Sashe 54
Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har ƙofar gidan baba fadawan maigari suka rako mu, suna zuba fadanci kace mai garin ne da kanshi, basu bar wurin ba saida suka ga shigewan mu ciki sannan suka tashi daga wurin da suke zube a kasa sukayi gaba,
Wajajen magriba kowa ya watse suka koma cikin garin yola, sai lokacin na samu daman kiran Sulaiman na roke shi kan zancen cutar mai gari kuma bai musa min ba ya amince zai taimaka a nema mishi lafiya dukda kuwa yana sane da abubuwan da yai min, amman shi bai damu ba saboda Allah yake son taimakon shi kuma saboda soyayyar da yake min babu abinda zan roqa da ya shafi kuÉ—i a yanzu da bazai iya min shi ba,
Muna gamawa mukayi alwala nida indo, sannan na fito mana da darduma mukayi sallah a nan waje, na taya su inna da matar JaÉ—e rabon abinci aka kaiwa kowa nashi É—aki sai wanda ya rage na Zayyad ne na É—auka a cikin akushi na nufi É—akin da aka kwantar dashi,
Cikin nutsuwa na karasa gaban gadon da yake kwance yana barci making sure i make no noise na ajiye akushin a hankali sannan na gyara tsugunona na zuba mishi ido cikin hasken aci-balbal da ya wadaci fuskar sa ina jin gaba É—aya tausayin sa ya kama ni,
"Ina sonshi, zuciyata tana sonshi sosai, kuma bansan meyasa take sonshi ba, Zayyad shine ɗaya ɓarin jiki na, shine zuciyata, ina ji a jikina kaman duk randa na rasa shi zan rasa numfashi na, b...."
Zancen zucin da nakeyi ne ya katse ganin yana juyin da ya kusa sanya shi mirginowa ƙasa zumɓul na miƙe da nufin tare shi kada ya faɗo amman na tsaya a hanya ganin ya bude idanun shi ya zuba su a kaina ina ta faman tsilli_tsilli da ido tare da sake min murmushin shi na koda yaushe,
"Babes!" Ya furta a hankali don har yanzu jikin shi is weak.
Tattaro kuzari na nayi na ƙaƙalo murmushi, na ɗan matsa baya daga gadon nashi sannan nace "sannu hamma zayd, yaya jikin naka"
Dariyan qarfin hali yayi yace "kema kinsan duk wani nau'i na cuta da nake dauke dashi idan ina tare dake ji nake kaman an É—auke rabi.."
Murmushi kawai nayi na sunkuyar da kaina qasa ina wasa da zobensa dake hannu na, yaci gaba da cewa,
"I'm so happy that I'm staying at same place as you, daga komai yazo ƙarshe, i will be staying with you till forever, zan sanya ki farin ciki saboda kin cancanta Saudat.
Ina kuma daÉ—a baki haquri kan abinda ya faru dake lokacin baya when I was not there, sai É—azu Rumaisa take faÉ—a min abinda ya faru and i was not happy..."
"Kawai kayi min alƙawarin ko me gobe zai zo dashi ba zaka rabu dani ba" nayi saurin katse shi ba tare da nasan zancen dake zuciyata ta fito fili ba,
Shiru yayi ya zuba min ido don bai gane inda zancen nawa ya dosa ba kana naci gaba da cewa
"Ko me zai faru nan gaba, ko wani irin jarabawa zamu fiskanta don Allah kada ka yada ni, an riga anyi ma zuciyata rauni mai girma, dan Allah kada ka barta ta tarwatse hamma zayd"
Tashi yayi ya zauna sannan ya riƙo hannu na na dama ya dunƙule a tsakanin nashi, abinda bai taɓa yi ba har saida naji hanjin cikina sun kaɗa idona a zare nake kallon shi, cikin gaskiya da gaskiya yace
"Koda rayuwata zan sadaukar saboda ke ko kuma don na kasance tare dake ba zan taɓa nadama ba.
Nayi miki alqawarin duk qaddarar da zata faɗo tsakanin mu tare zamu fiskance shi bazan taɓa yada ke ba"
"Allah yasa, kuma Allah ya baka lafiya" na faɗa cikin sanyin murya sannan na miƙe tare da zare hannu na daga cikin nashi a hankali na fice.
Ko babu komai yanzu inada nutsuwar ruhi da zuciya domin na aminta da duk abinda Zayyad ya faÉ—a min, ina dai fatan Allah yasa in samu farinciki mai É—orewa a gidan aurena na biyu, shine kawai burina a yanzu.
*********
Kishingiɗe take a jikin shi Abulkhair na kwance saman nata jikin ta riƙe shi da hannu ɗaya ɗayan kuma tana latsa wayan ta fuskar ta ƙunshe da alamun damuwa,
Rage volume É—in tv khamis yayi sannan ya É—an É—ago yana leka fuskar yusrah ganin yanayin fuskarta yasa ya tambaye ta abinda ke faruwa,
"Jibi ya kamata Saudat ta koma school abban Jannat kuma kaga har yanzu bata dawo ba gashi akwai sauran shirye_ shiryen da bamu ƙarasa na tafiyan nata ba"
"Ah! Ba na faÉ—a miki tana hanya ba, munyi magana da boss Sulaiman yace zai tura mota a É—auko ta"
A ɗan dame ta tashi ta zauna da kyau ta gyara zaman ɗanta a jikin ta, taɓe fuska tayi tace
"To dai gashi ka gani la'asar har ta kunno kai babu labarinta, kuma na kira wayanta yafi sau a ƙirga bata ɗauka ba"
"A gidan su take ba wani wuri ba fah" ya faɗa a bit annoyed saboda yanda yaga take marairaicewa "kuma ni banga wani shiri da ake ma makaranta da za'ace lallai sai saudat tana nan za'ayi shi ba, kawai ki siya mata abinda kike tunanin zata buƙata, that's all"
Tsuke fuska tayi tana sauraron mitan shi, bai gama magana ba wayanta ya É—au ruri, shiru yayi ya bata daman amsawa, ta É—aga tare da murguÉ—a mishi baki cikin salo tana jifan shi da harara ta qasan idanu,
"Kaga ma ita take kira ba sai ka gama ƙare min tanadi ba"
Murmushi kawai yayi bai tanka ta ba ta saka wayan a kunnen ta tare da sallama
"BoÉ—É—i har yanzu baku kamo hanya ba?"
Shiru tayi tana sauraron abinda nake faÉ—a ta É—aya layin kafin tace
"To shikkenan Allah ya kaimu goben, sai kin dawo" daga nan ta kashe wayan ta dangwala ma khamis Abulkhair a cinyar shi ta tashi ta shige É—aki.
********
Al'amarin babban yaya ya fara É—aure min kai kwana biyu, tun wani lokaci da mukayi magana dashi a kan Zayyad ya É—auke min wuta, kwata_kwata yanzu na kasa gane gaban shi da bayan shi,
Bazan yi ƙarya ma kaina ba, na fahimci sabon dake tsakanina dashi ya fara saka mishi wani abu a zuciyar shi game dani wanda baisan dashi ba, kuma ba zan bar hakan yayi tasiri ba domin duk wani nau'i na alaƙa da ya wuce mutunci ya haramta tsakanina dashi Saboda ni ɗin daff nake da zama mata a wurin ƙanin shi, shiyasa tun yanzu nayi mishi hannunka mai sanda shi kuma ya ɗauki abun da zafi sosai.
Da safiyar yau, ina yanke ma indo farce É—an aike ya shigo ya sanar ma baba da zuwan shi, banyi mamaki ba don nasan a ranar zan koma Yola saboda makaranta na, shiyasa nayi tunanin shi da kanshi ne zai tafi dani, amman suna gama tattauna abinda zasu tattauna yayi tafiyar sa ko ganin shi banyi da idanuna ba,
Bayan nan na kira shi yafi sau a ƙirga bayi ɗauka, gashi jikin Zayyad har yanzu da saura shiyasa bani son takura shi amman dukda haka saida nayi amfani da wayan shi na kira Sulaiman bai ɗauka ba, sai can da yamma liss aka sake shigowa sallama da baba, kafin ya fita ne yasa ɗan aiken ya tambaya waye ne akace wai baban su hamma Sulaiman ne,
Wani abu na faruwa ba tare da sanina ba, tabbas wasu abubuwa suna faruwa a kwana biyun nan ba tare da sani na ba amman bansan meye ba,
Haka nayi zaune ina jira har ya sallame su ya dawo lokacin ana shirin kiran magriba sannan ya shigo ya shaida mana abinda ya kawo su.
Kafin nan saida ya fara jifa na da tambayar da yayi matuƙar daure min kai cewa "ina son Sulaiman ne?"
Jin tambayar nayi yazo min wani iri, qwaqwalwata ta kasa tantance me ɗaya ya ƙunsa da kuma dalilin da yasa akayi min ita!
Ni kuma? Ta yaya zanso Sulaiman bayan tazaran dake tsakani na dashi mai yawa ne? Ƙaddara da tashi ba ɗaya bace, koda ace babu Zayyad a tsakanin mu ai Sulaiman ba irin mijin aure na bane samm!!!
Jin shirun da nayi yasa baba ci gaba da cewa "wakilan shi ya turo su nema mishi izini ya nemi auren ki....
... Aure na Sulaiman ya turo a nema mishi?.... seriously!!.....me ya É—auke ni ne? Yayi tunanin yana da ikon da zai iya juya ni duk yadda yaso ne da zai soma neman aurena haka siddin, ba wani proper shiri babu daidaito kaman a zamanin sayen bayi?!
"Saidai ban yarje musu ba domin kuwa yanzu ba da bane, ba zanyi miki dole ba.
Ko a Musulunce yanzu kece da ƴancin sama wa kanki abokin rayuwa, kuma bamu da wani burin da ya wuce ki samu farinciki mai ɗorewa, a saboda haka idan kina son sulaimanu ni mai yarje miki ne ki aure shi, idan kuma bakya son shi to bazan taɓa miki tilas a kai ba"
Sauƙe ajiyar zuciya nayi da jin kalaman shi, saidai duk da haka ba zan iya buɗe baki gaban mahaifina na faɗa mishi zaɓin zuciyata ba. Da ya fahimci haka sai ya bani dama naje nayi shawari a kai, duk abinda na yanke sai na faɗa wa Inna ta ita kuma sai ta sanar dashi zuwa gobe da safe don zan koma yola.
Ba ƙaramin ɗaga min hankali al'amarin nan yayi ba, tun yamma na rasa walwala ina fama da matsanancin bugun zuciya. I can't imagine my life without Zayyad, bansan yaya zan kasance idan bayi tare dani ba.
Ƙarfe 9 na dare ina kwance a gado Inna ta shigo ta zauna ɗan nesa dani tare da kiran sunana,
Tashi nayi na zauna tare da naÉ—e kafafuwana na tattaro dukkan nutsuwata da hankalina na bata su.
Shiru tayi kama ba zatayi magana ba tana ta rarraba idanu ta kasa koda haÉ—a ido dani, sai can kafin tayi gyaran murya a hankali ta juyo ta zuba ma kafafuna kallo cikin jin nauyin maganar tace
"Kinyi tunani akan maganar da kukayi da baban ki?"