← Book details Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 73

Sashe 37

Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙwalla na hango kwance cikin idanuwan shi wanda suka saka idon ya daɗa haskawa na taɓe baki a raina ina ayyana Zayyad akwai rago ko taurin rai irin na mazan nan bayi dashi abu kaɗan sai kaga yana shirin kuka, da shine yake da pressure na rayuwa daje kaina maybe ba zai sake murmushi ba saboda ƙunci, gwanda ma ya gode ma Allah mutanen dake zagaye dashi suna son shi kuma kowa na ƙaunar ganin shi sannan shi ba korarre bane,

"Kada kayi wannan tunanin a kaina babu abinda zai canzar dani in Allah ya yarda kaman yau ne zaka ga nayi makarantar na gama nima ina son naji an daina kira na daƙiƙiya" ya dai jini da kunne amman wannan kalamin nawa basu isa zuciyar shi ba, don na daɗa kwantar mishi da hankali na ƙara karya murya sannan naci gaba da faɗin

"sannu_sannu ba zata hana zuwa ba saidai mu jima bamu je ba amman indai ta fanni na ne nayi maka alƙawarin komai ruwa da iska, duk tsananin zafi da sanyi, cikin daɗi ko wahala ba zan taɓa barin ka ba ya Zayd koda kuwa kai zaka barni ruhi na ba zata rabuwa da kai ba HAR ABADA, kawai ka kwantar da hankalin ka babu inda boɗɗi zata je zata kasance taka har iya ƙarshen numfashin ta"

  ******

"Buge_buge bai dace da kai ba ai da ka koyi shan giya ne tun yanzu don ɓacin rai baka ga komai ba tukunna, ba ka haɗa sabga da ƙaramar yarinya ba? Hmm wani kayan ɓacin ran ma sai ka auro ta kuna kwance ta tsula maka fitsari a gado angon jaririya"

Cakk ya tsaya tare da riƙe punching bag ɗin a tsakanin hannuwan shi yana maida numfashi jikin shi ya jiƙa sharƙaf da gumi, juyowa yayi yana kallon Sadiya shi bai san lokacin da ɓera ya sace hankalin ta ya kai gidan shi aka cinye ba,

Tsaki yayi ya fita daga ɗakin da ya kasance personal gym ɗinshi with sweat dripping down his body yaje yayi wanka baice mata ƙala ba ya ɗauki ƴarshi ƙaramar bayan Muna ta haɗa mata madara suka bar gidan,

  ******
"Wayyo Allah, Ruma kiyi sauri dan Allah ko yaushe ke kike makarar dani, ina son na tafi kafin yayan nan naki ya sake waiwaiyan mu"

"Kin fiye mita wallahi bodɗi kaman baki ga saurin nake yi ba, kina cewa ni da yaya na bamu da haƙuri amman kin fimu ujila da rashin haƙuri" ta faɗa tana rufe zif ɗin basket ɗin gaban ta wanda ke cike dam da kalolin abinci sannan ta miƙo min shi,

"Gashi! Yauma ba zamu yi sake ladan ki ya wuce mu ba zamu ciyar dake lokacin shan ruwa"

Karɓa nayi ina washe hakwara, irin abin yayi min daɗin nan nace "thank Rumaisa, me is you sweet"

Dariya mai sauti tayi ta rungume ni "you are sweet too my dear, love you"

Da sauri_sauri muka ƙoma mua fito da kayan da already a shirye yake saidai da fitan mu waje muka ci karo da babban yaya a tsaye kaman daman fitowan mu yake jira,
Pa basket É—in hannu na silently ya shiga dasu ciki ya ajiye sannan ya fito ina tsaye a wurin da ya barni na kasa koda motsawa hawaye kawai nake jira suzon na basu daman zuba, lallai Sulaiman ya zamo min jaraba yanzu,

Dawowa yayi ya riƙo hannun Ruma ita kuma ta riƙo hannu na ya ja hannu na har ta baya wurin da aka jera wasu fararen kujeru da table a tsakiyan su, ga wani mutumi tsaye da zungureren whiteboard hannun shi riƙe da marker,

"He is your lesson teacher and ur classes will begin right away, sai ki saku wuri ki zauna"

Ya juya wurin mutumin yana nuna mishi yatsa yace "ina sake jaddada maka no mercy!, bani son sassauci ko kaɗan bani son wasa" ɗan duƙawa yayi cike da girmamawa ya gyaɗa kai "insha Allah boss"

Ganin su kawai nayi sun juya sun barni tsaye a wurin bani da zaɓin da yafi na haƙura nabi umarni kawai, malamin nan yanda ka san ciki ɗaya suka fito da boss ɗinshin shima dai babu sauƙi,

Wasa_wasa tafiya na gida ya gagara malamin lesson É—ina sau biyu yake zuwa a rana kuma idan aka fara karatu tun 8 bayi tafiya sai 1:30 da yamma kuma tun 3:40 sai an kusa shan ruwa,

Tun bani son karatun har na saka ma raina na fara ganewa don duk abinda aka koya min a rana sai nazo na juye shi ma oga kwata_kwata da daddare.............🤦🏻‍♀️

Love You my fans
#team SS💙
#team SZ❤️

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

🤍💚🤍
    *ƘARAMAR BAZAWARA*
           💚🤍💚

    _(Cigaban matar kulle)_

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

         *BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
  And *AISHA ALTO*

*I'm back*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*Mun dawo zamu ɗaura daga inda muka tsaya kuma babu wani tsaiko sai mun kai ga gaci insha Allah🤩jinjina gareku masoyan gaskiya😍 kun nuna min irin ana kyawun taren nan🤗 na gode sosai da soyayya da kulawa Allah ya biya ku da gidan aljanna🥰*

31🧝🏻‍♀️

Zaune nake a gaban board dawowan mu kenan daga saloon mutumin nan ya tsare ni ko cikin gida ban shiga ba, na saka lesson teacher na a gaba na kalle shi nabi na kalli littafi na,
kusan 10 minutes kenan ya bani class work amman ko karantawa na gagara ballantana nasan mai zan rubuta mishi, gashi mugun nayi_nayi dashi yace ba zai karanta min ba,

"Sir... Idan kana ƙaunar maman ka da babanka ka fassara min, wallahi ni ban gane abinda kace nayi ba kwata_kwata" na faɗa a gatsale,

Riƙe baki yayi kawai ya juya ya ƙara wani question a kan wanda ke jikin board ya kuma saka time 20 minutes idan ya cika ko ban gama ba zai karɓa, sannan ya tafi ya barni zaune a wurin da waya a kunnen shi yana amsawa, daman yayi alƙawarin ɗaukan fansar zagin da na jawo mishi jiya a wurin babban yaya saboda ya gyara min spelling, shiyasa ya ɗau alwashin daga yanzu ba zai sake min komai ba idanma ban iya ba ruwa na tunda shi yana kwasan kuɗin shi,

Ajiye pen ɗin hannu na nayi kawai na zabga tagumi ina ƙare mishi kallo tunda abun nashi baƙin hali ne na lura mugunta kawai yake son mun ba komai ba, yafi kowa sanin ban iya komai ba amman ya rubuta min wasu manya manyan turanci ya tafi ya barni a wurin,

Cikin sanɗa Ruma ta ƙaraso wurin da nake zaune tana waige_waige ganin ta a haka yasa hankali na ya tashi ina tambayan ta ko lafiya,

Riƙe hannu na tayi cikin damuwa tace "kiyi haƙuri Saudat na jawo miki..."

"Kaman yaya kin jawo min? Me ya faru?"

"Yanzu babban yaya ya shigo, bansan wani dalili ya shigar dashi bedroom ɗina ba amman daga ganin shi yana cikin farin ciki, ganin haka yasa nima na saki jiki dashi yana ta min wasu tambayoyi a kan karatun ki da ban gane kansu ba amman na ɓoye mishi halin da ake ciki,

To muna zaune muna hira sai na tashi na shiga bathroom kafin na fito na samu ya buɗe drawer ya ciro litattafan ki ainihin wanda lesson teachern ki yake marking yana dubawa, yanzu ya gane duk scores na assignment da test da ake kai mishi mu muke yin marking da kanmu amman na ƙaryata hakan, yace idan har da gaske baki karatu ba zai barki ko makaranta kiyi a garin nan ba, kuma idan kika tafi sai kin gama tass kafin ki dawo nan da shekaru kusan 6 kenan, yace idan ƙarya nayi mishi ba zai barki ki sake komawa gida ba sai kin ƙare karatu ko bikin sallah a nan zaki yishi yaya zamuyi kenan?"

Dafe gashi na nayi cikin takaici ina maimaita "hasbunallahu wa ni'imal wakeel"
Zuwa yanzu raina ya fara ɓaci haƙuri na ya kusa ƙarewa, na gaji da yanda sulaiman yake juya ni kaman waina a cikin kasko, shi waye da zai dinga yanke hukunci a kan rayuwa na ba tare da izini ko shawara ta ba? Menene haɗi na dashi duk yabi ya takura min ya hana ni sakewa, ya maida ni ha'ina maƙaryaciya ƙarfi da yaji,

Jefar da littafin nayi a ƙasa nabi da takalmi ina takawa a kan idon lesson teacher na shima mamaki ya hana shi magana don a gaban shi sulaiman ya kashe min warning idan yaga ko ƙwarzani ne ya samu littafin nan na kuka da kaina, naja hannun ruma mukayi part ɗin hajiya,

"Wannan masifa da me yayi kama? Wallahi idan kika ga ban tafi gida yau ba to mutuwa nayi a hanya" Ruma dai tana biye dani a baya taga ikon Allah ko wani irin mataki ne zan É—auka,

na tura ƙofar bedroom ɗin hajiya sannan nayi sallama cikin kasashiyar murya ina matsar ƙwolla,
Zaune take tana karatun ƙur'ani da reading glasses a idon ta, saida ta kai aya sannan ta ɗago tare da amsa sallaman mu,

"Subhanallah mai ya same ki saudat?"

Zama nayi a jikin ƙafar ta na kifa kaina tare da fashewa da kuka, ta ɗago ni tana share min hawaye amman gudun kada ta gane kukan ƙarya ne na sake kwacewa na kifu ina ƙara sautin kuka na,

"Rumaisa mai ya same ta?"

"Gata nan a gaban ki hajiya wallahi ban sani ba"

"Saudat tashi ki faɗamun wanda ya taɓa ki yanzu su fuskanci fushi na" murmushin jin daɗi nayi da jin haka ina sauƙe ajiyan zuciyan munafurci na fara kwararo bayani,

"Hajiya yanzun mama ta kira ni, babyn aunty yusrah babu lafiya yau kwana biyu kenan da kwantar dasu a asibiti shine baba yake ta faɗa da bai ganni ba yace idan ban dawo yau ba sai ya saɓamin"

"Toh shine kike kuka? Je ki haÉ—a kayan ki a maida ki gida daman bai ma kamata ace yau jajiberi kina gidan nan ba, inyaso bayan sallah sai ki dawo"
Chapter 37 · 0% Book details