← Book details Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 73

Sashe 65

Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai yanzu abin ya faɗo min, babban kuskuren da zanyi yanzu shine gujewa ƙaddarata idan nayi wasa hakan ya zamo sanadin rasa rayuwan iyayena,
Da gudun da na É—ebo na shigo dashi na É—iba na fita ban damu da mutanen dake kan hanya wanda ke tsayawa suna suna kallona har saida na isa gida.

Hanan ne ta fara tunkaro ni tana magana ƙasa_ƙasa da alama ba kowa bane yasan da fita na
"My dear ina kikaje? Mun zo dubaki baki nan, kin É—aga ma Inna hankali sosai"

"Sorry baby Hanan na zaga nan baya ne na É—an samu fresh air tunda na kasa baccin"

Cikin zolaya tace "Don't try that again, kinsan yanzu ke mallakin wani ne ya kamata ki tambayi izinin mijinki kafin ki fita ko ina, kinji ko?"

Gyaɗa kai nayi ina murmushin dole tace. "oya muje mu shirya sun kusan ƙarasowa"

Saida na shiga nayi wanka kafin na dawo na samu ta baje min kayana da duk wani abun da zan buƙata, na shafa mai da turaruka na saka kaya sannan na zauna Hanan ta fara shiryani.

"My dear" ta kira sunana kaman yanda ta saba lokacin da take saka min necklace,
Da "uhmm" na amsa ina kallonta ta cikin mirror.
"You are very lucky boɗɗi, kiyi haƙuri I don't mean to insult you amman ban taɓa zaton daga ƙauye kike ba saboda kin samu rayuwa mai cike da wadata gashi yanzu ma zakiyi aure a gidan wadata, bakiga gidan ki bane so masha Allah wallahi.
Shiyasa nima na yanke shawarar yanda na fito daga gidan daula ba zan bari soyayya ya kaini ƙasa ba wallahi, ni zan iya auren mai fitinannen arziƙi koda bani sonshi amman duk tsananin son da nake yi wa guy idan talaka ne ko kuma be kai gidan mu arziƙi ba toh gaskiya saidai a rarrashi zuciya amman ba zan iya ba"

Murmushi kawai nayi ina nazarin kalamanta a kaina, I'm very much sure Hanan have never been in love ammam da ta taɓa sanin menene soyayya na gaskiya da ba zata taɓa furta wa'innan kalaman ba. Ni koda ace Zayyad bayi da komai to zan zaɓe shi sau dubu akan Sulaiman because I love him so much.

"Baby Hanan you don't know what is love, amman indai kin tabbata wannan shine burin ki na rayuwa to zan shawarce ki da ki dinga roƙon Allah to not make you know what is love, musamman kiso wrong person idan kuma ba haka ba rayuwan ki zata ƙuntata dukda tarin dukiyan da kike ciki".

Ta baya ta sako hannayenta ta rungume ni muna kallon fuskar juna ta madubi cikin raÉ—a tace
"Yanzu na fahimci abinda yake damunki, amman Please ki daure ki koya ma zuciyan ki son mijinki you will find happiness somewhere, Allah ya baki ikon cinye jarabawan ki na rayuwa"

Zan saka kuka tayi saurin dakatar dani "don't! Kada ki maida min da aiki baya dan Allah, now smile"
Murmushi nayi dukda idanuna suna niman tara ƙwolla amman na dakatar dasu.

Har muka tafi ban sake ganin furere ba, naso ace tana cikin mutanen da zasu rakani É—akin mijina a matsayinta na tsohuwar aminiyata amman hakan bai samu ba.
In moderate speed convoy É—inmu yake tafiya har muka shiga cikin gari.
Muna zuwa wurin wani roundabout motocin dake gaban mu da bayan mu suka É—auki wani hanya daban zallan wanda nake ciki tare da Hanan ne yabi wani hanya wanda bamu san ina zai kaimu ba, dukda ni kaina na rufe da mayafi bansan bidirin da ake ba amman Hanan na ankare da abinda ke faruwa.

Matsowa tayi kusa da kunnena tace "dear ina zamu jene? Naga sauran ƴan ɗaukan Amarya sunbi hanyar da ze kaisu gidan ki amman gashi mu a nan Wannan ze tafi damu wani wuri, ko sace mu akayi ne?" Ta ƙarasa tare da ƙwalalo idanu.

Saurin yaye gyale na nayi ina kallon hanyar, no wonder mana suka sako ni a mota ni kaÉ—ai babu irin tsoffi Æ´an rakiyan nan.
Leƙa fuskar me tuƙa motan nayi naga Ya Nafi'u ne, ban gama mamaki ba sai ganinmu nayi a ƙofar City hospital.
"Asibiti kuma? Me ya kawo mu asibiti ya Nafi'u?"

"Wurin mijinki muka zo" shine amsar da ya bani a taƙaice.
Dumm naji ƙirji na ya buga, ko wani abu ne ya samu Sulaiman ɗin?
Ban samu damar tambayar shi ba don tuni ya riga da ya fice daga motar, ya zago ya buÉ—e mana muka fita sannan muka hallara ciki.

Muna yanko kwana na hango Sulaiman zaune kan waiting chairn da suke zaman jira tun safiya.
To kodai bashi bane mara lafiyan? Wa suka kawo? Me ya same ta ko shi?
Duk wa'innan tambayoyin ma kaina nakeyi na kas buÉ—e baki na tambayi shi wanda muke tafiya tare dashi.
Muna ƙarasawa inda yake zaune ya miƙe tare da buɗe ƙofar room ɗin da nake kyautata zaton a wurin aka kwantar da patient ɗin namu.
"Get in" ya faÉ—a cikin kasawar murya.
Ganin ban fahimci dani yake ba yasa ya sake cewa
"Ki shiga kiga halinda mijinki yake ciki"

Which kind of mijina?... Wait... Does that mean? Innalillahi wa inna ilaihirraji'un.

Tsayawa nayi na kafe Sulaiman da idanu cikin matsuwan jin ƙarin bayani, wani ɓoyayyanen numfashi yaja yace
"You got married to Zayyad and not me, saidai tun safe muka same shi a É—aki unconcious har yanzu kuma bai farka ba"

A firgice na faɗa ɗakin, ina shiga ya jawo ƙofan ya rufe.

Kwance yake kaman babu rai a tattare dashi, fuskar shi tayi haske bakin shi a bushe, sai zara_zaran lashes ɗinshi da ya ƙawata idanunshi, my Zayyad always look great.
Zama nayi a kujeran dake gaban gadon shi, tunawa da nayi da sulaiman ya kira shi da sunan mijina yasa na janyo hannunshi na kai saitin bakina na bashi peck hawaye masu zafi suna bin kunci na.
Me yake faruwa ne? Abubuwa da yawa na son nesanta ni dashi.
A da lokacin da yake cikin ƙoshin lafiya an shiga tsakanin mu an raba mu yanzu kuma da na riga na zamo tashi gashi nan yana kwance rai a hannun Allah what happened to him.

Daɗa riƙo hannun nayi na rungume a cikin ƙirjina naci kuka na sosai na ƙoshi ina jin kaina kaman ana sarawa da wuƙa har bacci ya ɗauke ni a haka.

****
6:06pm
BuÉ—e idanun shi yayi ya zuba ma fiskana da na kwantar da kaina a kan gadon shi ina bacci ina ajiyan zuciya ga shatin hawaye da ya bushe na kukan da na sha.
Murmushi yayi tare da tashi zaune ya fincike kanulan dake jikin É—ayan hannun shi ina manne da É—ayan matt.

Hannu yasa ya ture kallafina da daman ƙiris ya rage ya kama gabanshi, cike da birgewa yake shafa gashin kaina da yasha gyaran amarci.
Jin ana taɓani yasa na buɗe idanu tare da ɗago kaina ina kallon shi, kaman a mafarki nake ganin murmushin da yake sakar min wanda beauty point ɗinshi suka daɗa ƙawata shi, tashi nayi na zaune tare da matsawa daga kusa dani ina gyaran murya.

"Na san sun bani ke Saudat, tunda na buÉ—e idanuna na ganki tare dani nasan ke tawa ce a Yanzu, don't tell me otherwise please"

Tamke fuska nayi nace "Bari naje na faÉ—a musu ka farka" na faÉ—a tare da juyawa zan fita, cikin azama ya diro daga gadon ya fisgoni sai ji nayi na faÉ—a a jikin shi ya rungume ni tsam,
Wani irin shock naji tun daga yatsun ƙafana har zuwa tsakiyar kaina, ba don riƙon da yayi min ba na wasa bane da tuni na zube don ji nayi gaɓoɓin jikina gaba ɗaya sun sake, ga ɗumin numfashin sa dake sauƙa a gefen wuyana yana daɗa sakar min da kasala.

"Please stay... Stay with me.... please...stay," ya furta cikin jan numfashi.
Koda ina da ƙarfin gujewa daga gare shi yanzu ya riga da ya gusar dashi.

"Nayi kewarki sosai babes please kada ki zauna cikin fushi zaki cutar dani, you know that I'm madly in love with you, mafarki na a kullum shine na samu na aure ki, yanzu da na samu kika zamo tawa bazan iya jurewa kaman yanda na jure a baya ba, kada ki guje ni dan Allah"

Ji nayi jiki na ya daÉ—a mutuwa, fushin yafe soyayya ta da yayi da nake ji a duk lokacin da nayi ido huÉ—u dashi presence É—inshi kusa dani ya tafiyar dashi, i have no other option than to hug him back, a hankali na daga hannayena har suka kai gadon bayan sannan nan hawaye suka fara sintiri saman fuskana na É—aga kaina sama saboda yaji abinda zan faÉ—a don yayi min tsawo sosai.

"Hamma zayd..." Na dakata lokacin da kuka yaci ƙarfi na, kaina da babu ɗankwali ya saka hannu yana shafawa cikin sigar lallashi, yana juyi dani a tsakar wurin a hankali.
"I was afraid of loosing you! My life is filled with fear saboda kai hamma zayd because idan na auri wani ba kaiba ina tsoron ba zan iya masa biyayya yanda ya kamata ba, ina tsoron ba zan iya bashi zuciyana ba, ina tsoron ba zan saka shi farinciki, ina tsoron zama matar da mijinta zai auri gangar jikinta kawai Azaban Allah zai iya tabbata a kaina a saboda haka"

Ranƙwafowa yayi ya daidaita tsayinmu sannan cikin raɗa yace "maybe a da idan kina hawaye ƙona min zuciya kawai suke yi amman yanzu hakki ne a kaina in hana ki kuka" da faɗan haka ya haɗe bakinsu wuri ɗaya, UMMU NAJMA ma daga nan ta tattari masillan ƙafafuwanta ta bawa wa'innan sabon auren privacy...........🧚🏼‍♀️

*Three more pages to go insha Allah*

*Ku faÉ—i ra'ayoyinku a kan wannan haÉ—in, yayi muku ko baiyi ba, idan na duba ni kuma zan faÉ—a muku nawa dalilin da yasa ba'a bawa Sulaiman boÉ—É—i ba*

Love You my fans ❤️
Team SZ forever 21

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

*BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*
Chapter 65 · 0% Book details