← Book details Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 59

Sashe 31

Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Parking sukayi yan biki hankalin kowa ya koma kansu,Part din Momee suka fara zuwa,tana tsakiya cikin yan uwanta suna hira taga Ahleef tare da Shukura,Shukura har kasa ta gaidasu,amma Momee Bata amsa ba sai ma harara da take aikawa Shukura,Ahleef yana gaishe ta sai ta amsa da fara'a.Shukura a ranta tace kyayi kya gama duk abinda Allah yayi to Dan Adam sai kallo, Hannunta Ahleef ya rike suka nufi part din Saudatu,Momee kuma tana can suna gulmar Shukura.
Umma taga Shukura murna a wajenta ba kama hannun yaro ga kuma danta ya auri Shukura.
Fauziyya da kawarta mikewa sukayi tare da yi musu sallama.
Ahleef ma da sauri ya bar part din Sabo da ya kyale frnds nasa su kawai.

Washe gari aka gama komai mutane duk Sun watse komai ya dawo Normal,Abba da kansa yace Shukura ta shirya jibi za a kaita kauyensu za tayi sati biyu sannan dangi su kawota da kansu, baya son Gutsiri tsoma sannan sai da yayiwa Momee nasiha sosai shine tace to a kai Amarya amma duk abinda ya faru kar Wanda ya kawo min kara,kuma ni bazan shiga harkarta ba taje can tayi rayuwarta da Ahleef tunda ita an raina ta bata Isa tayi magana ba sai ace Bata kyauta ba, shi dai Abba bai ce komai ba yace nan da sati biyu za a kai masa Amarya bayan sunje kauyen su Shukura Sun dawo,baki Momee ta tabe tace a dawo lfy ni dai ko kofar gida bazanje ba akan yarinyar nan kodaddiya.

Washe gari da safe Shukura Shirin makaranta tayi abinta,Umma tace ki bari mijinki ya dawo ki tambayeshi idan ya barki sai kije dan Allah Umma ni zan koma kinga fa na dade ban je,Baba ne ya fito ke shirya ki tafi makarantarki,an gama biki me kuma ya rage,idan yazo zance ni nace kije,Cike da kunya Shukura ta karbi kudin Break dinta ta kara gaba,yau Driver tasa ya kaita har ta bude Zata shiga Momee dake saman bene ta buga mata tsawa,karki kuskura ki shigar mana mota,motocin mijinki basa gidan nan,Shukura Bata ce komai ba ta rufe motar ta fita haka a kafa taje ta makara sosai,Latifa ce me taren yan makara,tana ganin Shukura ta saki dariyar mugunta,sai da tayiwa Shukura bulala goma masu zafi sannan tace wato ke ga Amarya harda Lille kika zo,ubanwa zaki birge ? Shukura tace Ubanki,kawai sai fada ya kaure tsakaninsu,Latifa ta ciji Shukura a kunne kamar Zata cireshi,Shukura kuma ta dankara mata cizo a kumatu,teachers da kyar suka Iya raba fadan amma sai suka daurawa Shukura laifi me yasa tazo da Lalle kuma ta makara,ga laifin dukan senior dinta,ruwa suka Bata da wani ruwa daban suka ce ta dirje mata lallan,Kuka tayi sosai har aka tashesu Shukura aiki takeyi da suka Sata,Ahleef bai san ta tafi schl ba yazo suka gaisa da Umma da Baba anan yaji ta tafi schl, abin ya bata masa rai amma ya danne,taya za ace jiya a daura aure washe gari Amarya ta fita ita ba exam ba Bare ace dole,Mota kawai ya fada kamar zai tashi sama haka ya Isa makarantar.

Shukura sai shara da wanke toilet take faman yi tana kuka Sabo da ta gaji likis, idonta yayi jajir,kamar ance ta juyo sai taga motar Ahleef shima ya gane itace,tsintsiyar ta jefar ta nufo wurin Ahleef tana kuka,ba zato ta fada a kirjinsa tana Kuka wiwi hade shagwaba tace Yaya ta kara fashe masa da uka, hannuta ya kalla sai yaga lallen daya fiso har ya lalace,what ? Ya furta kana yace me ya samu lallen?labari ta bashi sannan tace sai da na fada maka ni bana son makarantar amma kaki yarda dani, Ahleef yaji haushin abinda aka yiwa Shukura,Office din pc ya nufa ya dinga masifa sannan yace schl zai canja mata daga yau.Shukura Murna kawai takeyi da sauri ta yi wurin motarsa yazo zai bude ya shiga,da sauri ta zagaya tare da bude masa tana cikin nishadi za a canja mata schl, murmushi ya saki wanda ke rikitawa yan mata tunani,Shukura tace sai ni matar me kudi wlh wa ya isa yaja Da ni ko lecturer ne dan ubansa,wlh Badan yar gidanku bace sai nayi sharia da ita a kotun koli,kotin daga ita sai Allah ya Isa.

Dariya ta kama Ahleef ,kai gani kake wasa nakeyi hmm,na tuna ma Yaya ana bina kudin lalle da wasu kaya dana siya,da hannu ya nuna mata inda yake ajiye kudi ta dauka ta vile 30k ta maida sauran, idan basu isheki ba kara,sun Isheni Allah ya kara budi na gode dan Umma.

Ya fara driving ba tare da ya kalleta ba yace mene ne aure Shukura ? Yanzu ka rasa tambayar da zaka yi min sai ta aure,aure waye bai sanshi ba bare ni da nake katotuwa, ba surutu nace kiyi min ba,tambayarki nayi mene aure ? Shukura ta kalli saman cikin motar ta tafi dogon tunani sannan tace Kaga idan kayi aurenka to shike nan kayi aure,sai mace ta dinga girkinta me dadin tsiya Tana cinyewa,sai kaga tayi kiba da haske,sannan kuma idan kayi aure Inna tace sai a dinga tararrayar mijin,ni yanzu yaya taya zan iya tarairayarka kayi girma da yawa sai dai na goyaka,Gaskiya ne Amarya cewar Ahleef,sai kuma me ? Uhmm ayi wanka da kwalliya,Ahleef yayi dariya tare da cewa zero baki ci ba tunda baki San mene aure,Allah na fada dai dai kaine dae baka Sani ba,tunda haka kace to bari na sake Sabo, ai dai ance mace ta dinga....sai ta rufe idonta wai kunya a hankali tace tana yiwa mijinta wanka tana silleshi da sabulu,haka aka koya mana a schl, yanda Shukura ke fada masa ya gane Bata ma san mene aure ba,a fili yace ai kuwa kin cinye Gaba daya,murmushi ta saki tare da cewa dama na fada maka ina ja,kwakwalwata na ja,babban kai ne dani,Dariyar da bai shirya ba ya shiga yi,baki ta turo gaba tana Shagwaba Haba Yaya dan Allah shike nan na daina fadama ai,Sorry na daina fada min inji.Shuru tayi wai tayi fushi,saida ya biya ta gidansu Fauziyya aka basu kudin data ranta sannan suka wuce har Maman Fauziyya ya gaisar tare da bawa Fauziyya 20k kauta.

Hafcy tun tana bin Niima har ta gano da kanta gwara ta nemi hanya da kanta,ita kuma Zahra tunda ta samu labarin da Shukura aka daura ta rantse Baza ta kara kula Shukura ba har abada. Malam Hari da Jamilu Bayan anyi musu sha tara ta arziki suka koma kauyensu, Shukura ta basu tabbacin Zata zo watara. Umma kuwa ganin Shukura Bata da gata sai ta fara gyara Shukura da tsumi masu inganci da kuma yanda Zata kula da mijinta sannan kullum Shukura ma tana zuwa wurin gyaran fata,Ahleef kullum sai ya shiga wajen Umma wai lafiyarsu yake dubawa.

4:30pm ya dawo daga Office a gurguje ya shirya Momee tana palo tare da Niima ya wuce da sauri yana tafiya yana sannu da hutawa Momee,tabe baki Momee tayi tare da cewa ga sallamamme an gama shanyeshi wlh da Abba baya kasar nan korarsu zanyi baki daya kawai ka sha wahalar rainon yaro sai yanzu za a nuna min iko,Niima tace ki bari idan Abban yayi tafiya Ahleef ma Sai ki kirkiri kasar da zaki turashi kafin ya dawo an gama komai.
Harara Momee ta bugawa Niima tare da cewa aike kika jawo tunda kika fasa aurenshi,na rike yaro a hannuna za a nuna min iko a kansa.

Ahleef direct part din Umma ya nufa cikin tafiyarsa me matukar birgewa,Door Bell ya danna Umma ce ta bude taga danta wai ita kunyarsa take ji, shi kuma Ahleef kunyarta yake ji lokacin da take ce masa Alhaji tana gaidashi ashe uwarsa ce guda,,Umma ce ta katse masa tunani da cewa shigo mana,cikin Ladabi ya durkusa tare da gaisheta,ta amsa da sakin Fuska sannan ta nuna masa bedroom din da Shukura ke ciki,ya nufi dakin ya kwankwasa Shuru kawai ya murda Handle din kwance ya ganta saman Bed tana sheka baccinta hankali kwance,sanye take cikin wata yar guntuwar Vest iya rabin cinyarta dark blue tayi mugun kyau cinyoyin kukuta lukuta gasu farare kar suna sheki,bai taba ganin Shukura haka ba.a hankali ta bude idonta fes a kansa yana tsaye sai kare mata kallo yakeyi,mikewa tayi ta zauna Gefen bed kafafunta suna lilo a kasa,Hannunta ta daura saman bed gefenta ta dan bubbuga kadan wai ya zauna,ita Shukura fa Bata San ana wani abu ba idan anyi aure ko tsoro Bata ji,sabo da bata da frnds tun asali, gefenta ya zauna.yana shakar kamshinta, itama haka,sai Mutsu mutsu takeyi kunya ta gama rufeta yana kallonta da guntayen kaya a jikinta.

Tana so ta mike domin dakko zani ta kare jikinta amma tana kunya ya kalle mata Mazaune subu subu wanda suke Masu matukar kyau kamar an zana mata su, shi kuma gogan ya ganeta sai gyarawa takeyi ta duburbuce amma sai ma kwanciya yayi abinsa saman Bed, Shuru tayi masa sai wasa take da yatsunta, shi dai kallonta yakeyi kawai,Kamar Baza tayi magana ba sai kuma tace bari naje na dawo,Ok kawai yace da sauri ta dakko Hijab kato har kasa ta saka, a ransa yace aiki ya sameki, 5mt ta dawa dauke da katon tire na abinci,ta jikin kofar tace dan bude min pls, yana budewa ya ganta da tire kato ta shugo a ransa yaji dadi kamar tasan yunwa yake ji sosai,so yake su hada ido amma taki Yarda,zuba masa tayi komai sannan tace gashi,ta bashi mamaki bai San tana da hankali haka ba sai yau abincinsa ya shiga ci ita kuma ta shiga wanka abinta.
Chapter 31 · 0% Book details