← Book details Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 59

Sashe 29

Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Makarantar su Shukura sunji labarin barin gida da tayi Latifa ta Baza cewar ta tafi yawon karuwanci.
Kamar Kullum Ahleef kwance yake saman lafiyayyan Bed dinsa yana faman tunanin Shukura bai ma san ya fara hawaye ba, Momee ce ta turo kofar a hankali,da sauri ya goge ido tare da fara baccin karya,Momee ta juya tuna ninta Bacci yakeyi.Tana barin dakin yaci gaba da tunaninsa wanda kullum karuwa yakeyi baya sauki,Harkar bikinsa kuwa Farhan da sauran frnds su suke komai.

Shukura tunda arna suka kifota da Adduna Bata tsaya ba sai da taje jikin wani gida shima a kauyen,Wani dattijon iyamuri yayi mata turanci Hey! Young Lady where are you going ? Whats Happening ? Shukura tana haki tace i need a help,wasu ne suka saceta amma ta manta inane garinsu,mutumin yace ta suje gidansu yana da mata sai ta zauna zuwa kwana biyu dodon tsafinsu zai fadi garinsu,Matarma me kirki ce ta bawa Shukura wajen kwana da abinci kalar nasu,tace amma da Snail tayi miyar,Shukura tace ko bera ne a ciki Zata ci haka bare wani snail, dare ya tsala gari tsit Mutumin ya sadada a hankali ya kwanta a bayan Shukura kamar matarsa yana mata goge,tana farkawa ta tsala ihu yatashi a guje zai koma wajen matarsa,matar kuma taji ihu ta fito a guje sukayi karo da kai gwaraf,sai Ihu suka koma daki Gaba daya,matar dama tasan halin mijinta, Washe gari kuwa da sassafe matar tace Shukura ta bar mata gida Zata kwace mata miji.
tafiya Shukura ta dingayi a hanya har ta hadu da wani matashi tace ya taimaketa ita yar arewa ce, nan take ya kaita inda Zata hau mota,Ba Bata lokaci ya sata a motar Anambra City tare da fada mata yanda zatayi,ya biya mata kudin motar sannan ya bata 3k,ta dinga zuba masa gidiya sannan suka wuce tana mamakin ashe a ko ina akwai mutanen kirki.

Me taxi ne ya sata a Motar Kaduna state da kyar ma suka dauketa kudinta bai kai ba, wani bahaushe dan cirani Wanda shima Kaduna zaije shine ya cika mata kudin motar.
sun sha tafiya sai cikin dare suka sauka a Kaduna lfy,Matashin yace to shifa kauye zaije a kauye yake,Shukura tace dan Allah ya taimaka ya tafi da ita gidansu can kauyen kaduna saceta akayi kafin ta gane gidansu sai ta tafi,Matashin yace ba damuwa muje,taji dadi tace ya sunanka ? Yace Jamilu ke kuma fa ? Shukura ta furta sannan suka shiga motar kauyen.

Jamilu neman kudi yake zuwa Anambra dan cirani ne,iyayensa Sun rasu kakanninsa suna raye su suka rikeshi har ya girma suke tare gida daya,baiyi karatu ba Sabo da rashin Gata shi yasa yake tafiya neman kudi.
Dattijon me Suna Malam Hari zaune yake kusa da matarsa Rahina suna hira a tsakar gida sai ga Jamilu da Shukura Sun shigo da sallama,Ko zama Jamilu baiyi ba ya sanar dasu abinda Shukura ta fada masa a kanta,babu wani damuwa suka tarbeta a mutunce,Tun Bata saba dasu ba har suka saba da juna ci sha da komai suke Bata duk da cewar na kauye ne Shukura Bata Jin dadinsa Sabo da ita ko a kauyensu ma cimarta dabance, sati daya Kakan Jamilu wato Hari yace tunda har tana iya tuna garinsu a kauyen Jos to zai Bata dubu uku kudin mota,baza su iya riketa ba dan Adam abin tsoro ne,Rahina ma tace wannan gaskiya ne ta tafi wurin danginta amma a kyaleta zuwa sati biyu ko uku.

Sati biyu tsakani Shukura ta koma Normal ta tuna Ahleef da Abuja da komai ma,ta dawo Hayyacinta,matsalarta daya tunanin Ahleef daya addabi ranta ba dare ba rana,yanzu ta tabbata Son Ahleef Ya kamata sosai,tun bata yarda ba har ta yarda,tana tsaye cikin daddazon mutane a kauyen mata da maza ana wasannin gargajiya,sai kallonta akeyi a kauyen anga kyakyawa,tunawa tayi yau rabonta da Abuja 3wks kenan karfa Ahleef yaje ya manta da ita ya auri wata,kara ta saki kowa sai da ya firgita ana kallonta ta dafe bakinta da hannu tare da tsayawa cak,sai ji akayi tace Ahleef zai so wata,sai ta fara falfala sauri kafin kace me ta koma gidansu Su Jamilu tace Zata tafi ita gida, Rahina tace ta bari sai gobe amma fafur Shukura tace tafiya zatayi, kakan Jamilu ma ya hanata tafiya yace ta bari wani satin zai kaita Abuja da kansa,ba damar tayi musu kuka kawai ta fashe musu dashi.Shukura Bata san ma bikin Ahleef saura kwana bakwai ba.

Kullum Shukura kuka takeyi ba ji ba gani Bata iya cin komai ita sai ta tafi tun Su Jamilu Suna Bata baki har suka kyaleta,Malam yace 'yar nan kudi nake jira na samu sai mu tafi,Cikin sheshekar kuka Shukura tace ni a kyaleni a gani ko ba sisi sai na koma Abuja ko da Allazi wahidin ne,dariya su kaka suka dinga yi, Shukura tace kaka wajen mijin da zan aura fa zanje, So kuke yayi sabuwar budurwa ina nan,Rahina tace oh yaran yanzu ba kunya,Shukura tace yo ke kaka me kuka iya a soyayya, Kin taba zama kamar yini daya kinyi tunanin Malam Hari? Rahina tace mu da ake mana Auren zumunci tun muna yara ina muka San wani tunani yar nan,.

Shukura tace tab wlh an cuceku ni kuwa ina yin tunaninsa kullum kullum,harfa tunaninsa nakeyi yana min dariya,Malam yace ya sunansa yar nan ? Ahleef sunan larabawa ne baku ganshi ba kyakyawa cewar Shukura, to wai kai malam ka taba siyawa Kaka kayan dadi ? Malam yace bazan iya tunawa ba, ni kuwa kullum sai ya siya min,muje yawo dan Allah kaka mu tafi gobe,Kaka yace sai kudi sunzo,Shukura tace sai kace mutum haka zasu zo su sameka da kafarsu?

Washe gari da safe Shukura dasu Malam suna zaune ta kalli buhunan masara,gero,dawa etc tace kaka kuna da wannan amma bakwa cin dadi,ku siyar dasu mana mu a yanka mana zabbi sai ku zauna kullum kuna cin tuwo,Kaka yace sarkin kwadayi kenan ke dole sai anji dadi, ba wai kullum ba Kaka amma idan akwai sai aci,idan babu an san babu sai a hakura, Kuka ta kara fashewa dashi sai an siyar da buhun masara Sun tafi Abuja,Hari da son kudi yace Baza ta sabu ba bindiga a ruwa, Shukura tace to bani bashi muje Ahleef zai biya me kudi ne,Malam yace bada ni ba yar nan. Jamilu yana son Shukura amma yasan tafi karfinsa matar manya ce shi yasa ma bai damu kansa ba.

Ahleef kuwa ya rame ya kara haske kullum tunanin Shukura yakeyi shine dalilin da yasa aka ce ba party ba komai kawai aure za a daura a kai Amarya,bangaren Amare ma sunyi shiri tsab an kashe kudi duk da cewar ango bai taba zuwa zance ba,itace take binsa Office baya saurarta ko kallon arziki Bata samu,Amarya kuma da iyayenta laifin Momee suke gani,Nafeesa taci alwashin tana Auren Ahleef Zata mallakeshi sai abinda tace,Momee sai ta koma abin kyama wajen Ahleef.
Umma da Baba su nasiha da addua kawai sukewa Ahleef.

Kwanci tashi yau ne daurin Auren Ahleef 12pm za a daura, mutane kasa kasa suke sauka,yaune kuma Baba, Jamilu tare da Shukura suka shiga motar dake tashi 7:30am na safe,mota ta tashi Sun fara tafiya duk inda Shukura taga mutane sai ta leko da kanta ta Window din motar ta kwala magana da karfi Sai Abuja ko da kafar katako Masu dariya suyi,murna takeyi kamar zatayi hauka.11:30am suna Abuja Sun shiga taxi tiryan tiryan Shukura ta fadi Adress gidan Momee a kofar gidan ta hango mazaje sunsha wankan Shadda da alama biki akeyi gabanta ya fadi,Baba ta hango ya dau wanka ya fito,da gudu Shukura ta karasa wajensa ta kyale Jamilu da kaka a mota,Baba ya dinga murna Shukura ta dawo,Shukura tace Baba ina yaya ? a takaice Baba ya Bata labarin komai,Shukura sai kuka,cikin kuka ta dan bawa Baba labarin komai na saceta da akayi.

Baba kaga Wanda suka dawo dani dan Allah shiga mota Baba muje wajen daurin Auren, Baba yace yar nan kina mace ina ke ina zuwa wajen daurin aure,Baza ka gane ba Baba akwai matsala babba Baba dole muje kafin a daura aure,haka Shukura tayiwa Baba wayo shima ya gigice ya fada motarsu taxi suka bi bayan motar su Salman, Malam da Jamilu sai kallon masu kudi sukeyi ashe Shukura gaskiya ta fada masu kudi ne Ahleef.

can Nesa sukayi parking,Shukura so take kawai taga Ahleef amma mutane sunyi yawa,har an fara khudubar daurin aure kowa naji,Shukura ta runtse ido tana hawaye da addua, Baba ma da Kaka har Jamilu sun karasa wajen,Ahleef da dasu Abba suna cikin masallacin,Baban Nafeesa da yan uwansu ne suka ce a dakata kar Wanda ya daura aure,Shuru akayi ana sauraronsu,Yace sunyi bincike an sanar dasu Ahleef baida asali, bashi da iyaye a gidan raino aka dauko shi,shi yasa suka fasa aurawa Niima shi dake yarsu ce shine aka kulla za a cucesu shine za suce yarsu ta aureshi to Allah ya taimakesu ba'a daura ba, kuma Baza ayi da tasu ba karshe yace zamu dawo da kaya tare da kudade da aka kawo amma aure a daura da yar wani ba tasu ba.

A bin Haushin ga yan jarida haka Abba cikin bacin rai ya Mike ya bada tarihinsu dana Ahleef har na Saudatu da Baba,kowa sai da ya tausaya gashi anyi tonon silili a bainar mutane,su kansu iyayen Nafeesa sai jiki yayi sanyi suka ce to Sun yarda a daura,Abba ya rantse sau uku bazai daura ba wlh shima bazai daura da Ahleef ba su bawa yarsu me asali ba dai Ahleef ba, Shukura tana Jin komai tar a kunnenta tsalle ta buga tare da cewa yessss Alhmdllh. Da kanta ta fara keta dubban mazaje ana kallon ikon Allah ta Isa har inda Baba, Kaka da Jamilu suke da sauri ta jawosu gefe can tace Baba da Kaka ku zama waliyai na dan Allah kuce a daura da Shukura Muhammad, Wani farin ciki ya lullube Baba,yace yan uwanki fa ? Ba matsala ? Cike da kunya tace Baba kun San tarihina fa, idan komai ya lafa zamuje kauyen.
Chapter 29 · 0% Book details