ɗaukar fansa gashi tun kafin muzo babban yaya ya bani wuƙa da nama ni kuma nayi alƙawarin ba zan bar wuroɓokki ba sai na tabbar an kama mai gari wanda ya kasace ƙanin tsohon mijina yarima tacaccen ɗan shaye_shaye aje ayi ta gana mishi azaba a rehabilitation center shima mahaifinshi yaji yanda uba yake ji idan an raba shi da jininshi, kaiii harda ƴan uwan shi da abokan shi dan saka a kama don na rama sharrin da furere tayi wa ya aminu saboda su,

A hankali motocin suka tsaya bakunan mu suna godiya ma Allah sannan baba ya fito, da mamakinsa babu gidanmu a wurin.....tabbas nan ne inda yake amman babu shi a wurin sai wani....wani mai ginin zamani wanda ƙauyen karankaf babu kamarsa,

Juyowa malam ardo yayi kaman zaiyi kuka abin nasu ya fara kaishi bango, koda ace fili ba nashi bane amman ai gida nasi ne shi ya gina da guminsa bai kamata a rushe ba tare da izinin shi ba,

"Mu shiga ciki mana baba! Mai muke jira?" Sulaiman ya tambaya,

A raunane ya juyo yana kallon mu murya can ƙasa yace
"Bamu da wurin da zamu shiga, sun riga sun fitar dani daga garin bani da matsuguni a cikinta a halin yanzu"

"Kaman yaya baka da matsuguni bayan ga gidanka nan? Duk duniya akwai wanda ya isa ya fitar da kai daga cikinta ne bayan ikon Allah?"
Chapter 52 · 0% Book details