← Book details Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 59

Sashe 16

Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shukura tunda ta siyo kayan zaki su kawai take ci kullum Bata dora tukunya dama Bata iya girki ba,tunda Ahleef ya murde mata kunne bai sake ganinta ba a daki take zama yawanci,sai yau ta fito 8pm yana palon kasa yana kallon American film,can nesa ta zauna tana nuku nuku sannan tace Sannu Kawu,Dan Allah Kawu Ahleef....ki daina ce min Kawu nifa ba dan kauye bane kuma ba Tsoho ba,to General Ahleef...yace Soja ne ni ? to Alhaji,yace No,to Sir ? Sir Ahleef ya kaji ? dama dama ya furta yana tabe baki,to dan Allah dan bani rancen dari biyar,Ba musu ya zaro Ya mika mata ta Mike da sauri tare da cewa ina yin kudi zan baka kaji? to kawai yace mata tunda yaga Kuruciya ce ke damunta baka fita Ko ina ba kana kwance kudin zasu sameta.
fita tayi me gadi da kyar ya bude mata shi tunaninsa ma kanwar Ahleef ce yanda take nunawa kamar gidanta.
always pad dinta ta siyo guda daya ragowar canjin ta siyo Bounty chocolate ta dawo tayi Sallama ta wuce shi,shi bai kulata ba Computer yake latsawa.
muryarsa taji yace kawo ledar mu gani ba tare da ya kalleta ba, ba musu ta mika masa,ya duba ya gani yace karba abinki.

AsmaBaffa
[7/22, 1:12 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO

8

Official

By
AsmaBaffa

MAMAN FATEE and MADINA ALIYOU wannan page naku ne Sabo da Jin dadinku.

Tana karba ta wuce Bedroom abinta bata fi 15mnt ba sai gata ta fito again tana so itama tayi kallo,Romantic film yake kallo yana ganin ta zauna a Palon tana ta shan Bounty Chocolate dinta sai ya canja Channel ya mayar bangaren News kawai, bata ce komai ba taci gaba da harkarta yana tasa Shima,Wayarsa tana kusa da ita ta fara ruri kallon Screen din tayi taga Farhan,hannu ya mika mata ta bashi wayar,mika masa tayi ya daga tare da sallama cike da shegen iyayi dinsa yace How Far ? Farhan ta waya yace baka da kirki wlh ace na dawo ina kasar amma ko ka shigo Ko Mamma ai kazo ka gaisar amma shuru tace tunda na tafi Qatar baka zo ba,am so sorry ina busy ne wlh ka Sani,ok kana gida yanzu zan shigo kuma kwana zanyi,gaban Ahleef ya fadi kar Farhan yaga Shukura me zai ce masa, Da sauri yace da daren nan Almost 9pm ka bari sai gobe,Ok Allah kaimu gobe cewar Farhan.

Ajiyar zuciya ya sauke sannan sukayi Sallama sai yanzu yaga Shukura Bacci ya kwasheta tuni saman Kujera a zaune, Har ya gama aikinsa Bata tashi ba,zuwa yayi da niyyar tashinta sai yanzu ya kare mata kallo gaskiya ta hadu ya furta a hankali, gashinta ya kalla Wanda ya kwanta a goshinta,kafa yasa ya bigi tata kafar kadan Shuru taki tashi yayi ta tashinta amma sai dai ta turo baki taci Gaba da baccinta,kyaleta yayi shi bazai iya daukanta ba gaskiya kawai ya kashe light yayi tafiyarsa ya barta nan zaune tana bacci abinta,wanka yayi tare da shirin bacci har ya kwanta ya tuna a zaune take bacci,Yana tsaki ya sake sakkowa kasa tare da kunna Light ya dauketa kamar jaririya yana kallon fuskarta yaji Bata da nauyi ko kadan,Bedroom dinta ya Shiga komai tsab Neat amma ko ina Sweet ne a zube,saman Bed din ya tsaya maimakon ya kwantarta sai ya cillata saman gadon da karfi kamar wata Bag,Amma ido kawai ta bude a hankali ta rufe taci gaba da baccinta,Sweet din da sauran kayan zakin ya kwashe kaf ya fita dasu ya boye a Bedroom dinsa ya kwanta tare da addua sai bacci.

Hafcy da gaske Son Ahleef ya kamata me zurfi,bata da aiki sai tunaninsa duk ta fita daga Hayyacinta,Tun tana boyewa har abin ya gagara,Zahra ma hakan take domin ita har wata rama tayi ta daban,Number din Ahleef ta sata a wayar babansu ta shiga Dialing ringing din duniya tayi amma baya daga ko wacce number sai yana da business da kai,haka ta zage ta rubuta masa text kamar haka
Hlo Handsome Hafcy ce yar gidan Alhaji Dauda pls idan kana da time ina so muyi magana,Ahleef yana ganin text din ya goge komai,Hafcy ana jiran Ko kira ko feedback amma Shuru kake ki, Zahra ma haka tayi masa amma ba labari,Hafcy ta gaji kawai ta sanarwa Babansu,Alhj Dauda yace ta bari sai Abba ya dawo daga tafiya zaije da kansa a hada su aure da Ahleef dole,Sabo da haka sai Hafcy ta samu kwanciyar hankali,Zahra tana Jin lbr tace Sam ita ke sonsa nanfa fada ya kacame tsakanin Hafcy da Zahra,Babu irin sasancin da iyayen basuyi ba amma sunki dainawa har suka kulla gaba me tsanani tsakanin Zahra da Hafcy,Mama tun abin baya damunta har yazo ya dameta haka Alhj Dauda ma hankalinsa ya tashi Jin Hafcy ta dauki wuka zata kashe Zahra Allah yasa aka kwace da kyar.
Gaba daya gidan yanzu basa zaman lfy sai fada duk akan Ahleef dan Saudatu.

Niima dawowarta kenan daga Office amma tun daga waje take kwalawa Saudatu kira ba wani mutuntuwa Saude...Saude kawai take cewa,Saudatu ta fito cikin nutsuwa tare da cewa Hajiya gani dai dai lokacin Ahleef ya Dauko Shukura Sun taho tare yana so ya cusawa Niima haushi sai kuma suka iske tana yiwa Saudatu rashin mutunci, tsayawa kawai sukayi a baya,Shukura Bata gane Saudatu ba Sabo da ta juya bayanta kuma tayi kiba da kyau sosai Alamar Saudatu tana Jin dadin gidan, Niima tace ke Saude me kika dafa Allah yasa dai ba irin naku abincin na mutan kauye kika yi min ba, tsawa ta buga mata dake nake fa,jikin Saudatu ya dauki Mazari tace Je ki duba Hajiya idan baiyi ba sai a sake Sabo,Tsaki taja tare da cewa naje fa kikace Common dalla je ki kawo,Kitchen ta shiga ta fito dauke da katon tire lemon Niima ta Dauka tare da watsawa Saudatu a fuskarta tare da furta Stupid,lokacin Shukura ta tabbatar Saudatun tace ai kafin kiftawar ido ta kwashe Niima da maruka har biyu karo na biyu, zuciya tazo mata iya wuya an wulakanta Saudatu Bata San ta ina tayi karfi haka ba nan ta Kwashe kafafun Niima ta fadi kasa tim,kanta ya kwalu da tiles jikake kwal ta kuma haye saman Niima ta rufe ta da duka ta ko ina,yakushi Da cizo Saudatu tana jawo Shukura wai ta bari,Ina ai dayan lemon ta dauka ta juyewa Niima a jikinta,ta dauki dukkan stew din Allah yasa ma ba zafi ta juye mata a kirji,Bata hakura ba ta ja rigar Niima ta yagata gida hudu sai bra dinta ce ta bayyana, da kyar Saudatu ta janye Shukura daga jikin Niima wacce a yanzu kamanninta Sun sauya Sabo da yakushi da cizo ,Ahleef yana kallo harda harde hannaye yau Shukura tafi kullum birgeshi bai ma san kyautar da zaiyi mata ba, Waya ya zaro tare da Kiran Momee ya sanar da ita iya abinda yaga Niima tana yiwa Saudatu,Momee taji Haushi ranta ya baci,Abba ta sanarwa,lokacin Niima tana ta ihu da zage zage tace saita salwantar da rayuwar Shukura sannan ta fada Bedroom da kyar,Momee da Abba ne suka kira Niima a waya suka mata tatas,Abba yace idan har kika kara Niima zan cireki daga jerin yarana,hakuri ta bawa Abba da Momee kamar gaske ta daina.

Shukura ta rike Saudatu tace Sannu Inna kina hakuri,Sir ga Saudatun dana ke baka labarinta, Inna kinga dan uwana na ne wannan a gidanshi ma nake zaune yanzu,ko zaki zo mu koma can da zama? Kiyi hakuri da abinda wannan tayi miki,Ahleef dai yana kallonsu Har Saudatu ta sanarwa Shukura irin taimakon da Ahleef yayi musu kaf, Ita kuwa Shukura tace dama dan uwanta ne,yanzu kin daina doyar ? Saudatu tace yaron kirki Ahleef yace ba sai na wahalar da kaina ba, Nan sukayi ta hirar bayan rabuwa,Ahleef yace Momee ta tsawatar inshaallah ba abinda zai kara faruwa,Saudatu tana murmushi tace ba damuwa Allah ya saka maka da Aljanna, yaji kan mahaifa,Shukura dai hakuri ta kara bawa Saudatu akan abinda ya faru dazu, Saudatu sai albarka take sawa Shukura da Ahleef,Shukura ta kalli Ahleef ta kalli Saudatu haka takeyi wai kama sukeyi sosai,gefe taja Ahleef tace ko na dawo nan da zama? No baki Isa ba ki gama kwanakin ki bar min gida kawai,lets go bazan rikeki ba idan ma kika dameni korarki zanyi baki daya,Baki taja ta tsuke tace Inna zan dinga kawo miki ziyara duk Wanda ya tabaki ki fada min zan gyara musu zama,Dariya Sukayi gaba daya harda Ahleef ya murmusa.

Sallama suka yiwa Saudatu Ahleef yace daga yau kin daina aiki a gidan Umma ki koma part dinku da zama akwai komai a part din na abinci ki dinga yi ke da Baba kawai shine zaman lfy mun gama magana ni da Momee tasan komai kuma duk abinda ya faru karki ce zaki bar gidan ki sanar min zan canja muku wajen zama,Saudatu tayi Godiya ta wuce part dinsu ta iske Mijinta yana hutawa ta sanar masa komai shima addua ya shiga Zubawa su Ahleef.
Chapter 16 · 0% Book details