← Book details Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 73

Sashe 30

Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****
Jujjuya kujeran yake yi yana karkaɗa biron hannun shi cike da nishaɗi don ya fara hango ma kanshi nasara a cikin shirin shi, da ya samu an amince da maganar komawar Saudat international academy Shikkenan zai samu daman maida ta ƴar gidan su don ba zai yarda taci gaba da zama a kalolin gidan da ta tashi ba, domin shi ba zallan wayewa da ilimi yake so ta ƙara ba she has to maintain her beauty, fatan ta yayi kyau taci abinci masu inganci da gina jiki daɗi ya samu matsuguni a jikin ta sosai, shiyasa ba ƙaramin shiri zaiyi a kanta ba dole ne kawai ya mallake ta,

  *****
"Ki kalli bayan allan nan yana rejecting call É—ina?"
Sadiya ta faÉ—a fuskar ta É—auke da tsantsar damuwa tana kallon Muna,

"To ki rabu dashi mana aunty halima, kinfi kowa sanin halin babban yaya idan yayi fushi babu abinda mutum zaiyi masa da zaisa ya sauƙo sai lokacin da yaga dama, ki bari da kanshi zai dawo ya neme ki"

"Na bar mene Maimoona kina ji yana min maganar kishiya wai aure zai ƙara? Tun jiya fa Sulaiman yaƙi kula ni yau da sassafe ya bar gidan nan hankali na ya kwanta ta ina?"

Miƙewa tayi da wayar ta a hannu ta saka takalminta sannan ta ɗauki hanyar cikin ɗaki tana
"Wannan mijin naki ya zamo mana jaraba wallahi bayi mana komai bayan saka mu a damuwa Allah dai ya raba mu lafiya"

******

Ni banga amfanin PCM da nasha ba don bayan gajiya da damuwa harda ciwon kai sitifid ya saka min,

Wannan maganganun nashi ta ɓangare ɗaya yayi min ɗadi sosai amman ta ɗaya ɓangaren ya zamo kaman ruwan kifiyoyi ne masu guba, don ni da Zayyad ba zamu taɓa kasancewa tare ba musamman ma idan ya san Asali na ya san labari na kuma ya san ni ba BUDURWA bace,

"Kada ki damu kanki ba gaggawa nake yi ba kuma wannan ba al'amarin da za'ayi wa sauri bane, idanma kina ganin kaman yanzu yayi wuri zan iya jiran ki zuwa wasu shekaru nan gaba saidai kawai ina fatan kasancewa ne a cikin zuciyar ki HAR ABADA, ki nutsu kiyi tunani bye kada na cika ki da surutu,

Ya san ba zanyi magana ba yasa kawai ya kashe wayan ba tare da ya jira wani amsa daga gare ni ba,

Zubewa nayi a kan gadon ina jin yanda kaina yake sarawa da ƙarfi ga hawayen dake sintiri a gefen fuska na, na kama salati ina kiran sunayen Allah don samun mafita daga gareshi,

  *******

20/Ramadan/1442

Da Mama ta faɗa ma yadiko ta nemi shawari na kan maganar makarantar nan banka tsaya na saurara ba nace na basu wuƙa da nama suyi yadda suka so dani, don tabbatar musu da suna da cikakken iko a kaina,

Da tayi magana da Khamis ya nuna mata babu matsala sai suka kira shi suka faɗa mishi sun amince, murna da sulaiman yayi a ranar da ya koma gida kaman ya goyi sadiya, ita wawiyar ta ɗauka ya sauƙo ne yana sake niman wani abu a wurin ta amman bata san tsiyan da yake shuka mata a ƙarƙashin ƙasa ba,

Zayyad bai sake kira na ba sai washe gari da yamma ina kallon wayan na barshi ya yanke ina kuka dan ba zan iya rejecting ɗinshi ba kuma ba zan barshi yabi hanyar da ba zai ɓulle ba, ai kuwa saida ya tado da matsatstsakun shi a ranar ya sake gutsure azumin............🤦🏻‍♀️

Love You my fans😍

#Team SS💙
#team SZ❤️

*Ummu Najma ce😂*

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

🤍💚🤍
    *ƘARAMAR BAZAWARA*
           💚🤍💚

    _(Cigaban matar kulle)_

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

         *BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
  And *AISHA ALTO*

25🧝🏻‍♀️
22/Ramadan/1442
Yau da zazzafan ciwon kai na tashi domin tun jiya da Ruma ta kira tana kuka ta faÉ—a min jinnun Zayyad sun motsa na rasa sukuni don matsawa sukayi wai sai nazo,

Da ƙyar muka shawo kan matsalar ta waya ina faɗa musu abinda zasuyi mishi, basu sani ba amman ni nasan nice sanadin hakan tunda ni na ɓata mishi rai,
Bazan so na shiga rayuwar bawan Allah bayan wahalan da yake ciki na ƙara mishi wani a kai ba,

11:07am na fito da kwanukan da mukayi suhur dashi zan wanke dan tun a daren jiya na samu tsarki shiyasa dani akayi tahajjud, ban samu barci a daren jiya ba ko kaÉ—an shiyasa yau na makara,

A gaggauce na fara aiki na don na samu gamawa nayi wanka na tafi gidan mama kafin azahar tayi, kwankwasa ƙofar gate da akeyi ya jawo hankali na, na miƙe tare da shiga ciki na saka hijab akan pjamas ɗina sannan na fita duba mai knocking,

Tsananin mamaki na ya gaza ɓoyuwa yayin da idanuna sukayi tozali da aunty Amarya fuskar ta yayi fayauu kaman mara lafiya, kaman ko yaushe hannun ta ɗauke da casbi,

"Zan iya shigowa saudat?"

Tattaro nutsuwa na nayi, nayi saurin matsawa a hanyar don bata daman wucewa, murya na yana rawa nayi mata sannu da zuwa na shigar da ita parlor dan nasan tabbas a kan Zayyad tayi tattaki,

Gaisawa mukayi sannan na shiga na kira aunty Yusrah da yadiko suka fito suka gaisa sannan ta fara sanar damu abinda ya kawo ta,

"Ban sani ba ko kun samu labarin abinda yake faruwa da yarona daga wurin Saudat to shine abinda ya kawo ni nan nazo niman alfarman ki saudat....."

"babu wanda ya sani aunty, daga ni sai ku sai kuma Allah, ba zan faÉ—a ma kowa abinda na gani ba tare da izinin ku ba" nayi saurin katse ta kada ta sanar dasu,

Murmushin jin daɗi tayi tana ƙara yabawa da hankali na, bata yi tsammanin ba za'a samu matsala daga ɓangare na ba lokacin da na fahimci ciwon Zayyad amman gashi saima waraka da sauƙi da ake daɗa samu daga gareni, yarinya ƙarama amma akwai sanin yakamata, ta faɗa a zuciyar ta,

"Naji daɗi kuma na gode sosai saudat da kika mutunta mana sirrin mu kuma kika taya mu ɓoye shi, Allah yayi miki albarka" "ameen Aunty"

Ta maida dubanta wurin su yadiko da suke zaune "dan Allah idan ba zan takuraku ba, ina son ku ɗan bani aron Saudat in tafi da ita can gidan namu idan babu matsala, a halin yanzu wani ƙaramin matsala muke fuskanta a gidan, kuma saudat tana da daman magance mana wannan matsalar ko kuma ta sauƙaƙa shi, don Allah kui min wannan alfarmar ku ceci rayuwar wanda yake a halin gangara"

My words sounds like a puzzle to them, duk sun shiga ruɗani musamman yadiko, gwanda ita Yusrah ta san wani abu kaɗan akai, tana da yaƙinin maganar nan da akeyi a kan Zayyad ɗin nan ne dukda bata san komi gane da hakan ba, amman yadiko kam an saka kanta a baƙin laida,

Ganin girman zancen da ya haɗa harda iwana a baƙon wuri yasa tace "hakan ba zai gagara ba Hajiya amman a bari yayan nata ya dawo daga wurin aiki ta nemi iznin shi in yaso sai tazo daga baya"

"To Shikkenan hakan ma yayi, na gode, na gode sosai, zan tafi yanzu amman ki É—an zo da wuri saudat dan Allah"

"Insha Allah aunty yana yarda zan zo"

Daga haka muka mata rakiya zuwa gate su Yusrah suka tsaya muka ƙarasa har mota na bata addu'a da zasuyi mishi kafin nazo, mukayi sallama suka wuce,

  *******

Dube_dube yake yi cikin drawern fuskar shi ɗauke da murmushin da ya bayyana haƙwaran sa, ya baza kunnuwa ne kawai yana jin endless lissafin sadiya, yana comparing duk wani action nata da na boɗɗi a cikin ƙwaƙwalwar shi ko zai samu banbanci, he just love the silent fulani babe so much!

"Dadyn Arifff kana sauraro na ma kuwa?"

"Inajin ki mana momyn Arif just continue" ya faÉ—a lokacin da ya ciro wasu takardu daga draqern ya zuba a kan bed yana arranging É—insu a cikin file,

Murmushi tayi jin amsar shi, lallai yau ranar sa'ar ta ce shiyasa tunda taga mood É—inshi kwana biyun nan is lightened take tatsan shi yanda taso, yauma ba zata bari ya wuce ba sai ta samu babban kaso,

"Yauwa to kaga bayan shi, akwai 200 thousand na takalman baby set 5 na Arif set 7 da nawa i think 5 ɗin zasu isheni saidai idan zaka ƙara a kai sai na ƙara yawan su, then kuɗin tailor shima i think dubu ɗari da..."

"Wait dan Allah, kinsan bani son irin wannan gutsi_gutsin lissafe lissafen ƙwaƙwalwa na ya gaji da ɗaukan caji, a nan wurin kinyi mun lissafi almost 1 million, ke baki san ana shan wuya kafin a samu kuɗi bane?"

Ɓata fuska tayi ganin yanzu ya ɗago yana kallon cikin idanun ta
"Yanzu ba zan samu ba kenan?"

"Zaki samu mana, daman wahalan ai maku akeyi idan baku amfana dashi ba arziƙin bayi da amfani kenan"

Nan da nan annurin fuskar ta ya dawo ta hau washe haƙwara tana zuba mishi ruwan addu'oi da godiya,

Murmushi yayi yace "halimatu kenan kada ki damu indai ta fannin kuɗi ne baki da matsala dani,akwai ma wani abu da nake buri nan gaba kaɗan, idan na samu nayi miki alƙawarin a ranar credit card ɗina a hannun ki zai kwana ki ciri duk amount ɗin da kike so ko nawa ne! Kawai ki taya ni da addu'a ki saka yara na ma suna min addu'a kullum Allah ya sa buri na ya cika nan kusa zaki sha mamaki wallahi"

"Ya Allah ka dube mu da idon rahama ka cika ma wannan bawan naka burin shi ko menene shi, ko menene wannan buri ya Allah ka cika masa idan ba alkhairi bane ka maida shi ya zamo alkhairi ka bashi ya Allah albarkacin watan Ramadan, ya zul_jalalu wal ikram, ya rabbul arshil azeem, ya rahaman ya raheem Allah ka biya ma mijina dukkan buƙatun shi na duniya,
Chapter 30 · 0% Book details