Sashe 15
Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
     *BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
 And *AISHA ALTO*
11ðŸ§ðŸ»â€â™€ï¸
Na daɗe ina mafarkin sake sake ganin wannan abun sai yau Allah ya gwada min shi a zahiri kuma ina da yaƙinin wannan karon zan mallake shi insha Allah,
Shiruu Sadiya tayi tana binshi da kallo haka kawai ta sami kalaman shi da É—aure mata kai, don ta san Sulaiman is straight forward amman yau yana mata magana mai harshen damo lallai wannan al'amarin babba ne,
"Whaaatt?" Ya tambaye ta yana fitar da dariya mai sauti ganin yanda ta zurfafa kanta cikin tunani,
"Kinga ni bani son irin É—aukan É—umin nan naki kina shiga damuwa ba gaira ba dalili, ki kwantar da hankalinki ki koma kiyi barci wannan al'amarin bai shafe ki ba, Allah ya tashe mu lafiya" ya kashe lamp É—in tare da juyar da ita ya lafe a jikin ta yana shafa bayan ta a hankali,
Wannan sabon yanayi na Sulaiman ya ɗaure mata kai matuƙa, tana dai fatan ba wani abu yake shiryawa ba don haka kawai taji ranta bai aminta da shi ba,
 *****
"Mtssww, ni zai kalla ya kira ni sitifid, wallahi duk ranar da na ganshi sai na rama wannan zagin, dama uwa na ko uba na ya zaga ba zan damu ba tunda wanda ya zagi iyayen wani iyayen shi ya zaga, amman tunda yace min sitifid babban zagin da yafi ko wanne a duniya to sai na rama"
Ai kuwa ina kai aya abulkhairi ya callara ihu bayan ɗumbin kashedin da aunty Yusrah tayi mun na nabar ƙananun maganar da tun bayan magriba nake faman yi kada na tada mata yaro,
Tashi tayi ta zauna ta kunna Torchlight tare da kaimun duka a cinya daman already idanu na a buɗe suke tsugul na miƙe ina sosa wurin
"Muguwa! kina gani awa na biyu da yaron nan a hannu ina jijjiga shi kafin da ƙyar na samu yayi barci saboda nima na rintsa amman ko minti 30 baiyi ba kin daga min shi"
Bance da ita komai ba don nasan nayi laifi, na zauna ina binta da ido ta É—auki yaron ta fara feeding É—inshi sannan taci gaba da cewa,
"Wai a dole muna kwana É—aki É—aya dan ki taimaka min da wasu abubuwa amman rana ta farko kin fara azabtar dani, haba da wanne É—aya zanji?"
Turo baki nayi ina ƙunƙuni, shiyasa ni banso kwanan ɗaki ɗaya tare da ita ba gwanda na kwana ni ɗaya yafi mun daɗi na faɗi abinda raina yake so a cikin barci ko a farke, amman ana niman takura min, kuma ma ai laifin Sitifid ɗin nan ne, yau nayi niyyan bazan ƙullaci kowa ba saboda kada nayi surutu cikin barci amman duk ya shiga ya ɓata min zuciya,
"Ke!!" Ta faɗa tare da taɓa ni, nayi saurin juyowa ina kallon ta tare da zare idanu na saboda yanda na ruɗa kaina bansan lokacin da nayi hakan ba,
"BoÉ—É—i lafiyan ki kuwa? Anya ke kaÉ—ai ce? Maganganun me kike yi ne ke kuma ana miki magana hankalin ki yana wurin?"
"Babu komai aunty Yusrah me kika ce?"
Sauƙe numfashi tayi tace "ki zubo min ruwan zafi daga plask nasha"
**********
Rufe ƙofar tayi ta bayan ta a hankali sannan ta zuba a jikin shi ta saka hannun ta da kullum bayi rabuwa da casbi ta zagaye shi tana sakin marayan kuka,
"Again!! An sake samun matsala Alhaji, innalillahi wa inna ilaihirraji'un"
"Shhh! Ya furta yana bubbuga bayan ta a hankali
"Kuka ba naki bane Madina, ba yau muka fara ganin matsalar Zayyad ba kuma bamu san yaushe ne zamu ga ƙarshen ta ba, dan Allah ki kowa ma kanki jarumta kuma ki zamo mai tawakkali insha Allah sauƙi na nan zuwa"
Tashi tayi daga jikin shi tana share hawayen fuskar ta a hankali take jan numfashi don ta sama ma kanta nutsuwa, yana tsaye ya zuba mata idanu cike da tausayi wannan damuwa na matsar Zayyad shekaru 25 kenan tana cikin sa,
Murya can ƙasa tace "dan Allah kada a faɗa ma Sulaiman maganar nan saboda na san zai ɗaga hankalin shi ne kuma hakan ba canza komai zaiyi ba"
GyaÉ—a kai yayi tare da faÉ—in "insha Allah ba zai sani ba, yanzu muje ki kwanta kinga dare ya raba"
Gaba ta shiga yana binta a baya suka bar wurin
 *****
28 /sha'aban/1442
11:07am
Tun asuba muke ta jigila don yadikon Khamis da aka kawo matsayin wanda zata yi ma Yusrah jego na wata 1 bata san zama ba, babban damuwa na ma ba wai zama ko hutawa da bamu yi bane yau gaba É—aya ban kalli TV ba, sai nake jin kaina kamar mara lafiya gashi jiya sunyi tallen wani sabon film jiya, da garin wucewa naga sun saka tallen shi don jiyan ma bata barni nayi kallon yafi na 20 minutes ba gaba É—aya ta shiga rayuwata,
"BoÉ—É—o"
Juyawa nayi ban tanka ta ba don fushi nake yi da ita, yanzu haka ma zaune nake ta haɗa ni da tulin alayyaho ta bani wuƙa wai nayi mata yankan burge mai gida irin siraran nan zata yi miyan taushe aci da rana,
Murmushi tayi don sanin ban cika son hayaniya ba yanzu ma hala ta takura ni ne, take ji a ranta amman dan niman ta ƙular dani ta jawo ni gaban ta dani da robar alayyahon,
Zungurin goshi na tayi tace "ke boÉ—É—o fillo, baki ji ana miki magana ne da ba zaki amsa ba?"
Nan hawayen da nake maƙakewa na rashin kallon su zango da banyi ba ya fara bin kumatu na, a zuciye na fisge jiki na daga riƙon ta cikin muryan kuka nace,
"Ni sunana ba boÉ—É—o bane, kuma kada ki sake cemin fillo babu abinda ya haÉ—a ni da fulani"
Riƙe baki matan tayi tana kallon abin mamaki ganin hawaye shar_shar a fuska na ta bata san na meye ba,
"Ikon Allah Æ´ar nan lafiyan ki kuwa? Me aka miki kike kuka? Daga na kira ki fillo sai ki fara min kuka ko ke ba bafulatana bane?"
"Ni ba bafulatana bace, ni bahaushiya ce ni Æ´ar garin nan ne babu abinda ya haÉ—a ni da garin wa'incan fukanin suci kansu"
Tafa hannuwa tayi tana dariya "heee, lallai zamani, don kin baro su shine zaki yi musu butulci ki raba kanki dasu? Ai shi tuwo duk daɗin shi ba'a canza mishi suna ko ina zaki je a duniyar nan sune asalin ki, kuma da kike cewa ke ƴar garin nan ne ai muma kusan dukkan mu hausa fulani ne kawai rashin riƙe al'ada ne ya kawo haka,
amman dai faÉ—a min meye ya saka ki kuka? Ko aikin ne baki son taya ni?"
Girgiza kai nayi ina daÉ—a matso kwalla don ta barni naje nayi kallo, nace, "daman..d..daman bani son a É—auke wuta ne ina..tna son kallon wani abu..a tv"
"Shine kike kuka? Ta tambaya cike da mamaki, gyada mata kai kawai nayi tace
"Tashi kije" ai kuwa da gudu na miƙe na nufi parlor murmushi yana suɓuce min, nasan yanzu sunyi rabi amman idan na nutsu zan fahimci abinda ake yi,
*****
"Nikam yanzu al'amarin Saudat yafi ƙarfi na abban Jannat har baba ta ƙare tayi magana, awan ta kusan uku a jikin tv tana kallo saida na kora ta kafin taje tayi sallan azahar, duk ayyukan da ya kamata tayi yau baba ne tayi su...."
Gani tayi kaman maganar ta kawai take yi Khamis kanma bayi sauraron ta, ya saka yaron shi a gaba yana faman mishi wasa dukda ba fahimtan komai yake ba, yana son yin barci sai lumshe idanu yake yi amman ƙaran abinda Khamis yake kaɗawa ya hana shi sukuni,
"Abban Jannat"
"Na'am ummin Jannat" ya amsa ba tare da ya É—ago ko ya bar abinda yake yi ba,
"Kaji abinda nake faÉ—a kuwa?"
Sai a sannan ya É—ago yana murmushi yace "sorry baby, me kike cewa?"
"Ayyah nafi 5 minutes ina maka magana tun na É—azu ma nasan ba ji kayi ba, cewa nayi maganar Saudat har yanzu tana kan kallon ta na babu ji babu gani É—in..."
"Dan Allah kada ki ɗaga min hankalin ki a kan maganar da kinsan yinshi aikin wofi ne, kina buƙatar hutu ki daina saka ma kanki damuwa da yawa, ita kuma saudat ki bari sai baba ta tafi zan sayi bulala ne na kewaya ta a sannan ne zata shiga hankalinta ta daina kallon ta na mamakin nan"
 ******
Cakalar abincin yake yi ya kasa kai ko spoon biyar bakin shi, tun yana jin daÉ—in kallon yarinyar nan da yayi jiya har kewanta ya shige shi, a tunanin shi tunda ya dawo kafin ayi sallan magriba idan ya shiga gidan su zai same ta amman shiru, yau da safe ma sau biyu yana shiga gidan amman bata nan kuma ba zai iya tambayar kowa ko ita wacece kuma daga ina tazo ba don baisan wani irin kallo zasu mishi ba,
Da ace yaga Zayyad ne da zai iya tambayan shi game da ita, amman tunda ya shiga gidan yau baiga Zayyad ba, wait!! Baiga Zayyad ba kwata_kwata hakan na nufin kenan... innalillahi wa inna ilaihirraji'un"
Da azama ya miƙe daga dinin table ɗin bai bi ta kan sadiya dake tambayar shi ko lafiya ba ya shiga ɗaki ya saka riga da hula ya fita bai tsaya ko ina ba sai gidan su,
*****
Tunda Muna tazo gidan take saka ido ko zata gane wannan sirrin amman shiru ita bata fahimci komai ba 'to ko ba a nan sirrin yake bane?' Ta tambayi kanta,
Tana zaune a balcony tana tunanin yanda zata ɓullo ma Sulthana ta samu ta sanar da ita wannan sirrin dan yau zuwa gobe kaɗai take dashi kafin lokaci ya ƙure,
Wucewar Sulaiman ɓangaren aunty Amarya kawai ta gani cikin hanzari kuma da alaman damuwa a fiskar shi tayi saurin tashi tabi bayan shi tana fatan wurin da sirrin nan yake zai je...