← Book details Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 73

Sashe 49

Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙara lafewa nayi a jikin inna ina dariya kasancewar gadon yana da girma abinka da asibitin kuɗi, don tuntuni abinda suke yi kenan shida matan shi da yaran shi da baba inna dai kaman kunyata take ji ya Aminu kuma ya zama wayayye yanzu zahirin shi kaɗai ya isa ya nuna hakan,

"Ka daina kiranta auta fah ka saka ta ƙara sakalci daman yaya lafiyan kura bare taga nama? Kin daiga ƙanwar ki a gaban ki yanzu itace da tutan auntan"

"A'a wallahi, ban yarda ba ita dai tazo daga baya amman ba ita bace auta dan na riga da na cire tutan auta har gobe nice Æ´ar gaban goshin inna da baba harma daku...nasan kunfi sona a kan kowa"

Yarinyar da aka kira da ƙanwata mai shekaru 5 a yanzu sai tsilli_tsilli take da ido tana bin dukkan mu da kallo musamman ma ni da bata san waye ba kuma taga naje na maƙale ma mahaifiyarta, an aifeta ne watanni 6 bayan guduwa na daga wuroɓokki lokacin da suke ganiyar cin azaban laifin da basu aikata ba, dukda yawancin aihuwan da innata takeyi a gida ne amman bata taɓa shan wahala da azaba irin na aihuwar Aisha ba wanda suke kira da indo,

"Ai dole ne mu soki so mai tsanani saudat, babu wanda ya shiga jarabawar rayuwa irinki, kinsha wahala sosai babu abinda zai kawo miki sauƙi a zuciya bayan soyayya shiyasa muke baki yanzu kuma zamu ci gaba da miki HAR ABADA"

Sassanyar murmushi nayi nace "ai kaima ka shiga jarrabawar ya aminu, kaman yanda na gudu saboda tsoro kaima haka ka gudu saboda tsoro, kaima hankali ya tashi ba'a san inda kaje kuma a cikin wani hali kake ba,.....mundai gode ma Allah tunda ka dawo lafiya lau"

"Nifa namiji ne kuma koda a lokacin na mallaki hankalin kaina, da na tafi ban buƙaci tallafin kowa dan yin rayuwa ba nayi amfani da ƙarfina na nemi halaliya na gina kaina dashi har nayi aure nake kula da iyalina amman kefa? Ba don Allah ya jefa ki a hannu na gari ba inada tabbacin rayuwar ki lalacewa zaiyi"

Tashi nayi na zauna kana na miƙa ma ƙanwata Aisha hannu na duka biyu ina gyaɗa mata kai alamun tazo gareni, bata yi ƙasa a guiwa ba ta ƙaraso da hanzarin ta na ɗaga sannan na ɗaura ta a saman cinyana a kan gadon,

"Baba!...nayi maka alƙawari da kai da inna rayuwar indo ba zai taɓa zama irin tawa ba, idan Allah ya yarda ba zata san meye wahala ba bazata zubar da hawaye mara daliliba matuƙar ina raye, zan jajirce nayi aiki tuƙuru don na zama wata watan watarana don nima na kula da family na nayi musu gata na mantar damu wahalar baya insha Allah, ina sonki Aisha zan inganta rayuwar ki da ikon rabbi"

   ******

Motar sulaiman na shigowa nashi ya biyo bayan shi zuwa cikin gidan da É—an iskan gudu, ya riga ya ganshi amman bai gwada damuwa ba dan yasan tabbas za'ayi hakan, shiyasa driver na parking ya buÉ—e marfin motar shi da kanshi ya fita,

Ko parking mai kyau zayyad baiyi ba ya ɓalle marfin motar ya fito sannan ya nufo sa gadan_gadan cikin sauri yasha gaban shi, saidai suna haɗa idanu yaga yayi mishi mugun kwarjinin da ya saka rabin fushin shi yabi iska,
"Wa kake nima É—an yaro? Ko yau anyi tunani ne aka zo gaida ni har cikin gida?" Ya faÉ—a cilin salon rainin wayo,

Sulaiman always look scary amman dukda haka saida yayi ƙoƙarin tattaro sauran kuzarin shi cikin kaushin murya yace
"Tana ina ya sulaiman? Ina ka kaitaa??".

"Ita wa??....oh Saudat wai?" Sunkuyowa daidai kunnen shi yayi kaman wanda bayison wani yaji abinda zai faÉ—a ya raÉ—a mishi "na kaita can da nisa wurinda za'a raba ta da kai tayi maka nisa na har abada, ka saka ma ranka daga yanzu ka fara sallamar boÉ—É—i daga cikin rayuwar ka"

Sai kuma ya ɗago yana murmushin da ya bayyana fararan haƙwaransa yace "bari na tafi wurin ɗayan iyalinan kada na barta tana jira kasan abinka da wanda ya ajiye ko yaushe dakon sa akeyi ta ko wani siga ana tarairaya shi"

Da faÉ—an haka ya juya ya shige gida ya bar zayyad daskare a wurin kaman an shuka dusa,

A parlor ya tarar da sadiya taci kwalliya na kece raini cikin shadda sea green da yasha paralysed paintwork har ƙasa saidai yanzu babu tarkacen jewelries tayi kyau fuskarta babu wani kwalliyan azo a gani tana kishingiɗe a kan kujera da glass ɗin juice da bowl ɗin cookies tana ci tana kallo hankalinta a kwance,

Tunda ta amsa sallaman shi taci gaba da hidiman gabanta har ya wuce yaga itqma bai kamata ya barta haka ba sai ya dawo parlorn ya zauna a kujerqr dake gefen nata kana ya cire hulan kanshi ya ajiye ya umarci maid É—insu ta kawo mishi ruwa,

"Halima" bata amsa ba ta juyo tana kallon shi saida taga bayi da niyyan sake cewa komai ne tace "na'am"

Ƙaramin murmushi yayi yace "daman so nakeyi nai miki ɗan ƙaramin albishir, alƙawarin da nayi miki na kuɗaɗen da zan baki idan na samu cikar vurina ya kusa cikawa saboda yanzu haka na samu kusanci da iyayen Saudat suna cikin garin yola kuma ba zasu je ko ina ba har sai sun bani aurenta insha Allah...........🤦🏻‍♀️

Love You my fans🥰

*team SSFOREVER21*😅
ba dai ni na faɗa ba sis muneerah ce 🏃🏽‍♀️🏃🏽‍♀️🏃🏽‍♀️

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

🤍💚🤍
    *ƘARAMAR BAZAWARA*
           💚🤍💚

    _(Cigaban matar kulle)_

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

         *BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
    And *AISHA ALTO*

*Ita ɗin masoyiyar masu masoya ce🥰 ita ɗin ɗaya ce cikin zaɓaɓɓu😍 ita ɗin tana zama abin alfahari ne ga wa'inda suka santa da wa'inda ke tare da ita🤩 ita ɗin ZAINAB BAWA ce marubuciyar BIBIYATA AKEYI, AUREN FARI and more💓 wannan shafin sadaukarwa ce a gareki😊 ina miki son so fisabilillahi💝*

42🧝🏻‍♀️ 
Gyaɗa kai baba yayi bayan yaji bayanin Sulaiman wanda kallo ɗaya zakayi mishi ka fuskanci tsantsar damuwa da fargaba da yake ciki, daman yasan wannan ranan tana zuwa....ko ba daɗe ko ba jima yasan rana irin wannan zaizo da asirin da yayi ƙoƙarin birnewa tsawon shekaru masu tarin yawa dai buɗu a idon duniya, saidai alhamdulillah tunda ya riga da ya cika alƙawarin da ya ɗauka ma zayyad da familyn shi gaba ɗaya kuma martabar su ya riga da ya ɗagu zuwa matakin da har abada ba zai faɗo ba,

Numfashi ya furzar a hankali yace "toh shulaimanu shidai lafiya Allah ke badawa shaidai ɗan adam yayi nashi ƙoƙarin wajen shamo magani, yanda aljanu shuka rabu kala_kala cikin jinsuna kaman ƴan adam haka hanyoyin kamuwa dashu da kuma rabuwa dashu shuka rabu kashi_kashi, yanzu dai ba zan baka tabbaci akan Zaidu zai warke ba amman zamuyi iya ƙoƙarin mu da ikon Allah, shaidai zansho shai mun koma wuroɓokki don al'amarin babba ne"

Jimm sulaiman yayi yana tunani, indai hakan zata faru tofa lallai shi zai tsara komai yanda za'a bawa su malam ardo da zayyad kariya yanda mutanen garin ba zasu samu wani dama na cutar dasu ba sannan ya kasance tare dasu don ganin komai ya tafi dai_dai,
Shi da yaso fita harƙan shi gaba ɗaya ya watsar da sha'anin shi saboda yaudaran shi da yayi! Me yasa ƙaddara zatayi mishi haka? Har ƙoƙon ranshi yake ƙaunar Zayyad ba zai taɓa barinshi da ciwo ba bayan sun sami hanyar maganin shi,

_shikkenan zaiyi masa saboda Allah idan yaga dama yaci gaba da cutar dashi Allah zaiyi mishi maganin sa_

Numfasawa sulaiman yayi yace "shikkenan baba insha Allah za'ayi yanda kace, daga zaran inna ta samu lafiya zamu je ƙauyen dukda dai kaman yanda na faɗa daga farko banso komawan ku can ba naso a sama muku matsuguni a nan ku zauna cikin kwanciyar hankali saidai babu matsala a hakanma, insha Allah ni nayi muku alƙawarin babu wanda ya isa ya sake cutar daku zaku koma gida kuci gaba da rayuwan ku kaman kowa"

Cike da jin daÉ—i malam arÉ—o ya gyada kai yana murmushi tare da jinjina karamci da dattakon wannan yaro,
"Allah yasha ka gama da duniya lahiya shulaimanu, banshan dame jan biya ka ba, ka inganta rayuwar shaidatu ba tare da kuna da wata dangantaka ba gashi muma kana ta hidima damu, Allah ya shaka maka da alkhairi, Ubangiji Allah ya kareka daga dukkan sharri da mai sharri,

Da "ameen" ya amsa daÉ—in addu'an malam arÉ—o yana ratsa shi, zama yayi kaÉ—an suka tattauna akan yanda tafiyar zata kasance sannan suka koma É—akin da inna ke kwance yayi musu sallama kan zai wuce, yana jin kaman ya É—auki saudat ya tafi da ita amman ba zai iya ba saboda idanun iyayenta,

Shi karankanshi yasan yayi kewarta sosai gashi kwana biyu yana ganinta a cikin yanayin da yake so dukda a halin yanzu tana cikin tashin hankali amma burinshi bai wuce kullum yaga murmushi a saman fuskarta ba kuma zaifi so ace idan tana tare dashi take yi,

Kawar da tunanin yayi a ranshi ya tada motar ya tafi saida ya isa gida ya umarci drivern zayyad É—in yaje ya É—auko shi sannan ya wuce wurin dady ya faÉ—a masa abinda ya faru da safen ya kuma sanar dashi hukuncin da suka akan lafiyqr zayyad É—in,

Dady ya gamsu kuma yaji daɗin hakan baiyi wani ƙorafi akan zuwansu wuroɓokki ba sai fatan samun nasara, daga nan ko ciki bai shiga ba ya wuce gida don yasan da zaran aunty amarya taji wannan zancen toh babu abinda zai tafi dai_dai musamman idan tasan sulaiman gaban kanshi yayi ba tare da ya shawarce kowa ba, don maganin da sukeyi kwanaki ma ita take kawo musu cikas idan akace su koma rana kaza sai ta saka zayyad yaƙi zuwa ko kuma taƙi bashi maganin da aka kawo, a cewarta wahala kawai suke ƙara bashi da maganin,
Chapter 49 · 0% Book details