← Book details Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 59

Sashe 36

Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shukura kuwa hadiye kukanta tayi ta ta fara bugar kirjinta tace Shukura Hadiye kukanki ki zama me zuciya,kinje birnin tarayya ma kinyi abinda kika ga dama bare kauye gidan kwana ya gagareki?kamar bake ce kika iya satar shiga gida ba komai kyansa da lalacewarsa, a fili ta furta kalamanta a ranta tana cewa zan iya canja gari ko state ma Amma Nan garin kadai Ahleef zai San Ina Nan,Nan zai zo ya daukeni mu tafi muji dadinmu.da murna har tana rera wakarta ta ja akwatunanta sai Gidan Aishalle wacce akayi mata aure tun suna Yara basa shiri da Shukura Amma Shukura yau ta yarda Aishalle tafi Yan uwanta kawai ta kwada sallama a gidan,Mijin Aishalle ya ganeta to shi Allah ya bashi hakuri shi yasa ya kasa korarta akwai Kara da alkunya a tare dashi,Shukura ta gaisheshi tare da cewa dan Allah kar gabanka ya Fadi ba wajen kwana na zo nema ba,yar Iskar matarka zaka Kira min na Bata ajiya,Sai ga Aishalle ta fito daga Bayi ta kalli Shukura sannan tayi Murmushi tare da cewa kina Nan dai da halinki to Dan Uwarki kawo ajiyar ki tafi kin San dai ko sanda kina garin Nan zaneki nakeyi,Mijin Aishalle ya kallesu yayi dariya ya tabbata kaf dinsu kuruciya ce ke taba su basuyi hankali ba tunda Yara ne har yanzu.

Kafin ya gama tunaninsa Shukura tace ke ja can da muninki Amma ni Baki ga Mijina ba wlh duk ranar da yazo garin Nan na tabbata sai kun sume inda kika San aljani kin San bana karya zaku gani kuma kyau ne ya auri kyau ba irinki ba Muni ya auri kyau,Mijin dai dariya yake suna ta zagin juna karshe Shukura ta bada ajiyar akwatunanta tayi gaba,tana fitowa sai da ta zage gidajen danginta kaf Bata kuma yiwa kowa magana zata fito abinta, ko ma ka kulata baza ta kulaka ba,gidan Kawu ne na karshe Matar sa ta gama miyar ta tare da tsame Naman kaza ta ajiye kazar a gefe tana gyara miyarta,Shukura ta shigo idonta ya sauka kan kwanon da kazar guda take ci har murfin kwanon ba ya iya rufe kwanon sabo da kazar ta tokare ko Ina, Alhmdllh Shukura ta furta tare da cewa an Dade ba a hadu ba, Kawu na gefe a zaune Yana jira a kawo kaza, Shukura ta tuno rashin mutuncin da Kawu ya mata kawai ta dauke kwanon kazar ta koma kofar gida abinta ta zauna gefe ta rike kazar Nan da hannu biyu tana yaga a nutse tana ci,sai da taci tafi rabi,Kawu da Matarsa tare da yaran gida duk Baki bude suke jira suga Shukura ko zata dawo da Kazar Amma shuru,har Kawu ya kasa Hakuri ya zari katuwar sandarsa ya fita neman Shukura sabo da kazar ma Bata da lafiya da kyar ya bari aka yankata Dan yaga zata mutu ne Amma shine tazo a banza to wlh sai ta biyashi kudin kazar indai taci.yana fita ya iske Shukura tana yagar kaza,tana ganin Kawu ta mike tsaye kuma tana ci gaba da yaga tana uhmmmm dadi wlh Kawu gaskiya nagodewa Allah da Kaine Dan uwan Babana na jini,kayan wa mutum ya Isa ya taba idan bana Dan uwansa ba,shi yasa nake Alfahari da samun Uba kamarka.

Kawu ji yake kamar ya hadiya zuciya har wani cije Hakora yake Sabo da masifa,Ki nemi ubanki,ni ba ubanki bane bana fatan ki zama yata ko wata yar uwata,kuma wlh tunda kika Ci kazar Nan ban yafe Miki ba ko yanzu kika mutu sai munyi sharia dake a gaban Allah sabo da Baki da gadona, Shukura ta fara yar dariya tana ja da baya gudun kar Kawu ya kamata tasan kawai ta mutu,ta yagi kaza tace ka Fadi kudinta naci bashi idan Mijina yazo zai biya,ba kunya Kawu ya dinga tsine tsine akan kaza sabo da son abin duniyarsa, Shukura tace za a biyaka Kawu relax calm down Ok,Kawu yace kin zagi Uwarki ta kabari ba ni ba,kuma tunda kika zageni da turanci wlh sai Naga bayanki a garin Nan,sai na tabbatar Miki barikin naki bai je ko Ina ba,yaja kwafa ya shige gida,Amma Shukura sai ta tabe Baki ta mayar da ragowar cikin kwanon ta rufe ta shiga har gaban Matar Kawu ta ajiya da sauri tace a rabawa Yara su maida yawu ni kuci na baku kyauta,ku Yan uwan nane na siyi kazar wurin Kawu, wata yar Budurwa wacce Kawu yace zai fara Bata rubutu Tasha, tace talaka Ina kika ga sisi? Me kikayiwa kanki bare wani,Shukura tace na tabbatar Miki ki bani lokaci kadan sai na siye garin kaf na bar muku kyauta ku zauna Zaki gani, Da ace ke ba yar uwata bace to siyenki zanyi ki koma baiwata Amma kinci darajar zumunci,Kawu ta kalla tace da sannu duk mutanen garin Nan sai sunyi nadama indai Allah ya bamu Rai da Lfy tana gama fadin haka ta Kara gaba abinta.

Gidan yar Uwar Innarta Yafendo take kallo daga nesa tana tsara yanda zata dinga shiga gidan ba tare da an gane ba, masifaffiya ce ta gaske gashi komai ita ta iya wani bai iya ba,tana da zaratan samarinta guda biyu suna zamansu a gida daya tare da matayensu,Yafendo akwai Tsafta da komai ita ta sani wani bai iya ba. Shukura ta zabi zama a gidan sabo da gidan Kato ne baza a gano ta ba, har dare tana can bakin Rafi tayi sallar Isha sannan ta karaso gidan dama su katangar Kara ce kawai ta Buda yar kofa dai dai ita ta baya ta shige gidan ta gyara musu katangarsu yanda take ta bi ta jikin rumbu ta buya a bayansa tana kallonsu suka Gama hirarsu da cin tuwonsu kowa ya tafi ya kwanta gida yayi Shuru, Yafendo tuni tayi bacci a kan Dan gadonta,Shukura cikin duhu ta lallaba sabo da ganganci ta shiga dakin Yafendo ta sadada ta shige karkashin gadonta dake gadon karfe ne me rumfa tun irin na zamanin da,Ko Ina a Tsaftace Shukura ta shaki baccinta har gari ya waye, Yafendo ta fita tana shararta da ta Saba har kofar gida take Sharewa Shukura ta fito a sace ta ebi ruwa a botiki da buta ta shige Bayin Tsohuwa da sabulunta tayi wanka da Alwala tare da maida kayanta da sauri ta koma dakin,tayi sallar asuba Yafendo Ana can Ana share share sarakan Tsafta,Surukar Yafendo Indo ita ta shigo dakin lokacin tuni Shukura ta koma karkashin gadon tana gani ta ajiye Koko da fanke me sugar,sai ga daya Surukar ma Gaje ta ajiye kosai da Kunun tsamiya yasha Nono lafiyayye a samansa,suna fita Shukura ta janyo Kunun da kosai sai ta dakko sabon ludanyin Yafendo Tasha dashi yanda take so ta mayar ta rufe komai ka rantse ba a taba komai ba haka aka kawo yanda taci da dabara ta mayar ta ajiye komai yanda aka kawo,haka ta jawo fanke ma taci guda uku ta mayar,Ludayin Yafendo kuma ta boyeshi can gefe cikin kasan gado.

Yafendo kuwa tana gama aikinta tayi wanka sannan ta dawo dakin tana masifa mata Basu iya abin duniya ba haba Ina rayuwa zata tafi a haka,ba tare da ta kalli kasan gadon ba ta zura hannu ta jawo kwandon kayan kwalliyarta ta shafa Mai ta shirya ta mayar ta tura,ta Kara zura hannu ta jawo a kwati ta sa kayanta ta tura ta mayar, Shukura na gefe can a kwance tana kallonta.

Yafendo ta bude kunu da kosai tace A'a yau kuma rowarce ta motsa aka kawo Dan wannan ba a ciko kwano ba,Baki ta tabe tare da kurba tace hmmm ai da akayi kunu ba irin na yaran yanzu ba,idan Dane wa zai Sha wannan kunu,Kosai ta bude da sauri ta bude Baki ta dafe kirji na shigesu sai kace jariri ne zaici Lallai Gaje ta fara canja hali Amma zata ci ubanta sai na yi maganinta a gidan Nan.

Shukura tana ji tana kunshe dariyarta,haka dai Yafendo ta Sha Kunu,ta Bude Koko taga Koko da yawa tace Allah sarki Indo mutuniyar kirki matsalarta daya ita kuma Koko Babu kauri a tsinka Masa ruwa yanzu mu a zamaninmu ka kaiwa me gida wannan ba sai kayi kwanan gidan ubanka ba ranar,Amma Allah sarki Iro na Yana hakuri,ludayi tasa ta ebo Koko ta sakeshi a kwanon tsiiiiiii tace ashasha kalli harda burbushin tokar Kara a ciki sabo da kazanta duk sai na gyara muku zama.Shukura a ranta tace Yafendo ba a iya mata Allah kyauta.

Shukura tana so ta fita Amma ba dama sabo da Yafendo ta share dakinta ta kwanta tana Jin radio su Gaje kuma suna wajensu suna girki,mazajensu Iro da Yahaya suna kiwo,wani yaro ya shigo da katon buhun mangoro a kansa jajaye nunannu Wanda yanzu aka tsinko su a sama,gaban Yafendo ya ajiye yace gashi inji Yahaya can wajen Kiwo ya bani na kawo miki, Godiya Yafendo tayi tace Kai yaro ka dinga sa takalmi a kafarka gashi Nan kazanta tasa duk ta tsatsatsage ina uwarka take da zata barka Haka,yaro dai yayi waje Yana Jin haushi,tsaki taja sannan ta raba ta bawa su Indo tasu ta ebi wata ta wanke ta zauna tana Sha sauran kuma a buhun ta tura kasan gado.

Dama Shukura yunwa ta fara cinta Yafendo ta fita wanke Mangwaro tayi sauri ta bude buhun ta ebo kusan guda goma,ta fito ta bude randar dakin ta kamfaci ruwa a wata roba me Fadi ta koma kasan gado,dake kusan komai har kayan kwanikan Yafendo suna kasan gado a wanke a shirye,a hankali Shukura take wanke magoronta tana Sha a hankali,idan Yafendo ta fita sai tayi taunarta yanda take so idan ta dawo kuma sai tayi a hankali,Yafendo taso taji kamar motsi a kasan gadon Amma sai tace Kai wannan bera da naci yake ya dameni tun rannan a kasan gado kwana Nan zan kawo Mage gidan Nan kowa ya huta.
Chapter 36 · 0% Book details