← Book details Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 73

Sashe 35

Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yaya daman saudat ne zata tafi gida...." dumm ƙirjin shi ya buga jin ana nima ɓata mishi plan, yayi tunanin yanzu komai zai daidaita saudat zata saba da luxury life amman ana niman maida ta cikin talauci,
" shine nake so na bita mu tafi ran jajiberi sai na dawo"

"Babu inda zaki je" ya faɗa a dake ba tare da ƙarin bayani ba ya kashe wayan sannan ya saka hular jamfan shi ya fita da sauri ya faɗa mota tare da bawa driver umarnin ya kaishi gidan su,

  ******
Harda aunty Amarya aka fito min rakiya wannan karon a matsayin ta na wanda taje har gida ta ɗauko ni itama ta zuba min kaya masu yawa, hannu na a cikin na junior muna tafiya kaman zaiyi kuka gashi malalacin saurayi ko handbag ɗina ya kasa riƙewa sai surutu da kwainane,

Da wani speed motar ta shigo gidan wanda har ya jawo hankin mu gare shi, ya fito a motar da sauri ya nufo inda nake yana tamabayan "ina zuwa?" Kaman bai sani ba,

Da ƙyar cikin tsoro na amsa mishi da "gida zan tafi"

"To ba zaki tafin ba, makarantar fah?!..........🤦🏻‍♀️

Love you my fans😍

#team SS❤️
#team SZ💙

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

🤍💚🤍
    *ƘARAMAR BAZAWARA*
           💚🤍💚

    _(Cigaban matar kulle)_

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

         *BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
  And *AISHA ALTO*

29🧝🏻‍♀️
"Zaki ɓace min da gani ne ko sai na ɓaɓɓalla ki?"

Ku gane min ikon Allah mutum da ƙarfin hali, ba shi ya kawo ni gidan ba kuma ba shine dalilin zuwa na ba amman yana min dole sai na zauna?
Kallon shi nayi sai faman muzurai yake yana hura hanci halin shi da ya ɓace na kwana biyu ya dawo sabo tarr, ban motsa daga wurin ba har saida yazo ya fincike jaka na yayi wurgi dashi tare da daka min wani uban tsawa,

"Wuce ki koma ciki nace!!!"

na tsorata sosai da yanayin shi amman na kasa bin umarnin shi ya rufe idanu sai faɗa yake yi wani sa'in ma ba jin abinda yake cewa nake yi ba saboda ɓacin rai don har cikin zuciya ta ina muradin komawa gida sosai, ina so naje na duba aunty Yusrah domin banyi wa kaina adalci ba tunda na musamman aka ɗakko ni daga gidan mama aka kai mata saboda ina taya ta ɗawainuyan jego amman gashi nazo nan nayi zama na, idan na ƙara koda kwana ɗaya ne ban kyauta ba,

"Ka barta ta tafi mana Sulaiman ai tace zata dawo kuma makaranta ba sai bayan sallah a koma ba?"

"Za'a fara mata extra lesson ne aunty, kuma daga yau zai fara banga amfanin komawan ta gida ba, so kindly take your luggage and go inside bani so in sake magana saudat" ya ƙarasa maganar yana kallo na da idanun shi da suka rikiɗe suka koma jajaye lokaci ɗaya,

Yi nayi kaman ban jishi ba na sake yima su Ruma da junior sallama na raɓa ta gefen shi zan wuce,
A zuciye ya hankaɗa ni baya har saida na kusan faɗi ƙasa da taimakon akwatin hannu na nayi maintatining balance ɗina sannan na ɗago ina kallon shi, ɓacin ran na menene kuma?

Dady bayi gida, Hajiya kuma tana can ciki bata san ma me akeyi ba daman aunty amarya ba wani jin maganar ta sulaiman yake yi ba, saboda yanda yake nuna min isa yasa ba zan ji maganar shi ba don ko Khamis da ya É—akko ni yake kula dani bayi min irin haka,

Haka na tirje ina mishi tsayayya daga ƙarshe muka hau cacan baki yana faɗa ina mayarwa hawaye na tsiyaya a idanu na babban yaya ji yake yi kaman ya saka ni a turmi ya kirɓa ni, bayi son tsayayya da taurin kai shi yana so a ko wani lokaci mutum yabi umarnin shi kawai,

Na buɗe baki zan sake magana Ruma ta tare ni a kunne na ta raɗa min "Mu tafi ciki dan Allah boɗɗi ki daina magana haka nan, zamu roƙe shi ya barki kije gidan daga baya for now just cool down please"

Kwace jiki na nayi daga riƙon ta cike da rashin kunya na wuce zan tafi tare da bari musu jakan kayan a wurin, motar da aka ajiye zai kaini gida ma ban kula shi ba na nufi gate abuna ko mai zai faru ya faru indai babban yaya ne saidai ya kashe ni amman nikam sai na tafi,

Cikin sassarfa ya nufo ni tare da finciko hannu na, na zube a ƙasa amman haka yake jana a wulaƙance duk suna gani babu wanda yayi koda magana dai-dai lokacin da saƙo ya isa kunnen Hajiya ta fito don ganin abinda yake wakana amman kafin tayi wani magana yaji an buge shi a ƙirji,

Ɗagowa yayi idanun shi suka sauƙa cikin na Zayyad da yake aika mishi wasu sharp look, ranshi yayi matuƙar ɓaci da abinda ya gani amman bai nuna hakan ba a fuska,
Buge hannun shi dake jiki na yayi tsugul na miƙe na koma bayan shi na laɓe ina kallon sulaiman da ya zamo confused don Zayyad ya shammace shi sosai,

"F**k off bro, me kake yi haka ne?"

Nuna kanshi yayi da yatsa yana tunkaro shi yace "Zayd!! Are You using this abusive word on me your own brother?!"

"To a kan me idan kalmar baki tayi maka zafi zaka wulaƙanta wata? Kai kaɗai ne mai zuciya da idan akayi maka abu zaka iya yin fushi amman wani sai kayi mishi abun da kaga dama?"

"Are You stupid?! Kana cikin hayyacin ka kuwa ka san da wa kake magana"

"I'm not stupid but you are, ka taka kowa yanda kake so ciki harda ni ba zanyi magana ba saboda dukkan mu kana da iko a kanmu amman ka kuskura ka sake ƙoƙarin cin mutuncin Saudat ba zan bari ba ya Sulaiman i will use all my power to protect her"

Daga kallon idon Zayyad na gane cewa ba shi ɗaya bane, bani tunanin zai taɓa ɗaga muryan shi saman na babban Yaya indai yana cikin hankalin shi saboda tsanin yanda yake girmama shi yake masa biyayya,

hakan na nuna min cewa aljanun shi ba kurame bane kaman yanda nayi tsammani daga farko duk iya ƙoƙari na wajen gane hakan na gaza domin ba wani ƙwarewa nayi ba kuma yanayin sautin da yake fitarwa idan sun tashi baiyi kama da masu budaɗɗen murya ba,

Tasa ƙeya na yayi a gaba zai fitar dani waje, ko shima bai san me zaiyi min idan mun fitan ba amman sai tafiya kawai muke yana riƙe da jakan kayana, riƙo shi da Sulaiman zaiyi ya taƙarƙare ya kai mishi naushi a ciki dukkan su biyu suka zuba a ƙasa,

  ***

Yau naga tashin hankali fari da baƙi harma da ja, bayan na gama amsan laifin da ya faru wanda ya kasance nice musabbabin faruwar komai kaman yanda Sulaiman ya faɗa an kuma haɗa ni wuri ɗaya da Zayyad don nima mishi lafiya,

It hurts ganin shi a cikin wannan yanayin ga raunuka a gefen fuskar shi har saman hancin shi a kuje yake, aunty ta fara kokwaton abun da yake ɗago su akai_akai domin kwanakin baya ya kan shafe kusan 1 month ko fiye da haka lafiya lau, amman yanzu bayi sati guda ƙwaƙƙwara cikin ƙoshin lafiya,

Ina gama aiki na muka fice aka rufo mishi É—akin sannan kowa ya kama gaban sa ina jin mugun kallon da sulaiman yake watsa min a jiki na da nazo wucewa,

Ban bar gidan a ranar ba don ina son tabbatar da lafiyan Zayyad kafin na tafi, ban koma part ɗin aunty Amarya ba gudun haɗuwa da zagi da habaicin su nana don nasan bakin su ba zai mutuwa ba sai sunyi sharhi a kan abinda ya faru a yau, dukda bani can ɗinma Batool ta faɗa min sunyi amman banji ba ballantana raina ya ɓaci,

Washe gari babu wanda ya tare ni da maganar don kusan tashi mukayi da babban yaya a gidan tun 8 yazo gashi lokacin Zayyad ya farka har doctor yazo anyi dressing ciwukan shi, ina so na tafi amman ina tsoron kada wani abu ya sake faruwa,

Ina jikin sink ina wanke naman da za'a haÉ—a ma Zayyad abin da zaici tunda yanzu azumi babu shi Rumaisa ta shigo "dan Allah saudat kije ya matsa yana son ganin ki, ko sai kin gama ja mana rai ne"

"Ke da yayan naki duk baku da haƙuri wallahi ku bari a gama wannan sai muje gaba ɗaya kada a ya zauna da yunwa"

Bata ce komai ba ta taya ni muka gama sannan muka nufi ɗakin shi da tray ɗin abincin a hannun Ruma, muna shuga muka ci karo da aunty Amarya tana zaune tana tofe shi da addu'oi shi kuma ya saka agogo a gaba yana kallon awa ɗaya kenan harda ƙari da ya tura Ruma ta kira masa ni itama taje ta zauna kaman an aiki bawa garin su,

Yana jin sallamar mu a birkice ya juyo yana shirin min magana nayi saurin dakatar dashi ta hanyar É—ora yatsa na a saman baki na nayi masa nuni da aunty amarya,

Shiru yayi ya koma ya jingina da jikin gadon duk inda nayi yana bina da ido, a tunanin shi aunty fita zatayi amman sai gani yayi ta saka spoon a cikin abincin da muka zo dashi ta kai saitin bakin shi,
Yana tsananin son magana dani amman ba zai taɓa iyawa a gaban ta ba tunda har yanzu bata san me muke ciki fa,

Kaman ƙaramin yaro haka ta dinga bashi abincin a baki har sanda yace ya ƙoshi sannan ta tattara ni da Ruma muka fita wai a barshi ya ƙara samun hutu shikuwa ba haka yaso ba,
Chapter 35 · 0% Book details