← Book details Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 73

Sashe 60

Karamar Bazawara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nitsar da kanshi yayi kafin ya ƙarasa jikin closet dinshi ya ɗauki sweatshirt da wando ya saka ko turare bai tsaya fesawa ba ya fito,
Zaune ya samu aunty tare da sulaiman fuskar ta babu walwala shi kuma ya rungumi wayar shi ya kinshigiɗe a gefen ta yana buga game, ƙura mishi ido tayi kaman mai son gane wani abu a jikin shi har ya samu wuri ya zauna.

"Aunty gani" ya faÉ—a ganin ya daÉ—e da zama bata ce mishi komai ba,

"Na ganka ai, ina dai so na tabbatar ba canza mana kai akayi ba, ina tantama idan wannan Zayyad wanda na sani ne Zayyad É—ana gudan jini na"

"Why are you saying this aunty me ya faru Please?"

"Ashe har zaka iya wani abu a duniyar nan ba tare da sani na ba? Abu mai girma kaman niman aure? Zayyad har bani da kima a idanunka da yakai ka fara nima abokiyar rayuwa ba tare da sani na ba? Under my roof?"

Kallon sulaiman yayi cike da takaici don yasan shine ya haɗa mishi wannan bomb din, gyara zama yayi tare da ɗan gyaran murya bakin shi ɗauke da ɗan ƙaramin shu'umin murmushi.

Ƙasa da murya Zayyad yayi yace
"Aunty I'm sorry! Wallahi ina zuci_zucin sanar dake ban samu dama bane"

"Muna zaune ƙarƙashin inuwa ɗaya da kai amman kace baka sami daman sanar dani zakayi aure ba ina matsayin uwarka?! Muna tare da safe, da rana , da dare amman ka kasa samun daman sanar dani?"

"Aunty I'm sorry"

"Sorry for yourself Zayyad, moreover da ace wata zaka aura zan iya hakura na amince maka amman indai Saudat ce Baka isa ba wallahi, kayi kaÉ—an ka jawo mana tozarci da abin kunya Zayyad, kana saurayi sabo fill a laida ka rasa wanda zaka auro sai bazawara? Ai matsalar taka yanzu tayi maka maganin shi ko? To Allah ya bata lada amman ba zan lamunci wannan shashancin ba ko kusa"

"Aunty dan Allah kada mu zamo masu mancewa da alkhairi"

"Zan iya biyan saudat alkhairin da take iƙrarin tayi mana, i can pay her any amount that she demand kawai ta faɗa maka abinda take so mu biya ta zan bata yanzun nan ta fita daga rayuwar mu...."

"Aunty habaa....! Ya faÉ—a a dan hasale amman kafin ya sake cewa wani abu tayi caraf tace
"Wallahi ko ka haƙura da Saudat ko nayi maka Allah ya isa nono na da kasha"

Har Sulaiman saida kalamin ta ya bashi tsoro, Zayyad kuwa sake baki yayi cikin tsananin mamaki da firgici yana kallon mahaifiyar shi,
"Indai kana so mu shirya da kai to ka haƙura"

Yanda zuciyar shi yake bugu ji yake kaman zai fasa ƙirjin shi ya fito, bai taɓa shiga firgici irin wannan ba, idan yaci gaba da tsayuwa a wurin zai iya rasa numfashin shi da azama ya tashi zai bar parlorn.

"Baka ce komai ba" ta katse shi a hanya.

"Na haƙura" shine amsar da ya bata a taƙaice ya wuce bedroom ɗinshi, Sulaiman ji yayi kaman ya tashi ya daka tsalle ya tiƙa rawa yana kwaso shoki saboda murna, today was the best day of his life.

Zayyad na shiga ɗaki ya danna mata key sannan ya zauna a dandamarin ƙasa tare da dafe kanshi da hannun shi yana rewinding abinda ya faru yanzun nan, shine yace ya haƙura da Saudat? Is he not dreaming? He really reject Saudat? Ya rabb!

Kuka mai gunji ya saka kaman ba namiji ba yana fiffisgan gashin kanshi kaman mahaukaci yake faÉ—e_faÉ—e,
Yafi 15 minutes yana wannan yanayin, idanunshi sum zama jazur yana jin kanshi kaman ana sarawa da adda, shaƙuwa ya fara yi babu ƙaƙƙautawa cikin lokaci kaɗan ya gama galabaita ya faɗi a ƙasa yana shure_shure.......🧚🏼‍♀️

Team SS let's celebrate anyi ma Zayyad leg over😅💃
I mooove🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

*BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*

*Ya Allah 😅 i just can't stop laughing at the sad faces😟😂 jiya anyi zaman makokin da babu mamaci, everyone is saying ba'ayi ma Zayyad adalci ba🤔, hakan na nuna ƴan hannun daman Babban yaya sun fara hijira zuwa wurin Zayd kenan bayan anyi mishi Leg Over 🤣🤣*
*Keep the sad faces babes😩 don't forget that I love you! because I love losers more🤭🥰😍*

47🧝🏻‍♀️
"Wayyo Allah aunty sadiya... Bayana zan mutu!" Shine abinda Sulthana take maimatawa tana murƙusuwa a ƙasan carpet kwanciyan gadon ya gagareta.
Fitowa Sadiya tayi daga toilet ɗauke da ƙaramin towel fari da kuma roba mai ɗauke da ruwan ɗumi ta tsuguna gaban sulthanan tana danna mata raunukan dake jikinta,

"Kema me ya kaiki Sulthana? Wa ya baki wannan gurguwan shawaran da kika je ana niman lahantaki? Wa yace miki haka ake kwace namiji kalli abinda kika jawo ma kanki!"

Ƙwalla ta daɗa matsowa tana yarfa hannu cikin zafin ciwo kaman zata saka ihu tace
"Aunty Sadiya dan Allah ki kaini asibiti zan mutu"

Rike baki tayi tace "kee ina na isa na taka kafa na a waje ba tare da izinin dadyn Arif ba? Yau sauran auren da nake taƙama dashi ma zai iya saka almakashi ya gutsure shi indai a kan wannan maganan ne, ki kalle shi kawai ki barshi indai a kan Zayyad ne bayi da daɗii..
Bari dai na kira doctor tazo gida kawai ta duba ki"

Taimaka mata tayi da ƙyar ta tashi bayan ta gama dubata ta kwantar da ita a gado ta rufa mata duvet kafin ta ɗauki wayan ta ta fice.

*********
Ƙura ma aunty amarya ido dady yayi kaman mai son gano wani abu a fiskanta amman expression ɗinta bai nuna komai ba, her face is just blank.

"Yanda yaron nan ya matsa min a kan zancen yarinyar nan da mamaki ace lokaci ɗaya ya haƙura ya janye ba tare da ya jira ya saurari abinda mukayi da mahaifin nata ba ma"

Tagumi aunty tayi tace "to Alhaji zanyi maka ƙarya ne? Idan Zayyad bai furta ya haƙura ba ai ba zance maka ya faɗa ba, sa'annan ni banma san yaya kukayi da shi ba sai yanzu da ya sanar mana ya janye"

Jinjina kai dady yayi ya juya ya fuskanci Sulaiman yace "kai tashi kaje ka kira min Zayyad É—in, ina so naji ta bakin shi saboda a fita hakkin shi"

"A'a shi Sulaiman ya zauna yayi mana shaida bari na saka Rumaisa ta kira shi"
Bata jira amsar su ba ta fara ƙwala ma Ruma kira, babu daɗewa sai gata ta iso.
"Aunty gani"

"Kije É—akin Zayyad kice yazo muna niman shi"

"Toh"tace ta nufi É—akin.

Cikin nutsuwarta take knocking har na tsawon wani lokaci no response, tura ƙofar tayi a hankali ta shiga tare da sallama amman babu kowa a ɗakin sai tayi tunanin ko banɗaki Zayyad ɗin ya shiga, har zata juya sai ta jiyo tarin shi, komawa tayi tana bin yanda ta jiwo sautin ta hango shi kwance a can gefen gadon a ƙasa yashe kaman gawa.

Cikin sassarfa ta zaga ta ƙarasa gaban shi ta tsuguna tana kallon yanda ya haɗa zufa idanunshi sunyi jawur kaman garwashi ga jikinsa sai shaking yake yi alaman zazzaɓin sa ya ƙaru.

"Ya zayd lafiyan ka kuwa?" Ta faÉ—a cikin muryar damuwa, abinka da mai arhan hawaye har ta fara zubar masa da su.

Ko motsawa baiyi ba yana nan kwance hancinsa ya toshe sai ta baki yake shaƙar numfashi, girgiza shi Ruma ta fara yi da ƙarfi ta saki kuka dan gani takeyi kaman mutuwa zaiyi yanayin shi ya matuƙar bata tsoro.

"Ya Zayyad mai ya sameka ne dan Allah ka tashi mana ko kayi min magana pleeease"
Shiru yayi kaman wanda take da gunki don bayi da karsashin magana a yanzu ya kwanta ne kawai yana jiran mutuwa yaxo ya É—auke shi tunda an raba shi da jigon rayuwan shi, baiso shigowan Ruma ba samm.

Miƙewa tayi da gudu zata fita taje tayi BBCn abinda ta gani, da sauran ɗan ƙarfin da ya rage mishi yayi amfani ya riƙo ƙafarta, cikin wani faint voice yace
"Ina zakije?"

"Zanje na faÉ—a ma su aunty halin da kake ciki ne, ka kalli fah baka da lafiya" tayi maganar hawaye na ci gaba da bin kuncin ta.

Girgiza kai yayi a hankali yace "daman me kika zo yi"

"Aunty ne tace nazo na kira ka suna jiran ka a parlourn dady, amman zanje na faÉ—a musu ba zaka iya zuwa ba"

"No don't! I will go"

"Ta ina zaka iya tafiya a cikin yanayin da kake, just stay please zan kira su suzo su duba ka"

"No Ruma! I said i will go" ya faɗa tare da dafa gado yana ƙoƙarin tashi, taimaka mishi tayi ya miƙe tsaye sannan ya fara takawa a hankali kaman mai ciwon ƙafa don gaɓoɓin jikin shi gaba ɗaya sun sake.
Saida suka isa ƙofar parlourn yace ta sake shi zai iya ƙarasawa ciki da kanshi da ɗingishi ya ƙarasa shiga.

Sallama yayi musu duka suka juyo suna kallon shi zuciyan aunty Amarya saida ya tsinke da suka haÉ—a ido dashi, in a matter of hours kalli yanda ya dawo kaman wanda ya shekara yana jinya?!

"Subhanallahi Zayyad baka da lafiya ne?" Dady ya tambaya in a concerned voice.

Girgiza kai yayi cikin maganar shi da bayi fitowa yace
"Bani É—an jin daÉ—i ne kawai, but I'm ok now"

"Which kind of ok bayan gaka nan ko tsayuwa da kyau baka iyawa?! Just go back to your room zan kira doctor ya duba ka"

Jan hanci shi yayi dan ya samu iska ya shiga masa cikin fisgan magana yace "no don't bother dady, yanzu nasha magani idan na kwanta na huta zanji dai_dai.
Ruma tace kuna nima na"

"Kana cikin wannan yanayin ba zai yiwu muyi maganar da muke so d.."

"Me zai hana Alhaji tunda magana ce ta fatan baki kuma zai iya amsawa just ask him what you want to ask"
Chapter 60 · 0% Book details