Sashe 23
Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Latifa ta Sanarwa Niima komai da Shukura ke ciki,Niima tace tana da saurin fushi kiyi mata wulakancin da Zata ji Haushi kuyi kokawa kice ta dakeki a gyara ta a schl din.
Latifa yau a dai dai gate ta jira Shukura da Sassafe ,Shukura Bata San da mutum ba tadan bigeta,Latifa taci kwalar Shukura ta fara zagin iyayenta,Shukura an zagar mata Iyaye yau ta gaji da hakuri, tunda tasan su Niima basu da mutunci ta daina shiga sabgarsu kuma kawar Latifa ta zago ta bawa Shukura labarin tuggun da suka hada mata iri iri, Shi yasa Shukura tayi zuciya suka fara kokawa ta zaro biro kawai ta cakawa Latifa a gefen kanta Wajen kawai ya tsille jini ya fara tsartuwa ta kafar,Nan fa schl ta hargitse malamai suka yo kansu tare da cewa a rufe gate kar kowa ya fita,Shukura ta kama katanga ta dane ta haure ta arce sai gida,Latifa kuma akayi asibiti da ita,Niima har taje tana ta kuka,Ahleef ma an fada masa,yana zuwa ya samu ba wata matsala har anyi wa wajen dinki an sallamesu,Gidan ya wuce Direct ya duba Latifa ta tsara masa karya da gaskiya amma yasan Sune da Laifi tunda yaga Latifa a schl din yasan Shukura zasu tsokana dole,Bai ce komai ba ya nufi part din Umma Saudatu kai tsaye yayi Sallama Shukura tana Sallar La'asar, Baba kuwa yana masallaci,Umma a zaune take tana gyara Garin Alkamar da zatayi tuwo.
gaisawa sukayi Umma tace kazo Jin rigimar da kanwarka ta kwaso ko,Murmushi yayi yace ai Bata ji ne Umma,Umma tace ta bani labarin komai gaskiya sune da laifi bari ta idar da Sallah tayi maka bayani 'yata Bata da laifi, suna hira sama sama Shukura ta Idar Umma kuma ta wuce kitchen.
gabansa Shukura ta zauna kasan kafafunsa ta kalleshi fuskarsa ba Rahma,a hankali ta gaisheshi,Me ya hadaku da Latifa dama fada na kaiki ki koya ? Shukura Bata Ce komai ba sai Shirin Kuka ma zatayi da kyar ta kwashe komai ta sanar masa har yanda Niima take bada kudi tana zuga malamai da Latifa,Ahleef ya jinjina lamarin,tace ka yarda dani Yaya bari na nuna ma sheda ka gani ta zare Hijab dinta abin mamaki sai yaga t-shirt dinsa a jikinta ta daura Skert a kasa,Damtsemta ya kalla ko ina shatin bulala,rigar ta janye kadan tare da juya baya tace kalla bayanta rudu rudu shima,Hijab dinta ta maida tace sannan kuma Last nazo gate taci kwalata ya ake so nayi,taya bazan tsille mata kai ba ko yar uban wace wlh Bata Isa ba,na baya ma hakuri nayi Sabo da Dan Adam ba komai za ayi maka ba kace lallai sai ka rama dole kayi hakuri.
Lallai sai yau Ahleef yasan Shukura tana da hankali ashe.
Kamar bazai ce komai ba yace gaskiya idan Saurayinki yaji Bazai ji dadi ba ana Dukar masa mata haka,Shukura ta turo baki cike da Shagwaba dan Allah Yaya ni ka daina ta furta tare da fadawa saman kujera kusa da shi,Kansa ya dauke daya barin tace juyo mu gani Sir, yaki juyowa ta koma can barin, gwiwoyinta suna kasa ta kifa cikinta saman kujera tana so wai dole sai tagani yana dariya ya daina fushi da ita,kansa ya Maida can barin,ta Mike tsaye tana dire diren kafafu wai sai ya tsaya shi kuma yaki yarda,hannayenta tasa biyu ta rike kan kam a saitin fuskarta tace to muga hakoranka,ido ya kafeta dashi tare da bude mata kuwa yana murmushi tace irin na Umma sai kuma taji kunyarsa ta.sakeshi da sauri,Umma ce ta kwala mata kira a kitchen,tana shiga tace haka ake saukar bako ? Tire ta nuna mata kai masa,a gabansa ta ajiye tire tare da zama a kasa kamar ita Zata ci,ta tsiyaya masa lemo ta Mika masa yace bazai sha ba shi ruwa zai sha,Shukura tace ni kuwa ina sha ta shanye lemon, ta bashi ruwa,Abincin kuma jullop Spaghetti ce taji hadi yace ta zuba masa dama yunwa yake ji, Umma fa ta gama yadda Shukura da Ahleef yan uwa ne sai ta bar musu Part din Gaba daya su samu suyi hirar zumunci,Ahleef hankali kwance yake cin abincinsa me dadi sosai,Shukura tana zaune kusa dashi ta zura masa ido kawai birgeta yakeyi a duniya ga komai nasa me kyau ne,shi kuwa yasan tana kallonsa kawai muryarsa taji yace Saurayinki zaki na kalla haka yace Sunday ma zaizo zance gobe kenan fa.
share zancen tayi tace amma ranar Monday kai zaka kaini schl din ? Indai naje ni kadai to kawai ku tanaji makara da likkafani, gaskiya Makarantun Birni basu da Imani a kauye kuwa ni kadai ce me kokari sai abinda nace,amma a nan shegu sai kokari kowa me kokari nice jakar ajinmu fa Yaya, dariya yayi yace jaka kuma ? Tace bakar ma kuwa irin marar mangala din nan, sai dai kayi hakuri nasan ta karshe zanzo yo wannan manyan kwari haka.
murmushinsa ya yi me tsada tare da cewa da bulala zanzo ranar karbar result kuwa,Zama tayi a gabansa kamar me daukan darasi tace kai yan gayu ne a makarantar mu kaga yanda suke tafiya wani dos dos ga daukan wanka,Kema sai ki koya ai,Ina nan zan fara kuwa amma ba a schl ba, yanzu Yaya inda kake me kyau haka ai sai me kyau akwai wata a class Dinmu sunanta Islam kyakyawa ce da zaka yarda da ka aureta kun dace,da ta ganka kazo wajena nace musu yayana ne, Sabo da Sonka fa yanzu take kulani kawata ce sosai har karatu take koya min Sabo da Sonka tayi ta siya min abubuwa,kuma tace gidansu Auren wuri ake musu kaga da tana gama secondary schl sai ka aureta wlh tana sonka tace dan Allah na hadaku,Ina da budurwa fa ni kin Sani karma ki soma a kai kasuwa,karki kuskura ki kara yi min zancen wata Mind ur Business bana sonta ya furta a fusace,Shukura tace Islam din ? Tsaki yaja ya mike tare da cewa Sai Sunday gobe zamu zo da Farhan zasu gaisa da Umma,har zai fita Shukura tace Yaya ga abu kamar ya makalema a hakori kawo na cire ma, Toothpick ta dauko,shi kuma ya zauna,tace mu gani ya bude kyawawan hakoransa tasa tsinken ta cire abin nama tare da cewa kalla ? kamar wani danta tana kula dashi,Zai Mike tace baka taje gashinka da gemunba, dariya yayi kadan yace dama ido kike sa min Ko,ya zaro Cumb dinsa da wani dan mitsitsin turaren gemu na gashi,da gudu ta dauko masa mudubi karami ta karasa masa a fuska yana kallo ya taje gashin da gemun tare da shafa masa turare yana sheki sannan ta matsar da mudubin tace Allah kaika lfy,yace Ameen ya wuce abinsa ba tare da ya kalle ta ba.
Zahra kuma kanwar Hafcy Babansu yace dole su jira har Abba ya dawo daga tafiya amma dole cikin su biyu wacce Ahleef yake so to ita za a hada su aure,Nan Suka fada neman mafita gwara tun yanzu ko wacce ta shigar da kanta gareshi Ko zai zabe ta, Hafcy tayi bincike sai da tasan yanda tayi ta nemi Niima suka zama frnds Sabo da ta hanyar Niima Zata dinga ganin Ahleef,sannan Niima ita kuma ta fada mata Ahleef ba a San asalinsa ba a gidan raino aka daukoshi ba dan Sunna bane, Sharri iri iri Niima ta kullawa Ahleef karshe tace shi yasa ma Bata aureshi ba,Hafcy tabe baki tayi tare da cewa Amma kin tafka asara irin wannan namiji haka to ni ko daga sama ya fado karewar rashin asali nasan Allah ne ya Halicce shi inasonsa,ko dan kudinsa da kyansa ai a so wannan gwarzon gwaraza, kawai ki tallafa min, nima idan kina neman wani abu zan ba abinda bazan miki ba, Niima kuma tasan Hafcy ta fita iya shege a kasar nan shi yasa sai ta yarda domin akwai wani mummunan kudirinta Wanda idan da Hafcy zai tafi dai dai,Ita kuma Hafcy ta sanarwa Mubaraq cewa ya zama ready Niima yanzu kawarta ce damarsa tazo shima,Murna kawai yakeyi ta fadi gasassa.
Zahra kuma bincikenta sai ya nuna mata Shukura yar uwar Ahleef ce da yafi so Sabo da haka idan tana tare da Shukura to zatayi Nasarar samun Ahleef cikin sauki,dama Service Zata fara sai kawai ta nemi a Bata teaching a makarantar su Shukura ta zama Malamarsu kuma tayi nasara an Bata yanzu kawai dole fa sai ta zama kawar Shukura ta gaske.
Islam kuma ganin Shukura kamar taki hadata da Ahleef sai ta koma barin Latifa domin hanata sakewa sannan Latifa ta hada ta da Ahleef.
Maman Su Hafcy akwai son kudi so takeyi Lallai Ahleef ya auri daya cikin yaranta sannan Mubaraq ya auri Niima yanzu itama jira kawai take Momee ta dawo daga tafiya ta koma kawarta sosai ta kwantar da kai yanda Zata ji dadin harka da ita,Shi kuwa Baban su Hafcy tsakani da Allah yake so Ahleef ya auri yarsa daya Sabo da burin yayansa ya cika shi duk abinda matarsa da yaransa ke so to dai dai ne kawai.
Oga Ahleef kuma Yanzu gani yake babu wacce ta Isa ya so ta a duniya,kuma Farhan yake so ya auri Shukura Sabo da yasan zai riketa da Amana,Shukura kuma so take Ahleef ya auri Islam tunda Islam kawarta ce Bata San cewar tuni Islam ta koma wajen Latifa ba.
Asm[7/22, 1:13 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO
11-15
Official
By
AsmaBaffa