← Book details Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 59

Sashe 55

Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayanta zuwa gashinta yake shafawa a hankali alamar lallashi har tayi Shuru sannan yace ki kwantar da hankalinki Zumata wlh kinji na rantse ba aure zanyi ba,bazan iya Miki kishiya ba sai kaddara wacce bana fata,naje gidan Momee na fada Mata gaskiya kinji na rantse kin San bazan Miki karya ba,Dan Allah ki daina kuka kina damun kanki 3days har kin rame.
Lallashi tare da dadan kalamai ya dinga fada Mata Yana nuna Mata yanda yake sonta,sai gashi ta yarda har ta saki ranta suna kyakyata dariya.
Farin ciki ya lullubeshi Ahleef Shukuransa ta daina fushi.ranar kwana sukayi suna farantawa juna rai.

Bayan Yan watanni ansha bikin Farhan da Fatima,Shukura babbar kawar Amarya,Ahleef a barin Ango sosai bikin ya kayatar.
Niima da Latifa suna gaban Momee,Sultan da Suhail Wanda jiya suka sauka a kasar suka shugo Suma suka nemi wuri suka zauna kusa da Momee, Sultan yace Momee munfa samu matan aure tunda muna da wadata aure zamuyi,Suhail tasa sunanta Basma Yar Kano ce suka hadu a schl,Ni Kuma Islam ce Yar Gombe ce yanzu sunce mu tura manya,Momee murna ta kamata tace Alhmdllh tunda dama kun dawo Nigeria Baki daya me ya rage kawai sai aure,Niima da cikinta Kato tace Hmm Bros na tayaku murna,Latifa tace Allah muma ya bamu sai a hada bikin,kowa yace Ameen daga Nan suka Mata sallama sun wuce gidan Ahleef zasu Kai Masa ziyara daga nan shima su sanar Masa sun samu matan aure.

Mubaraq dai har yau ba labarinsa tun Ana nemansa har an gaji an hakura,Mama Bata da aiki sai kuka sabo da duk cikin yaranta tafi son Mubaraq,Hafcy dasu Zahra su kansu abin Yana damunsu yanzu gidansu duk ya tarwatse Mama da Daddy Basu da nutsuwa,Alhaji Adamu yana cikin damuwa Wanda Dalilin Haka ya haifar Masa da ciwon Hawan jini,gashi Kuma wani Masifar Ashe Alhaji Adamu Baban su Hafcy manemin Mata ne kamar Dan akuya Haka yake,Koda ciwon Hawan jinin sa ya tashi Bayan yaje asibiti aka yi masa test iri iri Nan aka gano Yana dauke da cutar Hiv, Mama Basu sani ba ya boye mata,

Bayan wasu watanni Niima ciki ya tsufa sosai tana ja da kyar haihuwa ko yau ko gobe, da safe da wuri yau nakuda ta kama Niima Momee da Latifa suka tattara sai Asibiti,Latifa sai kuka takeyi sabo da yanda Niima ke azabtuwa da nakuda, Momee hankalinta ya tashi,su Sultan du suna asibiti,Ahleef Yana kitchen manne a jikin Shukura tana soye soyenta wayarsa tayi Kara ya dauka ganin Suhail ne ya Kira shi, hankali tashe ya fada Masa Niima na asibiti zata Haihu Rai a hannun Allah,da sauri ya datse wayar Yana sanarwa Shukura ta hade Rai tare da turo Dan lips dinta me shekin Pink color ta furta to Kuma ba sai ayi Mata Addua ba Kai mene naka ciki ko Kaine angwazoma din da zaka karbi haihuwar, haihuwar ma ta cikin shege har murna akeyi sabo da duniya tazo karshe to wlh sai dai mu tafi tare duk motsinka Ina gani bare ayi ma signa da Ido, gas ta kashe tare da wanke hannunta a sink da sauri tace muje na shirya mu tafi, dariya ma ta bawa Ahleef da wannan mitar Tata,wani farin ciki na ratsa shi Shukura na kaunarsa da yawa shi Kam ya godewa Allah Yana son yaga Ana kishinsa.

Tare suka wuce Bedroom ta Sa katon Hijab har kasa Amma duk da Haka tayi kyau,shi Kuma da 3qtr da Riga me shegen tsada da kyau,Shukura ta dauko jallabiya tace sa wannan so kake a kalle maka fata Ana hadiyar yawu, Murmushi ya saki me sashi sumar da mace ya manna Mata kiss a kumatu sannan yace I love u my wife,me too cewar Shukura ta fara tube Masa Riga sannan ta zura Masa Jallabiya akan wandon tace muje to,Bai Musa Mata ba ya bita tana rike da hannunsa,har Mota driver ya jasu sai asibitin da Niima ke nakuda.

Niima an Gama galabaita kamar zata mutu tuni su Shukura suna asibiti Kam Kam ta rike mijinta ta window ta leka ta dawo,Amma ta mutunta Momee sosai itama Momee haka,Su Sultan Suna ta tsokanarta saura ita Nan gaba tana dariya cike da kunya,Ahleef ya Rada Mata a kunne gaskiya ya kamata muma mu dage a samo Mana Baby, a hankali ta Dan dakeshi kadan da Wasa, Niima har ta fara barin wasiya iri iri tana kuka Allah ya taimaketa ta santalo yarta mace katuwar gaske zukekiya me kama da Mubaraq, Babu Wanda yayi Murna sai Niima ita taji tana kaunar yarta a ranta fiye da kowa.

Bayan ta samu sauki an gyarata tare da Baby Haka Su Ahleef suka dauketa ba tare da kyama ba aka dinga zuba Mata adduoi iri iri, a ranar aka sallamesu Bayan komai ya Lafa makwafta da Yan uwa sai tsegumi da gulma akeyi Dan ma a Haka Abuja ne ba ruwan wani da wani da arewa ne sai dai Niima ta koma kauye,Momee har gida taje ta sanarwa Alhaji Adamu da Mama Niima ta haifi Yar cikin Mubaraq, daga Mama,da Baban Mubaraq har su Hafcy ba Wanda bai zub da Hawaye ba,Amma Haka Dole suka je da Sha Tara ta arziki suka ga jaririya sak Mubaraq,Mama duk an fara saduda da Duniya sabo da balain da suke Sha kullum iri iri na kaddara.

Kafin Suna Mama tace a sa Mata Khadija kawai ko Allah zaisa tayi Hali na gari irin na Nana Khadija Matar Manzon Allah,hakika Ahleef ne ya yanka Mata rago manya har biyu taci gaba da raino Yarta ba tare da kyama ba,Haka dangi ma kaf tunda Momee ta sasanta tsakaninta da danginta,Haka ma da Dangin Abba.

Yau Niima tayi arbain yaune Kuma suna zaune suna kallon News suka ji labarin an kama wasu masu safarar kwayoyi zuwa kasar waje sai ga Mubaraq hannunsa daure da Ankwa ta ko Ina an kamasu a airport sannan an dawo dasu Nigeria za a Yankee musu hukunci.

AsmaBaffa.

Taku har kullum afwa bana typing da wuri Uzuri dai nake so ayi min fans Kar kuji haushi next Novel inshallah da time baza ayi Haka ba idan aka fara sai an gama.
Godiya dubu masu Sharhi 😍😍😍😍.
[7/22, 1:14 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SANO

END

91-100

Official

By
AsmaBaffa

ASMABAFFA FANS CLUB
JIN DADI SABO
HOUSE OF HAUSA NOVELS.
Ina Godiya sosai da kaunar da kuke nuna min,ga Sharhi akan lokaci Allah ya biya.

Yaune Friday yaune Kuma za a daurawa Niima da Latifa aure,ba wani biki za ayi ba sabo da Yan gulma da tsegumi,Latifa da Yousuf dinta sun so ayi party etc Amma Sabo da Niima za ayi ta surutu yasa Momee ta Hana tace Ana daurawa za a Kai amare ba wani gulma.

Shukura sabo da Murnar Niima zatayi aure ta bar Mata mijinta tun Ana gobe ta addabi Ahleef ita sai tazo ta kwana,yace baza ta kwana ba,Amma ta dinga naci Dole ya kyaleta driver ya kaita,Ana idar da Sallar jumaa aka daura auren Niima da Mubaraq, Latifa da Yousuf, Bayan sallar laasar aka wuce da amare gidajen mazajensu a cikin garin Abuja,cikin Yan Kai Amarya harda Shukura tana motar Sultan,maimakon ta dawo gida sai ta koma gidan Momee, Umma tana gidan itama Driver Yana zuwa daukan Umma sai ta tasa Shukura gaba suka tafi gida, lokacin Ahleef Yana tare da Baba suna Hira yaga Shukura da Umma farin ciki ya Kamashi yasan Umma ce tayi Mata Dole suka dawo tare.

Baba ta gaisar sannan suka hada Ido da Ahleef ya kashe Mata Ido daya,Murmushi tayi kadan Wanda shi kadai yaga hakan, ba kunya ya mike tare da yiwa Baba sallama Yana me yiwa Umma sannu da zuwa yabi Shukura harda daukar Mata handbag ya rike suka jera part dinsu sai zumudi yakeyi sabo da kwana daya kamar shekara yake gani,suna Shiga ya fara warwarewa Shukura hadda da salon love dinsa, dama Shukura kadan ake jira ta Shiga maida Masa da martani yanda taga dama take sarrafa shi shima haka, albarkatun kirjinta ya fara sarrafawa Wanda yasan Yana taba su Shukura zata rude,a nutse suke sarrafa juna sai da suka zauce, Ahleef Wanda dama kwararre ne a wannan fagen rada Mata yayi a kunne da akwai Dadi? Shukura cike da Shauki tace sosai ma itama cikin siga ta rada,
Tambayoyi yake Mata iri iri ba kunya take bashi amsa sai su Kara rudewa, yaudai ansha love,tunda yaje Office washe gari ba abinda yake tsinanawa sai tunanin Shukura da Daren jiya yanda ta jiyar dashi dadi,ba shiri ya tattara ya gudo gida ya Kara kwasar harkoki ya samu nutsuwa ya sake fesa wanka Yana nishadi ya koma Office.

Niima Amarya Suma sun kwashi love dama sun Saba da juna,Haka Mubaraq yaji dadin harkar sabo da Tasha gyara, yarsu Khadija tana wajen Momee anyi Mata yayen dole sai sun Gama cin Amarci za a kawo musu yarsu suci gaba da rainonta,Mubaraq da Niima sunce sun barwa Momee ta rike ta, Momee ta karba hannu biyu kuwa tunda yarinya ba ruwanta Kuma yanzu Babu kowa a gabanta sai Yan aiki.
Latifa da angonta Yousuf suna can Suma Ana kwasar Amarci, abinda Latifa tayi shi mijinta yayi shima ya tuba Dan Haka ba Wanda zai wa wani Gori,Sunyi shaye shaye sun tuba,Niima kuwa dama tare suka sheke ayarsu Kuma suka yi aure Bayan Sunyi Nadama.

Maman Hafcy da Alhj Adamu sun kwantar da hankalinsu suna Shan magani sai ka rantse sunfi kowa lafiya ma,Babu Wanda zaice suna dauke da HIV, haka ake so mutum ya kasancewa me yadda da kaddara,ba Wai dan cuta ta samu mutum ba ya zauna yayi ta tunani duk ya rame bakin ciki ya kasheshi a banza,ayi Addua Ana fadawa Allah ko maganin ne sai Allah ya kawo ma,idan ma Bata da magani sai kuga Allah ya Hana cutar tashi har ta cutar da mutum.
Chapter 55 · 0% Book details