Sashe 38
Jin Dadi Sabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ahleef ne ya Kira Momee yace ya gama komai da Company din nasu dake kasar Japan gida zai dawo gobe, Momee cikin fada tace idan baka son aikin Nan Dana ke saka Ahleef ka fada min,gaba daya ka damu ka dawo Nigeria uban me zakayi a kasar ga aiki a Nan kaca kaca,Dan kaga bani da manyan Yara irinka shine kake min Haka, Allah sarki Ahleef baya son yaga Momee tayi fushi dashi ko ace shi ya Bata mata Rai sai kawai ya rude ya shiga Bata hakuri Yana lallaba ta sabo da halaccin rikeshi ta raineshi fiye da yaranta data haifa, Afwan Momeena what Next kuma? Wasu Kaya zaka je north Korea ka turo minsu zan bude shagon butique, da mamaki yace Momee sai na kwashe more than 2mnth a garin kin sani kuma yanzu akwai nauyi da hakkin Shukura a kaina, Salati Momee ta saki yanzu Shukura ta fini?akanta kake so dama ka dawo?
Momee Bata San Umma ta sanarwa Ahleef komai ba sai tace yarinyar kana tafiya ta tattara kayanta ta shiga duniya ba a San inda take ba,ai Abba yace kin fada Masa kin maidata kauyensu kafin na dawo,Momee tace Kai da kanta ta gudu kawai fada Masa nayi Dan hankalinsa ya kwanta,Kai wai me zaka yi da wannan yarinyar ne?Ahleef tuni ya gane Momee Bata da gaskiya ransa yayi Mummu Nan baci daba Dan kar tace ya hada ta fada da Abba ba da sai ya sanarwa Abba komai,a fili yace Momee wlh I do really love my wife,Dan Allah na dawo ko 2wks nayi sai na koma nayi Miki aikin? Momee tace Sam baka Isa ba ta datse Kiran ma Baki daya.
Baba da Umma dai suna can hankalinsu kwance Farhan ke musu komai da Umarnin Ahleef.
Shukura yau ta kwashe wata daya kenan a kauyensu kullum cikin sa Rai take zata ga Ahleef yazo Amma Shuru ,Nan kuma Megari ya samu Dangin Shukura ciki harda Kawu da Yafendo zai auri Shukura karya take Bata da wani Miji a birni,Kawu haushi ya kamashi ganinsa idan Shukura ta auri Megari taci gaba kaf garin ta ciri tuta,shi ga yarsa zata auri talaka Amma Shukura me gari Guda me fada aji me mulki, sai yace Kai Megari da girmanka da hankalinka zaka auri Karuwa? Megari yace ko a gidan Karuwai take na ganta zan aure ta Haka,Yafendo kuwa Murna takeyi ai Shukura ta ci gaba Megari Guda, Kawu yace to ya zakayi da yaron cikinta?Megari yace karya ce ba wani ciki,tana da ciki zaka ganta haka?kawai maganar mutam kauyece, Yafendo tace Bata da wani ciki Shukura fa shirmenta kawai takeyi sabo da kuruciya ko rannan tayi alada.
Megari ya washe hakoransa na cin goro.
Bayan sati biyu tuni dangi sun Gama komai za a daurawa Shukura aure da megari, zance ya baza gari,ance kar a fada mata sai an daura ta ji daga baya, Ana saura kwana Uku a daura aure Shukura taje gidan Aishalle,Aishalle tace ke kuma da kike auren me kyau a birni ya naji za a daura Miki aure da Megari,Shukura tace aure kuma? Ban gane ba kefa kin cika hauka,Dariya Aishalle tayi tace to wlh boye Miki akeyi kaf garin da Yan uwanki sun sani Amma ance kar a fada miki yau saura kwana Uku ki zama Amaryar me gari,gashi can Talliya Matarsa tayi yaji ta bar gidan ma,idan Baki yarda ki tambaya kiji,Yafendo tasan komai,har an Kai kudin aure wajen Kawu,idan kin San kina da auren wani wlh ki San abinyi tun wuri.
Ai Shukura ko Gama ji batayi ba ta fito sai gida wajen Yafendo ta fado da gudu tana Hawaye tace Yafendo me nake ji wai za ayi min aure da Megari? Yafendo tace yo tsayawa zamuyi mu kalleki ko me,kinzo sai karya kike Mijinki zaizo Yana Ina?Baki da sheda,Wanda suka kawoki sunce karuwanci kike Zaki likawa wani Dan ya aureki Kinga sun tabbatar Mana Baki da aure kuma aure kamar anyi.
Ga Dubu goma Megari ya kawo sune kudin lefenki, da Sauri Shukura ta karbi Kudin lefen dubu goma,har Yafendo tana dariya tunaninta ta yarda da auren,Sai taga Shukura ta tattara kayanta a akwatuna tas ta fito ta kalli Yafendo tace wannan dubu goman ki fadawa Megari na ranceta zanzo tare da Mijina na biyashi kudin Lefensa,da sadaki ya kawo bazan ranta ba Amma tunda kudin Lefe ne na ranta na bar muku garinku wlh Akan na auri Megari gwara na koma ga Allah banyi aure ba.
Tasa Kai ta fice sanye da hijab tana Jan akwatunanta tana tunanin Ina zata je inda Ahleef zai San tana nan.
Tana cikin tafiya sai ga Megari a saman wani tsurar machine dinsa da ciyawar tumaki a bayansa ya dawo daga gona,kallo daya ya gane barin gari zatayi,ai da sauri yaci uban birki ya dirgo daga Machine ya rike hannun Shukura Kam,tunawa da tayi tana da aure wani bakin ciki ya kamata ta dage iya karfinta ta warware Megari da Mari,idonta cike da kwalla tace Ina da igiyar wani a kaina baku da hankali ko jahilci na damunku.
Megari yaja baya dafe da kumatu Yana mamaki,tace kaja mutuncinka Ina ganin mutuncinka,ta ja kayanta taci gaba da tafiya abinta ta bar Megari da jimami duk girmansa da mutuncinsa ga mulki babu Wanda ya taba ko Masa magana marar dadi Amma wannan so ya jawo Masa yasha Mari,Allah ya taimakeshi ba a gaban talakawansa bane da yaji kunya.
Shukura Machine ta hau Bata tsaya ko Ina ba sai wani Kauye me Dan Nisa gaban kauyensu,Suma Yan Fulani ne wai Dan kar tayi Nisa da garinsu sabo da zuwan Ahleef.
Rashin sani Shi kuma Ahleef yace Umma ta bawa Farhan Address din kauyen su Shukura su Shirya tare da Baba da Umma Farhan ya kaisu garin su dauko Masa Matarsa a dawo da ita kafin ya dawo, washe gari da Sassafe suka dauki wanka musamman Farhan daya ke ji da kansa,Umma kuwa kowa ya ganta yasan Balarabiyace Tasha lace tayi Masifar kyau gashi dama tayi kiba haskenta ya Kara fitowa,Baba ma yasha Shadda me tsada yayi kyau,Farhan a wata arniyar motarsa yazo driver na jansa,Umma suka shiga suma,Sai wata dalleliyar mota da escort din Ahleef a motoci biyu suna binsu a baya suka dau hanyar Jos.
Sunje garin Jos suka tsaya Suka ci abinci da sallah sannan suka dauki Hanyar Kauyen su Shukura,sun Sha tafiya me nisa kafin sannan suka Isa garin,tun a farkon garin Yara ke bin motar suna motoci ne motocine,sulluwa ce wlh har guda uku,Farhan ne ya sauke Glass yace gidan su Shukura yake nema,Suka ce Shukura Maji dadi ai jiya ta gudu ta bar gari Akan za a ayi Mata aure da Megari,Farhan gabansa ya Fadi yace to a wanne gida ta zauna? suka nuna musu gidan Yafendo.
Bayan sunyi parking Nan fa gari ya dauka Mijin Shukura bature yazo daga birni Ashe gaskiya Shukura ta fada,Mata har da masu leke ta katanga kallon Mijin Shukura,kafin kace me kofar gidan Yafendo ya cika dam da Yara da manya maza da Mata harda matan aure za aga Ahleef.
Farhan Yana fitowa kamshi ya turare wajen,Samari suka fara Kaine Ahleef Mijin Shukura? Farhan yayi Murmushi yace Ashe kun San Ahleef kuma? Nan suka dinga bashi labarin Ahleef yanda Shukura ta fada musu har dinkinsa da ake yayi a garin,Farhan yasha mamaki yau,yace bani bane Ahleef ni abokinsa ne,Ahleef Yana America,zuwa mukayi muga Shukura mu dauketa wannan sune iyayen Ahleef.
Yafendo ce tace babbar magana Ashe yarinyar da gaskiyarta to ku shugo ayi maganar a nutse,Yafendo tayi musu saukar mutunci sannan ta Kira manya cikin dangin uban Shukura da kuma manya cikin na Inna aka zauna,bayan an gaisa da addua,Baba ya zube musu zance tiryan tiryan ya Basu labari haka Umma ma ta bada Wanda Baba ya manta,
Yafendo tace to Wanda suka kawo Shukura kuma su waye? Nan Umma ta Basu tarihinsu,Dana Ahleef harda na Momee ta Basu kaf sannan tace wannan kuma Dan sabani aka samu shi yasa ta dawo da Shukura har ta furta munana Nan kalamai a kanta.
Nan fa kowa ya shiga zare Ido kunya ta kamashi yanda suka dinga wulakanta Shukura,Suma sai suka Basu labari yanda Shukura Tasha wahala a garin kowa ya gujeta,da auren da za ayi mata da Megari har ta gudu ta bar garin yanzu ba a San Ina take ba,Baba da Farhan tausayin Shukura ya kamasu,Umma har da kuka tace shi yasa ake son bincike Akan abu,gaskiya baku kyauta ba,Shukura yarinyar kirki ce wlh me yasa kuka kasa ganewa kuna Yan uwanta, Farhan waje ya fita can gefe ya Kira Ahleef, ring daya Ahleef ya daga tare da cewa dalla Malam bawa matata waya naji muryarta na lallasheta, Farhan kansa Ahleef ya bashi tausayin Amma Haka ya daure ya bashi labarin komai.
Son Shukura ne sabo ya Kara sukan Ahleef hawayen tausayinta ya zubo Masa duk a kan aurensa Shukura ta Sha wahala haka, Ahleef yace Farhan Amma Allah ya tsinewa Megari shi ya cuceni ya jawo min masifa matata ta bace wlh idan na dawo kasar Nan ba a ganta ba wlh sai yayi prison,Farhan Yana ta bashi hakuri Yana Lallabashi tare da kwantar Masa da hankali.
Umma tace ku tashi mu tafi to me zamu jira,Farhan yace Addua zamu ci gaba da Yi Ana bincikenta Allah ya bayyana Mana ita.
Farhan ya yiwa mutanen garin kyauta da yawan gaske sai murna akeyi har suka musu sallama suka bar garin, Koda suka koma gida tuni Ahleef ya bada sanarwa a kafafen gidan radio da tv anyi ko Ina idan Shukura taji ko wani da ya santa a sanar Mata ta koma Abuja da Address din gidan su Umma Amma Shuru tana can wani Kauye Wanda yafi nasu ma harkar shanu kawai akeyi na Kiwo a garin.