← Book details Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 73

Sashe 34

Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ko a mafarki kada ki saka ma zuciyar irin haka, sanin kanki ne ni ba lusari bane wanda bai san abinda yake yi ba ki maida hankalin ki gudun gani ba dai_dai ba" da faÉ—an haka ya fita daga É—akin yana jin yanda take kuka tana kururuwa yaja hannun Arif suka bar gidan gaba É—aya, za kaishi ma É—aya uwarshin tun yanzu su fara sabawa,

********
"Sweetheart, dear, baby, boo, my heart, ga dai su nan da yawa sai wanda kika zaba"

"Idan munyi aure fa? Ko shima shaƙuwan naki zaki ci gaba da kira na?" Ya faɗa idanun shi still a cikin nawa ko kyafta su bayi yi, ban samu bakin magana ba Ruma ta amshe da,

"A'a haba ya Zayd! Ai zuwa lokacin kuma matsayin ka ya ƙaru sai kuma a koma irin su honey, darling, my soul, my love, sahibul ƙalbi, nisful hayat, noorul ayn and so on,

Kaidai kawai ka kwantar da hankalin ka wannan ƙawar tawa zata kula da kai kaman jariri, zata shagwaɓa ka ta lalata ka da soyayya, har sai yace ya ishe shi ko Saudat?"

Juyowa nayi na banka mata uwar harara sannan na miƙe daga kujeran da nake zaune,
"Hamma Zayd zan wuce tunda naga jikin naka da sauƙi sannan gobe zan koma gida muje mu ƙarasa shirin Sallah yau sauran kwana 4 ko 5 gashi ko ɗinki na ban karɓo daga wurin tela ba"

"Amman babes ban gama samun sauƙi ba, ki duba halin da nake ciki mana don Allah, ki tausaya min ki zauna har na warke gaba ɗaya sai ki tafi" ya faɗa cikin raunanniyar murya kaman ba shi da ƙanwar shi bane suka saka ni a gaba yanzu suna min tsiya,

"Kayi haƙuri ka barni na tafi aunty Yusrah nake ji wallahi, ita kaɗai fa zatayi shirin hidiman sallah da na yarinyar ta ƙarama ga kuma ƙaramin goyo, babu yanda zatayi ne wallahi amman nasan da tuntuni ta saka na koma"

"To idan muka yi aure kuma aunty Yusran taki yaya zata yi? Ko dan kina tausayin ta sai kije kiyi mata nata hidiman ki bar naki?"

_lallai ma ya Zayd zancen yake so_

Turo baki nayi gaba ina faman ƙunci dan na lura so yake yi firr ya hana ni tafiya ni kuma ba zan yarda ba,
Idan muna musayya a tsakanin mu Rumaisa bata cika saka mana baki ba saidai ta nimi wani abu na daban ta maida hankalin ta gare shi,

Shima baice min komai ba ya zuba mun idanu yana ganin yanda nayi kicin_kicin na haÉ—e gabas da yamma gashi pouted lips É—ina looks kissable for him, only if he got the chance!!

"Hamma Zayd filis ka barni na tafi, ko kana so nayi sallah babu sabon kaya ne?"

"Ba bayanin ba kenan Saudat, indai sabon kaya ne nan gidan shi kika zo zaki same su da yawa daga wurin mu amman sabida tausayin ki ga aunty Yusran ki zan barki ki tafi ba don raina ya so ba" ya ƙarasa in a sad voice nima saida ya bani tausayi,

"Zan zo da sallan na duba jikin naka kaji? Kada kayi fushi a sake samun matsala indai da gaske baka son tsayar dani"

Dariya mai sauti yayi wanda ya bayyana beauty points É—inshi ya tashi ya zauna da kyau sai a lokacin na daÉ—a lura da yanda aka rufe raunuka da yawa a jikin shi,

"Duk abinda baki na zai faÉ—a miki tun daga zuciyata yake zuwa dan haka kada ki damu kanki kije ki taimaki aunty Yusrah ba zan saka a tsayar dake ba"

"Love birds, time up!! Yanzu aunty zata shigo bada magani dan haka mu ware" Ruma ta faɗa tare da jan hannu na mukayi hanyar ƙofa,

"Bye babes, ki kular min da kanki i will miss you"

Murmushi nayi ina É—aga mishi hannu nace "bye gandai, a dage gobe ayi azumi filis"

  ******
"Suna part É—in aunty ne? GyaÉ—a kai Fa'iza tayi tace
"Eh!" ÆŠazu suka shiga ina ganin zasu yi zaman su a can ne har a sha ruwa don banga alamun zasu fito yanzu ba"

"Na tambaye ki ne??" Ya faɗa yana jifan ta da mummunan kallon da ya sanya nan da nan ta sha jinin jikinta "A'a! Kayi haƙuri"

Baice komai ba ya juya hannun shi cikin na yaron shi zasu fita tace "babban yaya a bar mana Arif a nan kai kaje ka dawo"

"Naƙi! Ko zaki sanya ni dole ne?"

Saurin girgiza kai tayi tace "A'a sai kun dawo" yana bada baya ta kama mishi gwalo tana hararan bayan shi har saida ya mata nisa sannan taja tsaki tace "uban Nana a hali, Allah mana katanga tsakanin mu da shaiÉ—anun da suke yawan tunzura ku, a wata mai alfarman ma ba'a huta ba"

*****
A parlo suka samu Aunty Amarya tare da farouk da junior suna tilawan al-ƙur'ani sai kuka yake yi wai yauma zai karya azumi shi ba zai iya ƙarasawa ba ita kuma ta hana,

Har waje ana jiyo ihun shi yana yi kuma bai fasa karatun ba, lokaci ɗaya kaman anyi ruwa an ɗauke suka ji ɗiff yayi shiru, har saida tsoro ya shige aunty Amarya a tunanin ta wani abu ne ya same shi, ɗagowan da zata yi ta hango Sulaiman riƙe da hannun Arif baice dashi ƙala ba amman ya nemi sakata ya saka wa bakin sa sai zuru_zuru yake da idanu,

Sallama yayi ya shiga parlorn suka gaisa amman ya rasa ta ina zau fara tambayar inda Saudat take,

Yafi 10 minutes yana zaune yana sauraron karatun nasu sannan wani tunani ya faÉ—i masa yace
"Aunty ina Rumaisa? Ina so ta mayar da Arif gida ne idan ansha ruwa don ni ba wurin zanyi ba gaskiya akwai abubuwan da zanyi da daren"

"To Shikkenan kayi tafiyar ka kawai zan saka ta maida shi tana ciki ita da Saudat" ta dubi Farouk tace "ɗauke shi ka kai shi wurin su ya ƙaraci rigiman shi a can nima na yaro na ya ishe ni"

Murmushin biyan buƙata Sulaiman yayi ya mata sallama ya tafi amman yaso ya kalli fuskar ta ko sau ɗaya ne ko ranshi zai mishi sanyi,

  *****
Fitowa na daga wanka kenan ɗaure da towel, har wa yau naƙi sabawa da saka bathrobe don a matsayin kaya na ɗauke shi, banga amfanin ɓata kaya biyu haka kawai ba,

Da gudu ya shigo ya rungumi Ruma yana ƙyalƙyala dariya amman yana gani na ya fara ɓuya a bayan ta,

"Aunty Rumaisa ɓoye ni ga aunty mai magani"

Ƙarasiwa kusa dashi nayi ina murmushi na miƙa masa hannu na da nufin yazo amman fir yaƙi,

"Aunty Rumaisa kice ta rabu dani I don't like her"

"Aa Kaje ku gaisa ba zata baka magani ba, itama auntyn ka ce she is very nice and sweet"

"Are You sure?"

Gyaɗa masa kai tayi ya ƙaraso a ɗarare yayin da na sunkuya a kan guiwowi na don daidaituwa da tsayin shi yayi min light hug ya juya da sauri ya koma wurin ta, amman kafin mu bar ɗakin saida na san yanda nayi na jawo shi jiki na ya sake dani sosai yana min taɗin shirmen shi ina amsawa dake nima wata shirmammiyan ce muka ƙarasa kitchen na fara ɗirka masa ɗa'ami kaman zanyi kuka gashi ina gani amman babu daman ci,

Sai wuraren 9 kafin Ruma ta É—auke shi zata maida shi gida saboda maman shi ta matsa da kira don ita taso ya kwana a wuri na ne, nima haka,

Ƙin tafiya da ita yayi saida na shiga motan yana maƙale a jiki na har muka isa gidan suka yi yin duniyar nan na fito mu shiga ciki naƙi don har yau ban manta gorin da babban yaya yayi min ba, ni kuma nayi alƙawarin ba zan sake shiga cikin gidan shi ba har abada,

26/Ramadan/1442

"Da ke wata ne sai ki bari zuwa gobe kafin ki tafi amman kaman kina zaune a kan ƙaya sai Alla_alla kike ki tafi ki barmu"

Kaman ba dani take maganar ba, ta maida hankalin ta kan akwatin kayana tana haÉ—a min harda abubuwan da ba nawa ba da É—inkin da Hajiya tayi min lace 2 da atamfa 1ni kuma ina gyara wanda sulaiman ya siya min na makaranta da nufin zan barshi a gidan sai zan tafi makarantar tukunna na É—auka,

Tayi mitan har ta gaji naƙi kula ta Zayyad ma da na shiga mishi sallama kaman bashi bane jiya yace ya amince na tafi ba yanzu kuma ya sani a gaba wai sai lallai_lallai na zauna zuwa gobe, bansan meye a goben da babu a yau ba kuma bansan me ƙarin kwaba ɗayan zai amfane shi dashi ba,

"To ni ba wata bane, babu kwana ɗayan da zan ƙara amman idan ke wata ce ki bini gidan mu mune mu zauna a can mana! Ai nayi ƙoƙari"

"To wallahi bari ki gani, indai babban yaya ya amince babu abinda zai hana ni binki mu tafi tare, kuna zan baki kunya don sai mutanen gidan naku sun gaji dani sun koro ni gida"

Daga farko na É—auka da wasa take yi amman muna gama shirya kaya na ta É—auki waya ta kira shi,

_kaga ikon Allah, mutumin nan da ƙoƙari, bata nemi iznin ubanta da ko yaushe yake cikin gidan ba amman gashi tana niman nashi da yake can wata uwa duniya_

  ******

Gama wayan su kenan da sadiya har ta gama fushin ta sauƙo tana niman sulhu amman shi bai shirya ba tukunna, basu taɓa sa'insa da har ta nemi mishi rashin ɗa'a ba sai a kan maganar auren Saudat, shi harma ya fara tunanin raba musu gida kada idan bayi kusa ta cutar da yarinya,

Shikan ma kwana 1 kenan harda wuni É—aya baiyi tozali da ita a idanun shi ba, yana son ganin ta sosai amman baisan ta wani hanya zaibi ya samu ganinta ba tare da an zarge shi da wani abu ba kuma itama yarinyar bayi so ta gane ta raina shi,

Tsaki yaja ya jawo wayar shi dake fantsama ihu yayi picking ganin sunan Rumaisa ya saka a kunne tare da yin shiru yana sauraron abinda zata ce,

"Good morning dadyn Arif"

"Go straight to your point bani da lokaci"
Chapter 34 · 0% Book details