← Book details Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 73

Sashe 17

Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

         *BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
  And *AISHA ALTO*

13🧝🏻‍♀️
Shagwaɓe fuska nayi kaman zanyi kuka Ruma ta janyo ni jikin ta tana dariya,
"Haba ƙawata ba gani nan ba idan ma tsoro kike ji sai muje ɗaki na ki kwana, kinga aunty Yusran taki da kanta tace ki kwana gari babu lafiya ba zamu barki ki tafi ba gaskiya"

Shikkenan ni rayuwata a yawo da kwanan gidan mutane zai ƙare? Babu gida guda ɗaya da za'a kira da namu wanda nake zaune a ciki daga nayi kwanaki a nan sai a cilla ni can,

Saka ƙasan hijab ɗina nayi na share hawayen da ya fara sauƙo min, ina ɗagowa naci karo da nana tana watsamin wani mugun Kallo, ta miƙe tare da faɗin
"Idan bata son zama ku barta ta tafi mana! Duk abinda ya same ta ai ita taso" ta ƙarasa haɗe da tsaki ta bar parlorn,

Ohh Allah, ni bansan me nayi wa baiwar Allan nan ba zuwa na gidan nan kwata_kwata baifi awa 4 ba amman duk ta ƙuntata ma ranta tana neman hana ni sukuni,

"Hmm auntyn sakalci, bamu cinye mutane a cikin gidan nan ki kwantar da hankali na kwana É—aya dai ko babu komai comfort É—in yafi na wurin da kika fito, ga kuma luxury"

"Haba Sulthana, wannan wani irin magana ne?" Cewar Batool "idan ba zaku lallaɓa ta ba ku rabu da ita, yau ta fara zama cikin gidan nan amman sai kun nuna mata hali? Ao ko babu komai ita baƙuwar mu ce ya kamata mu karrama ta"

Taɓe baki tayi ta miƙe tabi hanyar da Nana tabi, karere ba'a iya samun wuri ba yanda take bragging ɗin nan sai ka rantse da Allah gidan su ne, don nima abinda nayi tunani kenan itama ƙanwar Sitifid ce,

Muna kam abin duniya ya ishe ta ita bama tamu take ba, ta zurfafa cikin tunanin yanda zata nima ma kanta hanyar tafiya ibadan, niman sirrin nan take ruwa a jallo dan shine kaÉ—ai makamin da zata yi amfani dashi wajen cikar burin ta,

Jin an fara kiran sallah yasa duk muka tashi suka jagorance ni zuwa É—akin su aunty Zaytoon muka yi alwala, ina fitowa na samu sun shimfiÉ—a min darduma ga hijab a kai na É—auka nayi sallah,

Daga nan muka fito wasu suka shiga kitchen suna fito da warmers É—in abinci wasu kuma suna shirya kan dining, nima don kar ayi babu ni na shiga cikin masu shirya dining saboda manyan ne su aunty Batool, na san ban isa na shiga cikin wa'incan ba yanzu fitinannu biyun nan su saka ni a gaba,

Ruma na ganin haka ta barsu ta dawo cikin mu sai arhantar mun da kyakkyawar murmushin ta take yi, cikin nutsuwa tace
"Saudat amman ke ba ƙanwar aunty Yusrah bace ko?"

Girgiza kai nayi nace "A'a ni ƴar uwan mijinta ne, daga ƙauye nazo zaki ma iya kira na da boɗɗi haka aka fi sani na da..."

Da sauri ta matso jiki na cikin kunne na ta raÉ—a min "kada kiyi su Nana suji, kawai idan an tambaye ki kice ke Æ´ar garin nan ne"
Kinji?
Gyada mata kai nayi muka ci gaba da aikin gaban mu,

Muna gamawa aka sake tattare parlor sannan aka sauƙe duka curtains ɗin gidan aka bulbule ko ina da turaren wuta muka shiga yin sallan isha,

**********
"Allah sarki ƴar ƙanwa ta, bansan yanzu a cikin wani hali take ba"

Gyara ma abulkhairi kwanciya a jikin shi Khamis yayi, sannan yaci gaba da cin abincin sa, duk yanda nayi ya kawo shi idan ya gama sai ya karɓe shi yaƙi,
"Kada ki damu baby, indai gidan su boss sulaiman take to kisa ma ranki wataƙil dawowa ma ba a son ranta zata yi ba domin akwai su da karamci sun iya karrama baƙo"

"Allah yasa amman ka san rashin sabo, lokacin da tazo gidan nan ma da ƙyar take iya barci hala ne yau ta iya cikakken barci, kuma ba lallai ta samu daman kallon TV ba wallahi tausayin ta duk ya kama ni saboda yanda take son film ɗin hausa"

Ajiye spoon ɗin hannun shi khamis yayi tare da jinjina kai yana kallon ikon Allah, har cikin zuciyan ta wannan maganar yake fitowa dan ta ɗauki Saudat kaman ƙanwar ta Nasreen yarinyar ta shiga ranta sosai,

"Lallai mata kuna da abin mamaki, kece fa kullum mai min complain É—in Saudat ta cika kallon TV amman yau da ba zata samu daman gani ba kamata yayi kiyi murna kuma kiyi fatan Allah yasa daga haka ta É—aure amman..."

Shuru kawai yayi ya kasa ƙarasa magana yana kallon yanda yusrah take ƙifi ƙifi da ido,

"Insha Allah gobe zata dawo sai ki ci gaba da kunna mata TVn tana kallo nidai kada a sake cemin Saudat tayi kaza tunda ke kike bata goyon baya"

********
Wurin yayi shiru sai ƙaran cokula kawai kake ji kowa hankalin shi yana kan abincin shi amman banda ni,

ɗaga ido nayi a sace na kalle su duka tun daga kan mahaifin su har zuwa kan junior dake gefe na sun saka ni a tsakiya shi da Ruma don tun da nazo ya maƙale min wai nice gyalfirens (girlfriend) ɗinsa,

Gaba É—aya nayi loosing appetite É—ina, wani iri nake ji gaba É—aya jiki na babu daÉ—i, kuma wani abu ma, naga kowa a nan wurin amman banga Sitifid ba kuma naji É—azu ana magana a kanshi saidai banji mai suke faÉ—a ba, haka kawai naji zuciyata tana son sanin dalilin da yasa Sitifid baizo cin abincin dare ba tunda ina da tabbacin nan gidan su ne, Allah yasa dai lafiya,

Saida muka gama sannan muka tattara kwanukan muka shigar kitchen maids zasu wanke, aka zuba a parlor ana kallon series film na Philippines ana gamawa aka kai na Korea, gani nan a zaune ina fama da kewar su Ali nuhu tsoron su Sulthana ya hana ni magana,

Ɗaya bayan ɗaya suke fita suna dawowa saidai bansan ina suke zuwa ba, zuwa ƙarfe 10 saura na fara gyangyaɗi a zaune don ba amfanuwa da kallon nake ba, nan ne Ruma tayi min jagora zuwa part ɗin su,

kafin na kwanta saida ta saka nayi wanka a nan ne kuma ake darun, don ma dai yarinyar ƴar gari ce ta lura da ƙauyancin dake jiki na yasa ta nuna min yanda ake amfani da komai na toilet ɗin amman duk da haka fa da ruwan sanyi ƙalau nayi wankan dan Allah ya gani ina tsoron na ƙona kaina ana zaman ƙalau,

Fitowa nayi ɗaure da towel, dan ta bani bathrobe naƙi sakawa banga amfanin ɓata kaya har biyu, na saka wannan rigan nazo na saka wani ba,
Wani lotion mai ƙamshi ta bani na shafa sannan ta bani set ɗin pjamas blue color mai taushi na saka, ta bani hula mai kunnen micky mouse shima blue,

Wani matsiyacin dariya nayi lokacin da na hango kaina a jikin madubi sannan na juyo hannu na riƙe da hancin mouse ɗin jikin hulana na kalle ta tana tsaye a baya na da murmushi a saman fuskar ta,

"Umm..." Na faɗa ina kókarin tuno sunan da naji suna kiran ta dashi, ba don na manta ba sai dan sunan baiyi min kama da na musulmai bane baima yi ma'ana ba kuma bansan asalin sunan da zan kira ta dashi ba,

"Rumaisa! You can call me Rumaisa"

Murmushi nayi nace "na gode sosai Rumaisa kayan sunyi kyau wallahi idan na koma ƙauyen mu ko su Inna ba zasu iya gane ni ba"

"To na baki su kyauta sai kije ƙauyen ki nuna musu, ko kina so na saka a kai ki ne?"

Girgiza kai nayi a sanyaye nace "ba zan iya komawa ƙauyen mu yanzu ba idan naje ba zasu barni da r..."

Sai Kuma nayi shiruu tunawa da kashedin da Khamis yamin na ko a gida bayi son wani ya san labari na, bama dalilin da yasa na dawo birni ba yace ko zancen na taɓa aure kada na faɗa ma kowa idan ba haka ba ya maida ni gidan su Yarima,

"Zo ki kwanta" ta faÉ—a tare da daga min duvet É—in gadon, a hankali na taka zuwa wurin na hau gadon tare da kwantawa ota kuma ta rufe ni,

"Bari naje na duba jikin Ya Zayyad ina dawowa" ta faÉ—a kafin ta fita, kaman nabi bayan ta nima naje duba shi haka naji, É—azu_É—azun nan muka rabu dashi lafiya lau to me ya same shi? Allah yasa ba Allah ya isan da na mishi bane ya kama shi indai shine na yafe don bani son in dinga shiga hakkin mutanen da ban sani ba,

*****
Yanzu kam dole ya san yanda zaiyi ya nemo ta tunda ya kasa cire ta a zuciyan shi, zaune yake ya hakince a kan 2 sitter ga TV a gaban shi sai faman zuba yake yi amman tunanin shi ma bayi wurin,

A kujeran dake gefen nashi ta zauna ta ƙura mishi na mujiya, gaba ɗaya ya canza, al'amuran shi sun juye ba wai ya canza hali ko yanayi ba har yanzu yana nan da tsaurin shi da zafin rai da tsanani da komai amman yanzu shi kaɗai sai kaga yana cikin nishaɗi wanda har yanzu bata san dalili ba,

kwana biyun nan yawancin lokutan shi a gida yake kashe su saɓanin da, da idan kaga ya shigo to wani abu ne ya kawo shi kuma yana gamawa zai fita,

Har ta gama zaman ta bai ko ɗago ya kalle ta ba har ta gaji taje ta kwanta don barci ne sosai a idanun ta ba zata ɓata lokacin ta wurin wannan mutumin ba tunda yau ba buƙatar komai take daga gare shi ba,

**********
29/sha'aban/1442

Bayan rashin ishashen barci da mafarkai masu abin tsoro, mun wayi gar lafiya cikin hukuncin ubangiji, idan ba ɓata gani nayi ba sai naga kaman safiya a cikin gidan nan yafi daɗi kana zagaye cikin mutane masu yawa to ko ina ƙamshin furannin dake zagaye da gidan ne suke shigowa,
Chapter 17 · 0% Book details