← Book details Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 59

Sashe 20

Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shukura an gama Shiri ana murna taji cewar Ahleef gidan Momee zai kaita ta zauna can wurin Inna Saudatu,cikin Shiri ya fito yana zuba kamshi yasha wani yadi me tsada da kyau, Kayanta suna leda tabi bayansa har mota sanye take cikin doguwar rigarta Pink, yauma Driving zaiyi da kansa,tana shiga yaja motar,Sai gani tayi ya tsaya a wani katon gida Farhan ya fito da trolley har biyu manya ya saka musu a bayan mota,Ahleef yace bazan shiga ba ka gaisar da Mama,gidan su Farhan kenan,Shukura a ranta tace dole kuyi wulakanci wannan irin kudi haka,Shagon dinki suka tsaya na mata taga nan ma an sa musu katuwar Ghana Must go a bayan mota,Ahleef ya ja mota suka tafi,bai tsaya ko ina ba sai wata schl me Arabic da boko ba nisa da gidan Momee ya shiga yayi mata registration da komai,makaranta ce me tsada Sabo da a kauye tayi makaranta yace a sata a ss1 a dawo da ita baya.
Bayan ya gama yace ga makarantar da zaki dinga zuwa an gama komai Uniform dinki yana Cikin kayanki akwai komai a ciki,Shukura Bata kaunar zuwa schl dama tun asali Gata da basira amma tun iyayenta na da rai sai da kyar take zuwa, wata waya me kyau da tsada amma yar Nokia ce Bata WhatsApp kawai ta kira ce yace gashi akwai number ta a ciki ko me ya faru ki sanar dani,kuka ta fara yi yanzu kullum sai taje makaranta,mene kike kuka? Tace ni tsoron yan birni nakeyi kuma kullum sai naje makaranta,kin fi so a barki cikin jahilci kina yiwa mutane kauyanci baki iya komai ba? Shuru tayi a mota tana shesheka har suka je gidan,ta fito Cikin yan aiki wasu suka shigar mata da kayanta kaf na Boot part din Saudatu,Tana mamaki ashe duk kayanta ne haka aka zuba,Ahleef yace jeki ciki zan wuce Office Sauri nakeyi,Murmushi tayi tace na gode Allah kara arziki sai kuma ta fara hawaye,lfy ? Tace shike nan na daina ganinka kullum kullum waye zai siyo min kayan dadi? Dan Allah ka maidani gidanka mu zauna tare ni nafi sonka yanzu akan Saudatu,dariya ta bashi yace indai akan kayan dadine Saudatu ma zata baki kici,ai ita tsohuwa ce irin naku na yan boko nake So,to jeki idan kina so ki kira wayata,yanzu baza ka dinga zuwa ba shike nan ? Yace da Momee tana nan kullum sai kin ganni,Amma to ai ga Inna Saudatu ko,a'a akanta ni bazan zo ba kullum to budurwarka fa wacce nake zanewa ? Ko dan ita kazo mana, yace a'a ba haka nake soyayyata ba ni kullum sai naga budurwata,to yanzu idan ta dukeni fa ko ta zagi Inna ? Ahleef yace na baki wuka da nama ki mata duk abinda kikaga dama, Shukura da kuri tace Allah ballata zanyi ba ruwana,mota ya shiga tana daga masa hannu ya bar gidan yana dariya, duk abinda sukeyi kan idon Niima,tace Alhmdllh dama tazo har gida da zan kassara rayuwar yarinya matsiyaciya.

Shukura da gudu ta shiga part dinsu wajen Inna Saudatu tare da rungumeta ta baya,ba Zato Saudatu taji Shukura ta fada a jikinta tana murna,Saudatu dama tasan da dawowar Shukura Ahleef ya sanar dasu,kallon part din Shukura tayi komai me kyau ne daki biyu da toilet ko Wanne da palo sai kitchen kamar bangaren Amarya haka wajen yake, Bayan Sun gaisa suna hira Saudatu ta yarda lallai Shukura yar uwar Ahleef ce tunda ba Momee ce ta haifi Ahleef ba, sannan taji yan aiki suna cewa Ahleef dan uwan Momee ne ta raineshi.
Trolley Shukura ta bude kayan sawa ne na mata babu kalar da Babu ciki, har Bra duk ya siya mata kamar yasan size dinta,komai dai dai ita,haka dinkuna dake Ghana mustgo laces ne Atampopi,Shadda dasu materials iri iri masu tsada da kyau dinkin kuma dai dai ita kamar an aunata na zamani iri iri, sai mayafai takalma da jakankuna, Uniform dinta kala hudu Har Sandals da schl bags kala uku da littatafai komai an hada ba abinda zata nema.

Inna tace Mashaallah gaskiya Dan uwanki yana ji dake wannan kaya haka kamar lefe,murmushi Shukura tayi ta kwanta tana latsa wayarta,sabo da Baffanta yana da waya tun tuni tana dauka shi yasa bata Bata wahala ba ta gano kanta,Tana Kwance Inna tace tashi mu kara gyara gidan nan sai muyi girki,Shukura ba musu ta Mike Sabo da tuntuni tasan Fadan Inna idan tace ayi ka zauna wasa masifa zaka sha Bata daukan raini kuma Bata bada kofar da zaa rainata sai irin su Hafcy da Niima marasa Tarbiya.
Shukura ta zage akayi gyaran duk inda baiyi dai dai ba sai Umma Saudatu tasa ta tisa wajen ta iya dole,Duk ta gaji likis,Umma Bata bari ta huta ba tace girki zasu yi yanzu, suna girki Umma taga Shukura Bata iya ba, haka ta dinga fada sai da ta koya mata dole sannan tace tayi girkin a gabanta tana Guiding nata,tanayi Umma na koya mata,ta kusa gamawa ta dauki waya ta latso Number Ahleef,tayi Ringing me tatsawo sannan ya dauka Sabo da yayi saving Number din nata,yana dagawa ta kwalla da karfi tace girki nake ta yi kai tun dazu,dariya ta bashi sosai da kyar ya danne yace Dan Allah fa? Na rantse baka ji kamshin bala'i ba Allah ta furta cike da murna, murmushi ya saki yana rubutu a Office dinsa yace to ya da dadi? Ban Sani ba Umma ta hanani dandanawa tace ba a dandanawa wai sai anjima,yace wow Har miyau na ya tsinke ya zubo,dariya ta kyalkyale da ita tare da cewa yau ga Babana wajen kwadayi,Bari idan Umma ta barni na Dandana to zan kiraka na fada ma irin dadinsa Ko kasa Driver yazo na zuba ma ya kawo maka Office ai dai ni ba kazama bace zaka ci,to yace kawai ta dinga Murna zaici girkinta karshe tace ka fadawa Abokinka na manta sunansa me suna kamar za ace Fari,Oh Farhan ? yawwa ae shi kace na iya girki ina ta yi,Dariya Ahleef ya saki ba tare da ya shirya ba yace Ok zan fada masa yazo yaci girkin Amaryarsa,cike da Shagwaba tace kaifa ka iya sa mutum kunya Allah ai tunda Baffa ya rasu to ni wa zai daura min aure,yace danginki mana,baki ta tabe Auren dole zasu min fa na tsere ka bari watarana zan baka lbr kaci dariyar kawunmu yanda na siyar masa da Akuya naci dadi da Kudin.to Allah kaimu yanzu jeki wajen girkin idan ya kone bazan ci ba,kashe wayar tayi,Umma tace keda Yayan naki ne ? tace ae mana lbr na bashi na iya girki,Dariya Umma tayi sosai,Shukura ta kafeta da Ido tare da cewa Umma wlh kama kukeyi da Yaya sosai,Umma tace rufa min asiri Tsohuwa da ni kina hadani da me kyau haka,Baba ne ya dawo daga Office ya gama aikinsa har Ahleef ya sallameshi ya dawo gida ya Iske Shukura da Saudatu suna girkinsu,Umma tace gafa Shukura yar Uwar Alhaji Ahleef ce wacce nake baka lbr ashe yarinyar nan yar uwarsa ce amma take zuwa muna soya doya a titi,Baba yayi dariya Shukura ta tsura masa ido tace yeee... Baba ma Irin yaya Ahleef ne kalli wlh Dimple dinku iri daya har hancin kamar wa da kani,Baba yace haka ake ta fada a Office kuma kama haka take yanzu idan za aje Turai sai kikaga mai kama dake Shukura ai duk Dan Adam ne yan uwane shi yasa ake samun wani yayi kama da wani, suna ma wani iri daya,Shukura tace hakane nima sanda muka je makka naga me kama dani Balarabiya,Baba yace gaskiya yayanki mutumin kirki ne,Shukura tasan karya tayi tace uhmm kawai tare da canja zancen tace Baba harfa Muryarka da tasa wlh iri daya,Umma cikin wasa tace ke kin damemu da kama kama fa, Sun dade suna Hira har suka gama girkinsu.
Lafiyayyar Fried rice tasha kayan hadi iri iri, ga hadin Couslow sai soyayyar kaji,kunun Aya sukayi da lafiyayyan zobo, duk Umma yau ta koyawa Shukura su sunyi tare.

Umma tace to Shukura kinga yanzu mun gama girki sai Yayanki kije bangaren su Momee Ki karbo foodflask da za a zuba masa kinga mu flask dinmu duk da masu kyau ne amma irin nasu na daban ne,kije ko yan aiki, ko Niima ko kuma Latifa su baki kizo a hada a bawa Driver ya kai masa.
Tsoro ya shigi Shukura yanzu fa ta dawo gidansu da zama,gashi ta daki Latifa watarana ga abinda tayiwa Niima rannan wai wai Yau ya zatayi.Shukura ta kware wajen satar Hanya ta shiga waje ba tare da kowa ya ganta ba ko Bata San hanyar shiga ba sai ta nemo ta da kanta,haka tabi ta barauniyar hanya ta hanyar Garden har ta samu nasarar shiga cikin Palon ba kowa,ta lalubi kitchen ta shige da sauri ta tarkato duk abinda take so,har zata fita ta bude fridge dinsu na kayan sha,ta dauki wani hadin lemo da Niima ta zauna ta Bata lokaci wurin hadashi Sabo da zatayi bako,yayi masifar dadi kuwa cikin wani juck na roba me kyau, Shukura ta bude juck din robar karami dashi ta kurba taji dadi,kawai ta kafa kai ta shanyeshi tas ta Ebo ruwa ta cika juck din ta mayar inda ta dauka, wani flask ta gani hadadde karami an shirya abubuwa kusa dashi a saman tire,sai ta bude a hankali tayi arba da farfesun Hanta da Koda kawai sai ta fara ci taji dadi ta dinga ci tana cewa nasan na wannan yan iskan ne,da Momee tana gidan bazan ci ba tare da na fada mata ba, amma tunda su Niima ne kadan zan rage,dama Shukura Bata ci komai ba,jira take sai tayi sallah sai taci Wanda suka dafa da Umma to yanzu ta fasa cin nasu sai zuwa dare yau Allah ya ciyar da ita nasu Latifa,baifi Guda Shida ta rage hantar ba duk tacinye,romon ma bata barshi ba sai da ta yagi bread a kitchen taci dashi kadan ta maida komai inda yake ta dauki kwanikanta ta kara bi ta barauniyar hanya ta koma Part dinsu,Niima tana daki sai kwalliya take zubawa,taji motsi tunaninta yan aiki ne suke zirga zirga, Latifa ma yau Sunday tana gida tana jin karar kwanika a kitchen amma tayi tunanin Niima ce.
Chapter 20 · 0% Book details