← Book details Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 73

Sashe 41

Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Babu komai boÉ—É—i, ki sanar min abinda ya saka kika min wannan kiran gaggawan Allah yasa ba wani abu ne ya kuma faruwa ba"
Ya faÉ—a yana kallon fuska na da yayi jaa ga kan hanci na kaman wanda aka baÉ—a wa yayi, idanu na sunyi ciki_ciki alamun nayi kuka duk kwalliyan fuskana na goge shi a jikin gyale na garin share hawaye bai ankare ba sai gani yayi wasu hawayen suna bin kunci na, kafin yayi magana nayi saurin tare shi,

"Kayi haƙuri ya zayd, ba zan iya auren ka ba don ban dace da kai ba"

"What?! What are you saying? Ban fahimce ki ba"

"Ni BAZAWARA CE hamma zayd, na taɓa yin aure da wani a baya"

Shiru ne ya ratsa tsakanin mu na Æ´an sakwanni, ya kasa gaskata abinda kunnuwan shi suka ji, ta yaya za'ayi yarinya mai shekaru 15 zuwa sha shida kacal a duniya ta kasance bazawara? Me yake faruwa ne? Ya tambayi zuciyar shi,

Jin yayi shiru yasa na fara masa bayanin abinda ya faru gudun zargi "ni ba ƙanwar khamis bace, iyayen shi ba su bane nawa kuma bamu haɗa wani dangantaka na kusa ko na nesa dashi ba, iyaye na suna can ƙauyen wuroɓokki kuma a can nayi aurena na farko" daga nan na kwashe labarin aure na da YARIMA da zama na dashi har izuwa mutuwan shi da kuma yanda baro ƙauyen, zuwa lokacin idanun zayyad sun gama tara ruwa ƙiris ya rage su sauƙo saman fuskar shi,

ÆŠaga kanshi sama yayi iskan fanka yana fifita mishi idanun shi ko zai samu ya iya controlling kanshi,
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel..... La ilaha ha illa anta subhanaka inni kuntu minal zalimin"

"Yanzu ni korarriya ce, bani da ikon shiga cikin wuroɓokki domin da sun ganni kashe ni zasuyi, tun ba yau ba ma naso kaika wurin mahaifi na mu gwada magani ko za'ayi nasara amman saboda wannan dalilin na gagara, ta yaya korarriya ta dace da mutum mai gata gaba da baya irinka? Kada ka manta kai saurayi ne ni kuma sauran wani"

Kifa kanshi yayi saman cinyar shi zuciyar shi yana suya, shi yayi tunanin ƙaddarar shi shine mafi ƙunci da wuya amman ashe akwai na wanda yafi nashi ƙuntatuwa, tunda shi yana cikin ƴan uwan sa ko wani garin Allah idan ya waye yana ganin Mahaifiyarsa tare da mahaifin sa ga ni'ima da wadata da Allah yayi musu,

"Saudat koda ƙaddarar ki tafi haka muni bani da matsala kuma na yarda dake a hakan nake son ki, ban damu ba, kuma ba zan saurari maganganun wasu mutane ba,
Ba kyanki ko kuma budurcin ki nake so ba, ke ɗin nake so zuciyar ki nake son samun matsuguni, buri nake ki zamo uwar ƴaƴa na kuma surkuwar mahaifiya ta, muradina kawai ki kasance ƙarƙashin inuwar aure na"

"Amman dangin ka fa? Zasu amince?"

**********
Anyi Sallah da sati 2 kowa ya watse muka É—au hanyar makaranta, sabon tafiya sabon rayuwa,
Fiye da rabin damuwa na sun ragu don tun daga ranar da na bar gidan su zayyad babban yaya ya fita sha'ani na kwata_kwata ko magana mai tsayi bayi shiga tsakani na da shi amman bai fasa min kowa ba cikin hidiman da ya saba, kafin na tafi school ma saida su aunty yusrah suka kwashi rabon su don idan ya waiwaye mu mukan jiƙa sosai,

Na fuskanci abubuwa da dama wanda suka ɗaure min kai lokacin da na shiga makarantar don a lokacin da za'a kaini ganin niƙi niƙin shopping da sulaiman ya saka a kaini dashi nayi tunanin yawan shi ya tsananta amman da naje naga yaran dake rayuwa a wurin irin tsadadden rayuwan da akeyi na ƙarya da tsananin gaye, jinkai, competition na nuna dukiya, da kuma gasar ilimi sai na ganni ni ba kowa ba a gaban su.............🤦🏻‍♀️

Love You my fans🥰

#team SS💙
#team SZ❤️

*Ummu Najma ce😘*

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

🤍💚🤍
    *ƘARAMAR BAZAWARA*
           💚🤍💚

    _(Cigaban matar kulle)_

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

         *BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
  And *AISHA ALTO*

34🧝🏻‍♀️
*2 years and 7 months later*

"Congratulations on your first day in office bro"

Juyowa zayyad yayi daga jikin windown da yake tsaye yana ƙarewa farfajiyar companyn kallo daga sama har ƙasa, sanye yake da single breasted suit black colour ya ɗan yi ƙiba kaɗan yayi fresh,

Kallon cake ɗin da sulaiman ya shigo ɗauke dashi yayi cike da mamaki gami da jin daɗi a cikin ranshi, ya tako zuwa inda yake tsaye yana ƙarewa cake ɗin kallo cikin birgewa, anyi decorating ɗinshi da edible office tools irin su stapler, pen, memo,sticky note, scissors da kuma pins, cake ɗin ya ƙawatu sosai,

"Woww this looks like a table" suka saka dariya gaba ɗayan su sannan ya karɓi cake ɗin ya akiye a kanshi ya juyo ya dubi babban yaya, saida ya bari ya karɓi box din hannun mutumin da suka shigo tare ya fita sannan yace,

"Na gode sosai yaya, ko birthday cake ɗina be kai wannan ƙawatuwa ba, bayan kuma duk nasaran da aka samu ta sanadin ka ne, kaine ka jajirce ka zaƙe wajen ganin mun cimma wannan matsayar.... Allah ya saka maka da alkhairi"

"ameen zayd....Well inaga ni ɗin kawai nayi abun da ya kamata ne kai kuma kaci nasaran biyayya, rayuwan ka ta ƙuntata sosai na shekaru masu yawa amman daga yanzu komai ya wuce zayd, ka saka ma ranka kaman babu abinda ya taɓa faruwa, kayi rayuwan ka cikin aminci da salama"

Ya ɓude box ɗin sannan ya fara firfito da kayan ciki yana ajiye su saman table,
"Here's your passport" murmushi yayi ya ƙarɓa yana juya shi
"yanzu kaima ka samu freedom na transportation, sai kaje duk inda kaso ba tare da izinin babban yaya ba"

Dariya zayyad yayi lokacin da ya danƙa mishi abu na biyu "your car keys, brand new Porsche irin nawa da ko yaushe kake muradi.... Saidai wani hanzari ba gudu ba" ya ƙarasa yana tsare gida kaman bashi bane mai murmushi yanzu,

Shima zayyad shiru yayi da ganin sauyin yanayin shi yana jiran yaji mai zai fada, saida ya maida hankalin shi gefe sannan yace
"Na banbanta mana kala don bani son ka dinga jera kanka dani, na girme ka so respect me"

Dariya ne ya kubce masa ya ƙame kaman sabon soja sannan ya sara masa "gaisuwa babbban yaya"

Cike da jin kai ya amsa da "uhm hmm" yana ƙunshe dariyar abinda yaga zayd ɗin yayi, ya miƙa masa na gaba,
"Your credit card sai a cika mana account da kuɗi yanda zamu dinga wadaƙa da dukiyar ƙanin mu........ and here's some cash wanda zaka ɗan riƙe a hannun ka zuwa wani lokaci sai ka ɗauki abinda zai maka ka ajiye sauran a safe, na gama maka iya abinda zan iya"

Runguma shi zayyad yayi idanun shi suna tara ƙolla, "na gode Ya sulaiman, kayi yaƙi kayi fafutuka wajen ganin ci gaba na Allah ya saka maka da mafificiyar alkhairi kuma ina roƙon Allah nima ya nuna min ranar da zan sadaukar maka da wani abu don ganin farin cikin ka"

"Kada ka sha mamaki ranan yana nan zuwa, yanzu dai sake ni a gajiye nake ko hutawa banyi ba na biyo nan"

Sake shi yayi ya zura hannayen shi cikin aljihun wandon shi,
"Yaya banyi tunanin zamu ci nasara ba da naga baka nan, haka kawai nake ga kaman sirrikan mu zasu bayyana a gaban su, amman da wakilin ka kaÉ—ai mun sami abinda muke so"

"Zama na a nan ɗin amfanin shi ragagge ne shiyasa ban dawo ba na ci gaba da mana addu'a a ɗakin Allah and here we are, komai ya tafi cikin sauƙi sai kuma mu ɗauki abu na gaba ko?... Nima maka lafiya idan Allah yaso"

Sosa ƙeya yayi yana dariya ƙasa_kasa yace "yaya maganar aure na dai ko?"

"Toh shikkenan tunda ka kasa haƙuri, ko da yake banga laifin ka ba don ka fara shiga sahun manyan tuzuraye..... Yanzu dai ka bari idan ka dawo gida zamuyi maganar don inason na huta a yanzu gaskiya"

"Shikkenan nima yanzu wani wuri na nufa, idan na dawo É—in sai mu zanta"

"Wani wuri ina? Daga ranar farko har zaka fara yawo ko? Ka maida hankali fa zayd ka nutsu ka san abinda kake yi"

"Wurin ta fa zani yaya, anyi musu hutun school yau dole naje nayi picking É—inta up"

"Hmmm dalilin da yasa kake sintirin hanyar international academy kenan? Zuwa ganin budurwan ka ko, Ko kayi tunanin ban sani bane?"

"Hhh yaya ba kace yanzu na samu freedom ba sai a barni naje na É—auko aba ta na kaita gida, kaga tun yanzu ya kamata tasan cewa ni É—in zan dinga bata kulawa"

dukan wasa ya kai mishi a kafaɗa yace "da nasan ɓata gari irin ku suna zuwa har cikin makarantar su ɗauki yaran mutane da ban kai Saudat wurin ba"

"Yaya kenan kwantar da hankalin ka basu bari baƙo ko bare yaje wurin kowa, itama ɗin kaman dangi take ka santa farin sani kawai ma ka bari na Musamman zanje na kawo maka ita"

"Hakan yayi, ni zan wuce sai ka dawo, amman ka kula da kyau Please...ayi driving a hankali"

  *******
Yana tsaye jikin sabuwar motar shi baƙa wuluk hannayen sa harde a ƙirjin sa idanun sa sanye da sunglasses saboda rana da ake ƙwallawa ya zuba mata ido cikin su,

Takowa take a nutse sanye take da uniform light blue da wandon shi wanda yake combination na blue, black and ash dankwalin ta ma ash colour da madaidaiciyar hijab ɗinta wanda sauran kaɗan ya ƙarasa guiwa, idanun ta maƙale da farin reading glasses wanda idan ba wanda ya san tana da matsalar ido bane babu wanda zaiyi tunanin ba na fashion bane saboda yanayin case ɗinshi da kuma yanda ya ƙarbi fuskarta,
Chapter 41 · 0% Book details