← Book details Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 73

Sashe 23

Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai a yanzu nayi nadaman faɗa mishin da nayi ganin yanda ya tashi hankalin shi sosai ina ci gaba da zubda hawaye, gashi saboda sakarcina na ɗauki ƙaramin abu na mulmula shi ya koma babba, sai me dan yace min daƙiƙiya? Da ace na faɗa ma Zayyad wani ya kira ni sitifid ban san me zaiyi ba idan yaji babban zagin nan ai daƙiƙiya ƙaramin alhaki ne,

Juyawa yayi zai tafi nayi saurin shan gaban shi ina bashi haƙuri
"Dan Allah a bar maganar nan ya Zayyad ko na faÉ—a maka ma ba abin da zaka iya yi, kada kayi fushi nace fa na yafe"

"Zaki faÉ—a min ne ko ba zaki faÉ—a min ba?"

"Ya Sulaiman ne!" Na faÉ—a cikin É—acin murya,

"Ya Sulaiman kuma? Da girman shi da hankalin shi? To a kan mene zai kira ki daƙiƙiya me ya haɗa ki dashi?"

Nan na kwashe labarin abin da ya faru É—azu a É—akin hajiya na faÉ—a mishi
"Ni ba ƴar garin nan bane ya Zayd, a garin mu ba'a karatun boko ban fara ba nima har saida na dawo garin nan da zama gidan ƴan uwana sannan suka saka ni a makaranta, amman a haka ne na zamo daƙiƙiya? Ko kowa ma irin wannan kallon yake min"

Harara ya jife ni dashi yace "look at you ance miki kowa halin shi irin na babban yaya ne?

Ni na riga da na san da hakan tunda na tambaye ki kin bani amsar gaskiya kuma ina fahimtan fashin ƙwarewar ki idan muna zantawa amman tunda har yanzu baki fasa makarantar ba babu wanda ya san gaba idan daɗa maida hankali maybe zaki shiga sahun masu ilimin, bai kamata ya jife ki da wannan kalamin ba kwata_kwata zanje na same shi muyi magana"

"A'a kada kace mishi komai dan Allah"

****
Da gudu ta ƙaraso inda muke tsaye ta riƙo hannun shi ta fara janshi don su bar wurin,

"Ya Zayyad mu tafi ga babban yaya nan zuwa yana ta niman ka a cikin gida"

Ko gizau baiyi ba ya tsaya a wurin yana jiran ya ƙaraso dan ya fuskance shi yaji a wani dalili zai kira ni daƙiƙiya,

Da tsananin mamaki sulaiman yake kallon su har ya ƙaraso wurin da suke tsaye yana bin Zayyad da kallon sama da ƙasa sannan ya tambaye shi
"Mai kake yi a nan Zayd?"

"Yaya kai ya kamata na tambaya abin da ya haɗaka da wannan" ya faɗa tare da maido da duban shi wuri na.........🤦🏻‍♀️

*Me zai faru gaba*
*Me zai faru gaba*
*Me zai faru gaba*😝😂

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

🤍💚🤍
    *ƘARAMAR BAZAWARA*
           💚🤍💚

    _(Cigaban matar kulle)_

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

         *BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
  And *AISHA ALTO*

19🧝🏻‍♀️
"Wannan wa?" Ya faÉ—a yana duba wurin da Zayyad É—in yake nuna mishi don shi baiga kowa ba,

guduwa kenan Saudat tayi ta barshi a wurin shi da yake shirin sama mata adalci amman ta tafi dukda yace mata ta tsaya wato bai isa da ita ba kenan?

"Wai maganar wa kake yi ne Zayd? Ni banga kowa a nan ba, moreover babu abin da ya haɗa ni da kowa a gidan nan, kana dai lafiya ko? babu abin da ya same ka?" Ya tambaya yana taɓa gefen fuskar shi cike da kulawa da tausayawa,

"Babban yaya daman yarinyar nan ce Sa..."

"Babu komai fa babban yaya, i was just pulling his leg wasa nake mishi nace naga ran aunty Batool a ɓace kuma ina tunanin akan faɗan da kamata take fushi, to da yaga wucewar ta yanzu  shine yake tambayar ka amman babu wani abu" Ruma ta faɗa tana murmushin yaƙe, amma wani zufa ne yake tsatsafo mata ta cikin jikin ta yanda taga Sulaiman na mata kallon tuhuma da rashin yarda, ita dai fatan ta kada gaskiyar magana ta fito a yanzu idan ba haka ba kashin su ya bushe,

"Yaushe ne dawowa na garin nan gaba É—aya da har nayi faÉ—a ma Batool?" Ya tambaya fuskar shi babu alamun wasa,

"Uhmm wasa kawai nake mishi"

"Wasa fa kika ce? Are You out of your mind? ko kinga munyi kama da sa'oin wasan ki da zaki saka mu a tsakiyar maganar vanzan ki making my brother go against me? Do you think it's funny?"

Sunkuyar da kamta ƙasa take yi jin yanda yake daka mata tsawa kaman bai san dare bane, a hankali yanda ba zata ƙara tunzura shi ba tace "I'm sorry babban yaya ba zan sake ba"

Tsaki yaja cike da haushin ta yace ta ɓace masa da gani, siɗin_siɗin ta ja hannun Zayyad wanda yake tsaye dumbfounded a wurin ya rasa wani dalili ne ya saka Ruma yin ƙarya ma sulaiman kuma me yasa ta ɓoye mishi laifin da yayi ma Saudat,

Bai san dalilin ta na yin hakan ba amman dake shi mutum ne mai dogon nazari da tunani yasa bai katse mata hanzari ba ya bita suka bar wurin,
  *****
Rufo ƙofar ɗakin shi tayi bayan sun shiga ta juyo tana kallon shi da already ya sama ma kanshi mazauni a armchair dake ɗakin yana jiran yaji ba'asi,

"Ya Zayyad me yasa zaka yi ma babban yaya maganar Saudat bayan na kira ka ne kawai don kayi maganin matsalar ba ka ƙara faɗaɗa shi ba, haƙuri fa kawai zaka bata daga ta bar kuka magana ya wuce"

"Ke! Ni sa'an ki ne da zaki na scolding É—ina?"

Turo baki tayi cike da shagwaɓa tace "I'm sorry tunda yanzu nice kuma mai laifin, shi yayi mun kaima zaka ƙara min"

"Forget it, Just tell me the reason that makes you said that lie, me yasa kika ɓoye maganar nan?"

"Da ace na barka ka tuhume shi da kaine zaka shiga matsala ko ka manta ne? Cikin sharuɗoɗin harda kiyayewa na daga alaƙa keɓantuwa ko kuma raɓan opposite sex wanda ba muharraman ka ba? Muharraman kan ma yaya aka ƙare da matsalar ka?

Duba ka gani fa har yanzu baka gama warwarewa ba, dalilin da yasa babban yaya ya dawo garin yola kenan ba shiri kuma daga zuwan shi ka tare shi da zancen Saudat? Bayan kana sane da dogon kashedin da aka yi maka kada ka raɓe ta don sama ma kanka kwanciyar hankali?"

"And now you are treathning me huh!" ya faÉ—a tare da jinginuwa da jikin kujeran " ni banda right É—in yin soyayya ne? Shikkenan saboda wata jarabawa da Allah ya É—aura min sai ba zan so raya sunnar ma'aikin shi ba ni ba zanyi aure ba?

Ban ƙetare wani doka da babban yaya ya shimfiɗa min ba don har yanzu ban faɗa ma Saudat ina son ta ba, nafi son sai sauran shekaru biyun da aka ɗiba min sun cika kafin na bijiro mata da buƙatata ta amince da aure na nasan lokacin ta ƙara girma da hankali kuma insha Allah ba zata ƙi amincewa ba saboda nasan itama tana jin wani abu a kaina"

"Duk ka ajiye wa'innan a gefe, nima ina bayan soyayyar ku ina son ganin kunyi aure wata rana, kuma zan tallafa maka da goyon baya har duk wasu burikan ka su cika yayana, amman ka ajiye wannan abu a matsayin sirri tsakaninmu mu uku gudun kada ka saka boÉ—É—i a matsala,

Yanzu kowa a gidan nan ta lafiyan ka yake, harta Sulthana da aka san da zancen auren ku an ajiye ta a gefe burin kowa yanzu shine ganin ka rabu da wannan matsalar idan allah yaso,

idan har ka bari aka san ka fara son saudat to za'a nisanta ku da juna dan an san tilas wata rana zata san da matsalar ka kaga sirrin mu ya fita daga gidan nan kenan, kuma a dalilin haka babban yaya zaiyi mata hukuncin da ba zata iya É—auka ba batare da yayi la'akari da cewa ita ba jinin mu bace"

"Ni kuma dake lusari ne na zamo mara amfani sai ina gani ya cutar da ita ban É—auki wani mataki ba?"

"Kana son saɓani ya shiga tsakanin ku ne saboda ita?"

Murmushi yayi yace "Ruma kenan! A tunanin ki kaman yanda Ya sulaiman yake a wurin ku haka yake a wuri na? We are more like friends than brothers yanda tsakanin mu yake kaman babu tazaran shekaru, har gobe yana faɗa min bayi da wani wanda ya kaini ta yaya za'ayi boɗɗi ta zamo silar samun saɓani a tsakanin mu?"

"Indai a kan matsalar ka ne wallahi zata zamo"
Ta ƙarasa gaban kujeran shi ta zauna saman carpet tare da ɗaura hannun ta a saman guiwowin shi ta ɗan ƙara karya murya dan ta samu nasarar lallaɓa shi ta lura shima wani ɗan taurin kai ne,

"Ya Zayyad"

ÆŠagowa yayi ya kalle ta tare da amsawa da na'am saboda yanda yaji tayi ma sunan wani irin kira

"Ya Zayyad dan Allah, i beg you kabi komai a hankali please kada ka ɓata rawan ka da tsalle just keep praying insha Allah saudat taka ce"

"A bari ya huce shi ke kawo rabon wani, ba zan juri rasa ta ba"

"Ba zamu ma bari ya hucen ba insha Allah, babu zancen matsala babu batun wata Sulthana, a gaba kai zaka auri boÉ—É—i in Allah ya yarda"

Jan dogon numfashi yayi ya furzar tare da daÉ—a zamewa a kan kujerar ya faÉ—a duniyar tunani, abubuwa sai daÉ—a dagulewa suke yi

**********

Da gudu na shiga part ɗin ta ƙofar baya ina tafiya ina waiwaye kada a biyo ni, da ace wannan zazzaɓin yaji na kai ƙarar shi da yau tusa na ya hura wuta,

Shiga na parlor ke da wuya naci karo da TV na playing film É—in hausa ga su gabon sai zuba love akeyi, babu kowa a parlorn kuwa sai aunty Zaytoon tana kishingiÉ—e tana latsa wayar ta,
Chapter 23 · 0% Book details